Nancy Yar Karya

Gidansu Nancy ya nufa ganin get d’in a bud’e yasashi parking d’in motarshi a nesa ya fito ya shiga gidan da sallama , lokacin Nancy na kwaliya Jamila ta kirata zata rakata bikin wata k’awarta Umma dake tsakar gida tace ”barka da zuwa , durk’usawa Khalil yayi cikin girma mawa ya gaishe da umma , bayan sungai sa ne yake tambayar Nancy , umma ce tace ”yashiga parlor bari taje ta kirawo ta shiga yayi ya zauna dakin tsaf tsaf kasancewar Umma mace ce mai tsafta batason k’azanta hakama Nancy halin Umma tabiyo , shiga umma tayi ta tarar da Nancy tanasa kaya ,cikin fara’a umma tace ”ga Khalil nan yana jiranki , umma ta fice tayi d’akinta , sanya gyale Nancy tayi ta fito fuskarta cike da fara’a , barka da zuwa tace ”tana k’ok’arin zama a kujera , ywwa beauty barka ya garin ya kwana biyu lpy tace ”a tak’aice , gyara zama Khalil yayi yace ”nasan dukkan mu bamu kyautawa junanmu ba ‘amma dawoda gaba baya bashida amfani , yanzu dai muyafewa junanmu , murmushi Nancy tayi wanda yakuma baiyyana kyawunta tace ”babu komai , Khalil ne yace ”dady na yanason zuwa gurin iyayenki akan maganar auranmu , Nancy ta girgiza amma bata nunawa Khalil ba , tace ”yaushe zezo , Khalil ne yace ”am inaga nanda 5 days yace , to Allah ya kaimu ,nan sukayi sallama ya mik’a mata bandir d’in y’an d’ari biyar biyar tak’i kar6a ya ajiye a kan kujera ya fita .”
Da fitarsa Nancy ta buga tsalle tace ”umma adu’armu ta kar 6u yanzu Khalil yace ”wai dadynsa zaizo to umma gurin wa zaizo alhali mahaifina ya rasu kuma y’an uwanmu na k’auye , Umma ce tace ”zankira yaya Ubale a waya sai atura masa kudi yazo ,rungume Umma Nancy tayi yaudai tayi kwanan farinciki.”
Yanzu momy batada zama itada wata k’anwarta kusan kullum a hanyar kasuwa suke saboda momy a ganinta tayi dacen surukar kirki yanzu Khalil zaisan yayi aure wasu mahaukatan kaya ake jidowa kamar ba’asan zafin kud’i ba sosai momy takejin auran Khalil da Nancy alkairi ne saboda ta yaba da hankalinta .”
Nancy ce ta k’irga kud’in da Khalil yabata dubi ishirinne 20k taji dad’in wanan kyautar sosai dan haka ta mik’awa umma kud’in dukka , umma ta cire dubu biyar ta tura garinsu saboda d’an uwan mahaifin Nancy yazo ya tsaya akan maganar auranta , ta ware dubu goma ta ajiye dubu biyar ,tace ”yau Nancy ta rakata kasuwa , bawani tsayawa shiri sukayi ba sbda umma najin labarin bikin yan birni basa sashi da nisa , da isarsu umma ta hango abubuwan buk’ata
Wato tanason fara gyara Nancy ????????.
Aya
Dabino
Kwakwa
Rid’i
Mazar k’waila
Minannas
Shinkafar tuwo
Gyad’a
Kafi malam
Asuwakin mata
Duk umma tasa aka had’a mata su takoma gurin masu saida saiwoyi please????kuyi hakuri zan wuce but nasan kunsani .”
Dawowa gida sukayi umma tafara wanke aya ta shanya ta surfa rid’i ta wanke ta wanke shinkafar tuwo da sauransu , tana jira subushe ta dakesu inta soya ayar sama sama
[03/02, 12:56 pm] Mom Islam ce????: ????????NANCY YAR KARYA ????????.
*STORY AND WRITING*
_BY_
*ZAINAB HABIB*
(Mom Islam)
????????????????????????????????
Ina mik’a godiyata ga masoyana masu karanta littafin NANCY YAR KARYA gaskiya inajin dad’in faranta min da kukeyi Allah yabar zumunci masu sharhi ina godiya Allah yasaka muku da alkhairi????.
_Allah ya had’amu a sabon littafina mai suna *JININ ABBANA!!*
SHAFIN KARSHE????.
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w
_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_
Page 79 _80
,,,,,,,,,,Yau kwana biyar da zuwan Khalil kawun Nancy harya zo Su
Su Umma sun shirya wa su dady tarba ta musamman da ragowar kud’in hanunsu , hak’ik’a dady ma ya yaba da karamcin da su Umma sukayi musu ,a take a gurin suka biya dukiyar aure dubu d’ari biyu ,aka sa rana wata d’aya dan sunce basason ad’au lokaci mai tsayi , daganan sukayi sallama cikin mutuntawa .”
Parking yayi a k’ofar gidan su Nancy ,yanzu ko kunyar Umma bayaji kai tsaye zeshige suyita hira , tambayar Nancy yayi dame _dame take buk’ata zatayi ,Nancy ce tace ”gara munemi albarka ayi walimah kawai kuma a raraba ‘alqur’ani hak’ik’a Khalil yaji dad’in hakan saboda yasan yaza6awa y’ay’ansa uwa ta gari , samun Umma yayi yace ”karta si komai saboda ya zuba komai a gidan, godiya Umma tayita zuma mai tare da sa albrka , cewa ”nancy yayi tazo suje ta kar6o kaya a mota , tare suka fice bayan yayiwa Umma sallama , da isarsu ya bud’e motar ya ciro wata k’atuwar leda cike da kaya ,godiya tayimasa tare da cewa Allah ya k’ara bud’i amen yace ”yana yimata murmishi .”
Riga da skirt na na atamfa sai swiss less da material ,d’inkin yayi matuk’ar yin kyau Nancy tayi farinciki hakama Umma tana ganin yarinyarta tayi sa’ar miji.”
*WEDDING*????????.
Allah ya yarda ‘a yaune asabar dubban mutane suka shaida d’aurin auran IBRAHIM KHALIL da amaryarsa AISHA akan sadaki dubu d’ari biyu ,daurin auran dayasami halartar manyan mutane daga 6angaren dady Khalil , momy kuwa kamar anyimata bushara da aljanna , ango ni kaina ban ganeshi ba bare kuma amarya Nancy da gidansu yake cike da yan garinsu da mak’otan anguwa , Khalil ne yadauki nauyin abincin da Umma suka dafa kayan miyane bai siyo ba amma komai harsu itace shiya siyo ,Nancy ko tanacan d’akinta itada su Anty Humaira da Jamila da Karima ,kowa ka gani cikinsu da fara’a a fuskarsa , anty Humaira ko kaza ta dafowa Nancy dasu magunguna , hak’ik’a tayi rawar gani , su Jamila kuwa jug da kuloli na abinci masu tsada suka kawowa Nancy.”
Misalin k’arfe 6pm motocin d’aukar amare suka iso Nancy kuka takeyi na rabuwa da Ummanta , Umma ma sai share hawaye takeyi tana kuma jadada mata nasiha ,akan gidan aure, da isarsu get man ya bud’e musu , wayo Allah gidanfa ya had’u kamar a turai babu makusa saboda komai na gidan ya tsaru Nancy ko da ganin gidan tafara zaro ido cikin zuciyarta tana cewa kodai mafarki nakeyi ,takuma mutsuka idonta ,dayake a cikin gyle ne anty Humaira tajata zuwa bedroom d’inta ,gidan sai k’amshi yake zubawa , misalin, 9 kowa ya watse Nancy ta rama salolin da ake binta ,lokacin taji alamar shigowar Khalil , gyara mayafinta tayi ta haye gado , da sallama ya shigo yazo ya zauna a bakin gadon ya d’aga hannu sama yana yiwa Allah kirari tare da godiya , daganan ya umarceta suyi sallah babu musu sukayo alwalah sukayi raka’a biyu ya d’ora hanunsa a kanta yafara kwararo adu’o , daganan ya yi mata tambayar da addinin musulunci ya tanadar na bayanin ibada babu Wanda bata kawoshi ba , janyo ledar daya shigo da ita yayi yaje kitchen ya d’auko please da cup yadawo ya zuba mata hollandia yafara bata kaza abaki kowa kagani cikinsu farinciki ne a fuskarsa , to nidai zan wuce ango Khalil a fito lafiya Nancy Allah yakawo twins fatan alkhairi.
ALHMDULILH
[ad_2]