HAUSA NOVEL

NIGERIA KO NIGER Complete Hausa Novel

mariama kam ta tausaya ma hafsat wannan lokacin sbd tasan mutuwa bata bar kan kowa ba……

yaronta musa da hafsat sai shehu sune abin jimami alakacin sun fita a hayyacinsu baki daya sun zama abin tausayi sosai ba kadan ba…

ahaka akayi zaman uku wanda daga masarautu dama yan gomnati sun halarci wajen ta’aziyar margayiya halimatu………

kuma har zuwa lokacin bata saka yaran a cikin idanunta ba tana fama da kanta farida kuma ke kula dasu da duk abubuwan daya kamata tabasu sbd karsu zauna da yunwa…

da dare wajen karfe goma ga tsohon shehu wato mahaifin su muhammad,shehu abdul rahman,muhammad,hafsat,farida dakuma maa wato asma’u…

inda suke wani takaddama amma ga dukkan alamu hafsat na tsanani farin ciki ganin yadda fuskarta ta washe daga damuwa zuwa tsantsar farin ciki…

Aliyu dayazo shiga part na kakansa jin abinda ake fada yasa shi labewa shima tsaf yaji abinda ake fada wanda bazai taba mantawa dashi ba tsawon rayuwarsa…

sadaf sadaf ya fece abinsa kamar babu abinda yaji…

washe gari dasafe ma akayi ta karban masu zuwa ta aziya itakam tasamu kyakkyawar sheda wanda akewa duk wani musulmi na kwarai fatar hakan……

ranar sadakan bakwai aliyu dalhat dakansa ya radawa yan biyu suna hassana taci suna HALIMATUSSADIYYA saikuma hussaina taci suna ASMA’UL HUSNAH……

Akoi banbancin kamanceceniyar halitta kwarai da gaske a tare dasu sbd kou kadan basa kama itama halimatu photocopy na mai sunar ce…itakuma husnah hafsat ta dauko sosai harma kuma kyawunta ya zarce na hafsat din dakomai da komai…

musa kam tunda yaga mai kama da mamarsa kuma mai sunarta har hanawa yake a dauke ta saidai shine zai riketa ko nono za abata sai anyi dagaske…

mariama tunda ta kyalla ido taga tsantsar kyawun da bata taba gani ba a wajen husna taji sam ta tsani yarinyar ga kuma wani kishin yar da ya shigeta farat daya  (kunjimin mata pha jama’a kishi da yar mijinki)…

yanda take son yaranta nan amma taga sun rabi inda hafsat da yayanta suke har dukansu takeyi kan miyasa zasuje wajenta…?

dan haka inoussa yashama kansa lfy yadaina zuwa amma aliyu kam satan hanya yakeyi ya tafiyarsa…

TEAM NIGER
TEAM NIGERIA

TEAM BUZAYEN AGADEZ
TEAM KANURIN BORNO

TEAM UMMIEN2018

*vote*
*comment*
*share*
*follow@ummien2018*
[9/8, 2:27 AM] ????oum muntaz????????????:     *NIGERIA KO NIGER…?*
(wacece bora)

*©HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*_( home of peaces, joint of entertainment to educate and enlight  our readers)_*

*wattpad:UMMIE2018*
*whatsapp number:09076427357*

page 5

Haka pha rayuwar ke tafiya yau da dadi gobe babu dadi…  wanda a halin yanxu anyi arba’in ma marigayiya…  addu’a kam tana shanta…

Bangare shehu kuma an kara aura masa yar gidan sarkin gashu’a a halin yanxu…

amni (mariama) tasamu labarin haihuwar matar yayanta  wato almustapha aykuwa farin ciki kamar tayi tsalle taganta a niger haka takeji…

muhammad ma nada labarin haihuwar dan haka kawai aka fara mata shirye shiryen tafiya cikin kwana uku aka kammala komai kan washe gari zasu tafi zasuyi sati daya ita da yayanta dakuma wasu matana cikin fada…

aykuwa fir aliyu yace shikam baisan zancen ba babu yanda batayi dashi ba amma yace alllah yakashe sa babu inda zasa…

takaici kamar tayi yaya da muhammad yace a barshi yaso ita tatafi da inoussa tunda shikam yana so…  haka suka tattara washe gari suka wuce masarautar agadez…

Bangaren hafsat kam tana kula da yayanta sannan tanaima yar uwarta addu’a domin neman ni’ima gurin rabbil izzaty…

gashi yara sai wayo suke abinsu…wanda aliyu da musa ne masu raino kowa da kanwarsa wanda zuwa wannan lokacin husnah ta riga data gane yayanta aliyu…

tana ganinsa daga nesa zakaga tayi ta binsa da ido ita ko kwarafniyar yara kananan da ake cewa allah bai daura mata ba…

Saidai ido amma ko irin gwarancin nan da sukeyi kam bazakaji bakinta ba wanda hakan ke damun momma ta tunkari baa da zancen har likita akaje gani amma yace lpiyar ta qlaou kawai lokacin farawannata ne bayyi ba…

itakam sadiya akoi da kiriniya nakin karawa yanxu zaka ajiye abinka na sawon minti daya idan baka gurin kazo zaka tarda ta fasa idan na fashewa ne kou kuma ta yaga maka abu…

kiriniya kam ba daga baya ba hakanne yasa kwata kwata bata shiri da aliyu itakam sbd shima ba maison hayani bane…

Bangaren amni kam tunda tayi tozali wannan yarinyar sai masha allah take cewa take tambayar kanta dama akoi masu kalan kyawun husna…?

itakam tama rasa wacce tafi wata kyau tsakanin su biyu…

inoussa yamakalewa baby kamar danshi aka haifo ta kullum yana gindin hadizatou ko gurin takwaransa ma baya zuwa koda yaushe shidai baby…

ranar suna ta zagayo aka sakama yarinya suna fadimatou mai sunar mmn su mariama…

aykuwa yarinya yar gata ce gaba da baya kowa sonta yakeyi gata kyakkyawa na kin karawa…

amni kam cewa tayi da akoi hali da ita za’a zauna ayi arba’in sbd allah kadai yasan yadda yadaura mata kaunar yarinyar nan…

bangaren yan borno kam aliyu ya tare a part na momma baki daya…

bangaren shehu jiki ya matsa aka kwashe sa domin ganin likita amma tun akan hanya ya koma zuwa ga mahaliccinsa…

tab wannan mutuwar ta jijjiga mutanen bama sosai ba kadan ba…anyi babbar rashi kwarai da gaske …

yan niger sunsamu labari inda suka garzayo zuwa nigeria ta jirgi a ranar tare dasu akayi jana’iza aka mikasa gidansa na gaskiya…

alllah kasa mucika da imani ameen…

bayan sadakar uku kowa yakama gabansa wayan suke daga nisa inda inoussa ya tubure shikam niger zai koma da zama baki daya…

ba dabi’ar masarauta bace barin yayan sarauta na zuwa wasu masarautar da zama amma kuma hakan bawai aybu bace…

dan haka da zasu koma aka tafi tare dashi birnin agadez suka rabu shida aliyu cike da kewar junansu… inda aliyu ke kara jaddadawa dan uwansa alkawarin da yamasa karfa yamanta…!

bayan shekara uku hafsat ta haifo zankadeden yaronta dayaci suna sadam…

alokacinne kuma baa wato muhammad yasamu karin girma inda suka koma cikin maiduguri da zama a cikin unguwar gra…

alokacin kuma aliyu yawuce makarantar sojoji dake can kasar birtaniya…

farida ce takara haihuwa saita samu ya mace aka sa mata suna zainab…

momma takara haihuwar da namiji sunansa kamaluddeen…

daganan kuma ta kara haifo wani yaron mai suna jalaluddeen…ibrahim… idriss

kamin ta haifo mace mai suna ilham wacce daga kanta bata sake haihuwa ba haihuwar ta tsaya daganan…

yayanta 8 acikin gidan kaf jameela da mariama kam bakin ciki kamar ta kashe su dan bakin kishi na tsiyar da bazai amfane su ba…

yayansu bibbiyu ne kuma duka maza ne sunason yaya mata amma bazasu jawo yayan mijinsu a jiki ba sun tsaya bakin rai…bama kamar mariama amma babu wanda ya fuskanci hakan sbd ta iya wanke allonta…

kudi yazauna ma baa dan haka yakara buda masu gidansu sosai yazamana dankareren gida daya ansa sunansa gida wanda ko a turai albarka…

Ayanxu shekarun su husna 15yrs ne wanda yayi daidai da tafiyar aliyu school of amy nashi shekara 10kenan wanda wannan watan ake ran ganinsa yadawo gida…

husna kyakkyawar yarinya wacce ta ansa sunanta kyakkyawa kamar aljana haka take hakan yasa ba abarinta tafita kou ina sai makaranta wanda shima da nikap ake barinta zuwa…

mutane da dama basu san ya yanayin kyawun fuskarta yake ba ko kadan saidai suji ana labarin kyawunta sunanta yaje inda bataje ba…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button