NIGERIA KO NIGER Complete Hausa Novel

*team aliyu and husna*
*team inoussa and fad’imatou*
*team ummie2018*
*comment*
*share*
*vote pls*
*follow me on wattpad@ ummie2018????????*
*INA MASOYAN KARANTA LITTAFAINA NA HAUSA NOVELS…?? GA HANYA NAN MAFI SAUK’I DA ZAKU NUNAMIN SOYAYYARKY TA HANYAR BIYAN KUD’IN KARATUN LITTAFINA MAI TAKEN “ANYA KUWA…?” AKAN FARASHI MAI SAUK’I NAIRA D’ARI BIYU KACAL NA KATIN AIRTEL KO MTN ZAKUYI SCREENSHOOT NASA KU TURA SHI TA WHATSAPP A WANNAN NUMBER????????09076427357 …! SAINA MASOYAN LITTAFAINA A DIK INDA KUKE???? A HALIN YANXU MA KUMA AN D’ANYI NISA DA FARA PAID PAGES????????♂️????????♂️*
[9/17, 5:52 PM] ????oum muntaz????????????: *NIGERIA KO NIGER…?*
_(wacece bora)_
*????????©HIKIMA WRITERS ASSOCIATION????????*
*_“`( home of peaces, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers✍????)️“`_*
*wattpad:UMMIE2018*
*oum muntaz✍????*
*whatsapp number:09076427357*
*page 35*
Husna tin ganin yadda ya aliyun ya fice ta tabbatar da cewa ba lafiya ba,hakan yasata mik’ewa tashige daya daga cikin d’akunanta ta sako kaya sannan tasa hijjap nata ta d’auki key na motar ta tafito mai gadi ya bud’e mata k’ofa…!
gidansu ta wuce domin kuwa tana da tabbacin can aliyu da mukarrabansa suka nufa,a k’ofar gida tayi parking na motarta hakan yasa babu wanda yasa da zuwanta,yadda taga y’an gidan nasu abin ya k’ulle mata kai,amma su babu wanda ya lura da zuwanta ma kwata kwata…!
yadda taga ya aliyun na jigatuwa a hannun ya inoussa abin ya sosa mata rai,amma kuma ganin iyayensu ma babu wanda yayi yunk’urin karb’ansa yasata sunkuyar dakai hawaye na zuba daga cikin idanuwanta,ta juya da niyyar barin gidan taji wannan dogon sallallami da aka farayi wanda hakan yasata cin birki ta d’ago idanuwanta na ganin abinda ke faruwa,inoussa tagani ya saita bindigarsa a goshin aliyu,hakan ya matuk’ar girgiza mata zuciya,batare da kowa ya lura a lokacin tayi wani kalar t’salle tashiga t’sakanin inoussa da aliyun,hakan yasa harbin yasameta a maimakon aliyu…! a kafad’arta…!
inda kuma a daidai lokacin d’aya daga cikin sojojin aliyu yasamu nasarar waftar bindigar hannun inoussan batare daya lura ba,wasu kuma suka samu suka rirrik’esa dan kar yayi wani yunkuri na sake aikata makamancin abinda ya aikata…!
a kid’ime momma da sai yanxu ta lura da zuwan husna wajen ta fasa gigitaccen ihu,a kuma lokaci d’aya tana dosan wurin da husnar ke yashe a k’asa batare data mot’sa ba tin fad’uwar datayi…!
aliyu ma da wani mugun gudu ya k’araso wajen har rige rigen d’aukarta sukeyi shida momma,allah yasa ya rigata d’aukar husnar,sauran y’an gida kuwa ba k’aramin gigicewa sukayi ba a wannan ranar…!
general hospital aka wuce da husna,inda aka wuce accident and emergency da ita,aliyu ,baa ,momma,su anty farida banda zirga zirga babu abinda sukeyi a wajen…!
amni da fad’imatou ma sosai suka razana da wannan danyen aiki da inoussa yayi,inda suma suna nan daga zaune suna tunaninnika…!
mik’ewa fad’imatou tayi da niyyar sayo ruwa sbd k’ishin data keji tin d’azu,batayi taku hud’u lafiyayyu daga wurinba jiri ya kwasheta ta zube wurin,nanma ba k’aramin dagula masu lissafi yayi ba,likitoci ne suka d’aurata akan gado akayi mata dik gwajen gwajen daya kamata sbd tasamu peace of mine nata gudun samun mat’sala,sbd gwaje gwajen da sukayi sun tabbatarr da cewa tana da karamar shigan ciki…!
damuwar dasuke ciki a yanxu ne ya hana su nuna farin cikin su a fili,saina zuciya…!
a wannan ranar an samu nasarar cire ma husna bullet d’in daya sameta a kafad’arta,an kumayi mata dik wani abinda yakamata na treatmen…!
inoussa kam yana gida ya kulle kansa a d’aki,sai kuka yakeyi akan wannan abu daya faru dasu a wannan ranar,yayi dama sosai shi kad’ai sbd yadda yagaza samun controlling na fushinsa akan aliyu har yazo yayima yarinyar illa da bata san hawa ba,batasan sauk’a ba…!
gidan yazama shuru sosai kowa ba dad’i,a haka nan su areef suka koma bakin aikinsu batare dasunyi sallama da mahaifinnasu ba sai iyayensu mata…!
an ci gaba da jinyar husna kuma alhmdlh ana samun ci gaba,shehu abdul dasu musa,sadeeya ma dik anzo an dubata…!
allah daya taimaki fad’imatou ma laulayinnata bamai wahala bane sai son bacci kawai,amni dasu momma ne suke kula da husna a asibiti,sbd yanxu amni ma ta shafama kanta lafiya ne ta fuskanci alk’ibla babu shiri…!
saida aka shafe watanni biyu ana jinyar husna kamin ta warke sumul abinta kamar ba ita tayi ciwo ba suka dawo gida,inda suka yada zango a gidan baa…!
wanda xuwa wannan lokacin dik wanda yaga aliyu da inoussa saiya tausaya masu ba kad’an ba,dik sunbi sun lalace babu abinda mutum zai gani sai k’asin wuya gwanin tausayi,babu wanda yasan halinda inoussa yake ciki na ciwon zuciyartasa…! sai shi kad’ai,gashi kuma ciwon ba k’aramin cinsa yakeyi ba batare daya ankare ba…!
harma takai takawo yanxu idan yayi tari sai jini ne yake fet’so masa abin dai babu kyan gani ko kad’an…!
arerf dasu aminulla na sun dawo gida,inda suka buk’aci kan suna son magana da kowa da kowa,bama aka tarkata aka tafi baki d’aya gidannasu…!
inda aka had’a meeting na family baki d’ayansu a shashin maa,kowa ya nat’su domin jin dame su areef yau kuma sukazo…!
flash back
a lokacin da baa ya fatattaki su aminulla akan wannan gidan,sosai sukaji ciwon kalaman mahaifinnasu dayace wai ai gidan na y’an lelensa ne…! hakan yasa sukaci alwashin aliyu da inoussan na bazasuyi rayuwa cikin wannan gidan ba…! k’iyayyar dasuke ma yayyun nasu ya dad’a bunk’asa cikin zuk’atansu…!
a can kaduna wurin aikin nasu ma su kawaii neman hanyar dazasubi sukeyi da zasu tarwat’sa rayuwa aliyu da inoussa,sai suka ta kwal uban dakan da baa zayyi akan yaran dayake ikirarin y’an lelensa…!
saida aure yazo daf,kamin suka samu mafita bisa ga jagorancin wani abokin aikinsu…;
wajen mallam yakaisu,inda suka narka ma malamin kud’i suka kwararo masa bayanin kalar aikin dasukeso ayi masu…!
munafukin kuwa mak’iyin allah yaga kud’i ya basu wani madubi yace suje dashi zasuna ganin dik abinda zai faru…!
so tin daga lokacin komai suna kallo daga wannan madubin kamar a tv,har zuwa ranar d’aurin auren…!
bak’ak’en aljanu mallam ya turama baa dakuma dik wa enda suke da ruwa da t’saki a wannan auren bayan an gama d’aurin auren aliyu da husna…!
suma ba cikin hayyacinsu suke ba aka d’aura auren wato auren aliyu da fad’imatou a maimakon da inoussa…!
inoussa kam dama shi yana cikin hayyacinsa,sbd sunso ne zuciyarsa dama ta buga yaji ya t’sani d’an uwannasa,yaso ya kashe aliyun ma baki d’aya idan yaso shima ya fad’i ya mutu sbd suma sunsan ba k’aramin so yakema fad’imatou ba,suga yanda mahaifinnasu zayyi idan ya rasa y’an lelen nasa…!
sannan aliyu ma aka dasa masa zazzafar soyayyar fad’imatou a zuciyarsa,ta yadda zai ringa jin idan babu ita bazai iya rayuwa ba…!
dik abinda yake faruwa saida suka fad’a da yadda mahaifinnasu ya nuna fiifiko t’sakaninsu da y’an uwansu basu rage komai ba sai suka amayar a wannan wurin…!
tak’aitaccen abinda yafaru kenan…!
kowa shuru yayi a parlon ana mamakin wannan abu da al’ajabi,banda baa daya sunkuyar dakansa,yana maijin nadama na taso masa daga can k’ark’ashin birnin zuciyarsa, ko kad’an baiga laifin wayannan yaran ba,gaba d’aya kocokan ya d’aura ma kansa laifinne a wannan gabar,sbd shine yakasa kwatanta adalci a t’sakanin iyalansa har wannan abu yazo ya auka…!