HAUSA NOVEL

NIGERIA KO NIGER Complete Hausa Novel

Bayan husna tayi wanka ta d’akko wani t’suminta da momma tabata akan kullum tana shansa kamin ta kwanta bacci kuma idan ya k’are ta k’irata a waya ta fad’a mata…!

bayan tasha ta shirya cikin wani riga da wando mai d’an kauri daya matuk’ar da siffofinta cikakkiyar d’iya mace kasancewar akoi d’an sanyi a garin…! kanta sanye yake da wani hula kalar mai fuskar kuliya d’innan na y’an gayu sosai tayi kyau tana fidda k’amshin wani shegen turare mai matuk’ar sanyaya zuciya…! sakkowa k’asa tayi tana lat’sar wayarta,inda kamshinta ne ya shaidama fad’imatoun isowarta tin kamin taganta…

wanda itama take sanye cikin wani mini skirt nata kalar pink had’i da wani rigarta mai hannun best,jikinta sai fitar da wani fitinannen k’amshi yakeyi ta baza dogon gashinta domin yasha iska sbd ta wanke kannata…! ga kuma yumna datake shayarwa…!

k’urama junansu idanuwa sukayi kamar masu son gano wani abu…!wani masifaffen kishin junansu ke taso masu a lokaci d’aya na ganin babu wacce zata nunawa y’ar uwarta wani abu a fagen iya kwalliya ko makamanci hakan…!

saikuma suka d’auke kawunansu a kusan lokaci d’aya cike dajin kunyar kallon k’urillar dasuke ma junansu mara dalili suna koran shed’an cikin zuk’atansu…!

yumna ma komawa baccinta tayi,hakan yasa ta kwantar da ita akan 3seater tana mai fuskantar husnar da gaba d’aya hankalinta yanaga chart d’in da sukeyi da y’ar uwar ta wato sadeeya…!

“husna idan bazaki damu ba ina son nayi magana dake dan allah…”

ajiyar wayar tata husna tayi tana mai fuskantar fad’imatoun da diikkanin hankalinta alamun ina jinki…!

“dama so nake dan allah nabaki hak’uri akan dik abubun daba aikata maki a baya a cikin gidannan…! da wanda na aikata maki shi dan gangan dakuma wanda na aikata maki bisa rashin sani dan allah…!”

fad’imatou ta k’are maganar tana mai dafa kafad’ar husnar…!

d’an murmushi husna tayi kad’an kamin tace “karki damu fatima…! wlhi ko kad’an ban rik’e ba a zuciyata…! na maki uziri a wannan lokacin sbd nasan d’an adam ajizine…! kuma ko nima banfi k’arfin aikata kuskure makamancin hakan ba…! dan haka komai yawuce kuma dan allah karki sake tadomin wannan maganar sbd bazanji dad’in hakan ba…!komai ya riga yawuce sai muyi k’ok’ari muga mun tari gaba mukuma kore d’ik wata b’araka da zata iya shigowa cikin rayuwar aurenmu dakuma hana kwanciyar hankalin mijinmu dama mu kanmu baki d’aya…!”

haka nan su husna da fadima suka sake samun kyakkyawar fahimtar juna t’sakaninsu…!

*bayan kwana uku*

*team aliyu and husna*
*team inoussa and fad’imatou*
*team ummie2018*

*comment*
*share*
*vote pls*
*follow me on wattpad@ ummie2018????????*

*INA MASOYAN KARANTA LITTAFAINA NA HAUSA NOVELS…?? GA HANYA NAN MAFI SAUK’I DA ZAKU NUNAMIN SOYAYYARKY TA HANYAR BIYAN KUD’IN KARATUN LITTAFINA MAI TAKEN “ANYA KUWA…?” AKAN FARASHI MAI SAUK’I NAIRA D’ARI BIYU KACAL NA KATIN AIRTEL KO MTN ZAKUYI SCREENSHOOT NASA KU TURA SHI TA WHATSAPP A WANNAN NUMBER????????09076427357 …! SAINA JIKU MASOYAN LITTAFAINA A DIK INDA KUKE???? A HALIN YANXU MA KUMA AN D’ANYI NISA DA FARA PAID PAGES????????‍♂️????????‍♂️*
[9/19, 3:11 PM] ????oum muntaz????????????:   *NIGERIA KO NIGER…?*
_(wacece bora)_

*????????©HIKIMA WRITERS ASSOCIATION????????*

*_“`( home of peaces, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers✍????)️“`_*

*wattpad:UMMIE2018*
*oum muntaz✍????*
*whatsapp number:09076427357*

 

*page 37*

*bayan kwana uku*

A yau aka tashi da shirye shiryen tarban major general aliyu muhammad bama bayan t’sayin watanni goma da baya tare da ahalin nasa…!

sosai aketa farin ciki da dawowarsa bama kaman matansa,dik kuwa dai da agefe d’aya na zuciyar fad’imatou na zullumin kalar tarbar da zata samu daga wurinsa…! amma haka nan ta daure itama tana kyautata masa zatoh cikin zuciyarta…!

sosai husna da fad’imatou da masu aikinsu da aka had’osu jattijuwa d’aya dakuma matashiyar y’arta suka kint’sa komai da komai…!

sannan kuma suka mawa oga girki mai rai da lafiya kala kala…! wanka fad’imatou tayi ma baby yumna aka kint’sata cikin kayanta mai matuk’ar kyau da t’sada da dik cikin kayan da ubanta inoussa ya saya mata…!

shareefa ma ta shigo taya su aikin,dan haka itace ta rik’e yumna sbd itama uwar yumnan tasamu damar kint’sa nata jikin…!

k’arfe biyu daidai jirginsu aliyu ya sauk’a a filin jirgin maidugurin…!inoussa,aminulla,areef dakuma sadam ne suka tarbosa daga filin jirgin …! ya buk’aci zai fara xuwa gaishe da iyayen nasu kamin ya wuce gidannansa…! babu musu sadam dake driving na motar ya danna horn a makeken gate d’in dake gidan nasu wani ingarman soja ya bud’e musa bayan ya tabbatar da cewa y’an gidane…!

a parking space suka ajiye motar dik suka fiffito,inda suka wuce part na mahaifinnasu dasuka samu sauran yaran dik acan sai hira akeyi cike da walwala dakuma k’aunar junansu…!

iyayensu mata ne kawai basa wurin,saikuma ilham da yanxu itama sam zaman gidan baya mata wanj armashi sbd an d’auke mata yayun nata baki d’aya tana daga gefen mahaifinnasu tana ta mat’sar k’walla alamun dai wani abu take so aka hanata…!

kowa yayi farin ciki da dawowar aliyu cikin k’oshin lafiya…!inda ya shiga dikkanin part na matan baban nasa yagaida su daga k’arshe ya shiga part na mahaifiyarsa da itama sosai tayi farin ciki da dawowar d’an nata cikin k’oshin lafiya…!

saida akayi sallar la’asar kamin aliyu yayi sallama da y’an gidan nasu,suka d’auki hanyar gida a motar inoussa ana take masu baya…! horn inoussa ya zuba wanu kurtun soja ya wangame masu k’ofa suka kunna kan motar tasu cikin gidan…!

wanda hakan yayi daidai da fitowar shareefa hannunta d’auke da yumna da niyyar wucewa gidanta da yarinyar,inda kuma allah ya taikamaka ma yarinyar bamai hayaniya bace da an banu…!

da fara’arta ta k’ariso wurin nasu wanda itama take sanye cikin wani alkyabba kalar na gidan sarauta d’innan…! hakan yasa ko ina na jikinta a rufe yake ruf ko kayan datasa ta ciki ba’a gani…!

“sannunku da zuwa yaya’s…” take fad’a fuskarta shimfid’e da murmushi!

cikin murmushi sosai aliyu yake ansa mata a lokaci d’aya kuma yana ansar baby yumna a hannun shareefa sosai ya rungume yarinyar for d first time cike da t’sant’sar shaukinta dakuma soyayyarta ba kad’an ba shikuwa oga inoussa ko kallon inda suke baiyi ba,sbd shifa babu wani jituwa kona second d’aya t’sakaninsa da yarinyar sam…!

karb’ar yumna inoussa yayi a hannun aliyun suka wuce gidansa bayan yayi sallama da aliyun shareefa ma ta take masa baya cike da sanyin jiki na halin ko in kula da mijin nata ke nuna mata…!

da kallon tausayi aliyu ya rakasu…! sosai yake tausayin d’an uwannasa yanzu shima…! sbd shifa shaida ne da kalar yadda inoussa keson fad’imatou tin tana k’ank’anuwarta amma gashi nan laifin da basu suka aikata ba yasa k’addara tayi ma d’an uwannasa yankan k’auna da muradin zuciyarsa…!

ajiyar zuciya mai k’arfi ya sauk’e bayan yaga fitarsu daga cikin gidan ya maida akalar kallon nasa akan sojojinsa dasukayi zuru zuru dasu…! fahimtar mai ogan nasu ke nufi yasa su sara masa dik suka wat’se suka barsa shi kad’ai a haraban wurin…!

cike da takunsa na izza dakuma t’sant’sar jarumta ya doshi main entrance na gidan,wanda sosai zuciyar y’an mazan yafara bugun kalangu sbd rashin sanin tak’amaimai kalar tarbar da zai samu daga matan nasa…!

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button