HAUSA NOVEL

NIGERIA KO NIGER Complete Hausa Novel

*ZAB’AB’B’U BIYAR___500*
*ZAB’AB’B’U HUDU___450*
*ZAB’AB’B’U UKU____400*
*ZAB’AB’B’U BIYU___350*
*IDAN DAYA KIKE SO_200* .

*Zaki biya kudi ta wannan Account din*

*Fatima sani Muhammad*
_Access bank_
*0796627818*

_tare da shaiidar biya ta wannan number????????07032266778_

_marasa account zaku iya screenshoot na kati mtn ko airtel ta wannan number???????? 07032266778_

*~SAI MUNJI KU MASOYAN K’WARAI????????~*
[9/12, 6:13 PM] ????oum muntaz????????????:   *NIGERIA KO NIGER…?*
_(wacece bora)_

*????????©HIKIMA WRITERS ASSOCIATION????????*

*_“`( home of peaces, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers✍????)️“`_*

*wattpad:UMMIE2018*
*oum muntaz✍????*
*whatsapp number:09076427357*

 

*page 32*

Ikon allah ne kad’ai yakai inoussa cikin garin maiduguri lafiya sbd kalar tuk’in gangancin dayakeyi…! yana shiga cikin gida ya wuce shashinsu ya kulle kansa a d’aki yana kuka sosai ba kad’an ba na tausayin kansa dakuma bak’in cikin abinda aka aikata masa da babu k’wak’k’waran dalilin dazaisa ya yarda bada son ran baa aka rabasa da farin cikin rayuwarsa ba…!wanda hakan yasa sosai yaji zafin mahaifinnasa ba kad’an ba…!

tin yanayin kukan na kad’an kad’an har abin ya girmama yafara tari sosai ba kad’an ba…! wanda hakan yasa wani dunk’ulallen jini mai had’e da t’soka yake t’satuwa a dik lokacin da yayi tarin…!????

a haka wani wahalallen bacci yayi gaba dashi cikin wannan yanayin…!

bai wani jima sosai ba su aliyu ma suka iso…! saidai shikam gidan da baa ya gina masu ya shiga…! gidan yakasance sama da k’asane daman,sama aka zuba kayan jeren husna da aka mata…! k’asa kuma empty ne…!

kamo hannunsu yayi da suke ta tirje tirje suna masa bori amma yayi kunnen uwar shegu dasu yayi biris…!

suna shigo cikin parlon k’asa daya kasance yalwataccen parlo ne sbd babba sosai mai d’auke da k’ofofi wajen guda hud’u…! saikuma ta gefe can inda mutum kan iya hawa upstairs nasu dake ta jikin bango wanda mutum idan zai sakko ma ba lallai a iya ganinsa ba idan yaso…!

labulaye ne kawai cikin wannan parlon kalan peach masu matuk’ar kyau da t’sari,inda pentin cikin parlon ma ya dace da t’sarin yanayin labulayen…!

 

husna ta d’ago da niyyar kartama aliyu rashin kunya da yazo mata gadan gadan idanuwansu ya sarke tare da fad’imatou a bazata…! wanda hakan yasa su zabura kusan lokaci d’aya suna nuna junansu jikinsu na b’ari sosaii ba kad’an ba,baku nansu yagaza furta koda kalma d’ayace…!

sam basu san junansu ba dik wannan budurin abubuwan da akeyi,sai yanxu suka shaida junansu…!

sosai zuciyoyinsu ke bugawa cike da mat’sanancin wani mai kama da kishi game junansu(???? anzo wajen fa????????‍♀️)…!

 

kamo hannun ya aliyu husna tayi jikinta na b’ari ta rungumesa ta kwata bisa faffad’an k’irjinsa tana sauk’e ajiyar zuciya kamar wacce tayi t’seren gudu…! shiko aliyu dama yazama statue ne yana kallonsu kamar tv cike da mamaki…!

fad’imatou ma sosai zuciyarta ke bugawa na ganin yadda husna tayi kanekane a k’irjin aliyun,wanda har cikin zuciyarta taji zafin hakan sosai…!

“ya aliyu,dan allah idan wannan ce wacce ya inoussa ke kuka akanta ka taimaka ka sakar masa matarsa ya aura…! wlhi baku dace da ita ba ko kad’an…! dan allah kasake……”

tun kamin ta k’arasa fad’ar abinda tayi niyya aliyu yayi mata wani shegen bangaza data kusan kaiwa k’asa allah ya tak’aita ta dafe bango,amma dikda haka saida ta buge k’ugunta …!

wani mat’siyacin kallo aliyu kebin husna dashi kalar na baki da hankali amma…! “wato sai yau na tabbatar baki da hankali asma’u! matar tawa kike ambata da matar wani banza wai shi inoussa…? to wlhi ahir d’inki…! ki kiyayeni! idan ba haka ba kuma billahillazi la’ilaha’illahuwa saina koya maki hankali cikin gidannan…! wawuya shashasha kawai…!” yana gama fad’ar abinda ke ransa ya kamo hannun fad’imatou da har cikin ranta taji dad’in abinda aliyun yayi,amma kuma fa bawai don tanajin wani sonsa bane cikin zuciyarta(????)

anan suka wuce sama suka barta tana sakin kuka sosai a wajen,na ganin wulak’ancin da aliyu yayi mata a gaban fad’imatou…! gashi babu halin guduwa sbd yadda ya gargad’i sojojin,kan kar abarsu su lek’a koda bakin k’ofa ne batare da izininsa ba…!

suna haurawa sama aliyu yafara bama fad’imatou hak’uri kamar zai durk’usa mata,amma tana masa bore ita kan lallai lallai saiya saketa shikuma yace bazai iya ba…!
saibin upstairs d’in itama takeyi na ganin yanda aka kashe dukiya sosai kamar baza’a mutu ba,wanda shima nan d’in kamar na k’asa yake 3bedroom da kuma kitchen guda d’aya sai babban parlo…!

a haka dai yasamu da k’yar ya lallab’ata bacci yayi gaba da ita…! shikuma ya t’sura mata ido sosai yakejin k’aunar yarinyar har cikin k’ok’on ransa kamar ya maida ta ciki…! a haka shima bacci yayi gaba dashi…!

Husna tana nan inda suka barta taga an fara shigowa da kayayyaki masu matuk’ar kyau da t’sari ana jibgesu a parlon…!

babu b’ata lokaci wasu garada kusan su takwas suka shigo suka fara aikin jeren wayannan kayayyakin…!

cikin awanni uku lafiyayyu suka kammala jeren d’akuna guda uku tare da parlo guda d’aya saikuma kitchen shima dik suka gamasa wanda ko wasu matan ma albarka…! ga dikkan alamu dai kalar aikin ba bak’onsu bane…! ganin yanayin kayan ya tabbatar mawa da husna kayan fad’imatou ne…!

 

sai bayan la’asar su aliyu suka tashi…! wanka sukayi cikin d’akin dasuka kwanta dashima shak’e yake da kayan alfarma na husnar…!

fad’imatou kam tagama plan d’in yadda zatayi ta bama aliyu wahala har ya gaji ya saketa taje ta auri masoyinta sbd taga aliyun sosai ya zurma cikin k’aunar tata…!

 

zaune suka tarda husna nata faman gyangyad’i a palon ga wani d’an banzan yunwa datakeji,wanda sud’inma sosai sukejin yunwar…!

 

ganin jere ba kamar yadda suka barshi d’azu ba yasa fad’imatou fashema aliyu da kuka sosai lokaci d’aya,wanda hakan sosai ya d’aga masa hankali yana tambayarta mai aka mata …?

itakuwa tace yanxu take son a canza jere a maida mata upstairs sbd ita batason down stairs…! wanda kuma itama kanta husnar ba k’aramin so takema upstairs ba amma babu halin magana…!

tanaji tana gani aliyu ya kira ma’aikatan a waya suka dawo suka fara exchanging na kayayyakin shikuma ya aika aka masu order na abinci ya cilla ma husna dake ta rakubewa cike da tsoron shi…! wanda har yanxu idan ya tuno tace masa ya saki fad’imatou sai yaji haushinta yakamasa sosai ba kad’an ba…! gidannan bai gama samun kansa ba sai bayan isha’i kamin…! inda wannan ranar kad’ai sosai aliyu ya jigatu a hannun fadimatou…!

itakam husnaty an zama abin tausayi ne sbd ko kallo bata ishe aliyu ba yau…!yana fushi ne sosai da itafa…!

B’angarensu baa magariba suma suka iso…! inda suka tarda masu t’saron inoussa wanda hakan ya tabbatar masu da cewa yana gida…!

babu kalar bugun k’ofar da ba’ama inoussa ba amma kuma shuru kamar babu shine cikin gidan,gashi anyi anyi a bud’e k’ofar nashi abin yaci tura…!sbd yabar key a jikin k’ofar tashi ta ciki…!

a wannan daren kam anga tashin hankali sosai ba kad’an ba,sbd sun tabbatar ba lafiya ba k’in bud’e k’ofar da inoussa yayi…! daga k’arshe ma wat’sewa akayi akabar amni da baa a k’ofar d’akin(nikam nace sbd ku ta shafa ne)…! kwanan zaune su baa sukayi anata masa magiya ya bud’e amma inaaa…? baimasan sunayi ba,sbd baisan inda kansa ma yake ba shikam ballantana yasan ana masa bugun k’ofa…!

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button