HAUSA NOVELNancy Yar Karya

Nancy Yar Karya

Ban sun koma gida sungama siyayyar dama su anty Humaira ta rako , tunda ta shige d’akinta domin rage kaya ta watsa ruwa,

Tana cikin cire kayanne taji wayar ta na ruri d’auka tayi kana tayi k’asa da muryar ta ,

Cikin sa sanyar murya yace “beauty gobe zantafi India , saboda hutun mu ya k’are kuma jigin safe zanbi please ki kulamin da kanki ‘kuka tafara / nikuwa nace????Duduwa d’azu fa kuka had’u amma har kinshiga kogin love????‍♀️,

 

Cikin kuka tafara magana tana cewa ” wallahi da su momy basuce mu dawo ba , bai gane mai take nufi ba yace ” ban gane ba , cikin sha shek’ar kuka tace “satinmu biyu da dawowar mu daga India ????,

Cikin farin ciki yace” dama kuna zuwa ne ? ,

Eh tace Khalil yace”to yaushe zaku dawo ?jimm tayi kana tace”gaskiya sai su momy sun shirya….✍️✍️✍️.

Wayo anty Duduwa ????am sorry anty Nancy????.

Kuyi hakuri please page d’in babu yawa , kumin adu’a kuma ku had’a da Nancy saboda ????‍♀️.

_Mom Islam ce_

*Please share* ????
*Comments*
*Vote*✔️

????????NANCY Y’AR K’ARYA????????.

_labari mai d’auke da nishad’i tareda fad’a karwa._

_story and writing_

By

*ZAINAB HABIB*
{MOM ISLAM}.

________________________________

*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*

PAGE 9_10

Daga nan sukayi sallama , tayimai Allah ya tsare , washe gari suna d’aki suna kallo dama bata da wani film daya wuce Indian film saboda sunan garin, data keso ne, duk wani yare ko turanci yana zama daram , wata safiya ce Hajiya ta tashi da matsa nancin zazza6i , kowa na cikin gidan jikin shi yayi sanyi , ganin ciwon bana wasa bane sukayi da ita ,Diza hospital dake maraba , saboda sun rud’e shiya sa,

Suna shiga cikin hospital d’in suka ci karo da Doctor Maryam ,wato matashiyar budurwar nan wace a shekaru zatakai 20 years a duniya,
Cikin azama tayo sauri tana tambayar su anty Humaira maiya sami marar lafiyar bakin anty Humaira na kar karwa tace” Doctor Maryam Wallahi bamu san mai yasami Hajiya ba , dafa kafad’arta Doctor Maryam tayi kana tace” ki kwantar da hankalin ki ‘insha Allah zamuyi ‘ iya bakin k’okarin mu , anty Humaira ce tayiwa doctor Maryam godiya kana suka shige emergency room da Hajiya ,
suna shiga doctors biyu suka had’u a kanta wato da fitacciyar likitar nan wace kowa yasanta da adalci bata da walak’nci ita ce doctor (Anty HAUWA) ana kiran ta da (Maman Uswan),

 

Tunda suka rufu akan Hajiya basu d’ago ba aiki sukeyi cikin k’wa rewa da nuna adlci ,

Bayan sun shafe minti hamsin suna aikin abu d’aya ganin jikin Hajiya ya tsanan ta yasa aka kirawo anty Humaira da sauran suka shigo , tunda suka shigo Hajiya take kallon su tana hawaye tace “idan ,na mutu karku zauna a gidan da muke ciki dan Allah , ku koma gurin uncle d’inku , cikin kuka Humaira tace ” Hajiya to Nancy fa yaza tayi ? Hajiya na hawaye tace…..✍️✍️✍️.

Kuyi hakuri da wanan zani anguwa please????.

_Mom Islam ce_✍️

*please share*????
*Comments*
Vote✔️
????????NANCY Y’AR K’ARYA????????.

_labari mai d’auke da nishad’i tareda fad’a karwa._

_story and writing_

By

*ZAINAB HABIB*
{MOM ISLAM}.
________________________________

*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*

PAGE 11_12

____ Hajiya ce tace” akwai wasu kud’a d’e da take bina sunkai , dubi d’ari uku , zaro ido Duduwa tayi, saboda har tafara tunanin kalar gidan dazata siya bayan an biya ta kud’inta,

Hajiya ce tafara wani ‘irin tari kana wani , miyau _wato yau mai kumfa yafara biyo baya , tana gamawa rai yayi halin sa, kowa na hospital d’in saida ya tausaya mata bare yaran da Hajiya tabari , wani ‘ihu Duduwa ta kurma tana cewa, na shiga uku bani da gata sai Allah, ganin kukan ‘nata yayi yawa ne yasa doctors d’in sukayi waje da ita,

 

Anty Humaira ce tadin ga kiran waya tana gayawa y’an uwa rasuwar Hajiya , hak’ika mutuwar ta ta6a kowa saboda Hajiya bata da son duniya ,

????Allah kasa muyi k’ya k’yawan k’arshe amen ????.

 

Bayan rasuwar Hajiya da kwana biyu, y’an uwan Hajiya suka ce zasu tafi da su Humaira garin su,
Duduwa bata gama tabbatar da , rasuwar Hajiya ba sai lokacin da wani dattijo wato d’an uwan Hajiya ya kira ta, yana cema ta yanzu kulle gida zasuyi saboda , umarnin Hajiya zasu bi,

Wasu hawaye ne masu zafin gaske suka zubo mata , duk da kud’in da take ganin kamar inta samu zata warke , amma yanzu jikin ta yayi sanyi sosai,

Washe gari ta tattara kayan ta tana neman gidan haya , cikin ikon Allah tasamu wani mutumi da yake kusa da gidan su yana dashi a can wata anguwa ta’ talakawa ana kiran anguwar Riga y’ar kasuwa ,

Tambayar shi kud’in hayar tayi , cemata yayi dubu hamsin shekara d’aya , bayan sunje gidan tagani tace” mai yama ta uzuri saboda ba’a bata kud’in taba , cikin ‘nuna rashin yarda yace” sai dai tabari ‘in aka biyata sai ta koma ,

Gidan da mutumin ya kaita gidane mai kyau ma’ana ‘akwai siminti kuma akwai bayi a ciki ga kitchen a waje bayi a d’aki ,

Mata biyu ne a cikin gidan kuma duk zasu girme ta d’aya tana da miji d’ayar kuma karatu ne ya kawo ta saboda bazata iya zaman hostel ba,

A yau ne akayi bakwai d’in Hajiya, an sallami Duduwa kud’in da Hajiya ta buk’ata ‘a bata, alhamdulilah uncle yabata dubu d’ari uku da hamsin , kuka Duduwa takeyi sosai saboda ‘a ganin ta sunyi mata hallacci,

*Wayoo kud’i ???? Anty Nancy bani aron two thousands????*

Bayan sun su Anty Humaira sun k’ara bata kaya sabba bi dakuma gyale da hijab , sosai suka yiwa juna fatan sake had’uwa , daganan Duduwa ta tattara akwatin ta zuwa anguwar da takama haya , bayan ta biya wanan mutumi dubu hamsin ,

Da shigar ta gidan taci karo da wata datijuwar mata da ‘a shekaru zatakai sittin a duniya , gaisheta Duduwa tayi kana ta nemi d’akin da ‘ya zamo nata ,

Tunda tazo birni bata tunanin komawa k’auye saboda wahala zatasha ‘a can ,

Tana zaune tana tunani , taji wayar ta na neman agaji , duba number tayi ganin Khalil yasata sauke gwau ran nunfashi , daga can 6an garen shi yace”, kya kyawa yakike yasu momy ?cikin sanyin jiki tace lafiyan su lau , daganan yafara janta da hira , bata wani sake sosai ba , ganin haka Khalil yace”kodai baki da lafiya ne ?eh tace “daganan yayi mata fatan samun sauk’i sukayi ssallama,

Washe gari ta ‘tashi da wani matsa nancin ciwon kai , saboda kukan data sha jiya da daddare , ganin wata jaka mai kwalin lifton har , uku yasata duba sauran kayan dake ciki suga na da bonvita dakuma biskit na shan shayi, in bazata manta ba Anty Humaira ce tabata leledar….✍️✍️✍️.

_mom Islam ce_

*please share*????
*Comments*
Vote✔️
????????NANCY Y’AR K’ARYA????????.

_labari mai d’auke da nishad’i tareda fad’a karwa._

_story and writing_

By

*ZAINAB HABIB*
{MOM ISLAM}.
________________________________

*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button