Nancy Yar Karya

******************
Kayan sawarshi ya ciro a drowa shadda ce mai ruwan k’asa tasha aiki ,hula ya sanya fuskarshi cike da fara’a ,turare ya fesa ya d’auki wayarshi ya fice , direct gidansu ya nufa , samun Nussy da momy yayi a parlor suna kallo cikin fara’a momy tace ”harka dawo ?eh momy dama ba wani guri naje ba , Nussy ce tace ”brother ya aikin ,momy na dariya tace ai rago ne da yasaba dadynshi ya d’auko ya bashi yanzu kuwa yakoma kasuwanci Nussy ce tayi dariya ta mik’e zuwa kitchen ta d’auko masa abinci takai dining …✍️.
Kuyi hakuri da wanan ????.
Nasan kanku zai daure fan’s kudai kubiyoni zaku fahimci komai takuce maison zaku nishadi mom Islam ✍️????.
Only comments 08141799224????
[31/01, 9:04 pm] Mom Islam ce????: ????????NANCY YAR KARYA ????????.
*STORY AND WRITING*
_BY_
*ZAINAB HABIB*
(Mom Islam).
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_
Page 65_66
,,,,,,,Mik’ewa yayi cikin farinciki sabda fuskar ta wani haske take yimasa baya iya yimata musu ,momy ce ta mik’e tayi d’akinta tabarsu a wajen ,k’arasowa Nussy tayi ta zauna a d’aya daga cikin kujerun dake zagaye a gurin kusa da Khalil ta zauna , jikinsu na gogar na juna , abincin ta zuba masa tafara bashi a baki , wanan hali na Nussy kaf gidan babu wanda zai iya yimata magana , tanayin iskancinta iya san ranta , bayan tagama ba Khalil abincin ta goge masa baki ,ta kamo hanunsa ,shidai binta yakeyi kamar’ rak’umi da akala haka suke tafiya ,bedroom d’inshi suka wuce ta cire masa kayan jikinsa anzo kan wando tana k’ok’arin zata cire Khalil ya rik’e kam a lokacinne yasami damar yin mgna yace ”haba kifita mana nayi wanka , wata uwar harara Nussy ta wurga masa da yabashi damar yin shiru da bakinsa, ya wayance da cewa baby fitomin da kayan da zansa, OK tace ”sanan yasami damar shigewa toilet ,yana fitowa ita ta shafa masa mai d’ibar kayan yayi kafin ta ankara yai toilet dasu ya sanya , yafito sbda tsoron kartace anan zaisa ,ko mai bai shafa ba ya taho zai fita hannu tasa ta tokare k’ofar d’akin dan dole ya koma ya zauna ,yana jiran umarni…✍️.
Kufayi hakuri wayata ce tasami akasi narasa komai nawa ina jiran sharhinku dafatan kunfahimci karatun????.
[31/01, 9:05 pm] Mom Islam ce????: ????????NANCY YAR KARYA ????????.
*STORY AND WRITING*
_BY_
*ZAINAB HABIB*
(Mom Islam)
????????Wanan page d’in nakine *DOCTOR MARYAM (Autar mata)kiyi inda kikeso dashi ????????????*
_????_kubiyoni yaukam zaku gane inda na dosa ????page din jiya ya rikirkita mutane sosai ???? ku kwantar da hankalinku yau zan k’ara yawan page zaku fahimta kubiyoni_✍️.
_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_
*~Wai waye adon tafiya~*????
Page 67_68
,,,,,,,,,Yau kwanan Suhailat hud’u a hospital , doctors sun yi ‘iya k’ok’arinsu na ganin sun shawo kan ciwon amma ina abin yaci tura , samun Khalil baban doctorn yayi, tunda shine mijinta , tambayoyi yafara yiwa Khalil akan ciwon Suhailat doctor yace ” yarinyar nan tana cikin wani hali amma baka ta6a sex da ita ta bayanta ba ,kuma gabanta na fitarda wani ruwa mai wari ,to jiya nurses sun kirani harda tsutsa , zaro ido Khalil yayi yace ”innalilahi wayo Allah na , doctor ne yak’ara da cewa gaskiya zaka fad’a mana ,munyi iya bakin k’ok’arinmu mugano ko menene ya janyo hakan mun kasa ‘amma inka sanar damu gaskiya wata k’ila musamo bakin zaren , gumi ne ke tsatsafowa Khalil jin furucin doctor, ya girgiza matuk’a gyara zama Khalil yayi jiki a sanyaye yace ”doctor walhi Allah watanmu biyar da ‘aure amma sau d’aya nata6a kusantar ta kasancewar ba son auran nakeyi ba ,kuma a ranar ta inda Allah ya halatta na kusanceta , doctor ne ya zare farin gilashin dake sanye a idanunshi yace ”yanzu tashi muje ka ganta k’ila ka fad’a mana gaskiya, mik’ewa sukayi izuwa d’akin da aka kwantar da Suhailat ta rame sosai tayi bak’i ,zanin da aka rufe ilahirin jikinta doctor ya cire , abinda Khalil yagani ne yai matuk’ar firgita shi………..hango gabanta yayi duk tsutso tsi suna yawo ga wani uban wari da yake fitarwa , wasu zafafan hawaye suka zubo daga fuskar Khalil , ganin tabud’e ido yasa Khalil da doctor maida hankali gurin ,Suhailat , tausayinta ne Yakama Khalil yace ”mata sannu Suhailat ya jikin ?” muryarta bata fitowa sosai tace ”da sauk’i , doctor ne ya dubeta yace ”munzo yimiki tambayoyi ne akan ciwon dake jikinki ,kuka Suhailat tafara tana girgiza kai , doctor ne yace ”kiyi mana bayani ko kinta6a had’uwa da y’an lesbian ne ?a’a a’a Suhailat tafad’a tana kuka , to gaya mana ,cewa tayi ”kafin nayi aure na had’u da wata k’awa tana sona nima ina sonta to itace ke saduwa dani ta cigaba da kuka , tari ne ya sark’eta babu k’ak’autawa ga wasu yawu masu kumfa hancinta kuma na fitarda jini , duk k’yan k’ya minta da Khalil takeyi ya mance ,da sauri yayo kanta yana kuka , cikin sark’ewar murya Suhailat tace Khalil ka ,ka ya, ya femin , wani uban ihu Khalil ya kurma ganin tunda Suhailat tafad’i kalmar k’arshe idanunta suka rufe jikinta ya saki , momy da tagama jin komai ta taho jiki babu k’wari ta tallafo kan Khalil tana kuka tajashi suka fito harabar hospital din .”
Bayan anyiwa Suhailat sutura ‘aka kaita makwancinta , labari ya isa London , momyn Suhailat tayi kuka sosai tana fad’i tashi a kanta gashi tabar duniyar ,amma k’awayenta sunbari a kan k’awar Suhailat ce ta kasheta hmm ,musamman Hajiya Zinat da take zuga momyn Suhailat akan karta yarda ta k’yale wlhi garata d’au fansa, wanan mutuwar ba k’aramin girgiza momyn Suhailat tayi ba ,amma ta godewa Allah da bai bata sa’ar yin amfani da sharud’an bokaye ba , k’awayenta kuma duk tayi watsi dasu .”
Kwanci tashi babu wuya a gurin Allah har anti bakwai d’in Suhailat dady da baya gari akayi raduwar shima ya girgiza lokacin da Suhailat tayi sati uku da rasuwa , ana gobe d’aurin auran anty Humaira , Khalil ne yaje gidansu Nancy suna cikin hira take gayamasa tanada zuwa bikin wata sistern ta , Nancy na kiran sunan layin Khalil yace ”ai mijin ma abokina ne ayya Nancy tace ”kaima zakazo kenan? insha Allah Khalil yace ”ai inbabu ni to ina tunanin bikinan za’a iya fasashi ,gashidai a school muka had’u amma munzamo y’an uwan juna nida angon , Nancy ce ta katse zancen ta hanyar cewa dan Allah kayi hak’uri ko ya k’arin hak’uri banceba , Khalil ne yace ”to kina zumud’in biki rau_rau tayi tace ”Allah sarki Suhailat Allah yakai haske k’abarinki , Khalil yaji dad’in wanan adu’ar cikin fara’a yace ”amen ,yanzu zan koma gida gobe ki shirya misalin 12:pm zanzo mu wuce ,insha Allah kafinnanma nagama komai , dahaka sukayi sallama ya wuce gida.”
Washe gari ,Nancy tad’au makeup tayi kyau sosai sbda gwana ce gurin iya kwaliya ankon da za’asa ranar d’aurin aure tasa cot less mai ruwan toka sai gyalenta fari siriri dakuma takalminta mai tsini ga faskekiyar wayarta data dauka ,taci sark’a da d’an kunne da war waro wani d’auri da tayi kaikace zuwa tayi aka yimata shi komai nata yayi kyau ,Umma ce kecewa walhi wanan takalmin kiyi a hankali karki tako y’a y’an mutane , Nancy na dariya tace ”Umma ayi mana ‘adu’a bayan tagama komai ne ta d’auki jakarta ta fice ,kasancewar wayarta tana ruri Kuma Khalil ne mai kiran, tafiya takeyi cikin yanga tun daga nesa Khalil ya hangota masha Allah yace ”wai gaskiya na iya za6e Allah ya mallakamin ke beauty na , tana isowa ta hangoshi yayi wani bala’in kyau raina tata kwaliyar tayi amma karta bada mata yasata waskewa ta shige , motar tare da sallama , amsawa Khalil yayi yace ” beauty ai zakiyi rawa ko kinga kyan da kikayi kuwa ?” dama hijab kikasa dakinfi haka kyau , Nancy ce ta shagwa6e fuska tace ”hijab kuma kamar matar ustaz uhm , dariya Khalil yayi yace ”inmun dawo zankaiki ki gaida momyna zaki? maize hana cikin farinciki Nancy tace ”inason momy sosai dariya Khalil yayi yace ”itama tana sonki sosai Nancy , cikin hirarsu duka iso gidan bikin lokacin ana shirin d’aurin aure , Nancy ce ta wuce inda humaira take , misalin k’arfe hud’u aka wuce reception Nancy a motar Khalil suka tayi , guri ba k’aramin tsaruwa yayi ba , gurin zama kowa ya nema Khalil kusada ango ita kuma Nancy kusada anty Humaira , Nancy ce t gaisheda ango, cikin fara’a ya amsa anty Humaira ce tace ”ka ganne Nancy kuwa , a’a angon yace ”anty Humaira tayi dariya tace ”toke Nancy kin ganeshi kuwa ? Nancy ce take tunanin a ina tasan wanan bawan Allahn takuna kasa tunowa , ango ne yace ”na ganeta koba itace ta zauna a gidanku ba , yar aikin hajiya , what!!!! cikin tashin hankali Khalil yace ”me kunnuwana suke jiyomin yar aiki fa kukace ? ina Nancy batayi kama da yar aiki ba cewar Khalil, banda hawaye babu abinda ke fita a idon Nancy ,sai a lokacin anty Humaira ta tuna cewar batayiwa Nancy adalci ba ,tana tsaka da tunani ne taji saukar tagwayen maruka har biyu , tashi d’aya guri ya kaure da fad’a abin babu dad’i ,Khalil ne yakai dubansa ga inda Nancy take a zaune yaga babu ita babu alamarta ,fitowa yayi daga hall din yanata waige_waige amma baiganta ba , wani jiri ne ke d’ibarshi, yana tuno kalaman Humaira mota ya shige yabar gurin rasa inda zai Sosa yayi dan haka ya zarce gidanshi , ikon Allah ne yakaishi ,zuciyarshi sai zafi take yimasa ,a fili yace ”to wai shin gaskiya ne Humaira ta fad’a ko k’arya ?”