HAUSA NOVEL

NIGERIA KO NIGER Complete Hausa Novel

**washe gari da safe ta rigasu farkawa inda ta mik’e a gurguje bayan tayi wanka ta chakare cikin adonta mai kyau da t’sari da wani fitinannen doguwar riga na roba daya kama jikinta sosai,tayima yarinyarta wanka itama ta shiryata ta fesa masu turare mai daddad’an k’amshi ta d’auko ta a kafad’a suka fito parlo…!inda ta tarda iya mai aikinsu tare da y’arta harsun gama share dik wani lungu da sak’o sun game masu da turaren wuta…!

y’ar iyance ta amshi yumna ita kuma fad’imatou ta fad’a kitchen cikin k’ank’anin lokaci ta had’a masu breakfast my sauk’i ta jere masu komai bisa dining ta wuce d’akinta ta sake shek’o wani wanka sbd wannan yariga daya game da k’arnin kitchen…!

zama tayi kan kujerar parlo bayan ta karb’o yarta ta shayar da ita suka fara kallonsu suna zaman jiran fitowowarsu aliyun…!

sai wajen k’arfe goma kamin tafara jin k’aran takalmi nansu…!maida hankalinta ka tv tayi tana korar shed’an sbd gangar daya fara buga mata akanta! take kuwa ta dawo cikin hayyacinsa ta mara masu murmushin yak’e sbd karsuga gazawarta tin daga yanxu…!

cikin wani riga da zani na atamfa husna kuma ta shryo ta kashe d’aurinta fuskarta sai fidda k’yallin amarci yakeyi…!aliyu kam cikin k’ananun kayansa na gado ya shirya,sbd shikam da wuya agansa da manyan kaya idan ba ranar friday ko kuma d’aurin aure ba…!

kunya ce takamasu sunsan suma basu kyauta mata ba,amma kuma ganin bata nuna ba ko a fuska sai suka sake da ita suna jinjina mata…!

haka nan aliyu ya karb’i y’ar tasa sai faman wasa yake mata,bayan sun gama breakfast nasu ma zama sukayi suna ci gaba da hirarsu…!

******Haka nan rayuwar cikin wannan gidan ke tafiya cike da farin ciki dakuma walwala da sanin yakamata! a t’sakankanin wannan lokacin sosai aliyu yayi wani uban tumbi sbd morewar dayakeyi a wajen way’annan matan nasa…!

sosai suka samu muhalli mafi girma da rinjaye cikin zuciyarsa,harma yana rasa wacece tafi samun babban mat’suguni cikin zuciyarsa sbd ba k’aramin kyautata masa sukeyi ba…! ga kuma kashe sa da uban salonsu kala kala…! kowaccen su na k’ok’ari wajen ganin itace y’ar gaban goshin oga sbd rik’e masa wuta dasukeyi babu dare babu rana…!

Bangarensu oga inoussa ma yanxu kam jikinsa sai godiyar allah sbd takanas ya tafi wurin likita aka rubuta masa magunguna kuma yana shan magungunansa akan lokaci dan hakaa yanxu kam sai godiyar allah…!
kuma dama ance kar mutum ya raina mace komai k’ank’antarta domin kuwa shareefar da inoussa kema kallon yarinyaa k’arama babu abinda tasani itace tausararuwarsa…! sosai yake tattalinta zuwa wannan lokacin dik inda yaje har alla allah yake ya dawo yasameta…! soyayyar da yayima fad’imatou kuwa yazamana tarihi da sunan soyayya na aure yakoma na y’an uwantaka…!

shehu musama zuwa wannan lokacin matansa uku ne acan garin bama…!
allah yayima maa rasuwa a shekaru kad’an na baya dasuka gabata…!

zaman lafiya da kwanciyar hankali, dakuma fahimtar juna ne ke wanzuwa cikin wannan family na late shehu ahmad dalhat saidai godiyar allah…!

******zaune suke cikin wani tangamemen parlon daya matuk’ar had’uwa suna hirarsu cike da nishad’i dakuma hutu…!

aliyu muhammad bama kenan…! tare da matansa kuma abin alfaharinsa fad’imatou el-mustapha dakuma asma’u muhammad bama…!

wasu yara ne suka su wajen takwas suka shigo ciki parlon bakunansu d’auke da sallama…!

saida aka basu iznini shigo kamin suka k’arasa shigowa sukayi ma kansu mat’suguni a wajen k’afafun iyayen nasu…! sai kuma k’aramar cikinsu data haye cinyar abbun nasu da basu da kamarshi sbd jajircewar da yayi akan yayansa t’sawon rayuwarsa batare da nuna gazawarsa ba…!

“ina wuninku su abbu,ammu duma ammi…”
yaran suka had’a baki a lokaci d’aya wanda hakan sosai yasa su aliyun dariya sosai ba kad’an ba…!

bayan an gama gaisuwa fad’imatou tace “momman mu maza tashi mi wuce da k’annenki dakunansu ki tabbatar dik sunyi alwala sbd magriba naga ta gabato…”

babu musu kuwa wacce aka k’ira da momma ga dikkan alamu itace babban a cikinsu ta kad’a kawunansu suka wuce wani corido dogo da zai sada su da dakunansu su husna da itama tazama uwa suka bisu da kallon sha’awa,sbd yadda kawunan yaran nasu ke a had’e…!

akoi hafsat mai sunar momma itace y’ar husna tafarko dake bin bayan baby yumna da yanxu tazama emmata harma ta tare a gidan dadynta inoussa dashima yanzu yaransa uku…!

sai kuma hadizatou yar fadimatou mai sunan mmnta…!

muhammad mai sunan baa(d’an husna),asma’u mai sunan maa(er fad’imatou),abdulrahman mai sunan shehu abdul( d’an asma’u),inoussa (dan fadimatou), elmustapha( dan fadimatou)…! musa (husna)…!

yaran asma’u husna hud’u saikuma fadimatou biyar …!

zaune suka bayan sun gama dinner suna hira inda husna da fadimatou sukasa aliyu a t’sakiya sukace masa suna da tambaya…!

bayyi musu ba kuwa ya maida hankalinsa kocokan bisa garesu domin jin da wacce sukazo…!

“abbu wai nikam t’sakanin nida maman yumna _WACECE BORA_ a cikin gidannan…?” fadimatou tayi maganar zuciyarta na dokawa sosai haka nanma husna domin kuwa basu san ansar da aliyu zai basu ba…!

aikuwa sosai aliyu ya fashe masu da dariya kamar cikinsa zai kulle sbd jin wannan tambayar dasukayi masa mai kama da wasan yara…!
“mai yasa kukayimin wannan tambayar matan aljanna…?” aliyu ya fad’a bayan ya t’sagaita dariyar tasa yana kallonsu…!

wannan karon kam husna ce tayi magana tace “abbu nidai ji nayi ana cewa wai idan aka had’a y’ar nigeria dakuma niger wai niger ne suke zama mowa a wurin miji nigeria kuma tasamo bora…! kuma banga kai kacire d’aya daga cikinmu a matsayin tauraruwarka ba…? shiysa muka yanke shawarar tambayarka domin muna so musa t’sakanin _NIGERIA KO NIGER(wacece bora)…?_”

sosai aliyu suka basa dariya nakin karawa a wannan lokacin saida yagaji dan kansa kamin ya tsagaita yana binsu da kallo na ganin yadda suketa babbata fuska alamun sun kule da wannan dariyar dayake masu…!

“abinda nake so na fahimtar daku anan shine! t’sakanin yar nigeria,niger,bakauyiya,yar birni,koma nace balarabiya ko yar america babu bora sai wacce batasan yadda zata kula da mijinta ba…

idandai mace kika kasance kina kula da shimfidar mijinki,bin umarninsa akan dik abinda yasaki,mutunta danginsa,kula da dukiyarsa,cinsa dakuma shansa,kula da t’saftar jikinki ko wani lungu da sako a takaice dai t’sfta to kuwa tabbas kin gama kaama zuciyar mijinki…!sannan kuma uwa uba ibada…! idan dai har kika rike wannan abubuwan to kuwa ko mata dari mijinki ya aura babu ruwanki da fargaba sbd rashin yadda dakai ne yake kawo dik wani kishi dakuma shirme…! idan dai harkinsa cewa kema kin kai,kuma kin isa to wlhi ko mata dari mijinki zai auro abin bazai dameki ba kona sisin kobo…! kuma ina godiya ga allah,domin kuwa nasan nidin dan gata ne dana hadaku ku biyu a matsayin matana da banajin zan samu kamarku har karshen rayuwata…!”

sosai farin ciki ya bayyana a fuskokinsu suka shige jikin mijinnasu ya had’esu ya rungumesu suna sakin dariya sosai…! yaransu ma dasuke labe tin dazu suna ganin komao suma sosai dariya yakamasu ba nasa wasa ba…!

ina masu cewa na inason had’a fad’a???????????? so nidai ban had’a fada ba kwarankwasi????????????????????????

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button