HAUSA NOVELNancy Yar Karya

Nancy Yar Karya

Da isarshi hospital din yasami momy a barandar asibitin a zaune parka motarshi yayi ya k’araso da sauri mik’awa momy abincin daya buya hotel yasiyo yayi ,kar6a momy tayi suka gaisa , Khalil ne yace “momy ya mai jikin ?” da sauk’i momy tace ”ammafa idanuwan nata duka sun rufe yanzu bata gani , zaro ido Khalil yayi tareda jan dogon salati yace ”abu kamar almara innalilahi momy daga mari ?!! haka Allah yaso cewar Momy , mik’ewa my tayi tace ”tashi muje ka ganta ku gaisa tun d’azu take kuran sunanka , mik’ewa Khalil yayi jiki babu k’wari , suka nufi cikin hospital d’in ,da shigarsu Nussy tajiyo sallamar Khalil dariya takeyi tana d’aga kai alamar inda makafi sukeyi, rung d’in wayar Nussy ne ta katse dariyar tata , batasan mai kiranba saidai ta d’auki murya , jiyo muryar bokanta tayi yana ihu yana d’ura mata zagi had’i da wasu dariyaku kamar na mahaukaci , hankalin Nussy ne ya tashi sosai dan tasan su momy sunji komai angama , ajiye wayar tayi ta maida kai ta kwanta , mik’ewa Khalil yayi zaije gurinta ,momy tayimasa alama da hannu akan yadawo , bahakan yaso ba amma dole yadawo .”

 

Bayan su Jamila sungama cin abinci suka mik’awa Nancy wata leda cike take da kayan makeup dasu chocolate da biscuit ,aiko ba k’aramin murna tayi ba , labarin fad’an dasukayi da Khalil tabasu amma bata basu labarin cewar su talakawa na harda k’arya ta shirya musu , sukadinga zagin Khalil , saida akayi magrib driver n su yazo ya tafi dasu Umma nata yimusu godiya , d’akin Umma ta nufa da kayan Umma tayiurna sosai Nancy ko abin nema yasamu lol.”

Yaune aka bawa Nussy sallama taji sauk’i saidai matsalar ido, sbda likitoci sune jijiyar idonta sun mutu ko ina zasuje a fad’in k’asar nan saidai suyi asarar kud’i , da isarsu gida kowa ya zarce part d’insa , momy ko tunani takeyi anya wanan yarinyar ba da wata manufa tazo gurinmu ba ,dan tasha mafarkin tazo mata da daddare zata caka mata wuk’a ,
Shima Khalil a nashi 6angaren ya tuno inda yasan Nussy a gidan shi babbar k’awar Suhailat ,amma meyasa kwanaki kowa kejin shakkarta
[02/02, 6:36 pm] Mom Islam ce????: ????????NANCY YAR KARYA ????????.

*STORY AND WRITING*
_BY_

*ZAINAB HABIB*
(Mom Islam)

Zainabhabibu713 @gmail.com

Whattpad Momislam2021

________________________________

*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

 

_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_

 

75_76

,,,,,,,,,, Washe gari da sallama momy tashiga d’akin Nussy ,samunta tayi kwance a kan gado idanunta tabb da hawaye dajin motsin shigowar momy yasa Nussy goge fuskarta , momy nuna mata tayi kamar batasan tana kuka ba , ta gyara zama tace ”Nussy waye kukayi waya dashi a hospital , uhm im am ,momy ta dakatar da ita dacewa wato mu munrik’eki da zuciya d’aya kekuma kinna nufinmu da mugunta ko?” bajinayi mutumin ‘na zaginki ba mekika aikata masa ? hawayen da take k’ok’arin tarewa ne sukayi nasarar zubo mata tace ”momy ku gafarceni momy ku yafemin ‘niba marainiya bace kamar yadda Na fad’a muku inada iyaye yawon duniya ne yasa na watsar dasu rabon da iyayena susani a idanunsu nayi shekara bakwai , momy ni ce silar mutuwar Suhailat!!! Innalilahi wa inna ilaihirraji’un momy tace ”tana k’arewa Nussy kallo ,kenan kece kika kasheta , cewar momy Nussy na kuka tafara bawa momy labarin lesbian d’in da sukeyi dakuma bin boka da sxx da boka yayi da ita komai saida ta fad’awa momy tace ”ita ba y’ar Nigeria bace , amma iyayenta haifaffun kano ne amma basa zama a Nigeria suna London ,cikin 6acin rai momy tace ”kinga irinta nan ai shiyasa akafi so mutum ya aikata alkhairi , to wanan rayuwar taku ishara ce ga y’an baya masu biyewa zuciya ,wlh da har unayiwa Khalil sha’awar auranki yanz kam banajin son muhad’a zuri’a dake wlh dole kikoma gurin iyayenki , kuka Nussy takeyi ta sauko a hankali ta dafa gado ta durk’usa gaban momy tana bata hk’r momy ko saurararta batayi ba , tace ”barinkira Khalil gobe yau yaje ya shirya komai a airport gobe ki wuce ai bazaki kasa sanin iyayenki ba , cikin kuka mai ban tausayi Nussy tace ”momy kitausayamin mana kema mace ce ,momy ce ta k’i kallonta dan batason fasa niyar da tayi ,zakutafi tare da Khalil daganan ta fice. ”

 

Nancy taga batada gaba batada baya dole ta zage tana kwasar tuwo gashi duk tayi bak’i ta rame yanz kam ko tunanin Khalil batayi sbda tama cireshi a ranta ,
Wata rana suna zaune da umma tace ”mata ke bazaki fito da mijin aure bane ?”rau_rau da idanu Nancy tayi tace “Umma wazan fitar babu mai zuwa gurina ina adu’ar za6in Allah ko mai amalanke ne yazo zan aureshi , dariya Umma tasa tace ”nagodewa Allah daya amsa adu’ata dakuma ya cire miki girman kai Alhmdulilh.”

Washe gari Khalil da Nussy jirginsu ya d’aga zuwa London , gidansu Suhailat yafara zuwa shida Nussy sunyi sa’ar samun momy suka gaisa tare da k’ara yimata gaisuwar rasuwar Suhailat ,ganin Nussy yasa momy tuno wa da itace shu’umar k’awar Suhailat , momy zatace Allah ya is….Khalil ya dakatar da ita da cewa makauniya ce tazo neman gafarar ki ne itama kinga inda Allah ya maidata momy Suhailat na kuka tace”na yafe miki Allah ya k’ara shirya mana ku amen.”

 

Nancy ce taje gidan anty Humaira tabata hak’uri anty Humaira mace ce mai fahimta suka zauna sunata hira kaya tabawa Nancy masu kyau da hijab da gyale Nancy tayi murna sosai suka yi musayar number ,Nancy tayi mata sallama .”

Da fitarsu Khalil daga gidansu Momyn Suhailat anguwarsu Nussy suka wuce da isarsu Khalil ya hango wani tsararren gida ,yafara tunanin to har me Nussy ta rasa take yawon karuwanci alhali iyayenta sun mallaki dukiya , shiga gidan sukayi da sallama wata mata fara ta fito da fara’arta ta taresu ,da ganin Nussy yasata fara zubda hawaye , tace ”NUSAIBA dama kina duniyarnan ?” Nussy bata ganin mahaifiyarta ta durk’usa tafara kuka tana cewa Ammi ki yafemin dan Allah , Allah sarki uwa kome d’anta yayi bazata gujeshi ba ,rungume ta Amminta yayi suka shige ciki Khalil ko said a ya zubar da hawaye , nayafe miki NASIBA ,Nussy ce tace ”Ammi nazamo makauniya wani razanannen kuka Ammi ta saki had’i da fad’uwa kasa sumammiya , da sauri Khalil ya d’auko ruwa a fridge ya shafa mata a fuska ,ajiyar zuciya ta sauke tafara adu’oi , bayan Khalil yaci abinci yayi sallah yayi musu sallama , Ammi godiya tayita masa ,yau zai kwana a hotel gobe ya wuce Nigeria
[03/02, 12:56 pm] Mom Islam ce????: ????????NANCY YAR KARYA ????????.

*STORY AND WRITING*
_BY_

*ZAINAB HABIB*
(Mom Islam)

________________________________

*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

 

_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_

 

77_78

,,,,,,,,,,Bayan Khalil ya sauka ‘a Nigeria drivern gidansu yazo d’aukarshi , gida suka wuce inda yasami momy da dady a zaune suna dinner ,shima zama yayi akayi dashi albarka momy taketa sanya masa hakama dady , dady ne yace ”yakamata kaje kayi wanka kashirya zuwa gobe kaje gurin surukarmu , Khalil da baigane zancen da dady keyi masa ba ,yasashi cewa dady wacce surukar taku ?”dariya dady sukayi shida momy yace ”au bakada budurwa to momyn ka ta fad’amin komai , kanshi a sunkuye ya wuce part d’inshi batare da ya k’ara magana ba , wanka yayi ya sauya kaya shadda fara yasa sai takalmi da hula bak’i ,wow Khalil yayi kyau sosai kamar kasaceshi ka gudu .”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button