HAUSA NOVEL

NIGERIA KO NIGER Complete Hausa Novel

amni kam farin cikin da take ciki idan taga yayanta waje daya allah ne kadai yasani…wanda tun shigowarsa take ta zuba murmushi tana alfahari da yaranta kwarai sbd ko ina tashiga a fadin kasarnan dama wasu kasashen ketare har nuna ta akeyi ana cewa ga maman

CAPTAIN INOUSSA MUHAMMAD BAMA daya tamkar da dubu wanda yakasance sojan dake kare kasarsa da rayuwarsa da lfy yarsa…kuma shine da na farko acikin gidansu wajen iyayensa…

saikuma kaninsa wanda ratar dake tsakaninsu kwata kwata na sawon mintina sha biyar ce wato…

MAJOR GENERAL ALIYU MUHAMMAD BAMA…..

daya tamkar da dubu wanda kasarsa dama wasu kasashe da dama suke alfari dashi a matsayinsa na matashin saurayi mai jini ajika yaro abokin manya wanda rayuwarsa ba abakin komai take ba a gurinsa muddin zai kare al’ummar dake karkashinsa

amma kuma a wajen al’umma rayuwar ba karamin abun girmamawa daraja bace a garesu dan haka suke matukar alfahari dashi dama duk wanda ya dangance shi……

Mahaifinsu ma babban soja ne a baya kamin yy ritaya tun a zamanin shagari …

amma ahalin yanxu yayi ritaya wanda suka kasance yan asalin garin bama ne mahaifinsu ne keda sarautar garin bama wato SHEHU ALIYU DALHAT BAMA…

shine wanda yake rike da sarautar bama yana da mata biyu ASMA’UM(MAA) DA ZAINABU (MAAGANA) rayuwar gidan sarauta ta gaji abubuwa da dama dan haka duk inda kazaka a fadin duniya kashiga gidan sarauta da tasu kalar matsalolin…

sun kasance kanurai gaba da baya mazaunan garin bama kuma sarautarsu gada sukayi bawai sama ta ka suka zo suka tarda ba……

matarsa ta farko asma’u itace uwar gida tsohuwa mai ran karfe yayanta biyu ne a cikin gidan kuma dukkansu mazana wato ABDUL-RAHMAN shine babba agurin iyayensa saikuma kaninsa maibi masa wato MUHAMMAD…

saikuma maagana wato zainabu itakam bata da yaya a gidan dashike ta dau haka a matsayin kaddararta bata tsaya  jayayya da hukuncin uban giji ba sai shehu ya dauki dansa na biyu wato muhammad yabata shi kyauta halak malak…

aykuwa wannan kyauta daya mata tayi matukar farin ciki da haka tana kula dashi yanda yakamata ga gatan dake masa watakila ko mahaifiyarsa ce baxata masa hakan ba…

alokacin da girma yakama su shi muhammad ra’ayinsa shine yayi aykin soja dan haka ne yasa shi tafiya can kaduna school of amy acan yayi karatunsa har yazama abinda yakeson zama…

shikuma abdul rahman sai ya karanci sociology wato ilmin halayyar zaman jama’a dan haka ne ma aka masa horon yanda kou yazama sarki baxai sha wahala ba…

alokacin da abdul yakai 27yrs shikuma muhammad 25 dan haka batare da naiman izninsu ba aka daura masu auren da yayan galadiman shehu wayan suka kasance suma wa da kanwa ne…

halimatussadiyya itace babba dan haka itace matar abdul sai kanwarta hafsat datake kyakkyawa na kin karawa a wannan lokacin…

itakam kou irin yawo a cikin gidan sarautarsu ba’a barin sbd gudun bakin jama’ah tsananin kyawunta har ya wuce yanda zan misaltawa mai karatu…

 

bayan anyi aure da shekara daya halima ta haifo zankadeden yaronta mai kama da ita akasa masa suna musa…

amma ita hafsat shuru gashi kuma allah yadaura ma muhammad son yaga jininsa sai yace ma iyayensu shi yana son su kara naimo masa mata…

basuyi kasa a gwiwa ba aka daura masa aure da yar gidan waziri wato jameela…

anyi gagarumin yaki da hafsat domin kou alllah ya daura mata tsananin kishin mijinta kuma kwata kwata aurensu shekara daya ne dawasu watanni gashi dama jinin kanurai ansansu da zafin kishi…

 

haka dai ta hakura dataga babu sarki sai allah…

jameela ma babu batan wata ahaka suka shafe shekara 2 da wani abun…

kuma alokcinne wani ayki zaikai muhammad kasar niger cikin garin agedez inda yasauka a gidan sarinsu…

 

tun zuwansa daya kyalla ido yaga yar gidan sarkin allah ya jarafcesa da tsananin sonta kuma bawai dan kyakkyawa bace kou kadan sbd hafsat ma uwar gidansa tafi wannan kyau nesa ba kusa ba…

itama bangaren MARIAMA sai allah yadaura mata sonsa bai bar garin ba saida aka daura masa aure da ita ya tattaro matarsa sukazo nigeria…

 

alokacin ma kam hasat abin ya bakanta mata rai wato shi tsabagen bai dauke su a bakin komai ba ne yasa shi auro masu mata saidai kawai sugansa yadawo masu da wata…?

 

hakanne yasa mata jin haushin maryama ga wani dan banzan kishi dayake daway niya da ita…

a bangaren mariama ma akoita da tsananin kishi kasancewar hakan kamar a jinin buzaye yake suma ba daga baya ba wajen kishi…

saidai kuma su sunfi yan NIGERIA wayo…ma’ana dai takasa suke gasa kishiyoyinsu batare da kowa yalura da hakanba…

TEAM NIGER
TEAM NIGERIA

TEAM BUZAYEN AGADEZ
TEAM KANURIN BORNO

TEAM UMMIEN2018

*vote*
*comment*
*share*
*follow@ummien2018*
[9/8, 2:26 AM] ????oum muntaz????????????:     *NIGERIA KO NIGER…?*
(wacece bora)

*©HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*_( home of peaces, joint of entertainment to educate and enlight  our readers)_*

*wattpad:UMMIE2018*
*whatsapp number:09076427357*

page 3

Matsalar nigeria anan shine akoisu da kishi amma kuma basusan yanda zasuyi controlling kansu ba…

ma’ana dai kishinsu a fili yake baro baro babu lillibi…sukuma yan niger suna da kishi sosai ba kadan ba amma sun iya boyrwa saidai su gasa kishiyarsu ta bayan gida…

sannan kuma mazajenmu na nigeria dama sauran mazajen kasashen mu na ketare basa son macen da zata zake akan kishi tanunawa duniya cewa itafa ganan halinta a faifai kowani jik and jak ma yazo yagani…

hakanne yasa idan aka hada nigeria da niger a matsayin kishiyoyi saikuga sune sama akan yan nigeria sbd sun iya wanke allonsu…

Hakan take tsakanin hafsat da mariama wannan takun sakar suka samu har ya zamana mariama ce sanyin idaniyar muhammad wato baa…

gashi dama itace matar daya gani yace yana so har ya aure ta sukuma dama bazabinsa bane dan haka a fili ma yakan nuna cewa itace pha matarsa ta so…

sukuma hadin iyayensa ne wannan ne ya haddasa masu zazzafar kishi akan ita mariama haushinta sukeji sosai ba kadan ba…

itakuma ganin itace ontop sai yazamana kamar yabata lasisin iskanci kala kala amma shikuma bai gane hakan…

watansu biyar da aure tasamu cikinta na wata hudu wai…!aykuwa wannan cikin data samu kuma sai wanda yaga irin tsiyar datake shukawa a gidan saitace abinci ma ga wacce take son ta dafa mata a cikin kishiyoyinta kuma idan banasu ba batajin dadin cin abincin kowa…!

aykuwa anyi karamin yaki a wannan gidan…dashike ana daukin cikin baiga wani aybu akan abinda take tsulawa ba karshenta ma sai yasa su a gaba saisun girka mata shikuma yakawo mata…

jama’ah kunji pha rainin hankali……?

wannan abu ya assasa tsanin tsana tsakaninsu kuma duk wainar da ake toyawa babu wanda yasani tsakanin shehu da maa amma maagana tsaf ta sani sai cewa ma da tayi ay duk sharrin cikine…

hafsat duk abunda ke faruwa bata fadawa kowa kasancewar tana rike sirrin gidanta itadai kubarta da kishi wannan zaku bata number daya amma kuma bata da wani matsala bayan hakan…

amma wannan karan kam sai ta tuntuntubi yayarta akan abinda muhammad da matarsa ke masu a gidan hakuri tabata kasancewa halima akoi hakuri irinsu ne wayanda ake cewa ko yatsa kasa masu a baki bazasu kalleka ba…

toh itama haka take ta gwammace ta zauna abun kasheta batare da dau mataki ba…hakanne yasa mijinta ke alfahari da ita kunsan shima hakuri ginshikin zaman gidan aure ne…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button