HAUSA NOVELNancy Yar Karya

Nancy Yar Karya

 

Ita ko Duduwa burin ta tagan ta ‘a cikin d’akin ta , seda tayi nisa sanan taga wani mai adai daita , hannu tasamai ya tsaya , tace “mai RUGAN JULI cemata yayi d’ari biyu babu musu yace” tashiga suka wuce”.

 

Da isar ta gida ta tuna da electri d’in ta da powdern da tasiya duk ta man cesu gidan su Usman,kamar zatayi kuka , sai yanzu takejin yunwa ta dawo mata sabuwa , k’ara fita tayi anan ta hango wani shago na siyar da kayan ci k’arasawa tayi kana tayi siyayar abin da take buk’ata , tana hanyar dawowa ne taga wani saurayi ,mai kamada Kalil , dad’a ware ido tayi kana tace” kamar Khalil ko?
Kashe mata ido d’aya yayi kana yace”nine kya kyawa nadawo jiya, amma mai kikeyi a nan anguwar ? gyara mayafin ta tayi kana tace”nazo duba wata yarin yar abokin dady na ne amma kai maikazo yi? dariya yayi mata kana yace”najiyo bugun zuciyar ki ne shiyasa nayo nan anguwar,
Amma inba damuwa maizai hana ki zo muje ki gaida momy na , wallahi kullum saina bata labarin ki , murmushi Duduwa tayi kana tace”to ai kaga ban sanar dasu Hajiya ta ba , ????(Allah sarki kidena yiwa hajiya karya saboda taci yalo????)”.

 

Cikin ta ttausan kalamin shi yace “please kya kyawa kokuma Nancy kizo muje a mota ta Allah bazaki dad’e ba , to tace ” mai kana suka shige motar , ammafa tabar kayan da tasiya gurin mai shagon anguwar su,
Suna cikin tafiya yana bata labarin irin missing d’in ganin kya kyawar fuskar ta dayayi , cikin shgwa6a tace” ai na fika wallahi ,

Seda sukayi tafiya mai nisa sannan suka shigo anguwar su Khalil wato (WUSE TWO , G.R.A),

Tunda take bata ta6a ganin kyau da tsari kamar na gidan su Khalil ba , ko gidan su ‘Usman baikai kyan’nasu Khalil ba , horn yayi wani dattijon mai gadi ne ya bude musu gate , bayan sun fito daga motar ne yaciro wata k’atuwar leda a bayan , motar shi”.

Dama ya sanar wa da momyn shi babu musu suka shige yana rik’e da hannun ta , bataso rik’e hannun da yayi mata ba amma saboda karta kwafsa yasata biye mai,

da sallama suka shiga cikin parlorn , ganin k’awatuwar d’akin’ne yasa Duduwa tsayawa tana kallon kowani ,ado na d’akin ,

Allah yasa babu kowa da kinbamu kunya anty nancy????”.

da bayan sun zauna ne saiga wata mata mai kamada ,Khalil amma saidai ,Khalil yafita haske, tunda ta k’araso momy tana ta fara’a da ‘alamun farinciki a shimfid’e a fuskar tta,

Bayan ta zauna ne Duduwa ta , sauko daga kan kujerar da take zaune , ta durk’usa tana gaida momy , bayan momyn ta ‘amsa ne tace”ai munzama d’aya yarinya taso zonan , cikin farinciki Khalil yace”Nancy kije momy na kiranki…..✍️✍️✍️.

Masu cewa bana typing da yawa kuyi hakuri wlh jikinne sai a hankali????‍♀️, fatan alkairi sisters and antys

_mom Islam ce_

*Please share????*
*comments*
Vote✔️
????????NANCY Y’AR K’ARYA????????.

 

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*

PAGE 19_20

_____K’arasawa tayi kusa da momyn Khalil , bayan ta zauna ‘a kusa da k’afarta momyn tace” a’a kitashi.”

Kin tashi Duduwa tayi , yin hakan da Duduwa tayi yasa momy k’ara jin sonta ‘acikin zuciyar ta, y’ar aikin gidan ce ta shigo da tire d’auke da kayan mar mari a ciki , a gaban Duduwa ta ‘ajiye , sunkuyar da kai Duduwa tayi ,kuma ‘acikin zuciyar ta tana son ta d’auka amma tana kunya , momy ce tace” Nancy ki d’auka kici mana , batayi magana ba sai ma mur mushi datayi, Khalil ne yace”Momy please kibamu guri wlh kunyar ki takeji , cikin shagwa6a yayi maganar , dayake Khalil d’in gwani ne gurin iya shagwa6a “.

Dariya momy tasa mai sauti ,kana ta mik’e tace kai ma taso muje saboda zaka iya hanata , jeka kiramin Ummi tazo ta kawo mata abincin inta gama had’awa , shima dariyar yakeyi , ya mik’e ya rufawa momy baya, amma har yabar gurin idon shi na kan gimbiyar tashi wato Nancy, bayan sun tafi ne ta gyara lulu6in ta, kana gyara zaman ta ‘tafara cin ayaba tsabar yunwar da takeji saida taci ayaba uku lemu biyu kan kana yanka hud’u sai tuffa guda d’aya,

,(oh????‍♀️Anty Nancy kinbani kunya daga cewa abaki guri , shine kika cinye abincin Allah yasa ma tiren a cike yake da kayan mar marin????”.

Ummi ce wato y’ar aikin gidan tafe da kulla abinci da jug na lemu mai sanyi wata kulla na hango cike take da farfesun kaji ,bayan ummi tagama ‘ajiyewa ne ta wuce tabar gurin “.

Cikin wanan abincin da ‘aka kawo abu d’aya Nancy taci shine naman kazan kuma guda d’aya ta d’auka ta mayar ta ‘ajiye”.

Burin ta kawai tagan ta ‘a gida saboda ‘a yanzu hankalin ta yafara tashi , Khalil ne yashigo da ‘alamu wanka ya kuma yi saboda ba kayan d’azu bane a jikin shi, kashe mata ido yayi kana ya matso kusa da ita ya zauna ‘a k’asa yace” Nancy mai yasa kika k’i sakewa da momyna ? cikin jin kunya tace”dan Allah ka maidani gida , dariya yayi sosai kana yace”ai anan zaki kwana yarinya, cikin murya kamar zatayi kuka tace “shikenan nagode babu komai ,dayaga ‘alamun ranta ya 6aci sosai ya durk’usa ya rik’e kunnen shi kana yace ” am sorry kya kyawa , murmushi tayi kana tace” to muje ka maida ni saboda yanzu wata k’anwar momy na ta kirani wai kakarmu babu lafiya???? , azama yayi yace”Allah sarki barinzo mu tafi”.

Komawa ciki yayi kana yafa k’iran momynshi , bayan sun d’auki lokaci saiga momyn ,d’auke da wata k’atuwar leda ta mik’owa Khalil tace” yabawa Duduwa , dur kusawa tayi har k’asa tana yiwa momy godiya , hak’ika momy ta yaba da hankalin Duduwa k’awarai “.

 

Bayan sunyi sallama suka fice momy na d’aga musu hannu , har suka fice daga gidan, suna shikin tafiya ne Khalil yake tambayar Duduwa , shin kina sona? jin kalmar tayi kamar saukar aradu , daurewa tayi tace” ai mutum baya k’in mutum d’an uwan shi ,????wallahi bacci nakeji , kila dasafe in k’arasa ????,

Itako tanada dalilai masu yawa na k’in auran Khalil , cema tayi wace anguwa zan kaiki ? cikin yanayin damuwa tace” kaini RUGAR JULI saboda dazu da ‘aka kirani ance wai sun wuce asibiti , Khalil ne yace “har ina sako manyan kaya saboda inshiga mu gaisa, murmushin yak’e tayi kana tace” ai suna ‘asibiti , Khalil ne yace “to inba damuwa kizo mu wuce asibitin mana , kallon jikin ta tayi kana tace gaskiya nayi datti da yawa saina shiga nayi wanka ,k’arewa gidan da yake gabansu kallo Khalil yayi , gidan kewaye yake da fenti sai k’ofa itama da fanti a jikin ta , to gidan dai za’a iya kiran su da masu rufin asiri”.

Bud’e murfin motar tayi kana tayi mai bye bye, kiran ta yayi cikin sanyin jiki ta k’araso mik’a mata ledar da momy ta bata yayi, kanta ‘a sunkuye tayi mai godiya ta wuce….✍️✍️✍️.

_mom Islam CE_

*Please share*
*Comments*
Vote ✍️
????????NANCY Y’AR K’ARYA????????.

_labari mai d’auke da nishad’i tareda fad’a karwa._

_story and writing_

By

*ZAINAB HABIB*
{MOM ISLAM}

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*

PAGE 21_22

 

____Bayan ta wuce cikin gidan tasami muta nen gidan a zaune suna hira,da wanan tsohuwar matar dakuma wanan budurwar, bayan tayi sallama sun amsaata sannu tayi musu ta shige cikin d’akin ta , kamar jira sukeyi ta shige suka fara gulmar ta , wanan tsohuwa da ‘ake kira da baba Dije tafara cewa kinga yarinyar nan duk lokacin da zata fita saita dawo da leda k’atuwa , to wai ma ina iyayen ta ne? ita dai wanan budurwa mai suna Nafisa batace komai ba saboda yawan magana ko gulma bai dame taba, baba Dija data gama surutanta ta wuce d’aki .”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button