NIGERIA KO NIGER Complete Hausa Novel

cikin sanyin murya dake tafe da kuka tace “shehu wlhi ba haka bane ba! ni bank’i zab’in da baa yamin ba amma kuma…!”
shuru tayi tana ci gaba da sheshshek’a!
murmushi mai sauti shehu yasake yace “amma kuma kina da wanda kike so ko asmaa’u…?”
d’ago kanta tayi da sauri saikuma tamaida kanta k’asa cike dajin kubya ta gyad’a masa kanta…! girgiza kai yayi kawai yana sakin k’aramar dariya cike da izza yace “toh kisa a ranki kan cewa wanda muka zab’a maki a mat’sayin mijinki shine ainahin masoyinki na hak’ik’a,kuma shine wanda kike masa soyayyar da har takansa kikan zubda hawayenki,dikda kuwa cewa ked’in mace ce mai t’sananin kunya sbd gudun makut’sar soyayyar ki dashi idan wani ya gtta t’sakaninku,allah ya maki albarka …!” “ameen shehu”
kamo hannunta yayi suka mik’e t’saye shehu ya rungumeta t’sam ajikinsa yana sauk’e zazzafar ajiyar zuciya a jere,itama kuma haka nan ta rungumesa tanajinta cikin wani yanayi mai wuyar fassarama mai karatu…!
wanda itakam ko baa ne bata tab’a shige masa har haka sbd kunyarta amma gashi ta shigewa wan mahaifinnata…!
t’sawon mintina goma ya sake ta ya d’ago kanta suka sakema junansu murmushi kamin suka fito daga sshashen maa…!
husna da sadeeya ne dake kwace kan gadon maa wajen 12zuwa lokacin sunyi bacci kawai husna tafarka a gigice sanadiyyar mafarkin datayi da fadimatou,wacce tama manta da babinta amma gashin sun had’u a mafarki tana fad’a mata wasu maganganu maras kan gado data gaza fahimtar na mainene…!
sai wajen k’arfe biyu kamin wani bacci yayi nasararyin awun gaba da ita,asuba ta garii…!
a k’ara hak’uri plss
*team nigeria*
*team niger*
*team ummie2018*
*comment*
*share*
*vote pls*
*follow me on wattpad@ ummie2018????????*
[9/8, 2:35 AM] ????oum muntaz????????????: *NIGERIA KO NIGER…?*
_(wacece bora)_
*????????©HIKIMA WRITERS ASSOCIATION????????*
*_“`( home of peaces, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers✍????)️“`_*
*wattpad:UMMIE2018*
*oum muntaz✍????*
*whatsapp number:09076427357*
*page 23*
washe gari da safe bayan su husna sun idar da sallar asuba suka zauna zaman karatu tare da hajiya ma’u…! sai wajen k’arfe 6 na safe kamin suka idar…! zuwa 6:30am shehu abdulrahman tare da baa dakuma sauran yara mazan baki d’ayan su suka shigo shashin maa…! inda su momma ma suka shigo baki d’ayan a tare bisa umarnin baa…!
bayan an gama gaishe gaishe as usual aka k’ara mawa matafiya gaisuwar gajiya kamin aka zauna aka k’ara yin hira na y’an uwanta ka…!
yesmen,zainab tare da malika ne suka aka masu iso zuwa cikin shashen maa d’in,y’ay’an galadima kenan suma ciikin shiri alfarma sunyi kyau sosaii…!
ilham k’arama wato y’ar momma dakuma ilham babba suka fara kokawa wannan tace itace mai hawa kan cinyar maa wannan ma tace itace zata hau,wanda hakan yakawo cecekuce t’sakaninsu,sai husna ce ta raba fad’an ta hanyar kwantawa a cinyar gaba d’aya hakan yasa dole suka nat’su kowa na masu dariya kamar wasu kishiyoyi…!
cikin sunkuyar da kai yesmen tafara gaida mutanen cikin parlon ganin harda sirikanta,inda malika ma tabi yayar tata wajen gaida su…!
cikin fara’a su baa ke ansa masu gaysuwar tasu,ana cewa ai ga matar aliyu nan husna kuma sai an koma zasu had’u da wanda zata aura! wanda hakan ya saka yesmen murmusawa,amni kam wani takaicin yarinyar ne taji yakamata,yanxu wai ace wannan yarinya y’ar k’aramar za’a aurama aliyun ta…? mai su baa suka gani a wajen yarinyar idan ba kyawun fata dakuma fuska ba…!? kasancewar yesmen ma k’yak’k’yawa ce badaga baya ba…! sannan kuma fara ce sosai saidae kuma kallo d’aya zaka mata ka fahimci zallar k’uruciyarta a fili! tinda a yanxu ne take cikin shekarunta na 17 a duniya…!
batare da kowa ya lura da ita ba tasake ma yesmen harara ta k’asan ido,wanda hakan ko karaf sai akan idon maa! amma batace k’ala ba ballantana ta nuna taganta…! itako yesmen ganin yadda amni ke mata kallon gala gala kasancewarta yarinya mara hak’uri ta murgud’a ma amni baki batare hdataji shakkanta ba ganin yadda take ta maka mata harara ta k’asa! wanda hakan ba k’aramin b’ata ma amni rai yayi ba sosaii! kuma tin daga yanxu zata fara shirye shiryen yadda zataci uban yarinyar wai idan ta zama matar d’anta …!
a k’alla an shafe awa d’aya a shashen maa kamin dik suka wat’se kowa yakama abgarsa…! sun sha yawo sosai ciki da wajen masarautar tasu cike da nishad’i wanda hakan yayi sanadiyyar yayewar damuwar dake dank’are cikin zuciyar husna kashi 90 cikin d’ari…!
wanda kuma hakan ba k’aramin dad’i yayima momma ba dama sauran y’an uwanta…!
saida sukayi kwana uku kamin suka bar bama suka dawo maiduguri cike da kewarsu,wanda har kukan rabuwa da shehu tayi wannan karan bacin kuma bata tab’a kamanta hakan ba…!
bayan kwana biyar da dawowarsu sun gama huce gajiya labarin dawowar aliyu gida ya iskesu…! gasu husna kuwa sai murna sukeyi yayansu zaizo dikdama dai zuwan nasa na kwana biyu ne da basusan dalili ba,tinda dai ba a bakin hutu yake ba daga shi har inoussa…!
hajiya amni kam girke girkenta ta bazama yima d’an nata kamar babu gobe ranar dazai dawo! fuskar nan tata cike da annuri dakuma fara’a a wannan ranar…!
k’arfe biyu na rana jirginsa ya sauk’a a filin jirgi na maiduguri inda yasamu tarban yayan nasu wato yerima musa tare da tawagarsa na gidan sarauta daga can bama d’in…!
cike da kewar junansu suka rungume junansu dikdama dai bawani shak’uwace sosai a t’sakaninsu ba sbd yanayin aikin nasu bana zama guri d’aya bane…!
motoci wajen guda bak’wai ne suka d’auki hanyar unguwar new gra tare da rakiyar rundunar sojoji guda mai zaman kansu bila’adadi a mat’sayinsa na *major general* …!
dik ta inda suka gitta sai faman d’aga masu hannu ake ana kauce masu akan hanya na ganin yadda way’annan sojojin k’et suke jira sukai ma mutane hari…! a haka har suka isa unguwar tasu! mallam mai gadi ya wangale masu gate inda k’arshenta ma sauran motocin a waje sukayi parking nasu sbd cikin harabar gidan bazai d’auki yawan motocin ba…!
dik sunyi ready da bindiga wanda hakan yakusa sumar da husna data riga kowa fitowa da gudunta na ganin ta fara tarban yayan nasu amma wani bak’in kurtu ya nunota dakan bindiga…! kasa mot’sawa ko nan da can tayi a wajen…! wanda hakan yasa su sadeeya cin burki daga bakin main entrance na apartment nasu suma sbd t’soro yadda suka ga sojojin nan sukayi…!
dariya ce fal cikin aliyu na ganin yadda kowa yayi t’suru t’suru bama kamar husna amma dole ya gimt’se fuska sbd gudun raini wajen sauran sojojin dake gurin! k’aramin murmushi yasake na gefen baki wanda hakan yasa kumatunsa lob’awa (dimples) cike izza dakuma jarumta yafara takowa zuwa inda take…! bata barima ya k’araso ba na ganin bai wuce saura taku biyu ya isota ba ya riske shi ta rungumesa gamgam cike da t’sora har wani uban gumi ne ke t’sat’st’safo mata a goshi,gana karkawa..!
“hey lil sis am your brother fa! bud’e idanunki kinji dik sun ajiye bindigar tasu ma”
girgiza kai takeyi cike da rawar murya tace “ya aliyu dan allah kace su tafi nikam” “cikin kakkausar murya kamar bashine yagama mata magana cikin salama ba yace “nace ki bud’e idanunki kidawo hayyacinki ko asma’u…”
jin abinda yafad’a ne dakuma yadda taji kamar ransa ya b’aci yasata d’ago kanta a t’sorace…! aikuwa d’ago kanta keda wuya taga yadda har yanxu suke ta muzurai da jajayen idanunsu batare dasun ajiye bindigar tasu ba yasata fasa ihu ta kwasa a guje zuwa apartmen nasu…! wanda hakan yasa wasu daga cikinsu kama dariyan husna dakuma mamakin ogan nasu da basuyi especting yana sakema y’an gidan nasu fuska har haka ba…!