NIGERIA KO NIGER Complete Hausa Novel

a gurguje pls????????
bayan wata biyu…! sosai rayuwar gidan baa ta canza t’sari ba kad’an ba,komai anayinsa ne daidai da koyarwar fiyayyen halitta…! dan haka a kullum idan kashiga wannan gidan yanxu suna cikin walwala ne…!
an t’saida bikin inoussa da shareefa k’anwar fad’imatou,mubarak da zainab,aminulla da zainab (k’anwar husna ta bama) saikuma areef da maagana…!
sosai fad’imatou ke samun kulawa a wajen kowa da koda dake cikin wannan gida ita da husna…! kuma yanxu aliyu ma baya gari,sbd ya tafi can k’asar rassia akan wani gagarumin yak’i dazai d’aukesu kimamin wata goma kamin su dawo…!
deeya ama anata fama da laulayin k’aramin cikinta itama yanxu ta zama matar sarki,sbd shehu abdul yayi murabus????
*zakuji ni shuru kwana uku saina k’arasa maku page d’in daya rage zan sake maku baki d’aya????????????????*
*team aliyu and husna*
*team inoussa and fad’imatou*
*team ummie2018*
*comment*
*share*
*vote pls*
*follow me on wattpad@ ummie2018????????*
*INA MASOYAN KARANTA LITTAFAINA NA HAUSA NOVELS…?? GA HANYA NAN MAFI SAUK’I DA ZAKU NUNAMIN SOYAYYARKY TA HANYAR BIYAN KUD’IN KARATUN LITTAFINA MAI TAKEN “ANYA KUWA…?” AKAN FARASHI MAI SAUK’I NAIRA D’ARI BIYU KACAL NA KATIN AIRTEL KO MTN ZAKUYI SCREENSHOOT NASA KU TURA SHI TA WHATSAPP A WANNAN NUMBER????????09076427357 …! SAINA JIKU MASOYAN LITTAFAINA A DIK INDA KUKE???? A HALIN YANXU MA KUMA AN D’ANYI NISA DA FARA PAID PAGES????????♂️????????♂️*
[9/18, 10:26 PM] ????oum muntaz????????????: *NIGERIA KO NIGER…?*
_(wacece bora)_
*????????©HIKIMA WRITERS ASSOCIATION????????*
*_“`( home of peaces, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers✍????)️“`_*
*wattpad:UMMIE2018*
*oum muntaz✍????*
*whatsapp number:09076427357*
*page 36*
An d’aura auren su aminulla,areef,mubarak dakuma inoussa baki d’ayansu…! zainab can bama aka kaita,saikuma areef da aminulla a dank’areren gidan da baa ya gina masu suma kamar yadda yayi ma su aliyu…! saikuma inoussa dashima aka kawo masa amaryarsa shareefa aka ajiyeta a gidan inoussa shima dasai yanxu aka bud’e gidannasa daya t’sara kalar rayuwar da zayyi da fad’imatou,amma kuma gashi k’addara ta gitta allah bayyi akan shine mijinta ba sai d’an uwansa…!
sadeeya ma ta haihu satin daya gabata ta haifi yarinyarta mace dataci sunan maman musan watoh haleema kenan mai sunar sadeeyar kanta…!
aliyu bai dawo ba akayi auren sbd yana can baki aikinsa,wanda a halin yanxu wata biyu kenan da d’aura auren…! dawowar aliyu daga russia kuma saura wata biyu…! inda a wannan ranar kuma aka wayi gari da nak’udar data tasanma fad’imatou gadan gadan…!
inda hankalinsu amni dasu husna da itama yanxu akoi kyakkyawar fahimtar juna t’sakaninta da surukar tata dakuma kishiyartata ya tashi sosai ba kad’an ba…!
momma dasu anty fareeda suma sosai suke tausayama fad’imatoun,umma jameela,amni,husna da baa ne suka wuce da ita asibiti mafi kusa dasu aka wuce da ita labour room…!
babu wanda yakira aliyu ya fad’a masa ko kad’an…! sai kiran inoussa da amni tayi ta shaida masa kan cewa suna asibiti,wanda hakan yasa shi xuwa tare da matashiyar matar tasa da yanxu ne take kan girma wato shareefa k’anwar fadiman…!
basu wani d’auki t’sawon lokaci ba suna zarya a bakin labour room d’in suka farajin kukan jaririya…! hakan yasa su dik mik’ewa cike da k’aguwa a fito masu da ita…!
aikuwa saiga wata likita tafito daga d’akin bayan kamar mintina ashirin da sauk’ar fadiman,hannunta nad’e da baby cikin towel fari k’al dashi fuskarta shimfid’e da murmushi ta nufosu sbd tasan su suka kawota…!
har rige rigen isa ga likitar suke na ganin kowa yariga karb’an yarinyar…! allah kuwa yabama amni damar karb’ar yarinyar fuskarta washe da wani kalar expression na farin ciki…!
banda hamdala babu abinda suke sauk’ewa a wannan lokacin,sai inoussa dako kallon inda yarinyar take bayyi ba yace “doctor yaya jikin maman babyn yanxu…!? dafatan dai tana cikin k’oshin lafiya ko…?”
kowa kallonsa yayi da mamakinsa amma sai kawai suka share…!
cike da sakin fuska tace “lafiyanta qlaou yallab’ai anata faman kint’sata ne yanxu bada jimawa ba za’a fito da ita…!”
sosai labari ya bazu cikin wannan ranar kowa sai son barka yake masu…!husna ce ta k’ira aliyu ta fesa masa albishjr na samun beautyfull baby mai kama da maman sak…!
wayyo aliyu ma kamar ya fiffike ya waro nigeria a wannan ranar haka yakeji sbd farin ciki…!
mai jego ma sosai take samun kulawa na musamman daga surukar tata…! kusan koda yaushe husna ma tana can shashen amnin tana mak’ale da baby,sosai take son yarinyar bana wasa ba…! itama kuma zata so ace tasamu baby nata nakanta sbd ba k’aramin son yara takeyi ba…! kunsan ance mai d’a kuma wawa,hakan yasa sosai fad’imatou ma ta k’ara sakewa da husnar fiye da baya…! idan ba wanda yasani ba a cikin masu zuwa barka babu mai tab’a sanin cewa kishiyoyi ne…!
ranar suna inoussa ne ya rad’a ma yarinya suna a bisa kyautar y’ar da aliyu yayi masa tin ranar da aka haifeta…! ta waya ya k’ira ya shaida masu amni kan ko bayan ransa wannan yarinyar ta inoussa ce halak malak yabar masa ita…! wanda hakan yasa dik wani haushi dakuma kishin aliyun a zuciyar inoussa kashi saba’in da biyar yabi iska ya ware…!
sunan yarinya mariam wato mai sunan amni akayi mata inkiya da yumna…!
sosai amni ta zage tana kula da mai sunarta dakuma sirikartata…! su aminulla ma an zama iyayen sosai suke son wannan yarinya ba kad’an ba…!
lokaci da sukayi arba’in ya rage saura sati uku dawowar aliyu aka fara shirye shiryen dawowarsa babu kama hannun yaro…! sosai momma ta k’ara zagewa da gyaran y’ar tata ciki da bai da ingantattun magungunanmu ma mata masu t’sari ciki da waje…!
aikuwa take saiga nan fatar ta ta sake fitowa,wanda zuwa wannan lokacin ita kanta saita keji tana buk’atar namiji bana wasa ba…! sbd yadda haka nan ita kad’ai t’siyayar zuwa takeyi ita kad’ai????…! gashi kuma ta d’aurata akan hanya na yadda zata zauna da mijinta dakuma abokiyar zamanta lafiya batare da wani b’araka ya b’ullo daga gareta ba…!
amni ma sosai take gyaran fad’imatoun da ingantattun magungunansu na can niger d’in da y’an gidansu sukazo mata dashi a lokacin da sukazo suna…!
abindai ba’acewa komai,yemmatan aliyun sun sake fitowa sunyi fes dasu abinsu…! sannan yumna ma sosai kyawunta dakuma kamarta da mahaifiyarta yana sake fitowa…! tayi b’ulb’ul abinta gwanin sha’awa…!
anje an ansake kwaskware gidan su aliyun an gyara masu koma…! ana saura kwana uku dawowar aliyun baa ya tarkatasu yasake masu nasiha sosai kamin su anty farida dasu umma jameela suka rakasu da sauran dangi da dik yakamata…!
abin mamaki da kuma suka dawo sai husna taga an maida kayanta upstairs ta fad’imatou kuma an dawo mata dashi k’asa…! da mamaki take kallon koma wanda idan bata manta ba ai itace dakanta fad’imatou tace ita sama takeso amma gashi yanxu taga akasin haka…!
bayan dik an wat’se an barsu su kad’ai husna tawuce sama domin ta wat’sa ruwa tayi shirin kwanciya tinda xuwa wannnan lokacinma wajen k’arfe tara na darene…!
itama bedroom fad’imatoun tashiga tana maijin farin cikin dawowarta gidan gwarzon nasu wato aliyu…! sbd dikta t’siya zama cikin surukai dole zakaji ka a d’an takure ba kamar yadda zaka sakata ka wala ba cikin gidanka… !