HAUSA NOVEL

NIGERIA KO NIGER Complete Hausa Novel

aliyu ma ya koma bakin aikisa a cikin maiduguri amma yake sbd ya gujewa zuwa k’asa daban daban tinda yana da iyali…!

a daidai wannan lokacin kuma aikin da akayima wa aliyu yafara sauk’a akansa yafara dawowa cikin hayyacinsa akan dik abinda yakeyi…! sannan kuma tausayin d’an uwannasa yafara samun gurmi cikin zuciyarsa…! kunsa cewa dama dik aikin sihiri idan takai kwana arba’in saita lalace,saidai mutum dashike yamanta cewa shima ba a bakin komai yake ba wurin ubangiji yakoma a sake masa sabon aiki…!

 

*team aliyu and husna*
*team inoussa and fad’imatou*
*team ummie2018*

*comment*
*share*
*vote pls*
*follow me on wattpad@ ummie2018????????*

*INA MASOYAN KARANTA LITTAFAINA NA HAUSA NOVELS…?? GA HANYA NAN MAFI SAUK’I DA ZAKU NUNAMIN SOYAYYARKY TA HANYAR BIYAN KUD’IN KARATUN LITTAFINA MAI TAKEN “ANYA KUWA…?” AKAN FARASHI MAI SAUK’I NAIRA D’ARI BIYU KACAL NA KATIN AIRTEL KO MTN ZAKUYI SCREENSHOOT NASA KU TURA SHI TA WHATSAPP A WANNAN NUMBER????????09076427357 …! SAINA JIKU MASOYAN LITTAFAINA A DIK INDA KUKE???? A HALIN YANXU MA KUMA AN D’ANYI NISA DA FARA PAID PAGES????????‍♂️????????‍♂️*
[9/16, 1:55 PM] ????oum muntaz????????????:   *NIGERIA KO NIGER…?*
_(wacece bora)_

*????????©HIKIMA WRITERS ASSOCIATION????????*

*_“`( home of peaces, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers✍????)️“`_*

*wattpad:UMMIE2018*
*oum muntaz✍????*
*whatsapp number:09076427357*

 

*page 34*

aliyu na hango kwance kan gado sai sharara uban bacci yakeyi gumi na t’sat’st’safo masa sbd mafarkin dayakeyi ya matuk’ar dagula masa lissafi ba kad’an ba…!

komai daya faru tin daga ranar d’aurin aurensu…!xuwa ga rok’on da akayi ta d’irka masa kan ya rubutama fad’imatou takardarta,rashin lafiyar d’an uwansa mafi soyuwa cikin birnin zuciyarsa,da yadda yayi ignoring na mutane yana karta masu rashin mutunci idan suka kawo nasa suka kan aurensa da fad’imatou…! bugu da k’ari kumaa yadda yayi ta shukama husna rashin mutunci tindaga farko har zuwa wannan ranan t’saf kome ya dawo masa…! dakuma yadda yazama bawan mata???? a wurin fad’imatou komai fa yadawoma bawan allah nan tiryan tiryan ya dawo hayyacinsa…!

a mugun firigice ya farka daga wannan baccin wucin gadin da yayi shi da ranar allah na t’sawon mintuna talatin…!

dirowa yayi daga kan gadon a mugun gigice yayi waje da gudunsa,sak’k’owa yayi daga upstairs a hargit’se ya tadda husna zaune tasa tv a gaba tana kallo bakuma wai don tana fahimta ba!,tunani ne sosai yayi mata yawa cikin kwakwalwarta…!

baibi takanta ba ya fice daga gidan da wani irin gudu ko mota bai t’saya d’auka ba…! masu t’saronsa dake cikin gida suma suka take masa baya da k’afafuwa sunyi ready da bindigoginsu suna jiran ace musa as suce cas????

kasancewar babu nisa gidajen nasu cikin abinda bai haura mintuna tak’was ba yakawo su cikin gidan t’sohon soja…! wanda hakan yasa attention na kowa da kowa yadawo kansu aliyu dayaketa faman rarraba idanuwa yama rasa ina zai fara shiga t’sakanin shashin amni,baa,momma ko kuma inoussa…!

abinka ga babban gida cike yake da ma’aikata har ansamu masu kai rahoto aiga can aliyu yazo shi da gudu kamar ma ba’a hayyacinsa yake ba…! su areef da aminulla ma kuma suna gida dama dik suna shashen baa…!

kwai da kwarkwatansu kowa fitowa yayi domin ya bama idanunsa hakkinsa a cikin gidan,hatta fad’imatou datazo wajen amni suna hurarsu kamar ba sirikai ba ana bin aliyu da kallon k’arin bayani…! bai samu zarafin magana ba saiga motar su inoussa ya kunno kai cikin gidan …! wanda zuwa yanxu dama already shikam ya ajiye aikinsa sai zaman gida dayakeyi yana jinyar zuciyarsa…!

kowa kallon motar tasa yakeyi,shikuwa yasha mur abinsa batare daya kalli shashin da kowa yake ba yayi hanyar shashinsu fuska had’e kamar hadari! gabas…!

cikin mugun sauri da azama aliyu yayi gaggawar shan gabansa ya zube yakamo kafafunsa ya kifa kans bisa k’afafun inoussan yana sakin marayan kuka mai cin zuciya…!

kowa kallon aliyu yakeyi cike da mamaki amma banda areef da aminulla da sukasan dama rana mai kama ta yau tana nan zuwa cikin y’an kwanakin nan…!

wani mat’siyacin kallo mai kama da lafiya mallam ka rik’emin k’afa inoussa ke antayama aliyu yana d’age gira d’aya…?

aliyu kam baima san yanayi ba sbd kalar kukan dayakeyi sosai na fitar hankali yana maijin bak’in ciki da takaicin abinda ya aikata da baisan tak’amaimai dalili ba…! shidai yasan banda gaisuwa babi abinda ke had’asa da fad’imatou sbd ba wata shak’uwa bace t’sakaninsu amma ace wai shine ya aure ta a maimakon d’an uwansa har sukayi rayuwar aure…?

fisge k’afarsa inoussa yayi,yana k’ok’arin rab’awa yawuce abinsa aliyu ya k’ara tarosa yana mai sakin kuka sosai…!

“dan allah kayi hak’uri d’an uwana…!na kasance d’an uwa mai t’sananin son kansa a duniyar nan…! kaico da halina…!wlhi bansan haka zata faru ba…! bansan maai ya hau kaina ba har na gagara sadaukar maka da abinda kake ta faman tattalinsa t’sawon shekaru ashirin da d’aya…! bansan mai ya sameni ba,dan allah ka yafemin…! yanxunnan zan sake fad’imatou a maida auren zuwa kanka…! idan ba haka ba kuma bazan tab’a yafema kaina ba…!” aliyu ya k’are maganar yana mai sakin kuka sosai…!

kowa kallonsa yake cike da mamaki maganganunsa…!baa kam dake t’saye tin d’axu ya gagara magana shima sai kallon aliyun yake kamar a shirin film…! zuciyar fad’imatou da amni sosai ya t’sinke,jin kalmar da aliyu ya ambata na zai saki ita fad’imatou ba kad’an ba…!

zuciyar inoussa sosai take zafi ba kad’an ba…! hakan yasa bayyi wani jinkiri ba yakai ma aliyu da wani kalar mummunar naushi a hanci…! take kuwa hancin nasa yafara zubar jini a wurin wanda hakan yasa kowa ya zaro idanuwa cike da mamaki…! a harzuk’e sojojin aliyu suka mat’so da niyyar shigama ogannasu aliyu ya dakatar dasu…! babu yadda suka iya haka nan suka zuba ido ma inoussa dasai faman kaima aliyu naushi yake cike da t’sant’sar t’sanarsa data cika masa zuciya dakuma sauk’e fushinsa a wannan ranar…!

an gaza samun mutum d’aya dazayyi yunk’urin k’watar aliyu…! gashi kuma ba k’aramin bugu inoussa ke masa ba…! take fuskarsa tayi jage jage da jini yana ta layi amma ya gagarayin wani yunk’uri guda d’aya na k’watan kansa…!

bindigar d’aya daga cikin sojojin wurin inoussa ya wafta cike da k’warewa ya saita bindigarsa akan goshin aliyu xuciyarsa na tafarfasa sosai…!

zaro idanuwa kowa yayi cike da t’sananin t’soro da shiga tashin hankali anata sallallami a wannan wajen…! amni ma sosai tafashe da kukan ganin wannan ranar…! fad’imatou ma sosai illahirin jikinta keta faman rawa yana k’iran sunan inoussa amma baima san tanayi ba,sbd zuciyarsa a bak’i k’irin take a daidai wannan lokacin…!

aminulla da areef ma sosai suka t’sorata,haka nan su momma,umma jameela dasu anty farida kowa yashiga cikin t’sananin t’soron abinda ke shirin faruwa a wannan gidan…!

“inoussa ka ajiye wannan bindigar…” baa yayi maganar cikin t’sananin t’sawa da hargowa…! batare da inoussa ya d’auke bindigar daga goshin aliyu ba shima cikin hargowa yace “bazan sauk’e ba…! wlhi yau saina kashe wannan munafukin…! banda shi harma bashi da kunya har zaizo gabana yana cemin wani wai baisa abinda ya hau kansa ba a daidai wannan lokacin…? yarinya ta nuna bata sonsa amma haka nan ya bad’ama idanunsa toka ya tafi da ita har yayi sanadiyyar tusa mata k’aunarsa sannan kuma yanxu yaxo yace saketa…?
wannan d’in zalinci ne ko kuwa cin fuska…? toh wlhi…! wlhi…! wlhi…! ko babu ni a doron k’asa idanka kuskura ka saki fad’imatou allah ya isa ban yafe maka ba…!na riga na hak’ura da ita nikam…! sannan kuma kaima dole kabarta…! amma bata hanyar saki ba…! wannan hanyar da ita ka dace karabu da fad’imatou…!” inoussa ya k’are maganar yana mai sakin harbi da bindigar dake hannunsa na AK47…!
wani kalar ihu y’an gidan suka fasa sosai cike da t’sorata na ganin inda harbin ya sauk’a…!

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button