HAUSA NOVEL

NIGERIA KO NIGER Complete Hausa Novel

 

anty farida da kuma umma jameela dik suma suna wajen dasu ake hiran tinda mak’iyan nasu basama k’asar baki d’ayansu ballanta na asamu abin fad’a!
ansha hira sosai a wannan ranar kamar babu gobe,sai wajen 11 na dare kamin kowa yasamu wajen ajiye hak’ark’arinsa…!

 

washe gari da safe ma su husna bada wuri aka tashi ba an huce gajiya,wanda a wannan ranar ma suka yi ta raha cikin y’an uwansu…!

saida suka shafe sati d’aya cur da dawowa daga dubai kana gida yagama dawowa daidai wanda amni ta dawo daga niger itama kwana uku dasuka gabata,su husna sunje gaisheta ta ansa babu kunya irin ta masu allah yasa an gama a sa’a d’innan kamar yadda sauran y’an gidan nasu suka masu,wanda hakan yasa deeya buga uban t’saki ta bar wurin batare da b’ata lokaci ba,itakam iyayen hak’uri ko a fuska bata nuna mata ba suka rabu lahiya…!

misalin k’arfe 6:30am bayan su baa sun shigo tare da sauran y’ay’ansa maza daga masallaci kamar yadda d’abi’ar gidannasu yake suka yada zango a parlonsa,sannan kuma sauran matan nasa dakuma y’ay’an nasa mata baki d’ayansu sun shigo kamar kullum bayan an gama gaisawa baki d’aya baa yayi gyaran murya alamun zayyi magana mai mahimmanci wanda haka yasa suka zuba masa ido baki d’ayansu domin jin da wacce yazo yaukuma…!

 

 

*team nigeria*
*team niger*
*team ummie2018*

*comment*
*share*
*vote pls*
*follow me on wattpad@ ummie2018????????*
[9/8, 2:34 AM] ????oum muntaz????????????:   *NIGERIA KO NIGER…?*
_(wacece bora)_

*????©HIKIMA WRITERS ASSOCIATION????*

*_“`( home of peaces, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers✍????)️“`_*

*wattpad:UMMIE2018*
*oum muntaz✍????*
*whatsapp number:09076427357*

*page 20*

 

“Alhmdlh ala kulli halin,ina k’ara tayaku farin cikin kammaluwar karatunku baki d’aya,allah yasa anyi a sa’a…! yakuma sa hakan shine yafi alheri a gare ku dama mu baki d’ayanmu…! ba komai bane yasa na k’ara taraku anan sai akan magana d’aya da baku santa ba…! asma’au uwata dawo kusa da baa kinji…?”

baa yak’are maganar yana mai sakinma husna idanu da kanta ke k’asa,wacce tinda aka zauna takejin fad’uwar gaba sosai ba kad’an ba…! yanxu kuma da baa ya buk’aci ta mat’so kusa dashi sai taji gaban nata na t’sananta fad’u…!

babu yanda ta iya haka nan ta mik’e kamar t’summma a randa ko kuma ince k’wai ya fashe mata a ciki taja k’afafuwanta izuwa gaban baa tasamu masauk’i tana d’an wasa da yat’sun hannunta…!

kallonta baa yayi da kyau yace “ni mainene a wajen ki husna…?” gabanta ne yabada sauti dam kamar ana buga ganga sbd tambayar da baa ya antayo mata!

d’ago kanta kad’an tayi aikuwa take ta maida kanta k’asa sbd ganin yadda mahaifin nasu ya zuba mata ido yana kallonta alamar yana jiran ansa…!

cikin rawar murya da sassark’ewar harshe tace “kai mahaifi nane…!”

ajiyar zuciya baa ya sauk’e yace “masha allah…! ba komai nake son sanar dake ba,illa ina so na sanar dake cewa insha allahu na maki miji,wanda nake da yak’inin insha allahu nan da wata biyu mai zuwa zan d’aura maki aure keda sauran y’an uwanki da yardar allah…! kuma mun riga mun gama yanke magana tare da d’an abokina zan had’eki…! shikuma babana akoi k’anwarku yesmeen ta can bama insha allahu da ita zamu had’a,tinda na lura daga ke harshi ba auren bane a gabanku…! sannan ina fatan kuma bazaki bani kunya ba…?”

banda lugude babu abinda zuciyar husna keyi a wannan lokacin…! dik farin cikin data dawo dashi cikin gidansu ta naima ta rasa nan da nan…! sbd masoyinta mrs unknown abin alfaharinta data mat’ukar k’wallafa rai a soyayyarsu zasuyi aure…! amma gashi lokaci d’aya komai ya ruguje! sbd tasan ko giyar wake tasha bata isa tacema baa bata son zab’in daya mata ba akan wani d’a namiji dikdama d’imbin son masoyin nata daya mata mugun kamu dole ta hak’ura dashi,ko ana ha maza ha mata…!

“mallakin kai na wuyane baa…! dani da dik wani abinda na mallaka naka ne…! dan haka ina mai farin cikin sanar dakae cewa dik abinda ka yanke akaina,ko da wanzuwata a wannan lokacin ko bana nan wlhi bazan tab’a maka kallon wani abu ba bazan wat’sa maka k’asa a ido ba! saima kallon ka da zanyi a mat’sayin masoyina na,na k’warai kuma abin tin k’aho na..! dan haka na amince da auren dij wanda kazomin dashi ina maraba dashi! da fatan ban fad’i abinda bashi ne ba baa…?” a lokacin da ta k’are maganar muryarta na cracking na kuka amma tayi k’ok’ari k’warai wajen ganin ta danne…!

kowa tausayinta ne yakama sa a wajen bama kamar sadeeya datasan kalar soyayyar da y’ar uwar tata kema mrs unknown nata! amma gashi a rana d’aya an wargaza ma twinyn nata plan nata! kuma babu halin yin magana ace tayi rashin kunya a wajen!

momma tausayin y’ar tata ne ke kai kawo cikin zuciyarta k’warai da gaske amma babu yadda suka iya sai biyayya! sbd tasan idan tace ba haka bama yanxu baa zai rufe ido ne yamata tatas a wajen ta yadda amni kuma za’aji dad’in yad’a mata magana! dan haka taja bakinta ta t’suke ta yadda idan sunje d’aki ta llalashi abarta sbd tana da labarin soyayyartaa da mrs unknown!

 

amni kam haka nan taji wannan abu bai mata dad’i ba har cikin zuciyarta,amma kuma saita waske ta nuna komai ba komai ba sbd babu mai iya gane cikinta kaf cikin matan…!

 

haka nan sauran y’an uwanta ma
sai murna suke sbd su basu san tanason wani ba,ballanta su tayata bak’in ciki ko wani abu…!

baa kam sai washe baki yake cike da farin ciki yana ta saka mata albarkaa ganin yadda yarinyar tasa ta basa had’in kai batare data basa wahala ba…!

 

saida aka gama hayaniyar kamin baa ya sallame su bayan ya shaida masu washe gari ranar sunday zasu tafi bama baki d’ayansu! wanda hakan yasa kowa murna za’a tafi wajen t’sohuwa mai ran k’arfe (maa)!

 

kama hannun husna da k’afafuwanta ke hard’ewa kamar zata kife momma tayi a lokacin da suka tinkari apartment nasu!dikda haka husna bata samu zarafin magana ba! sadeeya ma diktaji babu dad’i itama tana binsu a baya!

saida suka shiga cikin parlon momma kamin husna tasamu damar sake kukan dake cinta tin a lokacin da suke wajen mahaifin nasu…!

momma bata hanata ba,saima janyo ta datayi jikinta ta rungumeta itama tanajin da da hali da itama kukan zatayi wlhi,ko zata samu sauk’in abinda ke mint’sinin zuciyarta!

sadeeya ma sai mat’sar k’walla takeyi ganin yarda y’ar uwar tata me kuka dikda kasancewar husna nada dauriya sosaii da wuya kaga kukanta idan ba kukan shagwaba ba!

saida tayi kuka sosai a wannan ranar idanuwanta sunyi luhu luhu abinka ga farar mace ! momma ta mata nasiha sosai a wannan ranar kamar me? wanda hakan yasa taji zuciyarta ta mata sanyi sosaii,a wannan ranar da mrs unknown ya kirata ma bata d’auka ba,sbd bata so yasan abinda ke damunta,tasan kuma shima idan yaji labari hankalinsa idan yayi dubu saiya tashi!

ranar dik wanda ya shigo part na momma baya samun ganin husna sbd kar kowa ya fahimci halin da take ciki ta k’ule d’akin momma abinta ta rufe ta ciki abinta!

washe gari wajen k’arfe 9 na safe dika ahalin wannan gidan suka wuce garin su na gado wato bama! tare da rakiyar motocin manyan sojoji!husna na mak’ale da nikap mata sbd gudun a fahimci tayi kuka jiya!saidae nace allah yakaisu lafiya amen…!

_Idan naga kumin sharhi sosai,zanci gaba da kawo maku littafinnan a kullum kullum,amma idan naga bak’wayi abu mai sauk’i ne nikam na jingine typing kamar wancan karan…!_

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button