HAUSA NOVEL

NIGERIA KO NIGER Complete Hausa Novel

abinda basu sani ba shine abdul yazo shigowa domin daukar wanu abu yaji tabarar da muhammad da mariama suke aykatawa wanda hakan ya bata masa rai sosai take yakoma fada yakai kararsu wajen sheku aliyu domin adau mataki sbd gudun matsala…

an kira muhammad an masa tatas kuma an masa gargadin kar ya kuskura yasake sa daya daga cikin matansu suyiwa mariama girki idan duk kuyangi da yan aykin dasuke gidan bazasu iya ba shikkenan…

toh hakan da akayi ne suka samu salama har cikinta yashiga watan haihuwa inda ta suburbudo da kyawawan yayanta wanda suka gado tsantsar kyawu daga gurin kakansu wato aliyu dalhat…

anyi murna kwarai da gaske dasamun twins a cikin wannan gidan kuma dukkansu maza…

anyi shagali sosai ba kadan ba inda mariama ta tubure ita saida asawa hassan sunan babanta idan yaso sai husseini yazamana mai sunan sarki…

dashike giyar soyayya na dibansa ko hakan akayi ranar suna hassan aka saka masa suna inoussa husseini kuma aliyu…

haka ake rayuwa yau dadi gobe babu dadi lokuta na shudewa har su aliyu suka kai shekaru 5 babu wanda yakara haihuwa

toh a lokacinne aka bujurowa da abdul zancen kara aure baiyi jayayyya ba tunda yasan dama duk wanda zaizama sarki bai zama da mata daya…

taji ba dadi dukda ma dai tana da sanin cewa ba itakadai zata zauna ba amma haka tamikawa allah lamuransa sai sukazo mata da sauki…

yarinyar shehun borno aka auro masa

sai shima kuma muhammad yatada ballin kara aure aykuwa anyi babatu tsakaninsa da matar so…har yace mata da ace ba’a kara aure ita zai aureta ne…?

kunji pha halin namiji gaskiya sun bani da dariya…

bayanda ta iya sai yanxu ta fuskanci abinda suma sukaji da aka auro ta kuma gashi gwanda itama dukda hakan tunda kamin aure taji labari amma su sai ganinta sukayi kawai…

dolenta ta hakura ya auro wata yar gidan ogansa na wajen ayki mai suna farida itakam bata da wani matsala ko kadan dan bata shiga shirgin gidan tunda alokacin ma tana da wajen 26yrs irin wayanda suka jima basuyi aure bane…

za ta girmi mariama saida suyi sa’a da jameela…

wani abun mamaki shine alokacin da aka auro farida da fanna(matar abdul rahman)…

fanna,farida,jameela suka samu ciki a lokaci daya wanda wasu suka fara tsegumi ay wata kila hafsat juya ce…

dasuka tashi haihuwa duk suka haifo yayansu maza baki dayansu haka akayi ta murna da farin ciki…

yara suka ci suna  mubarak(fannah),areef(jameela) sai aminullah(farida mai sunan babanta)

zuwa wannan lokacin kam hafsat ta fawwala ma allah lamuranta kuma ta cire rai da haihuwa kwata kwata a rayuwar saita rungumi musa tunda shine zata iya tutiya dashi a ko ina nace nata ne…

shima yana son mommah nasa kasancewar haka yake kiranta…to kowa ma hakan yake cemata alokacin da musa yakai 15yra alokacin aliyu da inoussa suke da 10yrs saikuma yan uku wato areef,mubarak da aminullah suke da kimanin 5yrs

sannan kuma kananun yara guda biyu farida da jameela suka kara haihuwa kuma suma mazane  wanda suke da 2yrs faysat da abudulrahman…itakuma ma fanna takarasa haihuwar yaro shekararsa 3yrs mai sunan shehu aliyu ne kuma a halin yanxu abdulrahman shine sarki tun lokacin daya kara aure aka nadasa……

 

allah yayi wa zainabu rasuwa shekaru biyu dasu gabata gashi yanxu sarki baida lfy shima sai fatan allah yabasa lfy…

Ga babban abin farin cikin daya faru wanda makiya suke cikin tsananin bakin ciki sannan masoya suke cikin annashuwa…………

 

TEAM NIGER
TEAM NIGERIA

TEAM BUZAYEN AGADEZ
TEAM KANURIN BORNO

TEAM UMMIEN2018

*vote*
*comment*
*share*
*follow@ummien2018*
[9/8, 2:26 AM] ????oum muntaz????????????:     *NIGERIA KO NIGER…?*
(wacece bora)

*©HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*_( home of peaces, joint of entertainment to educate and enlight  our readers)_*

*wattpad:UMMIE2018*
*whatsapp number:09076427357*

page 4

HAFSAT da halimatussadiya sunsamu ciki a lokaci daya …  wayyo farin ciki idan kaga fuskokin makiya alokacin sai kasha mmk wasun kumaa kishi ne ke dawayniya dasu bawai basaso su haihun bane…

bama kamar cikin hafsat da akifi daukinsa kasancewar shine nafarko a gareta bayan ta shafe shekaru goma sha biyar da aure…

laulayi mai zafi halimatu ke fama dashi sosai ba kadan ba… ahaka sukayi ta rainon cikinsu wanda ba’asan wacce zata riga wata samun kanta ba…

wata safiyar ranar litinin halimatu ta tashi da tsananin nakuda wanda take shan wahala amma haihuwar baizo ba gashi kuma a gida suke ba’akaita asibiti ba…

hafsat bata da labari itama tana fama da kanta sbd yau ta tashi da ciwon mara amma babu wanda yasani…

irin kuskus dinda akeyi ne acikin gidan kasancewar duk suna gidan sarautar dazama a tsakanin bayi da yan aykin gida taji halinda yayarta take ciki…

tashin hankali kenan a kidime tawuce part na yar uwarta inda ta tarda farida ce ke kokarin karbar haihuwar kasancewarta likita ce mai zaman kanta amma bata ayki sbd kalan gidan datake rayuwar aurenta…

ganin halinda ta tarar da yar uwarta yasa cikin wani uban murdawa inda tazube a sume a wajen…

tashin hankali kenan bashiri aka kwashi hafsat da halima zuwa asibiti domin basu taimakon gaggawa tun a hanyarsu ta tafiya hafsat ta farfado sanadiyyar ruwanda farida ta shafa mata a fuska…

nakuda itama ta taso mata gadan gadan amma abin yaci tura ana isa asibiti aka wuce dasu dakin da aka ware musamman domin tun suna gida aka kirasu akan ana zuwa da matar sarki da yar uwarta…

farida ce akan hafsat tare da wata likita saikuma wasu likitoci mata guda biyu akan halimatu……

cikin mintuna 20 halimatu tasauka kuma alokacin hafsat ma ta suburbudo da yan matanta guda biyu…
ita kuma halima yar daya ta haifa…

inda take halima jini ya tsinke mata atake a wajen bata kara cikakken minti goma mai kowa mai komai wanda yafimu sonta ya dauke ta a fadin duniya mai cike da abubuwa na ban mmk…

hafsat bata gama dawowa seti ba taji shigowar shehu abdul tare da mohammad sun shigo suna mai maita kalmar innalillahi wa’inna ilaihir raji’un…

bata gama sani mai akewa salati haka ba taji ance ay yarinya ma takoma…

anan ne ta fuskanci abinda yafaru wai yayarta ce tarasu wacce suke uwa daya uba wacce bata da tamkarta a fadin duniya…

gawar halima shehu ya hade ya rungume wasu hawaye masu zafi suke zuba daga kuncinsa na radadin rashin mata ta gari wacce samun kalansu sai an tona acikin dari a samu masu kalan halinta guda biyar…!

kamar ba sarki ba haka ya kwakumeta ya gagata motsi ji yake kamar zata bude idanunta ko kuma yaji hannunta bisa kuncinsa tana share masa hawayensa tana fadin kuka bai kamace fuskarka ba jarumin miji na … wanda hakan tamasa alokacin mutawar zainabu…

hafsat kam tazama speachless a wajen domin kanta ya dau zafi ko kallon inda yemmatanta suke batayi ba…

tambayar kanta take wai shi dagaske ne abinda takeji ake fada yanxu yar uwarta ta tafi kenan har abada bazata sake ganinta ba sai a darussalam…?

innalillahi wa innailaihir raji’un kawai take ambata daga nan kuma bata sake sanin abinda ya kara faruwa ba…

sai bayan awa takwas wanda zuwa wannan lokacin halimatu na gidanta na gaskiya tare da yarinyarta mai kama da ita…wayyo mutuwa mai yankan kauna allah yajikan yan uwa musulmai na fadin duniya baki daya a duk inda suke ameen…

kowa mutuwar tashiga jikinsa inda jinjiraye suke tare da farida tana kula dasu kamin farfadowar uwarsu tabasu abincinsu…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button