Na Baki Rayuwa Ta, Complete Hausa Novel.

Adnan ya lalibo lambar Affan ya kira, lokacin Affan yana kan duba wayarshi yana kallon hoton Afnan wanda ya zame mishi kamar ibada, sai yaga kiran Adnan ya shigo cikin wayarshi.
Cikin sauri Affan ya d’aga, yasan zuwa yanzu dama Adnan ya iso gida, addu’a ya farayi a cikin zuciyarshi Allah yasa be fad’awa Inna komai ba.
“Assalamu alaikum, Adnan har ka k’araso kenan?” abinda Affan ya fara cewa kenan.
Adnan yace “eh wallahi gani ga Inna muna shan hira tunda kai ka gudu kak’i jirana in k’araso mu tafi tare in rakaka.”
Sai a lokacin Affan ya numfasa da jin haka, yasan Adnan be fad’awa Inna komai ba, Affan yace kayi hak’uri Adnan tafiyarce tazo a gaggauce kuma ba shiri shiyasa, ina Innar tamu take bani ita mu gaisa,” Adnan yace “ok gata.”
Inna tana karb’ar waya tace “Affan yanzu kuna daidai inane?”
Affan yace “muna hanya Inna kinsan daga zaria zuwa legos akwai nisa sosai.”
Ta k’ara yi mishi addu’ar sauka lafiya, sannan ta mik’awa Adnan, Adnan yace “to mutanen k’asa sai munyi waya anjima,” nan dai sukai sallama.
Bayan sun gama waya da Affan Adnan ya kalli Inna yace “Inna ga tsarabarku nan, harda kayan abinci ki duba abinda babu sai inje in siyo,” sannan ya zaro kud’i ‘yan dubu dubu ya mik’a mata yace tai cefane.
Inna ta kalli uba uban kayan da ya lafto musu, ta dawo da kallonta kanshi tace “duk wannan namu ne, to Allah ya saka da alkhairi, Allah ya shi albarka ya k’ara muku bud’i, ka fara aiki kenan?”
Adnan yace “eh Inna na samu aiki acan shinema ya rik’eni ban dawo da wuri ba, kuma bazan fi sati d’aya ba zan koma.”
Inna tace “to Allah ya taimaka ya sawa aikin albarka, a kuma ji tsoron Allah, a rik’e gaskiya da amana, a kuma kama kai a duk inda ake.”
Adnan yace “insha Allah Inna nagode sosai da addu’arki da kuma nasihohinki gareni.
Suna cikin hira k’annen Affan suka shigo cikin gidan dukkansu d’auke da sallama, Adnan ya saki baki yana kallonsu musamman ma Yasmeen yanda yaga ta girma ta zama budurwa, kallon Inna yayi yace “Inna haka yaran nan suka girma?” Inna tai dariya, sannan tace “kai kuwa banda abinka yaushe rabonka da garin nan kafa dad’e baka nan,” Adnan yace “masha Allah.”
Suna k’arasowa suka zube suka gaisheshi, a tak’aice dai Adnan ba shi yabar gidan nan ba sai bayan isha ya cika cikinshi da abincin Inna sannan yai musu sallama akan gobe insha Allah zai dawo.
B’angaren Affan kuwa tafiya suke ba k’ak’k’autawa, kamar da wasa yace bari ya sake gwada lambar Afnan ko zata shiga cikin ikon Allah kuwa yaji tana ringing.
Itama Afnan kunna wayarta kenan taga kiran Affan ya shigo, “Allah sarki masoyi,” abinda ta furta kenan a hankali, da yake tana cikin mutane sai ta tashi tsam ta shige cikin d’akinta, sedai kafin ta d’aga kiran ya katse.
Tana k’ok’arin kiranshi sai wani kiran nashi ya sake shigowa, Afnan ta d’aga ta kara a kunne sannan tace “hello rayuwata,” “na’am mahad’inta,” cikin tsananin farin ciki Affan ya amsa, fuskarshi d’auke da murmushi.
Afnan tace “nasha wuya na rashinka a tare dani kwana biyun nan, lallai na yarda ka zama komai nawa, sai ta marairaice kamar zatai kuka ta cigaba da cewa *na baka rayuwata* dan Allah kar ka sake kabar cikinta.”
“Affan yai murmushi harda dariya saboda tsabar jin dad’in kalamanta, yace “karki damu babu abinda zai rabamu har abada insha Allah, gani nan ma akan hanyar zuwa wajenki domin inga mahaifinki saboda tabbatar da tabbatuwar kasancewarmu tare har abada wato mu kasance ma’aurata.”
Afnan tai dariya sannan tace “kana hanya, to Allah ya kawoka lafiya,” shima dariyar yayi, saboda ga dukkan alamu yanda ta nuna sam bata yarda da gaske yana hanya ba, tasha kawai yana yi mata wasa ne, a haka sukai sallama.
Dare yayi dolensu Affan suka tsaya suka kwana, shima bayaso suyi shigar dare, dan besan inda zai nufa ba.
Sak’o ya turawa Afnan akan tahau whatsapp yana son magana da ita.
Lokacin Afnan tayi shirin kwanciya harma ta kwanta a daidai lokacin sak’onshi ya shigo cikin wayarta, murmushi tayi sannan ta bud’e data.
*AFNAN* _”Aminci a gareka ya masoyin k’warai.”_
*AFFAN* _”Aminci a gareki mamallakiyar zuciyata, yakike? kin wahalar da zuciyata da kewarki, damuwar rashinki ta haifar min da gagarumar matsala, dan haka dolene in hukuntaki.”_
*AFNAN* _”Ayya gwanina kayi hak’uri ka yafemin, nima kasan bana k’aunar yin nesa dakai, kaga kuwa duk abinda yasa nai nesa dakai babban abune, dan haka kaimin afuwa kaji.”_
*AFFAN* _”Bakomai gwanata, na dad’e da yafe miki duk laifin da kikaimin harma da wanda zakiymin a gaba, kuma har abada bazan daina yi miki godiya akan k’aunata da kikeyi ba duk da kasancewata talaka, ina godiya.”_
*AFNAN* _”Ka daina yimin godiya fa, shikenan kawai dan kana talaka sai in gujeka sai kace kai ba mutum bane, to bari kaji ba talauci ke gareka ba, koda ace cutar k’anjamau kakeda ita wallahi bazan tab’a iya guje maka ba, balle dan kawai kana talaka wanda nasan wata rana Allah zai azurtaka tunda babu abinda yake dauwama da arzik’in da talaucin, dan haka ni banama so kana irin wannan maganar, in ina sonka kawai ina sonka ko a ya kake babu abinda zai canzamin ra’ayina a kanka.”_
*AFFAN* _”Afuwan Afnan matar Affan.”_
Dariya tayi, suka cigaba da hirarsu gwanin ban sha’awa, kuma be sake fad’a mata cewa yana hanyar zuwa gidansu ba tunda ya fad’a mata bata yarda ba.
Washe gari saida su Affan suka nemi abin kari suka karya sannan suka cigaba da tafiya.
Wajen k’arfe sha biyu suka iso cikin garin legos, Affan sai farin ciki yakeji had’e da kalle kallen garin har suka k’araso inda zasu sauka.
Wannan saurayin shi ya tsayar musu da adaidaita sahu suka shiga yaja suka tafi.
Sun fara tafiya wannan saurayin ya kalli Affan yace “sannu da zama, kasha hanya yau, ya kamata ka sanar dasu ka k’araso dan mun kusa zuwa.”
Affan yai murmushi sannan yace “yauwa sannunmu, gajiyar tamuce duka.
Affan ya zaro wayarshi daga cikin aljihu ya dokawa gimbiyarsa kira, tana d’agawa yace “gimbiyata gani a unguwarku,” dariya Afnan ta sake yi, sannan tace “to sai ka k’araso,” Affan yace hayaniyar me nakeji haka kamar kuna shagalin biki?” ji yayi anzo ana mata magana akan ta fito za’a fara gudanar da shagalin bata wajen, ta basu amsa da to gata nan, Afnan tace “Affan yi hak’uri dan Allah ina zuwa zan kiraka,” bata jira taji me zaice ba kawai ta yanke Lateefa ta jata da sauri suka fita cikin harabar gidan nasu inda ake gudanar da shagalin.
Har k’ofar gidan suka kawo Affan, ya biya kud’in tare da yiwa saurayin nan godiya me yawa sosai, kuma saida sukayi musayar lamba domin gaisawa, suna wucewa Affan ya d’auki jakarshi ya fara kutsawa cikin taron sai gashi a gaba gaba, Afnan ce a tsakiyar fili ita da k’awayenta harda Lateefa sunata cashewa suna dariya, kowannensu fuskarshi d’auke da fara’a.
An saka Afnan a tsakiya k’awayenta suna gefenta suna takawa, Afnan tayi masifaffen kyau sai kace wata amarya, tasha ado ga zanen lalle da akai mata kai tayi kyau dai sosai.
Affan sai kallonta yakeyi zuciyarshi tana bugawa da sauri, ga wani irin k’aunarta da yakeji tana k’ara ratsa zuciyarshi, hango wayarta da yayi a hannunta yasa ya zaro tashi a aljihu ya kira lambarta, yana kira ta d’aga yace “Afnan wallahi ina masifar sonki, in na rasaki mutuwa zanyi, ashe kinfi kyau ma a fili, d’ago fuskarki ki kalli gabanki kiga masoyinki ganinan a gabanki ina kallonki.”