NIGERIA KO NIGER Complete Hausa Novel
shiiii !!! ya isa haka bagani yanxu na zoba husnaty…? ko kina so yanxu nabi wani jirgi nakoma ibda na fito ne…?
ni ay bance ka koma ba…! murmushi yasake yace toh shikkenan am sorry kanwata bazan kara ba…yanxu kam harsai kin gaji dani kinji yar gidan mommah…? ya karashe maganar cike da tsokana…
karamar dariya tasake itama tace allah ya aliyu nayi kewarka amma kai kamar ma bakayi kewata ba ko kadan…!
inji waye? ni asuwaye bazanyi kewar kantawa ba? baki ga deeya ta dameni da surutu ba daga shigowata nasan yanxu suna can suna fama da twiny sbd shima akoi surutu kamar ita…..
murmushi tayi kawai sbd sanin halin sadeeya da dan banzan surutu tsiya,shiysa itama ba zaman hira sukeyi ba ko kadan…
ya aliyuuu kaci abincinnan pls karya huce nida kaina na dafa maka pha yau danaji zaka zo…
cikin tsokana yace anya kuwa kunma iya abinci mai dadi yarannan…? kwata kwata baku wuce 15yrs ba ace har kun iya girki…?
alllah ya aliyu mun iya harma munfi wasu manyan iya girki pha… duk wannan dogon sharhinnasu cikin sanyi sukeyi sbd kowannensu bason yawan magana yakeyi ba haka suka ci abincinsu tare suna hira jefi_jefi saida suka gama ta kwashe komai takai kitchen haka momma tafito ta iske su……
TEAM NIGER
TEAM NIGERIA
TEAM BUZAYEN AGADEZ
TEAM KANURIN BORNO
TEAM UMMIEN2018
*vote*
*comment*
*share*
*follow@ummien2018*
[9/8, 2:28 AM] ????oum muntaz????????????: *NIGERIA KO NIGER…?*
(wacece bora)
*©HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*_( home of peaces, joint of entertainment to educate and enlight our readers)_*
*wattpad:UMMIE2018*
*whatsapp number:09076427357*
page 9
Har ka gama cin abincin kanwar taka ne mazan fama…? fadar momma cikin sakin fuska lokacin da take karasa fitowa daga bedroom nata…
murmushi yayi cike da karamar kunya yace ay momma gaskiya kanwata kam bataga baya wannan kalar gara haka dana kwasa ay abin kam ala sam barka…
cike da jin dadi momma tace aykam aliyu kraminka(kanwarka) kam tana kokari bakamar wacce magananniyar ba sai surutu da ya mata katutu a tsakar ka…takarashe maganar tana dariyan halin sadeeya…
shima cikin murmushi yace deeya kam sai du’ai momma ni har ciwon kai take samun wlhy in muka hadu…
cikin shagwabar da tazamewa husna jiki tana cuno baki tace wlhy adaena maganar twiny na a bayan idonta in ba haka ba kuma nasata ta hana mutum jin dadin gidannan…!
kallon ta aliyu yayi cike da birgewa sbd shikam kanwarsa nan na bala’in birgesa kaf cikin gidan wanda baisan dalilin hakan ba…(nikam nace sbd hali yazo daya ne)
kawai ya girgiza kai yayi murmushi momma ma dariya abin yabata a haka suka zauna cike da natsuwa da sanyi daya zamewa yayan sarauta jiki suke hirarsu cikin kwanciyar hankali…
sadam ne ya shigo da karamar sallamarsa…ansa wa sukayi inda yasamu daya daga cikin lumtsuma-luntsumar cusion din dake parlon yabawa kansa mazauni kamar wani babba
(am sorry nayi mistake a page din daya gabata aminulla nake son cewa na saka sadam so amin afuwa pls)
yaro dan shekaru 13 ne kwata kwata gayshe da momma yayi cike da kasaita sbd shima jinin sarautar a jininsa yake…
ansa wa tayi cike da son dan nata inda ya juyo yana babbata rai ya gaida aliyu batare da ya jira ansarsa ba ya juyo da kallonsa zuwa inda take yace yaa husna wlhy yunwa nake ji…
harararsa tayi ganin halin ko in kula daya nuna zuwa ga yayan nasu… cike da takaici momma ta daka wa sadam tsawa tace haka na koya maka yanda ake gayda na gaba kou sadam…?
cikin kunkuni yana tura baki yace amma ay momma na gaida sa kou?
kaci gidanku sadam ina tambayarka kaima kana tambaya ta …? ba dan uwanka bane wannan din kou kuma bare ne…?
mikewa yayi a fusace kamar wani babba saida yakai bakin kofa sannan ya juyo cikin hasala yace amma nikam wlhy wannan ba dan uwana bane momma…!
idan da ace dan uwana ne kamar yadda kullum kike cewa mai yasa baa idan muka muna son abu baya son yi mana…? amma sukam ko basu ce yamasu ba shida inuossa yakeyi masu…?
kin manta lokacin da akeyin gyaraan part naku ma saida su ya aminulla sukace tunda muna dayawa muma aka kara mana girman part namu amma haka baa yaki wai wannan ma ya ishe mu bayan sukuma su biyu ne kawai amma part nasu yafi namu girma sannan yafi namu kyau ay… dan haka nikam dukkansu biyu ba yan uwana bane… yana gama fadar haka yasakai ya fice…
momma kam suman zaune tayi a wajen mmk da al’ajabi ne yacika ta jin zantukan da karamin yaro kamar sadam ke zarowa ?
wannan wace kalar masifa ce fisabilillahi? baa da kansa keson haddasa rashin zaman lfy cikin yayansa…?
Aliyu kam tun lokacin da sadam yagaishe shi bai kallesa ba sbd jin salon raini dayayi amfani dashi wajen gayda sa… mmk ma yakeyi shikuma yaushe ma sadam din yasansa da raini zai shiga tsakaninsu har haka?
amma jin maganganun da yaron yafada daga baya yasamu amsar tambayoyinsa baki daya… baiji haushin yaron ba yanxu kam sbd yasan koshi akayiwa haka dole zaiji babu dadi amma kuma bai kamata kiri kiri ya nuna masa kalan haka ba…!
dukda yasan dakyar ne idan ba shirya mawa yaron akayi wannan maganganun ba sbd yana ganin hankalinsa bai kai zuwa wannan wajen ba(nikam nace kadan ma kenan)
Husna dukda tasan gsky sadam yafada amma bakaramin haushi yabata ba…
sbd ba akan haka momma ta daurasu akan tarbiya ba ta tabbata wasu cewa zasuyi momma ce ta zugasa muddin wannan maganar tafita babu wanda zayyi tunani makamancin haka…
mikewa yayi yana kokarin boye bacin ransa yace momma ni zan wuce Fajara(saida safe)…
cikin murmushi yace allah yabamu alkhairi aliyu ayi ta hakuri pha wata rana sai labari …allah yamaku albarka yakuma shirya mana ku baki daya…
koba komai yaji sanyin addu’ar data masu dan haka yasaki fuska kamar babu abinda yafaru ameen summa ameen momma ni na wuce saida safe…!
mikewa husna tayi tace momma bari na rakasa daga nan saimu dawo tare da deeya…
toh shikkenan adawo lpy uwata karku jima sosai sbd naga lokaci ya ja yanxu…
gyada kai tayi batare da tayi magana ba ta shiga dakinsu ta dakko hijjap nata har kasa ta zumbula tafito…mikewa momma tayi tace ni nashiga idan kun dawo saiku sanarmin…
cikin sanyinta takamo hannun dan uwannata suna tafiya batare da kowa yayi magana ba har suka isa part nasu…tun daga bakin kofa suka fara jiyo hayaniyar su sadeeya sai surutu take zuwa shima inoussa na biyeta kamar bashine mai cewa bacci zayyi ba dazu…
batare da sunbi takansu ba suka wuce dakin aliyi kasancewar kowa da nasa dakin suna shiga aliyu ya janye hannunsa daga nata yace maza kuwuce kar momma tace kun dade kou…? yakarashe maganar yana mai kafeta da mayun idanuwansa mai saka yemmata accident akan hanya…
sunkuyar dakai tayi tafara magana…
Yaa aliyu dan allah kanadi gone kila a wochare nyiro sadam sinnadu(ya aliyu dan allah kayi hakuri akan abinda sadam yakama dazu)
kallonta yayi ba sawon dakiku ganin yadda duk tabi ta damu akan abinda ba ita ta aikata masa ba…
murmushi yayi kamin ya kamo hannunta yajata zuwa bakin tankamemen gadon sa ya musu mazauni sannan ya fuskance ta ya bude baki yafara magana kamar haka
TEAM NIGER
TEAM NIGERIA
TEAM BUZAYEN AGADEZ
TEAM KANURIN BORNO
TEAM UMMIEN2018
*vote*
*comment*
*share*
*follow@ummie2018*
[9/8, 2:28 AM] ????oum muntaz????????????: *NIGERIA KO NIGER…?*
(wacece bora)