NIGERIA KO NIGER Complete Hausa Novel

musa saurayi mai kimanin shekaru 30 wanda yake babban lauya ne mai zaman kansa yana aykinsa tsakani ga allah babu ha inci wannan ne yasa shi farin jini cikin al’ummarsa wanda ake fada yazama shehu a gaba…
ma’anar shehu sarki ne amma kuma yafi sarki matsayi…akoi sarakuna da dama dasuke karkashin duk wanda yake a matsayin shehu amma dai sarki ne…
Tun husnah da sadiya na kanana momma ke kula da yayanta da wasu abubuwa da dama…
kamar amfani da ruwan zafi wajen tsaftace jikinsu kou kuma makamantansu…
sannan kuma man kadanya tun suna yara a kullu yaumi idan tayi masu wanka saita shafa masu man kadanya tafin kafarsu dakuma tafin hannunsu wanda haka ba karamin taimakawa yake ba wajen saka tsananin laushi tafin kafa da hannu…
ko irin faso ko kaushi dazaka ga mutum nayi indai ansaba masa tun yana yaro da yardar allah hakan bazata faru ba wannan ma wani sirrinne…
TEAM NIGER
TEAM NIGERIA
TEAM BUZAYEN AGADEZ
TEAM KANURIN BORNO
TEAM UMMIEN2018
*vote*
*comment*
*share*
*follow@ummien2018*
[9/8, 2:27 AM] ????oum muntaz????????????: *NIGERIA KO NIGER…?*
(wacece bora)
*©HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*_( home of peaces, joint of entertainment to educate and enlight our readers)_*
*wattpad:UMMIE2018*
*whatsapp number:09076427357*
page 6
bangaren inoussa yana can birnin agadez tare da kyakkyawar kanwarsa dayake matukar sonta fiye da komai a rayuwarsa idan ka dauke iyayensa…
yana kawa ma yan bama da borno ziyara wanda daya kammala secondry school nasa tun a 18yrs saida yayi zaman gida na sawo shekara biyu yana hutunsa…
kamin yabi dan uwansa sbd alkawari sukama junansu kan zasu zama sojoji saidai dayake bashine ra’ayin inoussa ba sai bai bawa abin wani muhimmanci ba…
hakanne yasa aliyu yafisa matsayi a gurin ayki…
fadimatou kam ana nan yar gata gaba da baya daya tamkar da dubu acikin wannan gidan sarautartasu… bata da hayaniya kou kadan idan kaji bakinta toh ya inous na nan…
tsantsar mulki yariga yazama jinin jikinta amma bata da wulakanci kou kadan sannan bata shiga abinda ba a sakota a ciki ba…
nml life nata takeyi wanda tun batakai shekaru 15 dinnan ba daga masarautu da dama ana zuwa neman aurenta amma kuma ba’a basu saidai ace masu anyi mata miji…!
kuma hakan bashi zai hana gobe kuga wasu ma sunxo da kokon bararsu ba wanda duk wannan wainar da ake toyawa cikin shekaru biyar da tafiya inoussa ne…
baisan ma mai ake tsulawa ba sbd yariga yagama sawa a ransa fadimatou tasa ce kuma yasan itama zata soshi ko dan shakuwar dake tsakaninsu…
ayanzu haka tare zasu dawo da aliyu sai sunje nigeria kamin suje niger domin gayda tsoho mai ran karfe wato mai sunan inoussa…
Aliyu na waya da iyayensa akan lokaci sannan yana kiran momma a waya suna gaysawa daganan harsu gaysa da kanwarsa daya fifitata da kowa acikin kannensa…wato husna
amma kasancewarsa miskili ba lallai ne ka fahimci hakan ba sai wanda yayi masa farin sani…basa shiri da sadiya har yanxu sbd akoi ta da dan banzan surutu…
muddin aka hadasa da ita a waya saita ishesa da surutu shiysa kullum basa rabuwa da dadin rai idan sun fara waya…
husna kam dama halinsu yazo daya domin kou allah yayita wata kalan shuru shurun yarinya da wuya mutum ya fuskanci abinda yake cikin zcyr ta…
dukda ma dai ba kowa ne yagama sanin aynahin yaya yanayin halayyarta yake ba dan haka ko ya kira dukkansu zakaju daga gaysuwa sai kuma a rasa abin fada hakan kou bakaramin dariya suke bawa momma ba tayi mmkin dasuke jituwa dukda halinsu yazo daya tunda dai ance muskilin mutum baya jituwa damai kalan halinsa…
momma tariga da ta koya ma yayanta yanda zasu zauna da mutane domin kou ita tasan illar hakan tunda yafaru akanta bawai labari taji ba…
tun suna kanana ta daura su akan karsu taba sawa aransu wai bazasu zauna da kishiya ba…
ta cire masu kishi wanda ga dukkan alamu suma abin sun gado hakan cikin jininsu amma hakan baya tasirin da za’a gane tunda already an riga da an masu wannan training din…
ayanxu haka kum suna matakin ss2 a makarantar dake cikin unguwarsu kuma suna da burin cigaba da karatu fatansu dai allah yasa kar a ce aure za’amasu a wannan matakin…
amin uziri pls nayi typing ya goge ayi manage
TEAM NIGER
TEAM NIGERIA
TEAM BUZAYEN AGADEZ
TEAM KANURIN BORNO
TEAM UMMIEN2018
*vote*
*comment*
*share*
*follow@ummien2018*
[9/8, 2:28 AM] ????oum muntaz????????????: *NIGERIA KO NIGER…?*
(wacece bora)
*©HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*_( home of peaces, joint of entertainment to educate and enlight our readers)_*
*wattpad:UMMIE2018*
*whatsapp number:09076427357*
page 7
RANAR FARIN CIKI
Gidan tsohon soja duk inda kashiga ka fita wani kafurin kamshi ne ke tashi ko wani lungu da sako na cikin gidan sbd murnar dawowan yayansa na fari…
dankareren part guda biyu ya kara kawata su wanda sukafi ko wanne haduwa kaf cikin part na gidan… daya nasa daya kuma na aliyu da inoussa…
kowa ka gani yana farin ciki wasu kuma suna cikin bakin ciki da dawowarsu sbd haushinsu dasuke ji ganin yadda mahaifinsu ke rawar jiki sbd dawowarsu…
sbd inda ace daya ne daga cikinsu sun tabbata ba haka baa zayyi farin ciki ba…
sannan kuma gashi part dinda yayi ma su aliyu mai shegen girma da kyau…amma sukuma an hadesu baki dayansu a part daya kuma baikai nasu aliyu girma ba… !
hakanne yake kara masu tsana da kiyayyar yan uwansu wayanda suka fito daga tsatso daya…
Bangaren amni duk inda kashiga karatso wajen part nata wani azababben kamshi ne ke tashi kamar me wanda yakasance sirrin yan agadez ne…
can na hango hajiya amni an dankara wani uban less dan ubansu mai azababben kyau da tsada bakinnan yawa gonar auduga tsabagen farin ciki datake ciki yau zataga yayanta abin alfaharinta da bata da tamkarsu…
girke girke kam ansha su an riga an jere koma akan dining
sai hura hanci take sbd itakam gaba takaita gobarar titi a jos miji yafi sonta akan kishiyoyinta sannan kuma gashi yanxu yayanta yafiso wanda baya iya boye hakan a ko ina hakan ba karamin dadi yake mata ba wlhy
(allah ya kyauta)
Bangaren sauran matan gidan ma kam abin sai a hankali farida data kasance shirgin gidan ba damunta yake ba amma yanxu itama abin yafara bakanta mata rai sosai ba kadan ba…ganin yanda baa kiri kiri ke nuna yafi son yayan kishiyarta akan nata yayan…
jameela kam dama har ila yau bata manta kalar tsiyar da aka shuka masu akan cikin yayanba wanda hakan ya dasa mata zazzafar kiyayyar yayan a ranta…
Bangaren momma kam yanxu ta saduda sbd ita yanxu duk abinda baaa keyi ganinsa kawai takeyi sbd ta tabbatar akoi ranar da zaiyi dana sani…
bata da matsala dasu aliyu kuma bata sakosu acikin abinda yafaru sbd badasu take takun saka ba da uwarsu takeyi dan haka bataga amfanin saka yara ba acikin hakan…
taja girmanta yanxu sbd ko babu komai tasan ta girme amni sosai ba kadan ba dole tayi hakuri tamaida komai ba komai ba…
Husna yau baki har kunne ya aliyu zaizo gashi sunje an masu wanki kai da kafa an tsantsara masu lalle mai bala’in kyau yaran momma kam badaga baya ba…
bama kamar husna har tuwon DALAYI DA MIYAR GWALTO (danyen kubewa) dayaji namar rago ta shirya masa sbd taji momma na cewa da muddin tayi dalayi aliyu saiya saci hanya yazoci…
sadiya kam ji take kamar lokaci baya gudu ta kosa dan uwa rabin jikinta ya iso dukdama tasan dawuya basu raba hali ba ayau dinnan…