NIGERIA KO NIGER Complete Hausa Novel

k’aramar dariya yayi kawai ganin mahaifin nasu da fitowarsa kenan kuma dik abinda ke faruwa kan idanunsa,wanda hakan yasa shi sakin k’aramar dariya…!
kamo hannunsa baa yayi inda suka shiga babban palon baa akayi masa sannu da zuwa tare da sauran y’an uwansa amma babu husna babu dalilinta…!
bayan sallar isha’i aliyu ya shishshiga palon na matan baban nasa kamar yadda yasabayi idan ya dawo daga tafiya domin yagaishe su…!
apartmen na momma ne yazamana a k’arshe inda ya tadda sadeeya,zainab da ilham suna kallonsu suna hira cike da raha…!
ilham ce ta taso tazo jikin yayan nata yana ta mata wasa kamar bashine mai d’ad’d’aure fuska ba…! deeya kam itama yau y’an surutun basa kusa shiysa daga gaisuwa tamaida hankalinta akan kallon da sukeyi…!
momma ce tafito suka gaysa da aliyu sosai kamin ta umarci sadeeya takawo masa drinks da husna tayima yayan nata na kankana d’azu tare da snacks…!
yaci ya sha abinsa kuma yaji dad’i sosai,inda ya baje abinsa a parlon momma suke ci gaba da zaman kuramen har momma tashiga ciki sbd tana da ayyukan datakeyi…!
tambayar zainab yayi ina husna ta shaida masa tana cikin d’akinsu…! cike da kasalar data rufe sa tin zaman a wurin ya mik’e ya shiga d’akin su husnar. inda ya hango ta tayi lamo akan katifa amma alamu ya nuna ba bacci takeyi na…..!
aci gaba da hak’uri dan allah????????
*team nigeria*
*team niger*
*team ummie2018*
*comment*
*share*
*vote pls*
*follow me on wattpad@ ummie2018????????*
[9/8, 2:35 AM] ????oum muntaz????????????: *NIGERIA KO NIGER…?*
_(wacece bora)_
*????????©HIKIMA WRITERS ASSOCIATION????????*
*_“`( home of peaces, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers✍????)️“`_*
*wattpad:UMMIE2018*
*oum muntaz✍????*
*whatsapp number:09076427357*
*page 24*
dikda taji k’arar k’ofan d’akin nasu hakan bai sata mot’sawa daga inda take ba ballantana ta juyo sbd tunanin dayake neman zautar mata da k’wak’walwarta a y’an kwanakin nan…! har ya zauna a bakin gadon bata juyo ba wanda hakan ya sosa zuciyar aliyun amma kuma ya maze kawai…! mik’ewa yayi ya dawo ta gurin da kanta yake ya zauna ya janye tagumin data zuba,sbd sai yanxu ma ya lura da tayi zurfi cikin tunani…! a d’an daburce ta d’ago kanta! ganin ya aliyu ne yasa sakin ajiyar zuciya mai k’arfi tare da kwantar da kanta akan cinyarsa tunda dama a kwance take…!
numfashi mai d’umi ya fesar kamin yakai hannunsa kan dogon hancinta yana jansa! sbd shikam allah yagani yana son yaga mace mai dogon hanci mai t’sari,sai gashi kuma cikin ruwan sanyi allah ya yoma k’annensa dogin hanci baki d’ayansu..!
jin alamun ruwa a hannunsa ne yasa zuciyarsa girgizawa yakuma lumshe dara daran idanunsa batare daya bude su ba…! saida ya shafe kusan mintina hud’u a haka kamin ya k’ara fesar da gaggauro numfashi ya d’ago husna da zuwa yanxu kuka take sosai kamar an kunna famfo haka hawaye ke zuba daga cikin idanunta amma kuma kuka mara sauti ne wanda ke tab’a zuciyar mai sauraro…!
masauk’i yamata a k’irjinsa inda itama ta k’ank’amesa cikin muryarr kuka ta yadda dik wanda ya saurareta sai ya tausaya mata k’warai da gaske…!
“ya aliyu na an rabani dashi…! bana son wanda za’a auramin ya aliyu! nikuma bansan ya zanyi ba! ina matuk’ar k’aunarsa daidai da bugun numfashina…! soyayyarsa tayima zuciyata mugun kamu wanda kuma bana tunanin zan iya daina k’aunarsa daidai second d’aya har k’arshen rayuwata…! ya aliyu dan allah kaje kacema baa yayi hak’uri ya janye auramin d’an abokin nasa! wlhi bana sonsa! ni mrs unknown d’ina nake…! idan bashi ba kuma na tabbata a ranar da aka kaini cikin gidan wanda su baa keson auramin gawata kawai za’aje a tarar da safe! bana sonsa wlhi…! ka taimaki zuciyata ka t’samota daga fad’a cikin mawuyacin hali…! idan ba haka ba mutuwa zanyi…!”
cike da t’sant’san tausayin k’anwar tasa dakuma tashin hankali aliyu ya k’ara k’ank’ameta sosai idanunsa sun canza launi daga fari k’al izuwa kalar garwashi! k’irjinsa har wani bada sauti yake sbd t’sananin rud’un daya shiga sanadiyar maganganun da k’anwar tasa ke zarowa…! gashi kuma mat’salarsa da tata kusa kala d’ayane,saidai shi yasan wacce yake so tinda har zaman hira sunayi gaba da gaba,amma ita fa…!? soyayyace fa kawai da ake koya mata shi batare data shirya ba…! gata kuma da raguwar zuciya dake dauk’e da matuk’ar rauni…! wannan bala’in damai tayi kama dan allah…? wai autan had’i za’a masu da girmansu da komai batare da su suka furta cewa suna so ba sai kace wasu mutanen da…?? shifa babu abinda yafi ci masa tuwo ak’warya ma kamar aura masa yesmen wanda yake ganinta k’aramar yarinya haihuwar jiya jiya wai…!?
k’ak’k’arfan ajiyar zuciya ya k’ara sauke bila adadin a wannan lokacin kamin ya tallafo kanta baki d’aya yayi switching na dim light d’in dake d’akin duhu ya mamaye ko ina na t’sawon minti biyar kamin haske ya maye gurbin duhun…!
kan husna na k’asa sai share hawayenta takeyi ta gagara d’ago kanta ta kalli yayan mata da idanunsa ke lumshe yana sauk’e ajiyar zuciya da sauri da sauri…!
batare daya k’ara mata kallon second d’aya ba ya mik’e yafice daga d’akin cike da wani kalar yanayi mai wuyar fassara wa…! sadeeya ce kad’ae a parlon take kallonta,sbd ilham yau tafi zainab apartment nasu sbd acan take son kwana…!
kallon yayan nasu tayi daya samu waje ya zauna kan d’aya daga cikin kujerun parlon kansa na kallon sama idanunsa alumshe yana karkad’a k’afa kamar wani basarake…!
mik’ewa tayi itama ta dawo gefensa ta zauna ta dafa kafad’arsa,wanda hakan yasa shi bud’e idanunsa ya zuba a fuskarta da saida taja baya sbd t’soratar da tayi na ganin yadda idanuwan sukayi jazur dasu kamar ba shi ba…!
cikin rud’u ta k’ara mat’sowa takamo hannunsa ta rike tace “ya aliyu miya same ka…? baka da lafiya ne…?bari na k’ira baa akawo maka magani yanxu…!”
mik’ewa tayi da niyyar tafiya aliyu ya kamo hannunta ya dawo da ita ta zauna a gefensa yasa hannunsa ya rufe bakinta,wanda hakan yasa ta dole yin shiru tana binsa da ido daya k’ara lumshesu…! sun shafe t’sawon mintina goma sha biyar a haka kamin ya k’ara bud’e idanun sa dasuka dawo farare tas kamar madara…! kamar basune suka canxa launi ba k’ank’anin lokaci daya gabata…!
ajiyar zuciya mai k’arfi deeya tasake kamin tace “ya aliyu mai yasami idanunka d’azu…?”
murmushi yasake mata cikin sanyin dakakkiyar muryarsa yace “babu komar mrs parrot…! haka dama idona yakemin a lokuta da dama…! kuma bakiga dakansa ma ya koma dai dai ba yanxu…?” cike da gamsuwa deeya take gyad’a masa kai…!
inda suka zauna suna kallon tare sai wajen goma da rabi kamin ya fice daga shashin izuwa nasa…! wanka yafarayi kamin ya feshe jikinsa da daddad’an turarensa yasaka pyjamas nasa yabi lafiyar gadonsa zuciyarsa cike da tunani kala kala wani daddad’an bacci yayi gaba dashi mai cike da mafarkai marasa kan gado…!
Tunda aliyu ya fita husna ke sharen hawayen wanda kamar k’ara masu gudu ma akeyi…! zuciyarta cunkushe da zullumin tunani iri iri,da k’yar tasamu ta shiga toilet a daddafe tayi brush,tayi wanka kamin ta fito zuwa gaban dress mirrow ta shafa daddad’an lotion d’inta had’e da wani had’in mai da momma ta basu wanda kullum idan zasu kwanta sai sun mulke jikinsu dashi…!