Nancy Yar Karya

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*
PAGE 13_14
____ Hajiya ce tace” akwai wasu kud’a d’e da take bina sunkai , dubi d’ari uku , zaro ido Duduwa tayi, saboda har tafara tunanin kalar gidan dazata siya bayan an biya ta kud’inta,
Hajiya ce tafara wani ‘irin tari kana wani , miyau _wato yau mai kumfa yafara biyo baya , tana gamawa rai yayi halin sa, kowa na hospital d’in saida ya tausaya mata bare yaran da Hajiya tabari , wani ‘ihu Duduwa ta kurma tana cewa, na shiga uku bani da gata sai Allah, ganin kukan ‘nata yayi yawa ne yasa doctors d’in sukayi waje da ita,
Anty Humaira ce tadin ga kiran waya tana gayawa y’an uwa rasuwar Hajiya , hak’ika mutuwar ta ta6a kowa saboda Hajiya bata da son duniya ,
????Allah kasa muyi k’ya k’yawan k’arshe amen ????.
Bayan rasuwar Hajiya da kwana biyu, y’an uwan Hajiya suka ce zasu tafi da su Humaira garin su,
Duduwa bata gama tabbatar da , rasuwar Hajiya ba sai lokacin da wani dattijo wato d’an uwan Hajiya ya kira ta, yana cema ta yanzu kulle gida zasuyi saboda , umarnin Hajiya zasu bi,
Wasu hawaye ne masu zafin gaske suka zubo mata , duk da kud’in da take ganin kamar inta samu zata warke , amma yanzu jikin ta yayi sanyi sosai,
Washe gari ta tattara kayan ta tana neman gidan haya , cikin ikon Allah tasamu wani mutumi da yake kusa da gidan su yana dashi a can wata anguwa ta’ talakawa ana kiran anguwar Riga y’ar kasuwa ,
Tambayar shi kud’in hayar tayi , cemata yayi dubu hamsin shekara d’aya , bayan sunje gidan tagani tace” mai yama ta uzuri saboda ba’a bata kud’in taba , cikin ‘nuna rashin yarda yace” sai dai tabari ‘in aka biyata sai ta koma ,
Gidan da mutumin ya kaita gidane mai kyau ma’ana ‘akwai siminti kuma akwai bayi a ciki ga kitchen a waje bayi a d’aki ,
Mata biyu ne a cikin gidan kuma duk zasu girme ta d’aya tana da miji d’ayar kuma karatu ne ya kawo ta saboda bazata iya zaman hostel ba,
A yau ne akayi bakwai d’in Hajiya, an sallami Duduwa kud’in da Hajiya ta buk’ata ‘a bata, alhamdulilah uncle yabata dubu d’ari uku da hamsin , kuka Duduwa takeyi sosai saboda ‘a ganin ta sunyi mata hallacci,
*Wayoo kud’i ???? Anty Nancy bani aron two thousands????*
Bayan sun su Anty Humaira sun k’ara bata kaya sabba bi dakuma gyale da hijab , sosai suka yiwa juna fatan sake had’uwa , daganan Duduwa ta tattara akwatin ta zuwa anguwar da takama haya , bayan ta biya wanan mutumi dubu hamsin ,
Da shigar ta gidan taci karo da wata datijuwar mata da ‘a shekaru zatakai sittin a duniya , gaisheta Duduwa tayi kana ta nemi d’akin da ‘ya zamo nata ,
Tunda tazo birni bata tunanin komawa k’auye saboda wahala zatasha ‘a can ,
Tana zaune tana tunani , taji wayar ta na neman agaji , duba number tayi ganin Khalil yasata sauke gwau ran nunfashi , daga can 6an garen shi yace”, kya kyawa yakike yasu momy ?cikin sanyin jiki tace lafiyan su lau , daganan yafara janta da hira , bata wani sake sosai ba , ganin haka Khalil yace”kodai baki da lafiya ne ?eh tace “daganan yayi mata fatan samun sauk’i sukayi ssallama,
Washe gari ta ‘tashi da wani matsa nancin ciwon kai , saboda kukan data sha jiya da daddare , ganin wata jaka mai kwalin lifton har , uku yasata duba sauran kayan dake ciki suga na da bonvita dakuma biskit na shan shayi, in bazata manta ba Anty Humaira ce tabata leledar….✍️✍️✍️.
_mom Islam ce_
*please share*????
*Comments*
Vote✔️
????????NANCY Y’AR K’ARYA????????.
_labari mai d’auke da nishad’i tareda fad’a karwa._
_story and writing_
By
*ZAINAB HABIB*
{Mom islam}
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*
PAGE 15_16
____Dauko su tayi kana tarasa inda zata dafa ruwan zafi, bayan tayi wanka da ruwan sanyi tayi kwaliya tana gamawa , ta d’auko , wani less mai ruwan ganye wow kuzo kuga kyan da , Nancy tayi , wani takal minta marar tudu ta d’auko kana ta yafo farin gyale ta fito , rik’e da mukullin d’akinta bayan ta d’ibo kud’i marasa masu d’an yawa ,
Tafiya takeyi cikin yanga , inka ganta zaka rantse y’ar shugaban k’asa ce saboda iya taku irin’na Duduwa , mai adai_daita ta gani yana tahowa , hannu tasamai ya tsaya, cemai tayi ya kaita kasuwa , maraba ya kaita , wani shago ta hango na kayan shafe_shafe , shine ya d’auki hankalin ta tayi wajen ,
Da shigar ta shagon wasu samari dabaza su wuce 27yrs ba suka fara cewa maraba hajiya mai kikeso ?” cikin yanga Duduwa tafara magana tana fari da ido , powder ta d’auka , mai kayanne yace” dubu d’aya , ko tayi batayi ba tafito da kud’in tabashi ,
Wani saurayi da naji suna kira da Usman ya k’araso gaban Duduwa ,itako ganin had’uwa irinta bawan Allah yasata rud’ewa , magana yafara yimata cikin wata da sanyar murya , saida ta lumshe ido kana tace ina lafiya tayi hanyar waje ,
Binta yayi cikin k’aware wa saikuma yaga taje gurin masu siyar da electri tana tayawa , mutumin ne yace ” dubu ‘uku zata bashi , sai wanan saurayi ya ciro kudin yabada , batasan yana bin ta ba ,
Godiya tayimai kana tafara tarar motar dazata kai ta gida , k’ara sowa yayi da sauri yace”please kibari ‘in kaiki gida ‘a mota ta ‘a’a tace”kana tacigaba da tafiya , saida ya rok’ota yanata had’ata da ‘Allah tukun tabari ya kaita a mota,
Suna cikin tafiya suna hira kad’an kad’an , yake tambayar ta inane anguwar su ?” saida tayi jimm kafin tace (A.Y .A),
*Wato cikin abuja kusada su baba buhari????*
Tamabayar ta number gidan yayi , bata nuna mai ba saidai tace”mai yabari ‘idan sukazo zata nunamai gidan ,
Wani tsararen gida ta hango , fad’in tsaruwar gidan ma 6ata lokaci ne amma , my Fan’s kuyimin afuwa , gidan kamar a k’asar waje,
Usman ‘ne ya kalle ta kana yace nanne gidan Ku ?cikin gadara tace ” eh nanne , yace to barin in shigo mu gaisa da momy , kasa magana tayi ,
Suna shiga na hango wata budurwa da bazata gaza shekara goma sha biyar ba , tana ganin su tafara bro, alamar tayi shiru yayi mata kana ta gimtse dariyar ta saboda ta d’auka yazo da budurwar sa ne,
Da shigar su cikin gidan sukaci karo da wata mata fara doguwa ba can can ba , ganin Usman yasata ,fad’a d’a fara’arta tace”Usman har kuntashi a shagon ‘ne? Duduwa ce tazaro ido tana tunanin wai’inama tazo ne, murmushi Usman yayi kana ya dubi , momyn shi yace”momy wanan itace budurwa ta, cikin farin ciki momy tafara yiwa Duduwa tsiya ‘akan tak’i sakin jikinta suyi hira , momy na fita , Usman ya cewa Duduwa yana zuwa, to tace mai saboda jitakeyi kamar k’asa ta tsage ta shige dan kunya , yana fitowa rik’e da zam6a leliyar bulala ya zuba mata biyu lafiyai yyau , ganin yana neman jimata ciwo ne yasata rugawa ta fice da uban gudu daga gidan…✍️✍️✍️
_Masoyana nifa burina baya wuce ganin comments &shar’hi indai kunaso in k’ara yawan Page to kudage????nikuma zan sambad’o muku shi ????_
_mom Islam ce_
*please share*????
*Comments*
Vote✔️
????????NANCY Y’AR K’ARYA????????.
_labari mai d’auke da nishad’i tareda fad’a karwa._
_story and writing_
By
*ZAINAB HABIB*
{MOM ISLAM}.
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*
PAGE 17_18
____Bayan ta fice ne daga gidan taci karo da wani mutum , a wata galle liyar mota mai nunfashi, ganin mutumin yasata saita tuna nutsuwar ta , cikin isa mutumin yace”Hajiya ina zuwa ne ? gyara muryar ta tafara yi kana tace ba da nisa zani ba , gidan mu yana can gaba , hango wani katafaren gidan da Duduwa ta nuna yayi , a iya sanin shi wanan gidan gidan k’anwar momyn shi ce amma baisan ko tayi bak’uwa ba , cewa yayi to inba damuwa ki shiga in k’arasa dake , k’in shiga motar tayi , shikuma ganin haka, yasa shi yadinga binta a hankali har sukazo dai’ dai gidan , ganin bata shiga gidan ba yasa shi tsayawa, da motar shi yafara dogon tunani”.