HAUSA NOVEL

NIGERIA KO NIGER Complete Hausa Novel

rayuwar garin bama tayiwa su aliyu dadi fiye da tunanin mai karatu daan haka suka shantake sukayi zamarsu acan sbd sun ajiye ayki sai bayan shekara daya wanda lokacin yayi daidai da kammala makarantar su husna…

saida suka shafe wajen wata 2 da sati 2 kana suka dawo maiduguri cike da kewar kakar tasu kasancewar ita bata cika zuwa mai duguri ba saida ita aje mata kuma idan kaganta kamar ba itace ta ajiye jibga jibgan jikoki kamar su musa ba…

sadeeya da husna an shiga ss 3 karatu suke babu kama hannun yaro sbd kusantowar waec nasu  dan haka dole suka natsu suka maida hankali abinsu…

bangarensu aminullah kowa uwarsa taja masa kunne kan su fita shirgin baa idan baso suke yace su farayiwa kansu komai ba sannan yazare hannunsa akansu ba sbd sun lura indai kan yayan goal ne to zai iya batawa da kowa…

dole suka zubawa sarautar allah ido amma ko duk suna da mugun kudurinsu akan su koda kuwa ba yanxu bane dan haka yanxu rayuwar cikin gidan anayinsa kadaran kadahan…

ko da su aliyu suka dawo suka tadda wannan chanjin yayi wa aliyu dadi sbd shi bamai son kananun maganganu bane dan haka yake jan yan uwansa a jiki wanda haka yasa sadam yasake jiki da yayannasa amma ko har yanxu bai manta komai ba sbd akoi shi da dan banzan riko kamar me…

haka rayuwa ke tafiya da dadi babu dadi harsu husna suka kammala secondary school nasu kuma a lokacin suke da 16yrs inda duk wanda yagansu sai yayi tunanin irin yan 18yrs dinnan ne sbd cikar dasuka kara da kuma girman jiki…

Alokacinne suka tada ballin sufa sai sunyi karatun jami’a baa da shehu sam ba haka suka so ba sbd sunso ace saisun cika kudirinsu kan yayansu amma maaa tace sam ba wanda zai tilastawa jikokinta yin abinda bashine ra’ayinsu ba…!

dan haka dole suka hakura aka tambayesu makarantar dasuke so aykuwa cike da zumudi sadeeya tace DUBAI  suke so suyi karatunsu acan…

nan fa baa yadire kan sam baisan da zancen ba…wannan karan kam husna har kuka tayi inda itama tace nan take so…

baa yacika da mmk sanin cewa husna bamai yin magana bace akan duk abinda ya yanke akansu amma sai yaga sabanin haka nanma dai hankalinsa bai kwanta ba ya kira yynsa ya fada masa halinda ake ciki…

wai aykuwa gwanda ma baa domin ko shehu yace sam ba acikin zuri’arsu baa sbd shi bay taba ganin inda mata na gidan sarauta ke fitayin karatu har wata uwa duniya ba dan haka baza’a fara akan tasa zuri’arba!

momma kam dama tunda tanasu mgn na farko taga yadda suka kafe saisun tafi ta zuwa sarautar allah ido tasan abu ne mai wuya…

aliyu ma saida suka saka sa agaba kan lallai sai yaje yataya su rokon baa yabarsu suje wannan kasar aykuwa shima dayaje baa ya fatattakosa wanda hakan yasa shi basu hakuri kawai su hakura da zancen dubai su nemo wani makaranta wanda sukasan cikin nigeria yake…

husna taso karaya ganin yadda kowa ya bijire amma kuma deeya takara zugeta kan muddin ta hakura tasan itama ba za’ayi ba sbd burinta kawai taganta a kasar dubai tana karatu tun tana karama…tasan ba barinta za’ayi ba dan haka dole sukayi ta nacinsu tare amma fur baa yashafa ma idonsa toka yace baisan zancenba…

duk wainar da ake toyawa maa batasan da zancenba sbd babu wanda ya tunkareta da zancen…nan kou deeya ta kwadawa maa kira da safiyar lilllahi…!

IDAN NAGA KUNA COMMENT YADDA YAKAMATA KAM ZAN KARA YAWAN TYPING IDAN BAKWAYI KUMA GASKIYA ZAN RAGE…!

TEAM NIGER
TEAM NIGERIA

TEAM BUZAYEN AGADEZ
TEAM KANURIN BORNO

TEAM UMMIEN2018

*vote*
*comment*
*share*
*follow@ummie2018*
[9/8, 2:28 AM] ????oum muntaz????????????:     *NIGERIA KO NIGER…?*
(wacece bora)

*©HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*_( home of peaces, joint of entertainment to educate and enlight  our readers)_*

*wattpad:UMMIE2018*
*whatsapp number:09076427357*

page 13

Jin abinda ke faruwa kam maa tace ma sadeeya sam itama batasan zance ba!

husna ma saida takirata sunaata mata kuka da kyar da sidin goshi suka samu maa ta yadda kan ita zata tsaya masu a barsu bayan sun mata alkawarin kula da mutuncinsu dana zuri’arsu dakuma al’adarsu…

hakan yasa ta amincewa gakuma takwararta husna ma naso inda ta hau daram ta zauna kan babu wanda ya isa ya hana jikokinta zuwa inda suke so !

duk tsiyar dasuke shukawa babu wanda yake da labari sbd an gargadesu ko da wasa kar maa taji labari sanin dasukayi cewa itakam maa kullum bayan jikokinta takebi…!

ballanta kuma wannan karan harda mai sunarta a cikin batun ay dole tabi bayansu!

meeting tace ma shehu a hada mata na family da jikokinta inda cikin kwana 1 duk sunxo garin bama cikin masaurautarsu kowa ya hallara!

taro musa yabude da add’a inda aka danyi hira tsakaninsu sbd sada zumunci anan kuma tace duk da mai matsala yafada sbd haka takeyi dama bayan angama kowa zai fadi matsalarsa da izinin allah zata magance masu…

dan haka dasukaji kiranta ma babu wanda yakawo kan su husna tayi taron !

masu matsala nata fada tun daga kan manya inda musa ma yakawo zancensa kan deeya yanason aurenta …harsu mubaraq duk suka fada mata abinda suke so baa yaki masu…

anan taji kalar ta’asar da baa keyi tamasu nasiha sosai kan kar ata dalilinsa kan iyalansa ya rabe dan haka yayi kokari wajen ganin ya kwatanta adalci tsakanin matansa dakuma yayansa…

har aka gangaro kansu husna tashin farko sadeeya ce tafara magana inda ta kara zanzaro mara zance kan makarantarsu…

maa ta nuna kamar batasan da zance ba sai yanxu nanko tace su sha kuruminsu ita zata tsaya masu su cika burinsu…

hakuri tabawa musa kan ya hakura idan sun kammala makaranta sai a daura masu aure dukda ba haka yaso ba amna ya hakura…

jin haka dasu baa sukayi dole suka hakura badan sun so ba sbd su a ganinsu karatun mace a waje shike lalata yarinya  (nikam nace koma mai nene sai yarinya taso rayuwarta zai baci koda kuwa cikin karuwan bangon duniya aka kaita)

haka dai taro ya watse kowa cikin farin ciki da walwala saida suka kwana biyu kana suka garzayo cikin mai duguri!

nan ko cikin kankanin lokaci aka sama masu admission abunku ga yayan manya  cikin wata daya komai ya kanmala kuma alokacin an ma yaran duk abinda suke so amma fa har yanxu baa bai masu kalar wanda suke so ba…

suko ko hakan ma dai sunji tunda dai sun rage hanya(  matsalar su kishin yan uwansu ne ke dawayniya dasu wanda shedan ke kara  rura masu watar abin cikin zcyrsu baa kuma ke bada gudummawa)

a lokacin yayi daidai da tafiyarsu aliyu dan haka aka wuce dasu kasar dubai inda suke karantar computer science baki dayansu kuma ana kawo masu ziyara akai akai hatta da su aliyu suna kawo masu ziyara kuma har yanxu basusan cewa tare da wacce inoussa zai aura suke aji daya ba…

gakuma masu tsaron lafiyarsu da aka zuba masu amma sukace sunki sbd kar ana masu kallan masu kudi ko wani abu amma baa yace wannan kam basu isa ba sbd akoi masu kawo mawa baa da ahalinsa hari wanda yasan duk wani shige da ficen gidansa akan idanunsu yake

dan haka bazaiyi kasadar barin yyansa aje a salwantar masa dasu ba hakanne yasaka suke binsu a baya wanda mutane da dama basusan hakan ba a shekararsu ta sha bakwai suka fara halartar university kuma dama shekaru uku akeyi a kammala makarantar…

a halin yanxu suna cikin shekaru na 20 ne a duniya”

bangarensu aliyu kam an zama manya manyan samari zaratan sojoji masu ayki tskaninsu da allah babu kama  hannun yaro saidai yafi inoussa matsayi a wajen ayki sabida shi inoussa a matsayin captain yake!

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button