NIGERIA KO NIGER Complete Hausa Novel

“a kwanakinnan wani abu ne da wasu daga cikin yahudawa suka k’irk’iro shi na sab’ama allah a mat’sayin ado wai…! misali yanxu idan an saka ma saurayi da budurwa ranar aurensu…! ya rage bai wuce saura kamar sati 5-6 ba…! zasu samu keb’antaccen guri batare da sanin kowa ba suyi mu’amalar da allah ya haramta yinta idan ba tare da igiyoyin aure ba(zina)…! fa’idar yin hakan kuma ba komai bane saidan kawai wai ku gwada jarumtakarku…! kusan cewa shin ko bayan aure zaku iya d’aukar nauyin junanku ta wannan fannin…? wannan babban abinda ya fara shigowa cikin al’ummar musulmi ne ya ingizamu izuwa laifin da in muka aikatashi bazamu tab’a daina aikata dana sani ba t’sawon rayuwarmu…!”
musa ya k’are maganar kansa na kallon k’asa daga shi har sadeeyar,sbd ganin yadda momma ke binsu da wani kallo na amma sai yau nasan cewa ku manyan mahaukata ne…!
nasiha sosai mai matuk’ar shiga zuciya da t’soratar da bawa zuwa ga aikata aikin haramun dayasa jikinsu yin sanyi luk’us tare da t’sant’sar nadama dakuma kunyan uban gijinsu…! saida ta tabbatar da cewa sak’onta ya isa inda yakamata kamin ta sallamesu suka tafi…!
ita kuma daga nan ta gabatar da sallolin nafila sbd wajen biyu da wani abu na dare ma tayi a wannan lokacin…!
fatar shiriya ta k’arayima y’ay’annata sosai har saida tayi sallar asubahi kamin ta kwanta sbd baccin dayaci k’arfinta,dikdama dai ita kam ba gwanar baccin safe bace…!
Sadeeya ma wanka tayi ta t’saftace jikinta ta shimfid’a sallaya ta hau yin salloli babu k’ak’k’autawa cike dajin kunyar ubangijinnata tana naiman tuba izuwa garesa har husna itama ta farka ta gabatar da sallolin itama yau suma ko azkar basu samu damar yi ba suka koma baccinsu…!
haka musa ma dai saida mu masu fatan allah ya yafe masu yakuma k’ara shirya al’ummar musulmi baki d’aya…!
(nasan wasu zasuce na shigo cikin wani fannin da bai kamata nakawosa cikin labarinnan ba…! so dan haka amin uziri nima kuma un-expected sak’o na isar zuwa gareku…! sbd naga abin yafaru ne dagaske a y’an kwanakinnan,shiysa na rubutasa bawai kawai fiction bane…! dan haka muyi k’ok’ari naganin mun t’sare mutuncin addininmu dakuma mu karan kanmu wajen sab’a ma mahaliccinmu…!
allah yasa mu dace…!
Sannan kuma ba kowane zai fuskanci abinda momma keji cikin zuciyarta a wannan lokacin ba,sai wanda wani abu makamancin hakan tafaru dashi kamin zai fahimta,sbd nasan wasu zasuce ainayi ta maimaita abu kaza kaza…! allah yasa mufi k’arfin zuciyarmu????????)
aci gaba da hak’uri dan allah,akoi book na kud’i danakeyu yasa ban na maku typing dayawa????????
*team nigeria*
*team niger*
*team ummie2018*
*comment*
*share*
*vote pls*
*follow me on wattpad@ ummie2018????????*
❤️ *ZAB’AB’B’U BIYAR(5)* ❤️
_Albishirinku ‘yan uwa????????, nesa tazo kusa, shahararriya kungiyar litatattafan hausa nan wacce ta saba fadakarwa da ku da nishadantar daku da dadadan littattafanta irinsu *SADNAF, WUTA DA AUDUGA, CHAK’WAKIYA, DOCTOR ZAHRAH, NIDA ARYAN, KYAN DAN MACIJI, ZURI’A D’AYA, NUNA SO GABAN KISHIYA, RAYUWAR AFREDARH, BAYAN AUREN DA SAURANSU* wato *HIKIMA WRITER’S ASSOCIATION,* ( *K’UNGIYA D’AYA TAMKAR DA DUBU*)ita ce wannan karan ta harrak’o domin sake kawo muku *ZAB’AB’B’U!, ZAB’AB’B’U!!, ZAB’AB’B’U BIYAR(5)!!!* ,wanda hazikan, fasihan marubutanta suka warware hikimarsu da Basirarsu wurin sank’amo muku labarai masu fadakarawa, ilimantarwa har ma da nishad’antar wa._
_Nasan zaku so kuji marubutan da kuma littattafan ko?????????, to ku karkade kunnuwanku????????,gasu nan kamar haka._
_*YAKIN MATA* wacce fasihiyar marubuciyar nan ta *DOCTOR ZAHRAH* ta sankamo muku wato *FATEEYZAH*_
_*ANYA KUWA?,* daga jajitacciyar marubuciyar nan ta *NUNA SO GABAN KISHIYA* wato *UMMIE2018*_
_*YOUSUF,* daga fasihiyar marubuciyar nan ta *KYAN DAN MACIJI* , ba kowa bace face *ZULAIHAT ALIYU MISAU.*_
_*RIBAR HAKURI,* wacce nagartacciyar marubuciyar *BAYAN AUREN* ta sambado muku wato *AISHA Y HANWA.*_
_*BAGIDAJIYA* , daga marubuciyar nan mai basira wacce ta kawo muku *RAYUWAR AFREDARH* wato *HASEENART MUHAMMAD.*_
*’Yar uwata, kar ki bari wannna litattafan su wuce ki, ko kuma ki tsaya sauraren labari, ki harrako ki siyesu don a dama tare dake, akan farashi masu sauki da rahusa kamar haka:*
*ZAB’AB’B’U BIYAR___500*
*ZAB’AB’B’U HUDU___450*
*ZAB’AB’B’U UKU____400*
*ZAB’AB’B’U BIYU___350*
*IDAN DAYA KIKE SO_200* .
*Zaki biya kudi ta wannan Account din*
*Fatima sani Muhammad*
_Access bank_
*0796627818*
_tare da shaiidar biya ta wannan number????????07032266778_
_marasa account zaku iya screenshoot na kati mtn ko airtel ta wannan number???????? 07032266778_
*~SAI MUNJI KU MASOYAN K’WARAI????????~*
[9/8, 2:35 AM] ????oum muntaz????????????: *NIGERIA KO NIGER…?*
_(wacece bora)_
*????????©HIKIMA WRITERS ASSOCIATION????????*
*_“`( home of peaces, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers✍????)️“`_*
*wattpad:UMMIE2018*
*oum muntaz✍????*
*whatsapp number:09076427357*
*page 25*
cikin kasalalliyar muryarta dake fitowa da sautin wacce taci kuka tagaji tace “hello habibi nah,nayi kewarka sosai…” tayi maganar tata cike da shashshek’a alamun gaf take da fara kukan daya zame mata jiki a y’an kwanakinnan na tausayin makomar rayuwarta tata dakuma masoyinta…!
k’ak’k’arfar ajiyar zuciya aka sauk’e daga can b’angaren nasa cikin wani kamilalliyar murya mai matuk’ar dad’i da amon daddad’an sauti yace “mai yafaru rabin raina…? kin daina d’aukan wayata a y’an kwanakinnan…! hankali na ya tashi k’warai da gaske…! zuciyata zata buga idan kika k’ara kwatantamin makamancin abinda kikamin a y’an kwanakinnan…!jikina na bani akoi gagarumin damuwa sosai amma kink’i fad’amin ainahin mat’salar dake faruwa…! zuciyata zata buga asma’u…! ki taimaki rayuwata koda na k’ank’anin lokaci ne ki bani damar mu had’u nida ke dan allah…! koda hakan zaisa ki fahimci yadda zuciyata ta girmama da k’aunarki…! gashi mahaifina na shirin auramin yarinyar da bansan da wanzuwarta ba cikin duniyata…!…” kamar ba namiji ba haka nan mrs unknown yake ta razgar kuka a wannan daren husna ma tayasa itama cike da tausayin junansu…!
saida suka sha kukansu suka k’oshi kamin suka sararama kansu suka fara gayama junansu kalamai masu matuk’ar dad’i da sanyaya zuciya t’sakaninsu,suka yanke kan gobe da misalin k’arfe uku na yamma zasu had’u,tinda daman ya shaida mata shima d’an cikin garin maiduguri ne…!
sai wajen sha d’aya da rabi sukayi sallama suka kwanta bacci cike da tausayin junansu na wannan wahalalliyar soyayyar tasu da suka gaza samun cikar burinsu a daidai lokacin dasuke tunanin mallakar junansu a mat’sayin abu d’aya…!
b’angaren sadeeya dake yau tasan abinda ta shiryama kanta yasata k’in kwanciya da wuri…! gashi kuma momma ce yau a d’akin baa ta tafi shashensa,wanda saida ta tabbatar da cewa su sadeeyama sun kwanta bayan ta kashe kallon tashiga d’aki kamin ta fice,nanko batasan deeya fakon fitar tata takeyi ba…! gashi kuma dik wacce rananta ne ita kan zuwa ta sami baa bashi ba…! amma ko idan gimbiya y’an mulkin nanan takan k’in zuwa ne saidae shi yaje ya sameta zuwa shashenta wato matar so (amni)…! amma sukam idan basuje ba ko shekarane bai damesa ba wai…!hmm