Nancy Yar Karya

Umma naganin kayan ta yaba dasu sannan tace” wa Duduwa ta kula sosai kar tabi maya daran samari , wasu hawaye ne masu zafi suka zubo a fuskar Duduwa , Umma na ganin hakan tasan ba k’aramin abu bane yake sata kuka , bayan tagama kukanne ta d’auki buta domin yin alwala ,Umma ma tashi tayi zuwa yin alwala ,
Washe gari misalin k’arfe takwas na safe sukajiyo sallamar dillaliya ,da cikin sanyin jiki Duduwa da Umma suka amsa sallamar ,bayan sungama shirye shiryen da zasuyi , tayi sallama da umman ta suka d’auki hanyar zuwa Abuja ,
Da isar su gidan dillaliya tayi nocking , mai gadi ne yazo ya duba , yana ganin dillaliya ya washe baki yace “barka dazuwa hajiya , goro dillaliya tabashi , yanata yimata godiya , ita dai Duduwa na biye da dillaliya , saboda duk inda tasa k’afa nan Duduwa take sawa,
Da isar su gidan wata kya kya kyawar mata fara sol, da ‘a shekaru zatakai shekara hamsin a duniya , amma inkaga yanayin jikinta bazaka gane yawan shekarun ta ba , tunda suka iso cikin parlorn matar take yimusu sannu da zuwa , gaisawa suka farayi Duduwa ma ta gai sheta ,matar tace” what’s is your name my daughter , jin wanan bahagon yaren yasa Duduwa mik’ewa tace “Hajiya zanyi kashi ……✍️✍️✍️
_mom Islam ce_✍️.
*Please share*????
*Comments*
*Vote*✔️
????????NANCY Y’AR K’ARYA????????.
_labari mai d’auke da nishad’i tareda fad’a karwa._
_story and writing_
By
*ZAINAB HABIB*
{MOM ISLAM}.
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*
PAGE 5_6
__Matar ce tace” bari azo a nuna miki bathroom d’in , Duduwa najin ance bedroom tasa ihu , Matar da ake kira da Hajiya tace” lafiya kuwa daughter ? cikin kuka Duduwa tace” Hajiya kiyi hak’uri karki sa ‘a maidani garin mu , cikin rashin fahim ta Hajiya tace” ban gane ba , Duduwa ce tak’ara share hawayen ta kana takuma duban Hajiya tace” kalma biyu zunyimin zafi , na farko kince min (bi dreba)???? yanzu kuma kince (buta) ni wallahi Hajiya ko wankin duka y’an gidannan ne zanyi akan a maidani garin mu , dariya ce taso ku6u cewa Hajiya , tace” yo daughter banda abinki , daughter yana nufin yarinya kokuma y’a , shikuma bathroom gurin wanka ne , OK Duduwa tace” kana ta waske tace ai nasani Hajiya kawai ‘inason jin ‘naku yaren ‘ne,
Dillaliya ce tayiwa Hajiya sallama tayiwa Duduwa nasiha ,kana ta wuce garinsu ,
Da tafiyar dillaliya Hajiya ta nunawa Duduwa ai yukan dazata dingayi , kamar su gyaran d’aki dakuma gyara d’akunan y’an matan gidan saikuma zuwa super market siyayya,
Hak’ik’a Duduwa tayi murna saboda babu aiki mai wahala , godiya tayiwa Hajiya kana ta nufi kitchen saboda cikin ta yana kukan yunwa,
Tana zuwa ta samu Nanny d’in tana farfesun kaji , lashe baki Duduwa tayi kana tafara magana a cikin ranta tana cewa , inama nice aka bari a d’akin girkin ‘nan da wallahi saina ci na k’oshi zankai musu sauran amma yanzuma bata 6aci ba,
Ganin hankalin y’ar aikin yakoma gurin aikin ta yasa Duduwa kwad’a sallama , amsawa tayi ba tare data d’ago kai ba saboda tana san kammala aikin cikin ‘nutsuwa,
Duduwa ce ta k’arasa kitchen d’in cikin taku sai k’amshi take zubawa mai aikin da take sanye da rigar aiki tace “sannu Duduwa da zuwa, cikin fushi Duduwa ta galla mata wata uwar harara …
Kana tace” as from today my name is Nancy..
Wani kallo y’ar aikin tayi mata kana tace to inma zagina kikayi keda Allah????,
Haka dai suka k’are kamar zasuyi fad’a haka Duduwa tabar kitchen d’in a zuciye ,
Washe gari bayan tayi sallahr asbah , taje ta gaida Hajiya bayan sun gaisa Hajiya take gaya mata anjima ita da su Humaira wato yaranta zasuje shopping ,wani tsalle ta daka kana tafara jerowa Hajiya godiya,
D’akin ta ‘ta nufa ta shiga wanka bayan ta fito daga wankan’ne tazo gaban mirror d’in d’akin da yazama nata tafara tsara kwaliya saboda ko gidan makeup sun shafa mata lafiya,
Wani riga da wando ,da rigar iya guiwa wandon kuma tsukakke , wayo kuzo kuga Nancy ,
Kar ince Duduwa ta fasamin baki????,
Kunsan fa ba mu muna bace kuma ko batayi kwaliya ba tanada kyau to inaga tayi kwaliyar ,
Tunda ta fito daga d’akin ta take yanga tana wata kalar tafiya kamar mai tsoron k’asa ,
Ganin y’an matan gidan a parlor suna jiran ta yasata k’ara sowa da sauri tana cewa( ai sorry sit ,wata dariya suka sa , d’ayar mai suna Humaira itace babbar su tace “ba haka zakice ba cewa zakiyi ,am sorry sis ,
Godiya tayiwa anty Humaira kana suka d’auki hanyar parking spice, ganin motar dazasu hau sukayi an wanke ta , Duduwa cikin bahagon turancin ta ‘tace….✍️✍️✍️.
_Mom Islam ce_✍️✍️
*please share*????
*Comments*
Vote✔️
????????NANCY Y’AR K’ARYA????????.
_labari mai d’auke da nishad’i tareda fad’a karwa._
_story and writing_
By
*ZAINAB HABIB*
{MOM ISLAM}.
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*
PAGE 7_8
“Tace very support???? anty Humaira da tagaji dayi mata gyara tace” please Nancy kidin ga daurewa kina k’yale turancin nan saboda , a gaban classmate d’inmu zaki bamu kunya , cikin k’awrewa Duduwa tace” au anty Humaira yanzu babu gyaran kenen, cikin takaici anty Humaira tace” cewa zakiyi very surprise , tsalle ta buga kana suka shige mota , da Isar su wani katafaren super market , kayane kala kala babu wanda babu , kuma duka gurin babu kayan talaka , suna shiga Duduwa ta sauya taku su Anty Humaira ko basu lura da ita ba , tana cikin takun ‘nata ne taji wani hansom yace hey Lady , cikin firgici ta juyo tana k’aremai kallo , farine sosai kamar balarabe , gashin kanshi kamar na larabawa , idanuwan shi kuwa lumsa sune gasu bak’ak’e ,sai dogon hancin daya k’ara fito da ainihin kyaun shi , ganin ta tsareshi da ido yasa shi cewa are you ok k’ak’alo murmushi tayi ganin turancin ma bai ‘iyaba , cikin zuciyar ta tace” mugu wai ‘inci wanan uban kwaliyar yacemin LADI , shikuwa wanan saurayi ganin bata kulashi ba yasashi cewa dan Allah kya kyawa kiyi magana , wani farinciki taji kana tace ” am barka da rana daganan tayi shiru , zaiyi magana ya hango su anty Humaira sun k’araso suna cewa Nancy kizo mu wuce , saurayin ‘nne yace”please sister kibari muyi magana koda ta 5mins ce , murmushi anty Humaira tayi ,kana tace bari muje mota , Nancy saikin taho , mak’ale murya Duduwa tayi tace tom ,
Bayan sun anty Humaira su tafi saurayin yake cewa , dafarko dai sunana Khalil ni haifafen Abuja ne , kefa ? farr, tayi da ido kana tace”amm my name is Nancy , can kuma sai tayi shiru tace”nima haifafiyar Abuja ce kaga babbar antyna can , fad’ad’a fara’arsa yayi , yana ganin yasami matar aure, musayar number sukayi , saboda Hajiya tasiya mata waya , bayan sunyi musayar number ,yayi mata sallama ya wuce tana d’agamai hannu , tunda ta shiga motar , Khadija da kausar suke hara rarta , ko kulasu batayi ba ta shige mota ,