Nancy Yar Karya

Allah ya zubawa Suhailat tsoron bulala haka ta fara tura ‘abincin tana tsayawa zai ce saita ci kuma yace” bayason ,nishin kuka haka taci abinci mai yawa da k’ayar take tafiya rasa wane d’aki zata shiga tayi ,parlor ta koma ta kwanta ‘a kujera .
Bayan anyi sallahar la’asar ne kowa na parlor dady ne yace ”Khalil ya kasuwa ?alhamdulilah yace ”daganan dady ‘yace ”banyi muku bayanin Suhailat ba ko ?amma ke momyn Khalil ai kinsanta saidai kin manta da ita, momy ce tace ”eh to ina buk’atar tuni ,dady ne yace ”kin mance brother na ABDURRAHMAN ?”shiru tayi tana kallon Suhailat can kuma tace ”yanzu itace ta zamo haka tabb lallai girman d’an mutum babu wuya ,dady ne yacewa Khalil to ga Suhailat nan tunda taganka ‘a photo tace”saita biyoni zatazo ta ganka ,humaid ne yace ”to nagode ,murmishi take jifanshi dashi amma ko kawota ‘a gabanshi baiyi ba .
Washe gari ta tashi da wani matsanancin ciwon kai ,momy ce tacewa Khalil yazo ya kaita hospital cikin fushi ya shigo d’akin da yazamo nata ‘yace ”inkinyi ra’ayi zaki ‘iya tashi munafuka kawai ,dariya ma yabata duk da ciwon kan daya matsa mata bai hanata darawa ba ,k’ufula yakuma yi ya zo kusada ita ya kaimata rank’washi a kanta jin zafin rank’washin yasata kurma ihu ,da sauri momy ta fito daga bedroom d’inta ta shigo d’akin ,ganin Khalil a tsaye yasa momy cemai to maiya faru naji kina ihu ,cikin shagwa6a tace ”momy nakasa tashi ne…..✍️✍️.
Mom Islam ce ????
Please share????
[31/01, 6:33 pm] Mom Islam ce????: ????????NANCY YAR KARYA ????????.
_Mom Islam tadawo????♀️????♀️????♀️????♀️_.
story and writing
By
ZAINAB HABIB
{Mom Islam
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Page 33 & 34
,,,,,,,,,,Kama mata momy tayi ta mik’e Khalil na jingine da jikin bango yana kallon su ,jin dady ‘yakira momy ‘yasata tafiya tabarsu , Khairat ce tace please my lovely brother help me dan Allah ,a razane ya d’ago kai yana yimata kallon kin rainani ma ,yana shirin ficewa ta rik’o mai hannu tana rok’onshi akan ya d’auketa ya kaita mota , zaro ido yayi ,yace ”ke bakida tarbiya ne¿ ko bakisan haramun ba? d’aga kafad’a tayi tace ”ni aganina maiya had’a d’aukata dakuma haramun ?”jin iskancin ‘nata yayi over yasashi ficewa ,da gudu Suhailat ta mik’e tana kiran sunanshi ,lokacin da tafito harabar gidan ta hangoshi ,harya shige mota ,k’wala ihu tayi tace ”momyy, cikin azama momy tafito har tana shirin kifawa ,kafin momy tace maiyyafaru har Khalil yaja motarshi yayi gaba ,zama suhailat ‘tayi tana kuka ,tayarwa da momy hankali takeson yi ,momy ce tace ”to maiya kuma had’aki da yayan ‘naki? cikin shagwa6a tace ”momy kaina kamar zai fashe walhi ,yakaini hospital yak’i shine ya gudu, momy ce ta juya zuwa d’auko wayar ta number shi ta duba ta danna kira ,ring d’aya ya d’aga momy ce tace ”yanzu ka kyauta kenan ?da katafi kabarta tana famada ciwon kai ko¿”Khalil cikin girmamawa yace ”afuwan momy na banyi nisa ba barinzo na d’auketa ,albarka momy ta Sanya mai daganan momy tace ”tashiga ta d’auko hijab d’inta ,to kwai tace ”le k’owa tayi taga momy bata parlor ,hakan yabata damar sanya riga pink color da wando blue sun d’an kamata sosai tasa dogon hijab har k’asa ,tasami k’aramin mayafi ta d’aura ‘a kanta ,fitowa tayi tacewa momy natafi ,Allah ya kiyaye momy tayi mata ,dagan ta fice tayi waje, tana bud’e gate ta hango shi a cikin mota yana waya yana dariya ….
Cikin azama ta iso jikin motar tana nocking bud’e mata yayi da hannu d’aya ,d’ayan kuma ya rik’e waya , shiga tayi ta zauna ‘a back side tanason jin ko dawa yakeyin hira ,tana kuma tunanin karya ce yafasa kaita inda takeson zuwa ,gashidai ba ko ina tasani ba ,kasancewar ‘rayuwar Nigeria ba damuwarta bace, jitayi yace ”kya_kyawa burina bai wuce ingani ace yau nine angonki ba ,dariya suka sa itako Suhailat tunda taji sunan daya kira zuciuarta tafara tafar fasa ,saboda tanada zafin kishi ,bud’e mirfin motar tayi ta fice ,wata shu’umar dariya Khalil yasa saboda dayaso yaje hira gurin ‘Nancy da ita kuma ya kulleta ‘a mota ,fitowa yayi daga cikin motar da keys a hannunshi yana waya yana cilla keys sama ,momy ce tafito tanason aikan driver ta ganshi ,murmishi tayi tace ”yaron kirki kaida wa kake waya ¿cikin fara’a yace ”momy nida y’arki ne fa ,fatan alkairi tayi musu daganan tashige ciki , 6angaren Suhailat kuwa kuka takeyi tana neman mafita saboda bazata iya bari wata mace ta ‘auri Khalil ba muddun tana raye ,dabara ce ta fad’o mata ,lokaci d’aya tasa dariya tace ”good ,number momynta ta lalubo kira takeyi amma ba’a d’agaba ,a karo na biyu ne momyn ta d’aga hello tace ”Suhy how a you? fine momy _momy akwai problems fa ,gyara zama momyn tayi tace ”bangane ba dama bakince zakije kiga yaron d’an uwan dadynku ba , eh tace ”daganan tafara kuka…..
Momy ce tace ”to kigayamin mana kinsan kukanki yana iya rusa farincikin mu ?,share hawayenta tayi tace ”momy inason Khalil momy da taji dad’in faruwar hakan tace ” to yanzu shi yasani ,a’a tace , shi wata ma yakeso fa ,momyn ce tace mata to ki kwantar da hankalinki ko ta halin yaya sai Khalil yazamo mijinki ,wani farinciki ne ya lulu6e Suhailat tafara yiwa momyn ‘nata kirari tana cewa kai kinyi a rayuwa momy ina alfahari dake godiya mai tarin yawa ,dagan sukayi sallama.
*LONDON*
Momy Suhailat ce kwance a ciyar dadyn Suhailat ,tana shafa mai kai cikin sigar wayewa dakuma k’warewa ,tsawa tayi dadyn ‘ne ya taso da kanshi yace what happen my only ?”cikin sigar jan hankali tafara kukan kissa ,janyota yayi ya mik’e yace ”to nikuma yau kike 6oyewa damuwarki ?shafo kanshi tayi tace ”mu muna nan muna farinciki Suhailat na cikin matsala !!dady jin kalamar yayi babu dad’i saboda babu abinda Suhailat zata nema ‘a duniyar nan baiyi mata shiba saidai bayan ranshi ,momy ce ta kwashe duk inda sukayi da Suhailat ta gayawa dady ,dady ne yace ”ina raye?tabb ,barin kira d’an uwan ‘nawa muyi magana , number dadyn Khalil ya kirawo ring d’aya dady ‘ya d’auka ,gaisawa sukayi cikin girmama juna da bisani kuma dadyn Suhailat yace ”dama inason zamuyi wata magana ne OK ina jinka dadyn Suhailat ne yace ”inababu damuwa d’an uwana mai zai hana mu had’a ‘zumunci a tsakanin yaranmu saboda zumuncin mu yayi k’arfi ,farinciki ne ya lulu6e dadyn Khalil yace ”aikwa danafi kowa farinciki sosai ma ,
Daganan sukayi maganar tsayar da rana two months sukasa bikin saboda tsaro.”
Washe gari ne dadyn Khalil ya kirawo shi bayan yazo yake cemai abin farinciki fa yasamu ,Khalil ne ya dubi fuskar dady kamar anyimai albishir da shiga ‘aljanna yace ”dady wani abinne yafaru ¿momy dake gefe tace ”oh kanata jamai rai koni ‘in gayamai ne ?”cikin zolaya momy take maganar ,dady kuwa sai fara’a yakeyi ,yadubi Khalil yace ”dama mun yanke shawarar had’aka ‘aure da Suhailat ,firgici tashin hankali duka suka dirar mai lokaci d’aya ,momy na karantar yanayinshi amma bata nunawa dady ba ‘dady na gama fad’a ya tashi domin amsa kira ‘a waya ,Khalil ne yaje ya rik’e k’afar momy ,idanunshi sunyi ja lokaci guda ,momy ce tace ”kayi hak’uri da za6in dadynka dan Allah ,Khalil ne yace ”kema momy bazakice komai ba ,dady fa ko tambayata inada wacce nakeso baiyi ba ya zartar da hukunci ,momy da tausayin Khalil ya kamata ,tace ”to yana tunanin ya isa da kaine shiyasa ‘amma ka daure kayimai biyayya ,mik’ewa yayi jiki babu k’wari ya koma d’akinshi ya kwanta kallon sama yakeyi amma zuciyar shi na kitsamai kodai Suhailat ce ta had’a wanan lamarin cije Lip’s d’inshi yayi yace”to walhi indai kuwa hakane saitayi dana sani a rayuwarta .”