Nancy Yar Karya

Nancy ce zaune a d’aki tana sak’a da war wara , saboda ‘a yanzu ne lokacin da take buk’atar iyaye acikin al’amuran ta, ‘amma gashi tazo tayi watsi da iyayen ta , tana cikin tunani ne taji wayar ta na ruri, d’auka tayi had’i dayin sallama , cikin sa’ssanyar murya tace” Khalil nazo gida lafiya kaifa? ka koma gidanne¿”.
A kasalan ce yace” kya kyawa bazan iya bacci ba muddun bansaki a idona ba , zaro ido tayi kamar yana ganin ta cikin sigar lallashi tafara magana , kamar mai shirin yin kuka tace”dan Allah ka huta mana nifa ina cikin kwanciyar hankali, k’ara marai raicewa yayi kana yace kodai baki san zuwana ne , da sauri ta katse shi tana cewa ina ai ban isaba ‘amma please kabari sai zuwa gobe,
Babu inda ya iya haka ya hak’ura ‘amma badan yaso ba, ita ko Nancy tunani ne yayi mata yawa tarasa wanne zata kama, washe gari tayi shawarar bude account saboda ‘ajiyar kud’in ta ‘a halin yanzu tanada dubu dari hud’u saboda ranar dasukaje gidan su momyn Khalil ta zuba mata kud’i a cikin ledar dakuma ‘atamfofi da kayan makeup.”
Washe gari ta shirya bayan tagama breakfast , tad’au hand bag d’inta tanufi bank ,saboda akwai masu bayani bata sha wuyar fahimtar komi ba, da dubu hamsin tadawo gida , bayan tayi sallahar azhar ne ta kwnta a madai daiciyar katifar ta’ takuma fad’awa kogin tunani .”
Gashi Khalil yace zai zo gidan su yau ,to ita bata san yaya zatayi da rayuwar taba, wata dabara ce tafad’o mata ,shiryawa tayi ta nufi gurin kayan ta akwati k’arami ta d’auka dayake cin kaya kala goma .”
Azama tayi ta nufi gurin da ragowar kud’inta suke ta sasu a hand bag d’in ta ‘ta fito bayan ta kulle d’akin ta nufi gurin, mutanen gidan tayi musu sallama , Nafisa ce tace” Nancy kibani number ki mana ko madinga gaisawa , amma dai ba dad’e wa zakiba? Nancy tace”eh gaskiya bazanfi two weeks ba .”
Da isar ta bakin titi ta nufa ,tayi sa’ar samun mota da wuri bayan ta isa tashar motoci ne taji ana cewa saminaka ,saura mutum biyu motar ta cika ,
Bayan tabiya kud’in motar ne , tana shirin zama taji wayar ta na ruri , amsawa tayi had’e da sallama bayan sun gaisa ne yake tambayar ta ‘akan tayimai kwa tancen anguwar su, cikin yanayin damuwa tace gani a tashar mota zani garin su kakar mu ,saboda jikin ‘nata yak’i ankoma da ita gida, cikin sauri yace kina wacce tasha ne?”.
Ina tashar saminaka tabashi amsa , cemata yayi to kijira ni ganin’an zuwa yanzu , to kawai tace mai , bayan wasu lokuta saiga Khalil nan ya iso ……✍️✍️✍️.
_Afuwan????kunsan dai banida lafiya shiyasa kukaji ni shiru love yau all my fan’s_
_Mom Islam ce_
*Please share*
*Comments*
Vote✔️
????????NANCY Y’AR K’ARYA????????.
_labari mai d’auke da nishad’i tareda fad’a karwa._
_story and writing_
By
*ZAINAB HABIB*
{MOM ISLAM}.
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*
PAGE 23_24
____DA isowar sa yafara dube dube, ganin bai san motar data shiga ba, yasa shi ciro wayar shi a cikin aljihu, number ta ya danna ,yana cikin kiran ‘ne ya hango ta cikin wata mota dake kusa dashi, lokaci d’aya ida nuwan su had’e .”
Sakkowa tayi daga cikin motar jiki a sanyaye tazo kusa dashi , kana tace” barka dazuwa ,yauwwa yace” mata ‘a tak’ai ce , bayan shirun daya wanzu tsaka ninsu , Khalil ne ya katse musu shirun ta hanyar ‘ruk’o hannun ta , jin wani yanayi a tare dasu yasa ko wannen su idanun su ‘sukawo ruwa ‘alamar hawaye ,
K’ok’arin janye hannun ta tayi daga na Khalil shikuwa kamar jira yakeyi wasu hawaye masu zafi suka zubo daga kuncin sa , bazata iya jure ganin kukan saba yasata juya baya .”
Jitakeyi ‘inama ‘ace mijin tane data nuna mai soyayya marar misaltuwa , ganin tsayuwa tana neman ga gararsu ne yasa Khalil juyo da ita tana fuskan tar shi , ganin idanun shi sun koma launin ja yasata cemai kaga mota tacika ni ake jira zan tafi saimun sake had’uwa, a san yaye yace” Nancy menayi miki dahar zaki gujeni ?gashi kin d’auki k’atuwar jaka , mir mishin yak’e tayi kana tace” soyayyar ka tana cikin zuciyata karka damu bazan dad’e ba insha Allah.”
Murfin d’in motar ya bud’e kana ya d’ibo wasu ledoji manya guda biyu , mik’owa Nancy yayi , cikin farinciki ta k’ar6a tana yimai godiya sabuwa waya ‘ya mik’a mata , zaro ido tayi tana cewa”to wanan ta hannuna inyi yaya da ita? ranshi a 6ace yace”oho nidai nasiyo kuma dole kiyi using da ita, cikin zuciyar ta tafara tunanin menene using ? ganin kar asami matsala yasata cewa to nagode Allah yak’ara bud’i .”
Amin yace”kana yace ” please karki dad’e bata iya sake kallon shiba ta shige mota “.
Khalil sai da yaga tashin su sanan ya shiga motar shi jiki a sanyaye , tana cikin mota yakira ta yakai sau goma duk saboda yaji muryar ta , bayan ta sauka ne ta ‘tari mai adai daita yakai ta ‘anguwar su ,bayan yafad’a mata kud’in tahau suka wuce , suna cikin tafiya ne wani yaro mai suna Ahmad lokacin tana k’auye shine abokin wasan ta , yana ganin ta yafara cewa” oyoyo DUDUWA tadawo .”
Runtse idanun ta tayi kana tafara cewa wallahi dana sani daban dawo wanan k’auyen ba kowa yahau samaka ido , a haka dai tak’arasa zuwa gida “.
Da shigar ta suka had’a ido da umma , wani farinciki ne ya ziyarci zuciyar Nancy , dagudu ta rungume Umma tana cewa oyoyo umma na , k’arasawa d’aki sukayi daganan , suka shiga hirar yaushe gamo.”
Nancy ce take cewa Umma nikam ina Dillaliya ne? nisawa umma tayi kana tace “Allah yayiwa dillaliya rasuwa!!!.
Cikin yanayin kid’ima Duduwa tace” yaushe kenan umma? bayan umma ta share hawayen da suka zubo mata tace” bayan kun dawo babu jimawa tafara ciwo sai dai tace “min zaki kasance cikin kwanciyar hankali a gidan da kike , Duduwa tayi kuka sosai , umma batayi yun k’urin hanata kukan ba , sai da tayi mai ‘isar ta kana tayi shiru.”
Bayan sunyi sallah ne taci farfesun da umma tayi mata , ta d’auko kayan tsarabar da tazo dasu , atamfofi ne guda biyar dakuma takalma biyu da hijab ,umma tayi murna sosai harda hawaye, kayan da Khalil ya siya mata ta d’auko dan batasan meye a ciki ba .”
Madara ce ta gwan gwani guda biyu manya sai millo dakuma biscuit da butter babbar roba , d’ayar ledar kuma kayan makeup ne dasu English wear riga da skirt dogo har k’asa sai riguna musu tsada sai kuma atamfa guda biyu.”
Mik’awa umma tayi ,Umma na ganin haka tace” waye yabaki wanan ?”….✍️✍️✍️.
_Mom Islam ce_
*Please share????*
*Comments*
Vote✔️
????????NANCY Y’AR K’ARYA????????.
_labari mai d’auke da nishad’i tareda fad’a karwa._
_story and writing_
By
*ZAINAB HABIB*
{MOM ISLAM}.
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*
PAGE 25_26
____Bayan taja gwauron nunfashi tace” wani d’an wahala ne wallahi , zaro ido Umma tayi kana tace” kul Duduwa kar in sakejin kin cewa wani d’an wahala, zum6uro baki tayi alamar shagwa6a tace” Umma wallahi shiya sa banason dawo wa k’auyen ‘nan ,saboda wanan sunan , baki a sake Umma tace” au zaki canza sunan ‘ne gyd’a kai tayi tace” ai nariga na sauya daga yanzu sunana Nancy, salati Umma tafara tace” zuwa barikin abin da ya koyar dake kenan , sawa kanki sunan arna ko .”
Dariya tayi mai sauti kana ta mik’e bata bawa Umma ‘amsa ba , washe gari Umma ta ‘tashi domin d’ora d’uma men tuwon jiya , Nancy na fitowa tace” gaskiya Umma wanan tuwon akai shi gidan su Delu ,Umma bata kula taba sai ma k’ara had’a wuta da takeyi , ganin haka yasa Nancy ficewa waje , sai da tafita ta ‘tuna da cewar ai tabar wayar ta ‘a gida , k’in komawa tayi saboda yunwa takeji ,tana son zuwa siyo risho .”