HAUSA NOVELNancy Yar Karya

Nancy Yar Karya

Shikad’ai yake tambayar kanshi, no Nancy ba y’ar aiki bace Allah yasa mafarki nakeyi ba gaskiya bane ,shikad’ai yaketa surutunshi kamar zararre .”

Da isarta gida ta shige da gudu fuskarta sha6e _sha6e da hawaye ,Umma da ta sauke abinci tana zubawa a kula ta taho tana cewa , DUDUWA maiyafaru ?”Nancy ce taji kamar Umma ta caka mata kifiya takuma tsala ihu ,tana cewa na shiga uku na lalace wayo Allah na wayo Allah na, ta shige d’akin tazube a k’asa tana kuka , Umma dai tayi iya yinta na ganin Nancy ta fad’a mata ‘abinda ke faruwa amma tak’i, kujera mai zaman mutum uku ta hau bacci mai nauyi ya d’auketa da mafarkai kala _kala dakuma na ban tsoro ,sada akayi akayi sallahr isha’i sanan ta tashi sbda umma tasan tana fashin sallah , wanke baki tayi ta nufi kitchen batayiwa Umma magana ba taje ta zubo jollof d’in taliya ta d’auko ruwan leda???? tana cikin cin abincinne tafara tunanin inhar Khalil ya gane gaskiyar lamari to babu makawa saiya gujeta , ta juya ruwan ledar dake hannunta tace ”shikenan yanzu bama ruwan leda ba har komai ma zaifi k’arfinmu , nashiga uku hatta kayan makeup d’ina wayo Allah na ,yanzu yazanyi da Khalil ? umma ce tazo ta zauna tafara yimata fad’a tana cewa”wato ni banida matsayin da zaki gayamin damuwarki ko?to shikenan kije da damuwar taki intai wari maji , Nancy ce tace ”ba haka bane Umma wata gagarumar matsala ce ta taso sbda wlh tashafemu dukkanmu , ta fashe da kuka , Umma da tashiga rud’u tace ”niwai bangane ba wace ”matsala ce ?”kuma kin hau kuka Nancy ce tace ”Umma Humaira ta tonamin asiri wlhi ta gayawa Khalil cewar ni y’ar aikin gidansu ce a gaban dubban jama’a ,jikin Umma yayi sanyi sosai sbda itama tafara tunanin yadda rayuwarsu zata kasance✍️.

Mom Islam ce ????.
[01/02, 10:29 am] Mom Islam ce????: ????????NANCY YAR KARYA ????????.

*STORY AND WRITING*
_BY_

*ZAINAB HABIB*
(Mom Islam)

 

 

_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_

 

69_70

,,,,,,,,,Umma ce tace ”karki damu insha Allah _Allah zai kawo mana d’auki , dagan an suka fara jajanta lamarin .”

Washe gari Khalil yatashi da wani matsanancin ciwonkai ,wanka yayi ya zarce gidansu da sallama ya shiga ya sami momy a parlor tana karanta wani litrafin adu’oi ,durk’usawa yai ya gaisheta cikin fara’a ta ‘amsa tare da sanya masa albarka ,ganin idanun sa sunyi ja yasa momy tambayarshi ,cemata yayi ciwon kai ne kawai , momy da tabi ta damu tace ”yakamata kaje hospital to kawai Khalil yace dan shiyasan halinda yake ciki .”

Tun had’uwarsu a gurin bikin Humaira yau kwana bakwai kenan bai k’ara kiranta a waya ba , rayuwa tayimai k’unci babban abinda yafi 6ata masa rai shine k’aryar da Nancy ta zuga masa ,in dadynshi yaji wanan zancen da wuya yabari ayi auranan ,mik’ewa yayi yace ”momy ayimin farfesun kifi anjima zan dawo ,da kallon tausayi momy tabi Khalil a tunaninta duk matsalar auran Nancy ne ya sashi rama .”

Muk’araban momyn Suhailat ne suka wai_wayo ta , rabonsu da gidan tun gaisuwar rasuwar Suhailat ,ganinsu da Momyn Suhailat tayi saida gabanta ya fad’i , Hajiya Zinat na taunar chingom tace ”oh mm Suhailat yanz zumuncin mu yaja baya , momy dake jera musu kayan ciye_ciye tace ”ba haka bane wlh ni yanzu fitar cema take yimin wahala , d’ayar ce tace ”to karkiyi tunanin zuwa gurin boka ya k’are dole muje mu d’aukarwa daughter fansa , girgiza kai momyn Suhailat tayi tace ”inma wani abinne nidai nabarwa Allah ita kuma Allah ya gafarta mata Allah yakai haske kabarinta , ta6e baki sukayi dukkansu kana sukace , to mekike nufi kina nufin yanzu bakya tare damu ne ?a’a momy Suhailat tace ”muna tare mgnar zuwa gurin boka ce gaskiya yanzu nadena but kuma ina nema muku gafara gurin Allah , eyeee y’ar iyayi ke harkin isa kice wai ga zance ga magana ,to tunda kince haka komai ya wargatse babu mu babu ke ko wata matsala ta taso miki to kimagan ceta da kanki karki nemi d’aya daga cikinmu , idanun momyn Suhailat na fitarda hawaye tace ”nifa ba haka nake nufi ba kunyimin wata fahimta ta daban , zata kuma magana suka mik’e suka fice ,kuka ne yakuma ku6ce mata seda tayi mai ‘isarta sanan ta koma wani tunanin da daban.”

Yau kwanan Nussy takwas tana k’arewa garin kallo tunda tazo bata kula kowa ba ,hijabai ta shiga kasuwa ta siyo manya ,yaune take shirin zuwa gidansu Khalil , bokanta takira a waya take gaya masa tagama duk wani shiri da yabata ,yanzu tanason ya rufewa mutanen gidan baki kuma kar Khalil yadinga yimata musu , komai tasashi tadinga yimata kuma yasawa mahaifinshi da mahaifiyarshi soyayyarta a cikin zuciyarsu , bokane yace ”angama karki damu buk’a tarki ta biya angama ,ya kashe waya , fitowa tayi ta tari mashin zuwan anguwarsu Khalil ,da isarta ta bawa mai mashin kud’insa tasauka tafara bubuga get d’in ,maigadi ne yazo cikin sauri zaiyi mgna yaga ta suri kayanta ta shige kasa yiwa Nussy magana yayi har lokacin da ta 6ace masa baya angota kasancewar kafin mutum ya isa cikin gidan da tafiya , samun k’ofar a bud’e ne yabata damar yin sallama ta shige da kayanta , momy ta samu a parlor tana kallo , da ganinta momy taso ganeta amma inna ta 6ace mata , Nussy ce ta gaida momy cikin fara’a ta ‘amsa Nussy tace ”momy nazo gaisuwar rasuwa ne na Suhailat ,oh momy tace ”kece k’awar tanan ko eh nice amma ba wacce take London ba ni iyauena sun rasu ta sanadiyar hatsarin mota , Allah sarki momy tace ”cikin tausayawa , nan suka fara hira da Nussy jefi_jefi, dady na shigowa yasamesu ita da momy a zaune bayan sungaisa ne yake tambayar Nussy ya k’arin hak’urin iyayenta ?tana kukan gulma tace ”alhamdulilh , misalin k’arfe 8pm Khalil ya shigo momy ce take gaya masa sunyi bak’uwa shima Khalil d’in yanason tuno inda ya santa ‘amma ya kasa , da fara’arta tace ”brother yakake lpy kawai Khalil yace ”sbda in yana kallonta kuwarjini take yimasa gashi sai yadingajin wani iri.”

Khalil ya mance da Nancy ko zancenta bayayi ,tunda Nussy tazo komai nashi ya sauya ita ce abincin sa komai ma gashi kosu momy nasan yin magana babu hali saidai subita da ido.

Yau Bikin Humaira sati biyu kenan shiri tayi dan zuwa gidansu Nancy dan tagane abinda tayi bata kyauta ba , tare da mijinta suka tafi , bud’e get din gidan sukayi suka shige ciki da sallama, Umma na bedroom Nancy kuma na parlor , ko amsa sallamar tasu batayi ba tafara zazzago musu bala’i , Humaira kinzo ne ki had’ani da nahaifiyata kokuma kinzone ki k’arasani da sauran kwana na ? wlhi nayi dana sanin saninki a rayuwa turr , hayaniyar da Umma taji ne yasata fitowa ganinsu Humaira a tsaye yasata cewa mekuma ya faru ne nakejin hayaniya , Nancy da kuka ya k’wace mata tace ”Umma karki yarda da ita wlhi ,umm ita ta rabani da Khalil tana kuka tana nuna Humaira ran Humaira ne ya 6aci sosai ,tace ”tunda ke ba kida fahimta munzo baku hak’uri ne shine zaki fara cimana mutunci ?”mijin Humaira ne yace ”zomutafi kawai ,Umma na cewa kuyi hak’uri Nancy da idanunta ya rufe tace ” wlhi wlhi Humaira ku fice mana a gida tana nuna musu hanyar waje , Humaira da ranta ya 6aci tace ”ank’i fita d’in kiyi duk abinda zakiyi banza kawai , Umma ganin abinnasu ya girmama yasata yiwa mijin Humaira magana akan ya tattarata su wuce , mota ya wuce tunda yayi mgna sunk’i jinshi , Umma tana kuka tace ”wlhi DUDUWA inbaki shige d’aki ba wlhi ranki zai 6aci ,Umma na magana Nancy na magana Humaira ma na magana ,maruka Umma ta wankawa Nancy dukda hakan batayi shiru ba ,tana cewa anty Humaira meraba masoya , Humaira da haushi ya isheta tace ”menene amfanin mak’aryaciya bazakiyi rayuwa a inda Allah ya ajiyeki ba kind’auki burin duniya kin d’orawa kanki ,garama da Khalil din yasani ba dukiyar momyn mu bace kikecin arzik’i ke banda butulci harzaki iya yimin rashin mutunci ,karki manta kwaliya a gurinmu kika koya kuma iya tafiya da magana ba a gurinmu kika koya mungama miki komai ai dole muzamo abin wulak’antawa , wawuya jaka kawai har mahaifiyarki kika dauko sbda san duniya kina tunanin soyayyarku da Khalil zata d’ore gashinan kinga k’arshen karya yazamo saniyar tatsa a gidan ku ,mahaifiyarki ma sbda San abin duniya tabiyoki kuka kama gida wani wawan mari Nancy ta tsinkawa anty Humaira nanfa fad’a ya kaure Umma ko tun d’azu tafad’i sumammiya ,Humaira ko kallon inda Umma take batayi ba ta wuce waje gurin motarsu .”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button