HAUSA NOVEL

NIGERIA KO NIGER Complete Hausa Novel

cike da ladabi aliyu ya ansa da kansa ke k’asa tin d’azu yamik’e ya fice zuwa shashin momma,batare da yayi knocking ba ya tura k’ofar shashinnata,kuma cikin sa’a a bud’e take…!

d’akinsu husna ya fara shiga,inda ya tadda su sunyi daidai sai shek’a uban baccinsu sukeyi kamar babu gobe…! k’afofinsu ma dik sunyi gabas da yamma alamun baccin na masu dad’i sosai…!

fuskar husna yayi tozali dashi da yayi rud’u rud’u,alamun taci kuka ta k’oshi abinka ga farar fata babu sirri…!

gashin kanfa dasuke gazar gazar marasa laushi kamar irin yadda na india wa yake akoi yawa sosai amma kuma gazar gazar me dik sun cark’wad’e akan nata sbd bacci…!

 

juya akalar kallon nasa yayi zuwa ga fuskar sadeeya,inda ya fahimci itama ba k’aramin kuka tayi ba,dikdama dai ba kasafai ake gane hakan ba duba da yanayin fatar tata,sai wanda ya mata farin sani…!

ajiyar zuciya mai k’arfi ya sauk’e,inda ya d’an d’aga murya ta yadda zasuji shi yafara k’iran sunayensu…!

 

sadeeya ce ta fara farkawa tana mut’sit’st’sika idanuwan masu kyau da t’sari dasuka koma d’an ja kad’an,alamun taci bacci kenan…!

ganin aliyu t’saye kanta yasata d’an waro ido kad’an,alamun mamakin abinda yakawo ya aliyun d’akinsu war haka…!

fahimtar hakan da yayi ne yasa shi t’sare gida cikin shan k’amshi yace “maza jeki ma momma magana baa ma k’ira a babban parlonsa yanxu…!”

bayi ta fad’a ta wanko bakinta kamin ta zumb’ula hijabi har k’asa ta fice zuwa d’akin momma…!

fitarta yasa aliyu takawa zuwa bakin gadon nasu yana sakin murmushi k’asa k’asa…! tattausan hannunsa yasa ya d’ago husna,wacce kamar ya d’ago babyn robber haka yaji sbd rashin nauyinta…!

wafce jikinta tayi ta mik’e zumbur tana sosa kai kamar wata munafuka wanda hakan yasa aliyu darawa kad’an yakuma gimt’se…!

“wato asma’u kema kin koyi rashin kunya ko…? kina jina wato ina k’iran sunanki amma t’sabagen rashin kunya kin gagara d’agowa ballantana ki ansamin sbd ga d’an iska na magana ko…?”

har yanxu kanta na k’asa batare data d’ago ba cikin rawar murya tace “kayi hak’uri ya aliyu bazan sake ba…!”

k’wafa yayi kawai alamun zamu had’u yayi hanyar k’ofa yanace mata “ki samo mu a shashen baa…!”

a gurguje ta k’ara wanke bakinta tare da fuskar tata itama ta saka hijjap d’inda tayi sallar dashi ta fito inda ta tarda sadeeya zaune tana jiranta ta buga uban tagumi kamar wacce akayiwa mutuwa…!

wanda sai yanxu husna ma ta lura da kukan da sadeeya tayi sbd fuskarta ta fallasa mata cewa y’ar uwar tata na cikin damuwa…! zare hannun da sadeeya tayi tagumin husna tayi “sis mai yake damunki naga idonki yayi jaa…?”

cikin murmushin yak’e da kana ganinsa bai kai zuciya ba tace “babu komai twiny kawai na kwana da ciwon ciki ne jiya…! amma yanxu da sauk’i,muyi sauri muje karsu baa suyi ta jiranmu…!
badan husna ta yadda ba suka rik’e hannun junansu suka fice…!

sallama sukayi daga bakin k’ofa aka basu iznin shiga,kansu a k’asa suka shigo kamar wasu sabbin munafukai(????) sunk’i yadda su had’a idanuwa da kowa…! kuma kowa binsu da kallo yakeyi,banda momma da itama idan kukaga yadda fuskarta tayi jawur abin tausayi wlhi…! sbd ita a ganinta husna taji labarin abin jiyane yasata taya y’ar uwar tata kuka,nanko momma batasan kowa da tasa mat’salar ba…i!

bayan sun gaisar da mutanen parlon shuru ne ya rat’sa wajen…! baa ne ya kat’se shurun ta hanyar k’iran sunayen husna da sadeeya da saida y’an hanjin cikinsu ya kad’a…!

mik’ewa sukayi sum sum suka dawo gaban baa sukayima kansu masauki,musa da aliyu ne dama suka saka baa a t’sakiya ta gefe da gefe suna d’an mammat’sa masa k’afa…! sukuma suka zauna agabansa suka sunkuyar da kansu ganin kallon k’urillan da baba yake masu…!

“Halimatu miyake damunku keda y’ar uwarki…?” wannan itace tambayar da baa ya jefo ma su sadeeya dasukayi t’sumu kamar t’summa a randa…!

kan sadeeya a k’asa tace “baa ciwon kai husna ta kwana dashi jiya fah……n.i…kuma……!” kawai saita fashe da kuka dayasa kowa zuba mata ido domin jin abinda zata fad’a cike da sonjin dalilin kukan nata…!

musa kam a wannan lokacin da zaka t’saga jikinsa ko jini bazaka gani ba,sabida t’sananin tashin hankali…! momma da dik tana lura dasu sai tausayinsu yakamata wanda itama kuma shaidace wannan ba halinsu bane…! kawai dai k’addarace da kuma t’sat’sayi ya kusa afka masu,dan haka itace ta bada na baa ansa dayasa kowa kallonta cike da gamsuwa sbd ganin yadda fuskarta ta nuna alamun rashin ishashshen bacci…!

“jiya ne na kwana da ciwon ciki,bamu samu bacci ba nida ita sadeeyar sai wajen uku na dare,gakuma kukan datayi tayi shiysa fuskarta ta nuna hakan…”

ajiyar zuciya mai k’arfi musa ya sauk’e,jin momma ta anshesu daga wannan tambayar…!

kowa sannu yayi tama momma dakuma husna na fatan allah yabasu lafiya…!

wani bafade ne ya dayake sanye da kayan fad’awa aka masa iso zuwa parlon,inda ya shaidama musa an gama wanke motocin…!wanda sai a wajen ya shaida masu zai koma bama yanxu,sbd akoi aikin daya taso masa agarin kaduna na gaggawa gobe da safe k’arfe 9 na safe…! momma kam sam bata yadda ba,abinda ta sani kawai dai kunya ce zata hanasa zama ba wani aiki…!

saida yayi wanka ya shirya aka kai masa komai mota kamin yayi sallama da kowa amma banda sadeeya dako kallonta fa tun jiya bayasonyi…! har d’aki yashiga ya tadda momma tamasa addu’a sosai tare da nasiha mai rat’sa zuciya kamin ya fito sukayi sallama dasu husna,zainab,ihsan da sauran yaran gidan…! inda aliyu ma yashiga mota sbd akoi inda yake son zuwa…!

 

2:00pm na wannan ranar kasancewar lahadi ne,kowa yana gida dama,dan haka a daidai wannan lokacin ma lunch sukeyi a parlon baa baki d’ayansu,bayan sun kammala aka tattara wajen aminulla da areef sukace suna son magana da baa,yabasu izini…!

“baa dama wannan gidaje guda biyu daga gida kala d’aya na can bayan layinnan namu ne mukeso kabamu nida aminulla,tunda ba amfani zakayi dasu ba,sbd wlhi ba k’aramin birgemu wajen yayi ba…! gashi t’sarin ginin ya mana dan allah baa karka ce a’a…!”

areef ya k’are maganar yana marairaice fuska t’sakaninsu da allah kuwa suke so a basu d’in sbd gidan watannan daya wuce aka kammala sa had’add’e na bugawa a jarida kamar a k’asar waje…! wanda ko gidannan dasuke ciki baikai wancan girma ba…!

wani hararan tara saura kwata amni tafara antayo masu areef kalar na baku da hankali d’innan,amma sam basu lura bama…!

“aminulla da areef saidai fa kuyi hak’uri ku dubo wani cikin gidajena…! sbd wannan gidan dakuga na kashe dukiya sosai akansa na manyan yayunku ne wato aliyu da inoussa da in sunyi aure cikin wannan gidan nake so su tare da iyalansu…! dikdama sud’inma basu san da zaman gidan ba! amma domin su na gida wannan gidan badan ku ba…! ina fatan zaku je ku duba wasu amma bana y’an lelena ba ko…?”

kowa shiru yayi kamar anyi ruwa an d’auke cikin wannan parlon sunabin baa da kallon mamaki…!shikam ko a kwalarsa wlhi!sbd shifa baiga wani aibu ba akan yadda yake tafiyar da rayuwar cikin gidansa,da mutane da dama suke cewa akoi gyara cikin lamarinsa dana iyalansa…!

cike da t’samin jiki ko kuma ince sanyin jiki areef yace “shikkenan baa!basai ma ka bamu ba!zamuyi k’ok’ari insha allahu mu tada wasu ginin ko na anan garin bane ma…” daga haka ya mik’e ya fice daga parlon dawani kalar expression akan fuskarsa dana gaza gane na mainene…? aminulla ma ya take masa baya yana sakin murmushi dakai t’saye zaka iya kiransa dana takaici ne…!

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button