HAUSA NOVELNancy Yar Karya

Nancy Yar Karya

_Labari mai d’auke dasa nishad’i tare da fad’a karwa_

*~ALKALAMIN DA BAYA RUBUTA SHIRME~*✍️.

_________________________

*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

 

Page 37_38

,,,,,,,,,Zaune take ta zuba uban tagumi ,oh na shiga uku ni Nancy kayan makeup d’ina sun k’are gashi bani da kud’i ,nakwashe duka kud’in ‘nayimana siyayyar kayan abinci ,jitayi duniyar tayi mata zafi sosai ,shawarar ta kalaci man shafawarta da ragowar powder ta shafa ta fice tunda tanada kud’in hawa mota ,kawai ta nufi kasuwa , tofa wanka tayi tazo tafara tsara kwaliya ,ragowar turarenta mai gigita samari tasa , ta fito da wata tsadaddiyar shadda pink mayafinta fari hakama takalminta ,inka ganta zaka rantse yar wani mai kud’inne ,fitowa tayi da gabjejiyar wayar da Khalil ya siya mata ,tana gogeta ,cewa umma tai natafi zani gidan su wata yar ajinmu lokacin ina gidan su hajiya, Umma ce tace ”kidai rik’e mutuncin ki Allah ya dawo dake lafiya ,amen umma Nancy tace lokacin da ta sanya farin glass a fuskarta .”

Tana zuwa bakin titi babu napep hakan yasata duba agogon hannunta tana tsaki ,wata tsaleliyar mota ce ta tsaya ‘a gabanta ,matsawa tayi tana yatsina fuska ,zuge glass d’in motar akayi tare da cewa ”dafatan gimbiya kuma sarauniyar mata ta tashi lpy ,juyowar da Nancy zatayi taga ko waye yake magana murya ‘a mak’ale oho .

Tunda Suhailt ta sauka Momy tafara yimata gyara da kayan gyran jiki ,kama daga fata har gashin kai dakuma gyaran magunguna acewarta wai sotakeyi taga yarinyar tata tafi shauran mata lol,
Tun Suhailat na shan ‘na marmari har tazo ta dena kasancewar maganin ya had’u sosai ,momy ta kashe kud’i.

Abu sai matsowa yakeyi yau bikin Khalil da Suhailat saura kwana biyar hidima ‘akeyi ta kowane 6angare dady da momy basuda lokaci sbda hidin dimu sunyi musu yawa ,y’an uwan momy harsun fara zuwa kasancewar bikin na y’a ‘yan manya ne , wanki lafiyayyen gida dady ‘yabashi ,gidan ya tsaru komai na ciki tsarre ne baki bazai iya fad’an kyaun gidan ba .

Yau ta kama Monday yau akayi Indian day ,washe gari talata Suhailat takira Khalil akan cewar yakamata yazo fa akwai wani wasa da k’awayenta suka shirya mata ,Humaid da ‘abubuwa suka taru suka cunkushe masa guri d’aya yace ”waike wacce irin marar lissafi ce wlhi kika sake kirana zanyi maganinki ,da haka Suhailat ta kashe waya haka sukayita gudanar da ‘al’adunsu babu ango .”

Yau alhamis yaune dady ‘ya dawo da furniture’s d’in Suhailat wow abin sai wanda yagani bama ‘a London aka siyo ba wata k’asar aka tafi kashe kud’i sukeyi kamar basu san zafinsu ba ‘a cewar momyn Suhailat y’a d’aya tilo ce dole a tsara mata komai na rayuwa .”

Yau juma’a da fitowar Suhailat wata k’warta mai suna Nussy tazo ,momy take cemata bana hanaki fitowa ba ,kushiga ciki ,da shigarsu suka fara hira sosai kuma hirar dukta inda za’a maida Khalil masoyi akeyi Nussy da ‘a shekaru batafi 23 ba amma batayi aure ba ‘sai dai shu’umanci irin nata sai _ita, wani turare ta ciro cikin wandon ta tace ”kinga gudunmawata nan banason tarkace wlhi kikayi wasa da tirarennan to Humaid zai ‘iya ku6ce miki ,matsowa Suhailat tayi ta ruk’o Hanun Nussy tace ”nifa indai Khalil zai zamo nawa ni kad’ai to ina murna ,dariya Nussy tasa tace ”bakida dama gaskiya kin shige da yawa , to yazanyi da turaren ,cewar Suhailat ,Nussy ce ta kashe mata ido tace ”inason kibani tukwaici ,zaro ido Suhailat tayi sai dai wani abu da mai karatu bai sani ba ,shine duk wanda Nussy tabawa umarni to kwarjinin ta shikesa ba’ayi mata musu ,kasancewar bokaye kuma yare kala kala take amfani dasu yanzu haka ma bata gaban iyayenta a makaranta suka had’u da Suhailat, gaskiya Suhailat bata ta6a aikata wani iskanci ko akasin hakan ba itadai barta da rashin kunya.

To My Nussy tukwaicin mai zanbaki ?✍️.

Nasan kun matsu kuji ko ?dafarko dai kunason jin dawa Nancy ta had’u?”

Na biyu kuma wane tukwaici Suhailat zata bawa Nussy ?”.

Karku damu muje zuwa innaga sharhi to anjima zan sambad’o muku wani inko bangani ba sai gobe ko jibi love you all????.

[31/01, 6:33 pm] Mom Islam ce????: ????????NANCY YAR KARYA????????.

_Labari mai d’auke dasa nishad’i tare da fad’a karwa_
_________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Page 39_40

,,,,,,,,,Sanye yake cikin bak’in yadi mai laushi ga shek’i ,fuskar sa na sanye da bak’in glass wanda ya rufe kyawa wan idanunsa,gyara tsayuwar ta tayi tace ”Khalil !!! lumshe murmishi yai tare da ”cewa mai kyau kin manta dani ko?” hawayen da take k’ok’arin tarewa ne sukayi nasarar zubo mata ,ya ilahi yafad’a lokacin da ya bud’e murfin motar yana shirin fitowa ,ji yakeyi kamar ya rungume ta ko zuciyar sa zata yimai dad’i ,juya masa baya tayi tana share hawayen fuskar ta .”

Takowa yakeyi cikin tak’ama ya iso gurin ta ya sunkuceta tana k’ok’arin sauka ‘amma babu hali sbda Khalil d’in ba rago bane , yasata a mota key yai wa motar suka bar wajen ,sunyi tafiya mai nisa babu mai magana sai sanyin AC dake kad’awa had’e da had’a d’en turare mai k’amshi , guraren da Khalil ke shiga tunda tazo Abuja bata ta6a shiga ba ganin yana shirin shiga wani katafaren guri mai kamada Zoo yasata ware ido bata daiyi mgna ba ,da shigarsu gurin aka Khalil yaciro kud’i yabada ‘aka basu wani kati ,yana tafe tana binsa ‘a baya ,mutane ta hango iri _iri har dasu turawa da sauransu kowa kagani a gurin tafe take da saurayin ta wasu na d’aukar hoto wasu kuma na wasa da flowers wasu kuma na gurin cin abinci , wani guri taga Khalil ya shige yana yimata nuni da tayi sauri, da shigarsu ta hango kayan ciye ciye wanda tasani da wanda bata sani ba ,Khalil ne yace ”zoki za6i abinda ranki keso ,shiru tayi tana kallon shi ,k’arar wayar shi ce yasata kuma maida hankali gurin kallon shi ,tsaki yayi yace ”ke wace irin dak’i k’iya ce menace miki jiya don’t worry zanbaki mamaki ba lefinki bane ,ya kashe wayar ,kuka Nancy tafara ,ta fice a guje tana kuka ,Khalil ne yasami guri ya zauna yana cewa wlhi Suhailat karkiyi tunanin farinciki zaki tarar a gidana lol.”

Wasu y’an mata ta hango sanye suke da dogayen wanduna na jeans dasuka kama jikinsu ,d’ayar ce tace ”dan Allah sis zoki rakani gurin wacan beautiful d’in inason muzama k’awaye ,tashi sukayi suka nufi gurin da Nancy ke zaune tana kuka tana ganin mutane sun doso gurin ta tafara share hawayen fuskar ta, sallama sukayi ,bayan ta amsa musu ne suka fara janta da hira kasancewar sunga bata cikin walwala , tad’an sake dasu sosi d’ayar ce tace ”ni sunana Jamila ita kuma lil sis sunanta Karima ,masha Allah Nancy tace ”tana k’are musu kallo sbda tasan dukkansu ba ‘ajinta bane jikinsu ma ya nuna daga inda suka fito ,Karima ce tace ”to baki fad’a mana sunanki ba ,murmishi Nancy tayi tace ”sunana Nancy nice name Karima tace lokacin da take ruk’o hannun Nancy ,amma Nancy naga kamar kina cikin damuwa ko ,eh tace ”can k’asan zuciyarta batason susan halinda take ciki ,amma lokaci guda taji ta yarda dasu ,kwashe labrin soyyayar su da Khalil tayi dakuma labarin Suhailat tabasu babu abinda ta 6oye musu , murmishi sukayi suna cewa to yanz ai kece da laifi because dayace dadynsa ya….hango Khalil tayi yana shirin tahowa gurinsu …..✍️.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button