Nancy Yar Karya

Khalil ne kwance a d’akin aminin nasa wato KB _KB ne yace ”mutumin na yanaga ka rame da yawa ko madam bata kula dakai ne ¿”murmishin yak’e yayi yace ”wlhi ‘ina cikin tashin hankali abokina , dadyna yak’i fahimtata ‘akan yarinyar nan gashi tana bala’in sona kuma nima haka , KB ne yace ”to abokina mezai hana ka rabu da ita kawai ka hak’ura da matarka , cikin fusata Khalil ya cakumo wuyan KB yace ”bakada hankali ne kana nufin yarinyar da tazamo.jinin jikina in barta kenen , wasu zafafan hawaye suka zubo a fuskar Khalil ,ya sake KB yace ”kaima bazaka fahimceni ba? ashe babu mai sona sai mahaifiya ta dakuma budurwa ta abokina ba bai damu dani ba ,wayo Allah ,yana kuka mai ban tausayi cikin tausayawa KB ya kama kafad’ar Khalil yace ”abokina karkace haka matsalarka tawace ka zamo jarumi ina tare dakai Khalil ,suka rungume juna cikin so da k’auna .”
Yau kwanan su momyn Suhailat biyu da zuwa gurin boka , komai ya kwance mata batada wal wala ko kad’an gashi k’awayen sun gudu ,duk dan bata yarda da umarnin boka ba , tagumi ta zuba tace ”my daughter kota halin k’a k’a saina kwato miki y’ancinki a gidan mijinki, lalubo number wata babbar k’awarta da rabonsu da waya zasuyi shekara biyar , dalilin rabuwarsu da momyn Suhailat kuwa shine ,ita k’awar tata mai suna Baraka ta shiga harkar karuwanci ne shiyasa momy tayi watsi da ita , amma yau gashi tana nemanta ido rufe lalubar number Bakara momyn Suhaital tashiga yi cikin sa’a kuwa ta ganta danna kira tayi , tana ring amma ba’a d’aga ba ,sake kira tayi a karo na biyu , jin muryar baraka na nishi yasa momyn Suhailat cikin tsoro tace ”lafiya kuwa baraka?” Baraka dake shek’e ayarta tace ”lafiya momyn suhyy ykk wanan tsohonne ya dameni da jaraba , momyn Suhailat ce ta kawar da zancen ta hanyar cewa dan Allah temako zakiyimin , jim Baraka tayi can kuma tace ”to kibani 6 minutes innayi wanka zan kiraki , OK momyn Suhailat tace ”sukayi sallama .”
Nussy ce kwance a k’irjin wani k’aton arne ,cemasa takeyi ‘inason zuwa Nigeria fa , cikin kulawa yace ”bakuda kowa ‘a Nigeria gurin wa zaki ?”Nussy ganin tambayar tayi yawa yasata cewe nifa ba kud’i na tambayeka ba , rungumota yayi yace ”to koma nawane ai zanbaki masoyiyata nawa kike buk’ata , juya masa baya tayi ,kasancewar ba tun yanzu suke tare ba yasashi fahimtar abinda takeso da wanda bataso , d’aukarta yayi yakaita toilet yai mata wanka shima yayi ,yana fitowa ya shafa musu mai , suka shirya , super market suka nufa ta sisiyo abubuwan da take buk’ata , suka dawo, shikuma ya koma inda yake da zama kasancewar Nussy tace ”yayi mata shirye _shiryen komai gobe zata d’aga zuwa Nigeria.”
Washe gari misalin 2pm bayan ‘Nancy ta idar da sallah taji wayarta na ruri duba number gani takeyi kamar tasan ‘number amma takasa gano ko number waye , d’agawa tayi tare da sallama , jin muryar anty Humaira yasata murna suka gaisa anty Humaira take tambayarta ya k’auye ?”Nancy ce tace ”ai run rasuwar hajiya ban koma ba ummana ma tadawo nan , cikin murna anty Humaira tace ”aikuwa zan kar6i address d’in inda kuke muzo , Nancy ce tace ”kinyi aure ne ? dariya anty Humaira tayi tace ”saura one week bikina wow Nancy tace ”insha Allah baza’ayi babu mu ba anty Humaira ce tace Allah ya kawoki amma zuwa gobe zanzo in gaida Umma to Nancy tace sukayi sallama .”
KOMAI NISAN DARE GARI ZAI WAYE ????.
Zaune take a jirgi tana sanye cikin riga da skirt na Pakistan ba k’aramin kyau tayi ba kannan yasha adon da indiyawa sukeyi fuskarta sanye da bak’in glass k’afarta na sanye da takalmi mai tsini , kunnenta na mak’ale da eyepiece , NUSSY kenan , babu wanda yasan da zuwanta sbda bata gayawa kowa ba .
Kirane yashigo wayarta da gudu ta taho dan tasan wacce take dakon jira ce ta kirawo ta , tana zuwa taga ita d’ince ,cikin rawar jiki tace ”ya ‘akayi ne ?” momyn Suhailat ce tace ” Baraka ina hatsabibin bokanki dan Allah kizo muje gurinsa inada damuwa dan Allah ki temakeni , dariya ta sheke da ita kana tace ”wata sabuwa yaukuma ? keda ko zancen boka bakyason ji to meyasa kike son zuwa gurinshi? shiru momy tayi can kuma tace ”k’addara ce kitemakeni dan Allah , Baraka ce ta ce ganinan zuwa ,amma kiyiwa securitys d’in gidanku mgna dan ba lallai subari in shigo ba , karki damu zasu barki suka katse waya
[31/01, 9:04 pm] Mom Islam ce????: ????????NANCY YAR KARYA ????????.
*STORY AND WRITING*
_BY_
*ZAINAB HABIB*
(Mom Islam)
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_
Page 63_64
,,,,,,, Da sallama ya shiga gidan ,tun daga parlor yafara tsorata saboda ganin yanayin gidan inda ya koma ,k’arasawa yayi ciki har zai wuce part d’inshi saikuma ya dawo yayi part d’in Suhailat, ganinta yayi kwance a sume ko motsi batayi , salati yashiga yi cikin tsoro .”
Anty Humaira ce takira Nancy tace ”ganinan a k’ofar gidan ku , dama tagama yimata abinci mai rai da lpy ,da gudu ta janyo mayafinta ta fice ,oyoyo tayiwa anty Humaira cikin farinciki ta rungumeta suka shige ciki , Umma ce take cewa maraba da bak’i ,bayan sun gaisa ne taci abinci ta k’oshi ,Nancy taja ‘anty Humaira d’akinta suka fara hirrar yaushe gamo , anty Humaira ce ta ciro wani less mai kyau rigada skirt ne ba k’aramin kyau yayi ba kasancewarsa pink ,murna gurin Nancy abin ba’a magana shine ankon bikin ?cewar Nancy ,eh shine yau saura kwana shida bikin fa ,Nancy cikin d’oki tace ”insha Allah baza’ayi babu mu ba ,misalin k’arfe biyar na yamma anty Humaira ta koma gida .”
Janyota yayi kamar gawa yasata a mota suka nufi hospital , emergency room aka kaita suka fara bata kulawa ,doctors sun duk’ufa ‘a kanta dan ceto rayuwarta , Khalil ne ya kira momy ‘ya shaida mata Suhailat babu lafiya , cikin sauri momy ta janyo hijab tasa driver ya kawota hospital d’in kasancewar anan suke komai nasu sunada family doctor , da zuwan momy ido na zubarda hawaye ta hango Khalil a zaune a benci ,k’arasawa tayi cikin muryar kuka tace ”ina Suhailat?” Khalil ne yace ”momy basu bari kowa ya shiga room din , gurin zama momy tasamu suka cigaba da jira kowane doctor fitowa yakeyi fuskarsa babu wal_walah ,da sauri Khalil ya tari wani doctor yace ”meyake faruwa ne naga kuna fitowa ranku a 6ace , babu komai yace ”ya wuce ,tun k’arfe 2:pm sune har 6pm a hospital basusan halinda Suhailat take ciki ba …
Yau saura kwana hud’u bikin anty Humaira Nancy tagama shirye shiryan biki saidai , rabonta da jin muryar Khalil kwana biyu kenan ‘number shima a kashe .”
Hostel Nussy ta kama mai tsada bata kula kowa kuma bata cika fita ba yau da shigowarta Nigeria kwana uku tana san saitayi sati sanan tafara aikin da yakawo ta .”
Momyn Suhailat ce zaune itada Baraka ,labarin damuwar da take ciki tabata dariya Baraka tayi tace ”kwantar da hankalinki sister tunda kika sameni ai angama komai yanzu kisa mana rana , momyn Suhailat tace ”ko gobe OK to nizan tafi cewar Baraka ,kud’i masu yawa momyn Suhailat ta bata ta wuce .”
Dady da momy da Khalil hankalinsu ya tashi ganin har yau kwana biyu doctors basuce komai a kan ciwon Suhailat ba , cikin 6acin rai Khalil ya nufi office d’in babban doctor , bayan anbashi ‘izinin shiga ya nemi guri ya zauna , duban doctor yayi yace ”ina ganin bai kamata kudinga 6oye mana abinda ke faruwa ba , akan wacce muka kawo , doctor ne yace ”kai menene a gurinta ?” Khalil ne yace ”ni mijinta ne sunkiyar da kai doctor yayi yace …