HAUSA NOVELNancy Yar Karya

Nancy Yar Karya

Sharhinku yasa nayimuku typing da yawa ???? my fan’s ina yinku nagode da adu’a sosai ????.

Yanzu wasan ya fara zamuga waye mai nasara kuma waye bokanshi yafi aiki muje zuwa Allah yak’ara shiryamu ????.
[31/01, 9:03 pm] Mom Islam ce????: ????????NANCY YAR KARYA????????.

_Labari mai d’auke dasa nishad’i tare da fad’a karwa_

 

Story and writing

By

*ZAINAB HABIB*
{Mom Islam}.

_MARUBUCIYAR_

*ZAINABU ABU*
*ZAZZAFAR KISHI*
*LADIDIN KAUYE*

_AND NOW_

*NANCY YAR KARYA*.

Special gifts to my fan’s ana tare????.

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Page 59_60

,,,,,,, Khalil ne ya hango wani matashin yaro kiransa yayi yace ”dan Allah ka mik’amin ledar nan gidanan , to yaron yace ”ya kar6a ya shige , da shigarsa ya tarar da mutan gidan a tsakar gida , mik’awa Nancy ledar yayi ,yace ”inji wani a waje , kar6a tayi tana yimasa godiya , d’ari biyu taciro ta mik’awa yaron , k’in kar6a yayi ya fice lokacin Khalil harya tafi. ”

 

Bokane ya cewa ”momyn Suhailat , bakida matsala amma munada sharud’a dole zakibar sallah harna tsawon wata biyu , a razane ta kalleshi tana tunanin anya ya dace kuwa? hajiya Zinat ce ta kalli Momyn suhailat tace ”kiyarda mana daga baya saikiyi sadaka , hmm kaji 6atattu , jikin rawar jiki , Momyn suhailat ta yarda da wanan sharad’i na boka , cigaba boka yayi da magana yace ”sharad’i na biyu zakibar tarraiya da mijinki sbda zaki 6ata mana aiki , zufa ce tafara keto mata tace ”….

 

Bayan Nussy ta shige rumfar boka sungama sa6onsu ta fito tana gyara mayafinta , rik’e da maguguna a hannu , tasoma tafiya da baya da baya har tafice daga gurin , da isarta bakin titi ta bud’e motarta ta shige , gidanta ta nufa dan iyayenta ma bata ta tasu a yanzu …

Sallama yakeyi amma shiru babu alamun da mutum a cikin gidan , lek’awa d’akin suhailat yayi , ganinta a kwance duk ta sauya kamanni yasashi cewa ”Suhailat dama bakida lpy ne , jikinta na rawar sanyi tace ”eh nafi sati ma ,tausayinta ne ya kamashi ya temaka mata ya mik’ar da ita yace ”suje hospital , Suhailat ce tace ”naje wanda kake zuwa anyimin test har result aka bani , Khalil ne yakai dubansa gun result d’in ya d’auko shi , dubawa yayi ganin abinda ke rubuce ne yasashi tashin hankali ….

Momyn suhailat ce tace ” boka bazan iya dena kula mijina ba dariya boka ya shek’e da ita kana yace ”kutashi kubani guri matsiyata , hak’uri suka Shiga bashi amma inna yaki yarda ,tafiya sukeyi suna yiwa mom suhailat masifa akan k’in yarda da aikin boka datayi Hajiya Zinat ce tace ”baki damu da y’ar taki bane shiyasa , momyn Suhailat na kuka haka sukabar wajen zuciyoyinsu babu dad’i ….

Cikin yanayin damuwa , Khalil yace ” Suhailat garin yaya maiya sameki , kuka takeyi amma tarasa mai ya jawo mata wanan ciwon , Allah ya kayauta Khalil yace ya wuce d’akinshi …

Washe gari Nancy ce ta k’irga kud’in dubu ishirin , cikin murna Umma tace ”ayi mana cefane kinsan ni ba ko ina nasani ba , kuma dan Allah mu iya talaucinmu kisiyo mana garin tuwo da gero da citta da barkono mudinga shan koko da safe tabb Nancy tace ”tana kallon Umma walhi bazanci tuwo ba kuma nikam bazansha koko ba haka kawai ga kud’in ina gani da class d’ina chab ,ta koma ta shafa powder da janbaki ta zura madai_daicin hijab d’inta ta yiwa Umma sallama .”

Tunda momyn Suhailat ta koma gida da k’awayenta suka fara zazzaga mata masifa , kowa na fad’ar albarkacin bakinsa ,kuka tafara tanace musu ”toya kukeso nayi da raina sokukeyi mijin da nake alfahari dashi in rasashi , yaushene za’ace in k’auracewa mijina ?” Wata Hajiya ce ta tako ta dafa kafad’ar Momyn suhailat tace ”kiyi shiru sister yanzu ba lokacin kuka bane ,yanzu shawara yakamata muyi dan walhi daughter na cikin hatsari , Hajiya Zinat ce ta amshe da cewa ”wanan ma ai ba yibane keda mijinki yake tafiye tafiye ai ‘ina ganin babu matsala yin hakan ,tunda rayuwar Daughter zaki ceto…

 

Tunda Nancy ta shiga kasuwa tafara siyo kwalin indomie da macaroni da taliya , juyawa tayi gurin masu manja da mangyd’a ta siya tasi magi kala² ,hango mai dankalin turawa tayi taje tace ”nawa kwando fad’a mata kud’in yayi ba musu tace ”juyemin kwando biyu , bayan tagama da kayan abinci ta koma gun masu kayan make-up ragowar kud’in hannunta ma bashida yawa , haka taje ta siyo wata powder me tsada dubu d’aya da d’ari biyar…

 

Kwance Suhailat a d’akinta tana fama da ciwon ciki jitayi gidan nayi mata wani girgiza kamar yana shirin rushewa , k’ank’ame bargon da ta lulu6a dashi tayi tanajin wani tsoro na shigarta abinda tagani ne ya tsorata ta tana jada baya …

 

Nussy ce kwance tana tunanin Khalil ,inta tuno rayuwar da zasuyi saita rungume pilo tana dariya .

Dan Allah kuyi hakuri da wanan????.

[31/01, 9:04 pm] Mom Islam ce????: ????????NANCY YAR KARYA????????.

 

*STORY AND WRITING*
_BY_

*ZAINAB HABIB*
_(Mom Islam)_

 

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

 

Page 61_62

,,,,,,,,,Nancy na dawowa gida ta haye kan cinyar Unma , tana cewa umma wlhi na gaji ,tashi tayi ta d’auko kayan ta shige dasu ciki tana cewa Umma zomuje kiga kayan da nasiyo , Umma dake zaune a tsakar gida kan tabarma ta mik’e tana cewa “to muje ganina , da shigarsu Nancy tafara fito da kaya ,zaro ido Umma tayi ganin macaroni kwali taliya kwali indomie kwali gakuma k’wai ga madara da dankalin turawa da su maggi , tagumi Umma ta zuba tafara da cewa ”mekika d’auki duniya ne ?” ba cemiki nayi ki siyo mana dawa ko gero da garin tuwo ba , Nancy da ta kunna TV tana kallo tace ”umma in lokacin dad’i yazo to aci kawai , kinci gidanku ‘Umma tace cikin 6acin rai wlhi kiyi a hankali da duniya DUDUWA ki guji k’arya zaro ido Nancy tayi tace ”wai Umma sau nawa zan gaya miki ni ba sunanana DUDUWA ba ni gaskiya banason kalan Khalil yaji yahau tsokanata , Umma da takeyin fad’an da gaske tace ”to yaji mana ina ruwana nidai ina jiye miki ranar da Khalil zaisan gaskiya dan wlhi sewani ‘ikon Allah , Nancy cikin 6acin rai tace ”Umma dan Allah kibar maganar nan haka ,yanzu me za’a dafa , oho Umma tace ranta a 6ace ,cikin yanga Nancy ta mik’e tace ”indomie da k’wai zan yi yess yess tana rawa ,Umma ko kallonta batayi ba ,tagama rawarta ta fice da kayan.”

 

Wani girgiza gidan yakeyi kamar zaki cire gashi Khalil baya nan ihu takeyi amma inna babu mai temakonta sai Allah , ganin wani abu da bata ta6a gani ba yana yawo a saman d’akin yana kuwwa kamar na dodo yasata komawa bedroom takuma rufo k’ofa , da shigarta takuma cin karo da wasu abubuwa jikinsu duk jini abin tsoro wani sabon ihun takuma sawa saboda babu wata kalma ko adu’a da zata iya ambata ,subhanallh, ganin abubuwan masu kamada y’ay’an 6era suna nufota kuma jikinsu duk jini ,yasata hayewa gado tana kuka tana yarfe hannu , k’ok’arin haurowa gadon sukeyi amma sun kasa gashi batada damar sauka daga gadon ,kasamcewar sun bai baye gefen gadon jini na zuba a jikinsu ,gani tayi k’ofar d’akinta ya bud’e da kansa ta maida idanunta ga k’ofar halittunne suka fice bazata iya k’irga yawansu ba ,sbda sunada yawa sosai ,a tsorace ta sauko ta nufi bayi kayanta tacire domin yin wanka da d’aura tawul zata wanke fuska ta hango wani abu ta cikin mirror d’in toilet d’in jikinshi duk gashi ,wayo Allah na tace ”lokacin da taga yana rikid’a izuwa halittu da ban daban ,k’ok’arin tunkarota yakeyi ta jikin mudubin tana gudu ,da sauri ta bud’e k’ofar ta fice ko kayanta bata tsaya d’auka ba .”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button