Nancy Yar Karya

Hajiyan ‘taci gaba da cewa , lokacin da mahaifiyar mijina ta matsamin kome mijina yayi min sekiga tana yimai fad’a ‘akan cewar wai yayi yawa nikuma mijina maison ganin ya faranta min ne hhh kunsan maiya faru? sauran mutanen ne suka ce a’a , Hajiya tacigaba da cewa sawa nayi shed’anin boka ya kasheta , a firgice momyn Suhailat ta kallete tace ”ina gaskiya bazan iya sawa a kashe mutum ba ,dariya sauran mutanen gurin suka sa suka fara kowa na fad’ar albarkacin bakinsa cewa sukeyi sukam sungama bata shawara tunda bazata yarda ba ,cikin kid’ima momyn Suhailat tace ”na yarda ,ko kefa suka fara tsara yadda abubuwan ‘nasu zai kasance .
Yau 1 month da bikin su Khalil , yau da safe misalin karfe 10:am ya tafi gidansu ,tarar dasu yayi a dinning suna breakfast , bayan ya gaida momy da dady ya nemi guri ya zauna , k’are masa kallo momy tayi cikin zuciyarta ko tana tausayawa Khalil ,sbda rashin dacen mata da beyi ba , Khalil yanaga ka rame ?”momy ta jefo masa tambaya ,dady ne yakai dubansa ga Khalil d’in yace ”tabbas my son ka rame sosai , maiya faru , abinci Khalil ya zuba yafara lodawa cikinsa ,saida yaci ya k’oshi sanan yace ”alhamdulilh yana shirin tafiya dady ‘ya haushi da fad’a ‘akan cewar suna yimasa magana yayi musu banza , dawowa Khalil yayi ya zauna yace ”dady matsalata bata wuce Suhailat , kullum banida kwanciyar hankali abinci ma saidai naci na waje ,6acin rai ne ya baiyana a fuskar momy tafara kuka , hak’uri dady yashiga bashi yana cewa kayi hakuri zata gyaru insha Allah , sunkuyar da kai Khalil yayi yace ”dady ina neman aure what!!! dady yace ”da kakkausar murya ,walhi last kenan karna sake ji dududu yaushe kayi wanan auran , momy ce ta tashi tabar wajen idanunta cike da hawaye , kuka Khalil yasa yana cewa dady ka fahimceni ba zanyi yi ne dan na wula…wani mari da dady ya wanka masa saida yaga haske , mik’ewa yayi yana danasanin zuwa gidan dayayi….
Nancy ce kwance a gadon Umma tana kuka ,umma tayi rarrashi harta gaji ta k’yaleta , tafara danasanin had’uwarta da Khalil sbda yana neman tarwatsa zuciyarta , yace mata inyai aure itama zai aureta to haryanzu shiru babu labari ..
Bayan ya dawo gida yasami Suhailat a parlor taci kwaliya tasa wani matsa tsen wando iya cinya sai riga mai hannu d’aya iya k’irjinta saman a bud’e , tafiya takeyi cikin salo ta iso gabashi yana shirin zama tace ” sweetheart ,harka dawo ?” zama tayi a kan ciyarsa tana taunar cingam , tace ”wlhi I miss you my sweetheart , wani azababen mari ya wanketa dashi yakuma k’ara mata , yace ”kinyi missing d’in ubanki dan uwarki shegiya watsatsiya kingama zubar da budurcin ki a titi , zaro ido tayi tana mamakin zantukan Khalil , mai_mai tawa takeyi tace ”zubar da budurci fa kace ,eh kina musu ne ?ko kina tunanin kiyayyar da nake yimiki zatasa na gaya miki abinda ba shine ba ,zaro ido Suhailat tayi tace”wlhi wlhi Khalil tunda nazo duniya banta6a zina ba , ka yarda dani kodan kaga kana yimin wulak’anci ina zurewa yanzu kuma zakazo kana jifana da wanan mumunan kalamin ,ta k’arashe maganar tana kuka mai ban tausayi , wani mugun kallo Khalil yayi mata yace ”dama ace na sameki da darajarki wata k’ila na iya daraja ki , to akasin hakan nasamu , shiyasa kika mannemin ashe da ‘abinda kike aikatawa , mazinaciya kawai , yayi gaba yana hararata , kuka Suhailat ta fashe dashi tana cewa tayi bedroom d’inta ,fad’awa gado tayi tana kuka nice mazinaciya nashiga uku , tunda na taso babu namijin da yata6a iskanci dani amma Khalil na jifana da wanan mugun sunan , wayo Allah na ..
Tunda Nussy ta sauka ta zarce gurin bokanta kud’i masu yawa a zuba masa tace ”tanason yayi mata wani aiki , dariya bokan yayi yafara zagaye gurin da wani bak’in ruwa yana dariya , Nussy da tariga ta saba ko d’arr batayi ba , zama bokan yayi yace ”akwai wani sirri da nakeson fad’a miki sirrin shine….
[31/01, 9:03 pm] Mom Islam ce????: ????????NANCY YAR KARYA????????.
_Labari mai d’auke dasa nishad’i tare da fad’a karwa_
Story and writing
By
*ZAINAB HABIB*
{Mom Islam}.
_MARUBUCIYAR_
*ZAINABU ABU*
*ZAZZAFAR KISHI*
*LADIDIN KAUYE*
_AND NOW_
*NANCY YAR KARYA*.
Special gifts to my fan’s ana tare????.
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Page 55_56
,,,,,,, Akwai wata yarinya da saurayin da kikeso yake sonta kuma burinsa ya aureta , muddun kika bari ya aureta to babuke babu samunshi har abada , kan uba Nussy tace ”cike da razana , bokane ya k’ara da cewa a halin yanzu wata mata tanada burin tasa ‘a kasheki , Nussy ce tace ”to wace matace kenan? boka ne ya had’e fuska yace ”munyi ,iya yinmu amma bamusan matar ba , gyara zama ,Nussy tayi tace ”yanzu dai boka ‘abinda nakeso kayimin shine sona keyi ka cire masa son yarinyar ita kuma matar karka bata damar samuna , wani ganye boka ya d’aga sama yana yare , dubanshi yakai ga Nussy yace ”ywwa ansamo na matar amma wanan budurwa bazata bar saurayin ba kuma bazamu iya yimata komai ba , kuka tafara tana me kankat ka temakeni please wata uwar tsawa ya daka mata saida ta tsorata yace ” yarinyar nan babu gurinda aljaninmu zai zauna a jikinta , sbda jikinta duk k’arfe ne….
****************
Kwance take zazza6i ya rifeta ga amai da yasata a gaba inbazata manta ba rabonta da ganin Khalil zatakai sati d’aya , momynta ta kira ‘a waya , momy na d’auka tace ” daughter ,meyafaru naji muryarki kamar kina cikin damuwa ? kuka ta fashe dashi tace ”momy banida lafiya amai ga zazza6i ,cikin farinciki momy tace ”alhamdulilh , kice ansamu rabo Suhailat da bata gane inda zancen momy ya dosa ba tace ”bangane ba momy, dariya momy tayi tace ”cikine dake daughter , amma kice mijinki ya kaiki hospital mana , to kawai Suhailat ta iya cewa sbda batason tayarwa da momynta hankali , bayan suna gama waya da momy ta mik’e jiri na d’ibarta taje ta d’auko hijab , dinta fitowa harabar gidan tayi tana k’walawa driver kira , da gudu ya k’araso ya durk’usa a gabanta , zaka kaini hospital yanzu cewar Suhailat dake cije le6e , driver jiki na rawa yace ”to to wane zamuje ?” ko kallonshi batayi ba ta koma ciki , y’an kud’a d’enta ta d’iba ta d’auki hand bag d’inta da wayarta ta fito , ganin murfin motar a bud’e yasata shigewa ,suka fice daga gidan , suhailat ce tafara tambayar drivern wanne hospital Khalil yake zuwa ?”driven nne yace ”na can cikin gari ne , to kaini can cewar Suhailat , da zuwansu driver ya shiga da motar yayi parking a gurinda aka tanadar ,Suhailat ta fito ta shige cikin hospital d’in ,hango wani d’aki tayi da kuneru da tebur da alamu nanne office d’in likitan , shigewa tayi da sallama , wani matashine kya kyawa ya ‘amsa yayi mata nuni da tazauna ,zama tayi tace ”banida lafiya ne shine nazo ni matar Khalil ce ,matashin likitanne ya k’are mata kallo yace ”wane Khalil d’in ?”kwatance tayi masa k’warai ya gane Khalil d’in amma ai kusan kullum suna tare kuma baita6a cemasa yayi aure ba , matashinne yace ”a iya sanina Khalil baiyi aure ba ,Suhailat da zazza6i ya addabeta tafara fitar da hawaye tana cewa wlhi Allah ni matarsa ce , number Khalil likitan ya dannawa kira ,ring d’aya Khalil ya d’aga bayan sun gaisa saurayin yace ” Khalil dama kayi aure ne ? a zabure Khalil ya amsa da cewa aure kuma sainayi aure ink’i fad’a muku , matashinne yace ”to ga wata tazo batada lpy wai matarka ce , matashin ya kalli Suhailat yace ”baiwar Allah ya sunanki ?” cikin muryar kuka tace ”Suhailat , matashinne ya cewa Khalil to kaji sunanta suhailat what!!! to niban ma san wata Suhailat ba , katse waya matashin yayi ya kalli Suhailat yace ”yiwa mutum sharri bashida kyau to menene ribarki in temakon magani kikeso basai kinyi masa sharri ba , jikin Suhailat na karkarwa ta mik’e tana nuna matashin da yatsa …..