NIGERIA KO NIGER Complete Hausa Novel

tashin hankali kenan take amni ta k’ara farkewa da wani sabon kukan takaicin abinda inoussa yace,tana so ta t’sawatar masa kuma ta t’saida shi akann wayannan maganganun da yakeyi amma kuma sam ta kasa…! ita t’soronsa ma takeji kar taje yayi mata abinda bashi ne…! gani take kamar ba aliyu d’anta ba!
mik’ewa baa yayi da niyyar kwad’ama aliyu mari amma kuma saiya koma jagwaf kan kujera kamar wanda aka hankad’asa kan kujerar…!
kowa idan yayi wani yunk’uri na ganin ya dakatar da aliyu amma sai ya kasa…!
husna dasu sadeeya kam sun zama y’an kallo ne a wajen sai ido ne nasu…! umma jameela kam zuciyarta fari tas take na ganin wannan abu daya faru,wanda ko ita kanta bata tab’a tunanin faruwar wannan abu ba t’sawon rayuwarta…! amma kuma ta wani wajen tana d’an tausayin inoussa sbd itama tasan zafin kaso abu ammma kuma kananji kana gani yafi k’arfinka…! kamar yadda mahaifiyarsu(amni),ta shige masu hanci da k’udundune a cikin gidan…! wanda idan ta tuno hakan ma allah shi k’ara take masu cikin zuciyarta,tace wata kila sun fara girban abinda iyayen nasu suka shuka masu ne ta wannan hanyar…!
momma kam dikda abinda ke faruwa ma batayi yunk’urin tofa nata albarkacin bakinba…! tunaninta gaba d’aya ya karkata ne ta yadda zata gyara y’arta sosai na ganin zatayi farin ciki gidan aurenta batare data shiga cikin damuwa ba,tinda k’addarar husnar tazo akan zata zauna ne da abokiyar zama tin farko aurenta batare data d’an more kalar amarcinnan da akeyi ita da mijinta kad’ai ba…!
kowa dai da tunanin da yakeyi cikin zuciyarsa a wannan wajen…!
“shikkenan aliyu! ga nan fad’imatoun na bar maka ita har gaban abada…! kaje da ita!kuma a yau na fuskanci kalar ikirarin soyayyar da kakc cewa kanamin tin muna k’anana! kasha cemin kome na gani a duniyar nan idan ina sonsa muddin kana da hanyar mallakamin shi ! to kuwa na d’auka cewa ka gama mallakamin,amma gashi yanxu ka gagara aikata hakan a gareni? babu komai kaje da fad’imatoun,allah yabaku zaman lafiya cikin zamantakewar aurenku…!”
ya k’arashe maganar yana mai sakin kuka sosai mai matuk’ar tab’a zuciyar mai sauraro ! kowa tausayin inoussa ne ya kama masa zuciya a wannan wajen,haushi dakuma takaicin aliyu ya cika masa zuciya na ganin ya gagara sadaukarma da d’an uwansa farin cikinsa…!
aliyu ma sosai yaji zuciyarsa ya karye,amma ko a fuska bai nuna ba,wanda kuma nan take yaji kamar ana controlling zuciyarsa yaji tausayin inoussan yama baje t’saf…!
batare da yayi ma kowa magana ba ya fice daga cikin parlon yana sharar k’walla gwanin ban tausayi an rabasa da yarinyar dayake matuk’ar k’aunarta tin tana cikin t’summarta…! a haka nan dai zuciyarsa na matuk’ar zafi ya hau motarsa ya kama hanyar maiduguri cike da gudun ganganci masu t’saronsa suma suka take masa baya cike da zullumin kalar gudun da yakeyi a wannan lokacin…!
A cikin shashen maa d’inma kuma mik’ewa aliyu yayi xuwa gaban momma batare dayace ma kowa ci kanka ba yakamo hannun husna ya mik’ar da ita yamaida kallonsa kan mutanen dake cikin parlon…!
“babu abinda zan iya cemaku saidai nace allah ya kawoku cikin maiduguri lafiya a dik sanda kuka tashi dawowa…! wannan dai matata ce kuma inada iko da ita! dan haka a mat’sayina na mijinta na d’auki matata mun yafe rakiyar dangi damasu zuwa mana gulma cikin gidanmu kalar su wancan t’sohuwar (ya k’are maganar yana mai nuni da maaa data sake baki da hanci tana ganin rashin kunyar aliyun da basu san yana dashi ba????????)…!”
babu wanda yasamu zarafi magana saima turjewar da husna tafarayi tana kuka tana kiran sunan su momma amma an gaza samun mutun d’aya dazai dakatar dashi…!
ganin yadda take k’ok’arin b’ata masa lokaci yasashi d’aukarta kamar jaririya suka fice kowa ya bisa da kallo baki sake…!
bai direta ko ina ba sai ciki d’aya daga cikin jerin motocinsa wajen guda goma shabiyar da sha hud’u ke d’auke da sojojinsa,d’ayar dake t’sakiya kuma ta kasance wanda ake tuk’asa ciki kuma a cikinta yasaka husna ya rufe motar ya doshi shashin dayake da tabbacin fad’imatou da danginta na ciki ya shiga fuska a had’e kamar hadari…!
fad’imatou data farka itama safiya yau ko ruwa ta gagara sama cikinta banda sallar datayi sai kuka take ta famanyi ita a maidata gidansu tama fasa auren kowana daga cikin aliyu da inoussan…!
a wannan yanayin yasameta batare da yayima t’sofinnan magana ba ya sungumeta ita tanata yakushinsa ya sauk’eta amma yayi kunnen uwar shegu da ita! saida yaje bakin k’ofa da ita yaja burki ya juyo ya kallin wayannan t’soffin dakuma su shareefa dasuma sukebin aliyun da kallon mamaki yace “idan kuka gama gajiya da zama cikin nigerian kuje ku samu way’anda suka gayyatoku k’asar su maidaku inda kuka bullo saduwar alkhairi…”
yana gama maganarsa bai jira ansarsu ba yayi ficewarsa…! inda ya shiga motar daya ajiye husna a ciki ya shiga inda husna sa fadimatou suka saka shi a t’sakiya ya rungume ko wacce ta gefe hakan yasa suka gagara raba jikinsu danashi saikukan su ne tashi cikin motar…!
a haka suka kama hanyar maiduguri suma d’in…!
in tak’aice maku a wannan ranar y’an niger suka tattara yanasu yanasu sukabar nigeria !
musa ma d’aukar matarsa yayi suka wuce shashinsu dake cikin gidan sarautar…! baa ma da yamma ya kwaso kwansa da k’wark’watansa suka dawo maiduguri aka sallami dik bakin dasuka halarci d’aurin auren…!
farin ciki ne sosai ya cika zuciyar aminulla da areef kamar me a wannan ranar suna daga can kaduna amma komai gashi nan suna kallonsa kamar a tv…!
SABIDA WASUNKU NAYI TYPING AMMA NA RAGE YAWANSA INSHA ALLAHU…!?????????
*team aliyu and husna*
*team inoussa and fad’imatou*
*team ummie2018*
*comment*
*share*
*vote pls*
*follow me on wattpad@ ummie2018????????*
❤️ *ZAB’AB’B’U BIYAR(5)* ❤️
_Albishirinku ‘yan uwa????????, nesa tazo kusa, shahararriya kungiyar litatattafan hausa nan wacce ta saba fadakarwa da ku da nishadantar daku da dadadan littattafanta irinsu *SADNAF, WUTA DA AUDUGA, CHAK’WAKIYA, DOCTOR ZAHRAH, NIDA ARYAN, KYAN DAN MACIJI, ZURI’A D’AYA, NUNA SO GABAN KISHIYA, RAYUWAR AFREDARH, BAYAN AUREN DA SAURANSU* wato *HIKIMA WRITER’S ASSOCIATION,* ( *K’UNGIYA D’AYA TAMKAR DA DUBU*)ita ce wannan karan ta harrak’o domin sake kawo muku *ZAB’AB’B’U!, ZAB’AB’B’U!!, ZAB’AB’B’U BIYAR(5)!!!* ,wanda hazikan, fasihan marubutanta suka warware hikimarsu da Basirarsu wurin sank’amo muku labarai masu fadakarawa, ilimantarwa har ma da nishad’antar wa._
_Nasan zaku so kuji marubutan da kuma littattafan ko?????????, to ku karkade kunnuwanku????????,gasu nan kamar haka._
_*YAKIN MATA* wacce fasihiyar marubuciyar nan ta *DOCTOR ZAHRAH* ta sankamo muku wato *FATEEYZAH*_
_*ANYA KUWA?,* daga jajitacciyar marubuciyar nan ta *NUNA SO GABAN KISHIYA* wato *UMMIE2018*_
_*YOUSUF,* daga fasihiyar marubuciyar nan ta *KYAN DAN MACIJI* , ba kowa bace face *ZULAIHATw ALIYU MISAU.*_
_*RIBAR HAKURI,* wacce nagartacciyar marubuciyar *BAYAN AUREN* ta sambado muku wato *AISHA Y HANWA.*_
_*BAGIDAJIYA* , daga marubuciyar nan mai basira wacce ta kawo mukur *RAYUWAR AFREDARH* wato *HASEENART MUHAMMAD.*_
*’Yar uwata, kar ki bari wannna litattafan su wuce ki, ko kuma ki tsaya sauraren labari, ki harrako ki siyesu don a dama tare dake, akan farashi masu sauki da rahusa kamar haka:*