HAUSA NOVELNancy Yar Karya

Nancy Yar Karya

Da shigarta mota mijinta yafara surfa mata bala’i yana cewa”koma me akayimiki keka jawa kanki da bakizo gidansu ba da hakan bai faru dakeba , yaja mota suka wuce gida .

 

Yau kwanan Nussy goma a gidansu Khalil babu mai cemata komai kowa na gidan tsoron 6ata mata rai yakeyi , kuma bata ta6a nuna musu tana taraiyya da maza ba kasancewar tunda tazo bata fita koda k’ofar gida ba .”

Khalil ne yakira KB wato mijin Humaira a waya yace ”masa ganinan zuwa cikin murna KB yace ”Allah ya kawoka lpy mekakeso a dafa maka ?”Khalil na dariya yace ”ai kasan cimata farfesun kifi OK suka kashe waya , Nussy na bakin k’ofa tanajin hirar tasu , cikin kulawa tace ”brother nima zani , zaice a’a ta kafeshi da idanuwanta baisan lokacin da yace ”jeki shirya ba , saida ta tafi yashi haushin kansa shin wanan wacece dazata dinga yimasa shishigi ? bashida mai bashi amsa hakan yabashi damar yin shiru✍️.

 

Gaskiya jiya banga sharhi ba ????????.

 

~Mom Islam ce~✍️.
????????NANCY YAR KARYA ????????.

*STORY AND WRITING*
_BY_

*ZAINAB HABIB*
(Mom Islam)

Zainabhabibu713@gmail.com

 

_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_

 

71_72

,,,,,,,,,,, Nancy na kuka ta yayyafawa Umma ruwa , ajiyar zuciya Umma ta sauke daganan tafara kuka Nancy kuka Umma kuka babu mai bawa wani hak’uri , Umma ce ta mik’e taje tayo alwala ta dawo tafara sallah .”

Misalin k’arfe 2:pm Khalil da Nussy suka isa gidan KB wato gidansu Humaira , Nussy na sanye cikin riga da zani da hijab ba k’aramin kyau tayi ba , horn yai maigadi ya lek’o ya bud’e masa gidan , da shigarsu KB ya lek’o yana cewa ”wata sabon gani ,fitowa sukayu a motar suka nufi ciki ,anty Humaira ta cika musu tirai da kayan motsa baki gakuma farfesun kifin a kula , hira sukeyi sosai , anty Humaira ce kejan ‘Nussy da hira amma batason yin mgna , saida sukayi sallar la’asar sanan suka wuce , yana shirin d’aukar titin da zai sadashi da unguwarsu ,Nussy tace ”my lovely brother please muje shoppin mana ,kasa yimata musu yayi yajuya motar suka nufi super market , suna sauka ta kamo hanunshi ta rik’e , Khalil kuwa wani bak’on yanayi ne yaji ya ziyarce shi haka suka wuce ciki tana ta jidar kaya , Khalil ne ya wuce gurin turaruka wata kyakyawar budurwa tazo kusa dashi tace ”barka handsome zaro ido Khalil yayi saikuma yace barka yakk lpy suka gaisa , tace “masa inba damuwa kabani number ka mudinga gaisawa kayimin kama da brother na ,bakomai Khalil yace yana cikin fad’a mata number Nussy ta k’araso ta wankawa budurwar nan mari ,nanfa fad’a ya kaure aka yiwa Nussy duka harda kumbura baki bayan le6enta dake fitar da jini
Haka Khalil yasata a mota suka nufi hospital akayi mata treatment aka basu magani amma a gefe dariya yake kwasa ,da komawar su gida momy taga fuskar Nussy tambayar Khalil meya faru tayi cikin in insa Khalil yace ”fad’uwa tayi ,badan momy ta yarda ba ra k’yalesu , ranar dai Nussy tasha bak’ar azaba dan idanunta sun kumbura sosai .”

 

Ragowar dubu goma ne a hanun Nancy , damuwa da tashin hankali sun shiga sbda daga ita har Umma suna tunanin halinda ,zasu shiga idan kud’innan ya k’are tagumi suka zuba suna tunanin hanyar data dace , Umma ce tace ”DUDUWA zani k’auye ko Allah zaisa insamo mana wani abin kuma a d’akina ma inada buhun masara , 6ata rai Nancy tayi tace ”amma dai Umma inkin kawo masarar za’abada canji ne subamu shinkafa ? dak’uwa Umma tayi mata ,kana tace ”ke bakya tunanin abinda zaije ya dawo ko ,baki tunanin halin rayuwa ,ko sokikeyi wataran mud’auki kayan kallo ko gado da katifa musiyar gashi me hayan ma yakusa wai_wayar mu , Nancy dai bata k’ara magana ba taja bakinta tayi shiru.”

Yau kwanan Nussy biyu da zuwa gidansu Humaira gashi haryanzu ido yak’iyin sauk’i , kwance take idanunta nayi mata wani azabar zafi gashi babu dama ta kalli mudubi sai taji kamar an zuba mata barkono , washe gari dady ya dawo daga tafiya ya cewa Nussy ta shirya suje wani hospital din , rabonta da wanka tun jiya haka tasa hijab suka nufi hospital itada dady da Khalil , sunsami ganin likita aka wuce da ita d’akin masu larurar ido , doctor ne yace ”sai anyiwa idon aiki , hak’ik’a ciwon idon Nussy ya gir giza su momy amma basu isa suja da ikon Allah ba, doctor yace ”musu suje sudawo gobe insha Allah sai ayi aikin Nussy ko ba haka taso ba sbda wanan ciwon idon yasa Khalil bayajin maganarta ko kad’an .”

Yau Umma taje k’auye mutane da ganinta suka hau gulmarta wasu na cewa aikatau tajeyi wasu kuma na cewa tuwo tuwo tajeyi kowadai na tofa albarkacin bakinsa ,duk maganar da umma taji dole take shanyewa sbda batada bakin mgna , kwananta d’aya ta tattaro abubuwan da suke dashi buhun masara da daddawa da kuka da ku6ewa da wake na shinkafa ,mak’otansu ta shiga tayi musu sallama ta fito ,bataji dad’in gulmarta da akeyi a garin ba alma dole ta hak’ura ,ta hau mota ta nufi Abuja ,mai motar da ya kawota ne ya temaka mata suka shiga da kayayyakin Nancy kuwa batanan ,kasancewar key kuda biyu ne d’aya a gurin Nancy d’aya a gurin Umma , kud’in shigo da kayan ta biya tayimasa godiya , je jera kayantayi taje tayo alwalah tayi sallah , tana idarwa ta nufi kitchen hango plet tayi cike da taliya da kifi , girgiza kai tayi dan tasan yarinyar tata tayi nisa batajin kira , Nancy ce tashigo tana cewa oyoyo Umma kinsha hanya seda Umma taci abinci sanan suka fara hirar k’auye

 

Yaune za’ayiwa Nussy aikin ido an shige da ita d’akin ,????‍♀️sedai muyi mata fatan fitowa lafiya.”

 

[02/02, 3:13 pm] Mom Islam ce????: ????????NANCY YAR KARYA ????????.

*STORY AND WRITING*
_BY_

*ZAINAB HABIB*
(Mom Islam)

 

 

_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_

 

73_74

,,,,,,,,,,Khalil ya koma gida , yabarsu momy da Dady a Hospital d’in ,

Kwance yake a makeken gadonsa tunanin Nancy ne ya yafara ziyartar shi cikin azama ya mik’e ya na shirin fitowa , kome ya tuna oho saiya koma ya kwanta zuciyarshi babu dad’i ,tunanin farkon fara soyayyarsu dakuma yanzu daya gano gaskiyar lamari gameda Nancy , wayarshi ce tafara ruri sunan momy ne ke yawo a fuskar wayar cikin azama ya d’auka tare da sallama ,Khalil kazo yanzu cewar momy , Khalil da hankalinshi ya tashi yace ”to ganinan zuwa , tunani yafara kodai jikin Nussy ne kokuma ba’ayi nasara bane oho bashida mai bashi amsa ya mik’e batare da ya sauya kaya ba ya fice , yanufi mota …

 

Tunda su Nancy sukazo Abuja basu ta6a yin tuwo ba ‘amma gashi yau ,umma shitakeyi , tarasa inda zatasa rayuwarta gashi batada kud’in kayan kwaliya bare akai ga cikinta dan tafi buk’atar kayan makeup , lek’owa kitchen d’in tayi taga Umma na kad’a miyar kuka chii ,Nancy tace ”tana toshe hancinta da gefen d’ankwalinta ,ko d’ago kai Umma batayi ba bare ta kulata , d’aki Nancy ta koma tanata juyi sbda wata azababbiyar yunwa takeji ,sallama Nancy tajiyo ,da sauri ta fito dan taso tagane masu muryar , hango su Jamila da Karima tayi aikuwa ta buga tsalle suna dariya d’akin bak’i dake can wani part daban ta kaisu dan batason suga Umma na tuwo , Umma ko taji zuwan bak’in kuma taci alwashin kaimusu tuwon ko Nancy zatayi menene ,hira sukeyi sosai ,d’auko musu exotic tayi dama jiya ta siyoshi tana burin yau tasami biscuit taci dashi tunda Umma nayin tuwo , to gashi yanzu anyi manyan bak’i ,zuzuba musu a cup tayi sukaci gaba da hira , suna cikin hira ne Umma tayi sallama , cikin girmamawa suka amsa suka gaisheta , Umma ce ta ajiye musu tuwon leda a plet da miyar kuka da taji daddawa da citta sai k’amshi take zubawa , cikin farinciki sukace kai mungode Umma wlh kamar kinsan munason tuwo a gida ko munaso basayi mana kuma bamu iyaba dariya Umma tayi tace ”zaku iya a hankali Allah yabaku miji nagari ,suka amsa da amen Nancy kuwa kamar ruwa ya cinyeta, Umma na fita su Jamila suka janyo plet d’in tuwon suka fara ci suna santi Nancy ce kallonsu takeyi ga bak’ar yunwa data gallabe ta .”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button