HAUSA NOVEL

NIGERIA KO NIGER Complete Hausa Novel

ganin ta lumshe idanunta yasaka murja kara kallonta dakyau a tunaninta batasan tana kallon ta ba…

cikin zazzakar muryarta da sarautarta ta bude karamin bakinta wanda yake kalar marun inda tace murja kinsan bana son kallo kou…?

cikin daburcewar murja ta sunkuyar dakai kasa tace amin afuwa uwar dakina nayi kuskure bazan kuma ba takare maganar cikin dardar…

sanin datayi cewa muddin kana son ka bata da fadimatou a lokaci daya to kawai ka kureta da ido kana kallonta wanda hakan sam ita bata so ko kadan…

batare da tayi magana ba ta mata nuni da hannun ta daya sha jan lalle…fahimtar abinda take nufi yasa murja kwashe kwamutsan komai na abinci wajen tayi waje dasu…

ajiyar mai nauyi tasauke a rayuwarta zaka mata komai ta iya jurewa amma banda kallo wanda batasan dalilin hakan ba…

yanxu tanajin yunwar amma kallonta da murja tayi yasa taji komai tafice mata akai…mikewa tayi ta cire hijap da zanin datayi sallah dashi ta nade su ta adana sabida dasu takeyin sallarta wanda hakan nada kyau…

lafiyar bed nata tabi domin tadan huta nan wayarta tafara kukan neman agaji…jin karar da wyar keyi yasakata sakin lallausar murmushin wanda hakan yasani suman tsaye domin kou har dimples na saida ya lotsa…

my wife……

《》《》《》《》《》

TEAM NIGER
TEAM NIGERIA

TEAM BUZAYEN AGADEZ
TEAM KANURIN BORNO

TEAM UMMIEN2018

*vote*
*comment*
*share*
*follow@ummie2018*
[9/8, 2:29 AM] ????oum muntaz????????????:     *NIGERIA KO NIGER…?*
(wacece bora)

*©HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*_( home of peaces, joint of entertainment to educate and enlight  our readers)_*

*wattpad:UMMIE2018*
*whatsapp number:09076427357*

page 15

oh masu karatu wato cak na tsaya domin gano maku wannan genus data matukar startled dina tsabagen kyawunta ya wuce misali…

abin mmk ma shine a tunanina bazan kara cin karo da kyakkyawar halitta kamar fadimatou ba amma ganin da nayiwa husna saikuma na fara kwakkwanto domin kuwa ma kaina ya rabu kashi biyu dayana kokarin rinjayata zuwa husna daya kuma na rinjayata zuwa ga fadimatou…

fara ce tas ta gaban misali,gata da dara daran idanuwa manya masu matukar daukar hankali masu kalar blue a cikin kwayar idanunta nata…

saikuma siririn hancinta mai kyawun gaske and bakinta daya kasance light pink dan karami dashi dadin……

kirar jikinta ne ma abin kallo dakuma al’ajabi abin dae sai wanda yagani kawai…!!

cire kayanta tayi tazaman tumbur kamin ta shiga wanka wannan dabi’ar husna ce…toilet ta wuce ta sillo wankarta daganan ta dauro alwala kana tafito da wanu guntun towel nata…

saida ta goge jikinta tas as usuall ta tsane ruwan jikinta tabi jikinnata da lafiyayyen humra na asalin barebari mai mugun kamshi na gaske…

tasaka duk inner wears dayakamata amma banda bz sbd sam bata sawa a cikin gida hakan na matukar damunta warai da gaske…

zura wata doguwar rigarta tayi kana ta zumbula hijap nata ta tada sallah… tana cikin sallah deeya ta shigo cikin wani half gown wanda dashi da babu duk uwar ubansu daya iya rabin cinyarta ya tsaya wanda yayi matukar ansar chaculate skin nata gata komai dam dam but it’s not compare to husna…!

waje tazamu ta zauna a gefen bed itama tana tashim kamshi exactly gleaning to husna’s fragrance…

she’s busy charting extent husna ta idar bata sani ba… batare da tayi mawa deeya magana ba ta mike ta linke sallaya da hijab nata kana ta sami waje ta zauna a gefenta ta dakko phone nata ta latso ma momma kira…

aykuwa ringing na 4 momma takama cike da dokin yayannata tun kamin tayi magana husna tayi magana cike da shagwaba tace”momma nayi kewarki sosai wallahy”

daga can dake tare da baa dakuma aliyu daya shigo ya iskesu suna dan taba hira shima yasamu waje ya zauna har zai fita amma dayaji kiran daga kannensa ne yasashi komawa wajen zamansa…

momma kuma dama tasa wayar a handsfree dan haka duk sunajinta…

cikin murmushi momma tace”nima nayi kewarki diyata fatan kuna lafiya…?”

“lafiyarmu qlaou momma saidae kewarku ce ta mana yawa allah”takare maganar cikin wannan shawabartata ta yan fari…

baa ne yayi dariya daga inda yake ya daga murya yace “ja’iren yara kawae ay da mun hanaku tafiya kuka ki harda su kukanku kou”

jin muryar baa yasa deeya dake chart nata mikewa zaune ta wafto wayar”baa nikam allah momma bata sona”

cikin dariya baa yace”amma gaskiya momma bata kyauta ba mai ta miki har haka …?”

“baa kana gani fa suke waya tun dazu amma batace ina nake bawai…?”

haka dai suka saka iyayen nasu sai shiririta suke masu kamar wasu kananun yara aliyu dake gefe ko dago kai bayyi ba  ballanta na yace kanzil…

saida suka gama kana sukayi sallama wanda kullum dama saisun kirata a waya sun gaysa abinsu…

deeya ce tamike tafito parlon nasu cikin wannan shigartata

umartar yar aykinsu tayi kan ta kawo masu lunch inda tasamu wajen kan rug dake malale a cikin parlon busy chart wanda itakam bata da wata damuwa sai charting always…

saida aka kawo masu komai kana husna tafito tasamu waje tazauna tana dan tsakura kadan kadan sbd itakam sam batason cin abinci sai kayan ruwa ruwa…

anan inda suke zaune wayar husna tayi kara alamun sako ne yashigo wayartata nan naga tasake wani lallausan murmushi dayasa nazama butum butumi na wucin hadi sbd dimples nata daya loba…

wanda suka kasance akoi har guda hudu a fuskartata ko magana takeyi sai angansu irib wanda ko wani side koi su guda bibbiyu dinnan ne hakan ya tabbatar min akoi wata a kasa…

flash back

Wato tun ranar da suka dira a kasar dubai wani bawan allah yafara rikita mata lissafi da tsantsar kalaman soyayya tun tana sharewa tana basarwa har abin yamata mugun kamu wanda muddin ko daidai da rana daya bata ga sakonsa ba har zazzabi takeyi…

gashi yaki yafito fili ya baiyana  kansa zuwa gareta kullum yakance mata dasauran lokaci…kuma basu taba waya ba iyakacinsu su a sakonnin waya suke tsaya wa dan haka ko kalar nuryarsa bata taba ji ba a rayuwarta hakan na matukar damunta…

back to business

saida suka kammala kana ta karanta sakon da masoyinta datayi saving da boyayyen masoyi …

a lokacin ma la’asar tayi dan haka sukayi sallah kana suka nufi garden na apartment nasu wanda sam hakan bai dame su ba amma yau kuma haka kawai sukaji suna da interest dazuwa wajen…

saida suka kwashi tarukucen littafansu da wayoyinsu dakomai suka bude kofar kichen nasu ta nan suka fice suka zauna kan couch-grass…

anan suka baje handaout nasu busy reserch sabida sun kusa fara rubuta jarabawarsu na final dan haka suka maida hankalinsu kan littafan nasu baki daya…

wanda ba karamin kyau sukayi ba wlhy kamar kasace su ka gudu…yau kam husna babu nikap ta fito wanda haka kawai taji yau bata sha’awar sakawa sai wani siririn scarf data yanesa akanta…

wanda har zamewa yakeyi ana ganin  gashinta daya kawatu da mayuka na musamman sai sheki yakeyi da daukan ido abindai ba a magana…yanxun ma iska ne yadauke scarf dinnata amma bata damu ba tunda taga  su kadai ne ta wajen garden din makotan nasu duk suna ciki ga dukkan alamu…

《》《》《》《》《》

Fadimatou saida suka gama wayansu tsap har la’asar kana sukayi sallama bayan ta idar da sallanta ta kwaso takaddunta tawuce garden domin tadanyi karatunta sabida dama ita bata da wurin zuwa sai wannan wajen…sbd tana son kamshin grasses

itama samun waje tayi kan daya daga cikin couch-grass dake wajen inda taji wani kamshi na ziyartar hancinta wanda kuma yayi matukar tsaya mata a rai domin ko ta tabbata wannan ne kamshin da kullum idan taji shi take da muradin tozali da mamallakinsa…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button