HAUSA NOVELNancy Yar Karya

Nancy Yar Karya

Ahmad ne yashigo yana sanye da wata kod’a d’iyar ‘riga , Umma na ganin shi zuwa d’auko wayar , kasa receive dukayi dak’yar sukayi sa’a suka danna , jin wata murya yasa Ahmad cewa heeloo nine ahmadu d’an uwan Duduwa, zaro ido Khalil yayi kana yace “ban gane ba waye Duduwar?” Ahmad ne yace”me salular nan mana.”

 

Khalil ne ya kashe wayar shi kana yafara tunanin kodai Nancy ta yarda wayar tane?”yanata zancen zuci “.

 

Da shigowar ta ‘ta hango Umma da ‘Ahmad gakuma waya ‘a hanun Ahmad , zaro ido tayi tafara ruwan masifa , zuwa d’akin girkin su tayi ta ‘ajiye rishon, kana ta fito tacigaba da masifa , itadai Umma batace komai ba , shikuwa Ahmadudu fecewa yayi yana tu nanin kar yaci na jaki, duba wayar tata ‘tayi ganin sunan Kahlil yasa ta zaro ido, tafara salati tana sharce gumin da yafara bara zanar jik’a mata fuska.”

 

Tana cikin k’ara duba number shine sai ga kira nan ya shigo , sauke gwauron nun fashi tayi , kana tayi amsa wayar, daga can 6an garen nashi yace” Aslamu alaikum , jin shiru yasa shi mai maita sallamar , sai saita muryar ta tayi kana tace” Khalil yakake ? wani farinciki yaji dama yayi missing d’in muryar ta , bai cemata wani ya ‘amsa kiran shiba ,haka ita ma bata fara yimai maganar ba ,bayan sun gama wayar ne Umma tace” shid’in wanan daga ina kika samo shi ?”cewa tayi Umma ni wallahi yunwa nakeji, kibari ‘idan naci abinci zanyi miki bayani , badan Umma taso hakan ba ,ta k’yaleta .”

 

Bayan tagama girkin ‘ne taci ta k’oshi Umma takuma tambayar ta akan wanan saurayin wato Khalil , ajiye wayar dake hanun ta tayi kana tafara bawa Umma labarin abin da yafaru tsakanin su tun farkon had’uwar su sai dai bata bawa Umma labarin rasuwar Hajiya ba dakuma d’umbin kud’in da ‘aka bata har koma warta gidan haya ,bata fad’awa Umma ba”.

 

Hak’ik’a Umma ta yaba da Kahlil sosai sai dai tana tunanin yaza’ayi Khalil yaso yar talakawa bayan shid’in d’an masu hali ne .”

Nancy ce kwace a cinyayyar katifar Umma tana kallo a wayar ta , jin k’arar massage ya sata kashe kallon tahau duba sak’onni ganin wasu mahauka tan kud’i da Khalil ya turo mata yasata zare ido 50k tagani , wani tsalle ta buga kana tace kai Khalil dole in aure ka kodan wanan 6arin nerar dakakeyi min , amma yanzu wasan yafara ,dole in samo mafita ,cikin kwana d’aya.”

 

Yau satin Nancy d’aya ‘a village d’in su , bayan tayi wanka ta had’a musu abinci ,tazo kusa da Umma ta zauna , ganin haka Umma tace” to yau kuma nikike jin ‘nauyin gayawa damuwar ki ? bayan ta k’a k’alo hawayen k’arya tace “Umma dama dama cikin k’osawa Umma tace” dama me?” Nancy ce tace”dama Umma so nakeyi mu tafi tare , zaro ido Umma tayi kana tace meyasa kikeson k’ir k’iro abin da bazai yiyu ba ? k’ara share hawaye tayi takuma cewa , wallahi Umma hardai bakizo mun tafi ba to nima bazan koma ba …..✍️✍️✍️.

 

_Mom Islam ce_

*Please share*????
*Comments*
Vote✔️
????????NANCY Y’AR K’ARYA????????.

_labari mai d’auke da nishad’i tareda fad’a karwa._

_story and writing_

By

*ZAINAB HABIB*
{MOM ISLAM}

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*

PAGE 27_28

___Jikin Umma ne yayi sanyi tana tunanin to idan tabi Duduwa ita gurin wa zata zauna , kamar Nancy tasan tunanin Umma, matsowa tayi ta kama hanun Umma kana tace” indai gurin zama ne Umma baki da matsala , jikin Umma babu k’wari ta ‘amince da bin ‘Nancy ABUJA , aikuwa Nancy najin haka ta rungume Umma tana murna , mik’ewa tayi ta fice zuwa d’akin ta nada ta kunna wak’a jirgin so ,ta Umar m Sharif , tadinga tik’ar ‘rawa , tsgai ta rawar tayi kana tafara maga tana cewa, ai tunda Umma tace zata bini angama saboda ‘auran Khalil babu fashi muddin iyayen Khalil suka san ‘ni y’ar talakawa ce to na shiga uku, amma yanzu tunda Umma ta ‘amince no problem zan san inda zanyi , tunda inada kud’i Kuma zan d’inga tatso Khalil ,tana cikin maganar ne taji Umma na k’awala mata kira ,ficewa tayi a guje taje kiran Umma”.

 

Umma ce ta dubi Nancy tace ki fad’amin gaskiya , mene ne dalilinki nason inbiki?”zaro ido Nancy tayi a zuciyar ta tana cewa ‘ai nad’auka mun wuce gurin , Umma ce ta katse mata tunani da sabuwar tambayar da takuma jefo mata, ganin bata da mafi ta yasata fara kuka tana bawa Umma hak’uri akan abubuwan da suka faru bata fad’a mata ba ta bata labarin mutuwar Hajiya dakuma kudin da haliya tace abata , dakuma ‘alkairin Khalil da momyn shi.”

 

Salati Umma tayi tace” to yanzu a ina kike zaune ? Nancy ce tace” gidan haya nakama, shine naga zaifi kyau tuwa mukoma tare , Umma tayi na’am da shawarar Nancy, dan haka suka fara had’a kaya dan barin gari .”

 

Washe gari Nancy ta kwashi kayan da tasiyowa Umma dakuma wanda momyn Khalil ta bata takai gurin d’inki kayan kala bakwai ne tace” ayiwa umman ta d’inkin zamani.”

 

Nancy ce zaune tana tinanin yanzu ta gama da fannin Umma saura, na Khalil , saboda idan har ta dawo to zai ze zo, gai da maman ta dan haka dole ta nemi mafita , number mutumin da yabata hayar gidan da take ciki , ringing d’aya ya d’aga , daga can 6an garen yace” dawa nake magana ? Nancy ce tace “nice wace take haya ‘a gidanka Nancy, washe baki yayi kana yace” lafiya dai ko?eh lafiya tace” mai ,can kuma ta nisa tace dama so nakeyi ka samar min gida mai kyau tsararre me tails , washe baki yayi kana yace “akwai gidaje sosai , kinga inada wani a WUSE 2 shi price d’insa dubu d’ari biyar ne ,akwai wani a A Y A shi kuma price d’insa dubu d’ari uku , sanan akwai wani a WUSE 2 shi kuma price d’insa dubu d’ari buyu da hamsin .”

 

Tunanin ragowar kud’in ta tayi yanzu sau ran dubu d’ari hud’u , cemai tayi ina son ‘na WUSE 2 d’in amma kasan banfi wata biyu a gidan kaba, zaka bani ragowar kud’in , mutumin ne yace” karki damu shi na WUSE 2 d’in kibada dubu d’ari biyu ,inyaso sai ‘in cika da ragowar kud’in ki godiya tayi mai suka yi sallama .”

 

Washe gari Nancy ta kar6o kayan Umma’a gurin d’inki ,Umma tayi farinciki sosai akuma sanya mata ‘albarka, Nancy ta hana Umma d’aukar kayan ta saboda bata san Umma tasa Khalil ya ganota wasu ,sababbin hijab guda uku ,tabawa Umma, sun gama had’a kayan da zasu buk’ata sabo da washe gari zasu koma ‘ABUJA…..✍️✍️✍️.

 

_Mom Islam_

*Please share*????
*Comments*
Vote✔️
????????NANCY YAR KARYA????????

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*

PAGE 29_30

Misalin k’arfe 8am su ‘Umma sun gama shiri Nancy ce tace”wa Umma jiya kince zaki shiga mak’ota kuyi sallama , jikin Umma a sanyaye tace” eh walahi barin zo inshiga tunda kince karfe tara zamu tafi, mik’ewa Umma tayi kana ta janyo sabon hijab d’in da Nancy taba ta sanyawa tayi a jikin ta kana ta fice zuwa gidan dake mak’ota ka da nasu , da sallama ta shiga gidan matar gidan mai suna inna tace” lafiya uwar Duduwa naganki da sanyin safiyar nan? Umma ce ta nemi kujerar da tagani a gefen ta ‘ta zaune ,bayan sun gaisa ne tace “wallahi zamu wuce Abuja ne , cikin tuhuma inna tace”zakije gurin su illu kenen ?eh umma tace” a tak’ai ce saboda batason kowa yasan abinda suka shirya ita da Nancy, saboda idan har mutane suka san ga dalilin tafiyar su to lallai babu makawa sai yazamo gutsuri tsoma ‘shiyasa ta ‘amsawa inna tambayar ta .”

 

Bayan tafito daga gidan inna bata gida ta koma suka fito domin tafiya tashar mota , da zuwan su sukayi sa’ar samun motar Abuja , Nancy ce tabiya kud’in motar , suna cikin tafiya ne sai ga kiran Khalil nan cikin farinciki Nancy ta d’auka tana cewa ‘al bishirinka cikin k’aguwa Khalil yace”goro sai da tad’au lokaci sanan tace” ina hanya insha Allah wani tsalle ya buga kana yace “yau akwai surprise me girma ‘amma burina inganki kin iso lafiya ,sallama sukayi da Khalil , juyawar dazatayi taga umma nata sharar bacci tace” tabb umma tun yanzu bacci , game tafara ‘a wayar ta batayi nisa ba saiga kiran Khalil yakuma shigowa d’agawa tayi tana cewa munkusa fa big boy wata uwar dariya yasa sai kuma Nancy tafara zargin ko tayi turancin ba dai_dai bane yasa yake dariya , kawar da tunanin ta tayi kana tace”meka tanadar min idan ‘na iso ?kamar jira yakeyi yace”kya kyawa kina isowa zan zo dagudu nayi hugging d’inki, rufe ido tayi can kuma tafara tunanin menene hugging? ” tunawa tayi ai tanajin wanan kalmar a gurin ssu Anty humaira suna cewa runguma , Khalil jin tayi shiru ya katse shirun da cewa yanzu dai nabar komai saikin zo , to kawai tace” dan wanan kalmar tanada girma .”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button