NIGERIA KO NIGER Complete Hausa Novel

(wanda kuma ana son hakan sosai yazamana anayin sallar a gaban yaron da bashi da wayo hakan zaisa sha’awar yin hakan ta shigesa tun yana yaro idan ya girma baxayyi wahala tankwasuwa ba)
hijabansu har kasa suka zumbulo dukkansu suka kamo hannnun ilham suka sata a tsakiya suka wuce dakin momma wacce ke zaune kan abin sallarta tana lazimi…
saida ta ida kana suka gaydata ta ansa tana tambayarsu yaya suka kwana…? lpia qlaou suka shaida mata inda dukkansu suka dunguma zuwa part na baa domin masa barka da safiya wanda hakan kullum sai anyi…
sun shigo inda baa tare da mariama na zaune akan kujerar 3seater (kasancewar kwananta ne) sai kuma farida da jameela dake 1 seater a zaune yaran kuma baki dayansu gasunan a zaune a tsakiyar parlon inda momma ma ta zauna kan daya daga cikin one seater…
aliyu na wajen kafar baa sai inoussa dake geden kafar amni…
sauran yaran duk sun gama gaysawa dan haka momma tagaida baa inda farida da jameela ma suka gaysa daganan kuma momma tace ma amni mun tashi lafiya maryam?
babu kunya babu tsoron allah ta ansa…hakan baywa husnaty dadi ba ko kadan amma sai ta dauke kanta kawai inda suma suka gayda baa sannan suka gayda matan mahaifinnasu…
saida aka gama gayshe gayshe kamin baa yake tambayarsu babu mai wani matsala ko…? inda kowa ya shaida hakan amma mubaraq yace shi yana da matsala…!
izini baa yabasa inda budar bakinsa cewa yayi baa tunda muma yanxu mun girma nida aminulla muna so ka ware mana part namu daban sannan kayi mana irin yadda kayiwa su inoussa…!
kowa shuru yayi a parlon ana jiran aji dame zai wanke kansa sbd kowama abin naci masa tuwo a kwarya…
inda baa yazuba masa ido rannan nasa na tafarfasa wato ya lura kaf cikin yayansa maza haushin su aliyu sukeji sbd yana sonsu sosai shikuma bayajin zaiso wasu kaf cikin yayansa kamar yadda yake son yam biyunsa…
(wannan itace matsalar baa kowa ma yasan cewa dole a cikin yayanka zakafi son wani akan wani amma kuma anfiso kayi kokari wajen ganin ka boye sabida gujewa matsala da rabuwar kan iyalanka…..wannan itace matsalar baa)
cikin kakkausar murya yafara magana inda yace wlhy babu yaron da zai ginawa part a gidannan idan sunga bazasu iya ba saidai su nemi kudi su gina da kansu sbd shikam yayi abinda zai iya dan haka baiga wanda zai chanxa masa ra’ayi ba…!
duniya sabuwa a wajen amni inda take ta faman doka murmushi wanda hakan ya kular dasu baki daya hatta da momma datake kauda kai abin ya bakanta mata rai…
dauke kai tayi ta shanye bacin ranta yau taso ta mammake sadam akan abinda ya aykata jiya sbd tun jiya da fita bai kara leko part na momma ba amma ganin abinda ke faruwa anan ta kudurtawa ranta babu maganar dazata masa tunda ubansu ne ke kunnawa gidansa gobara dakansa babu ruwanta…
jameela kam dama a wuya take dan haka kawai ta buga tsaki da fuu ta bar parlon kamar zata tashi sama…
kowa binta yayi da kallo inda amni tayi karamar dariyarta kawai itakam dariyama wai suke bata…
batare da baa yayi magana da kowa ba ya shige bedroom nasa inda aliyu ma yafice a parlon gsky shima bayason haka tana faruwa acikin gidansu ko kadan sbd yana son yan uwansa bayason irin haka na faruwa ko kadan…
duk sauran yaran ma kowa yafita yakama gabansa inda farida da momma ma suka fice suka bar zainab,sadeeya,husna da ilham a zaune itama karama kamar tasan abinda ke faruwa sai tayi lukus a jikin zainab…
share abin sukayi kawai sukayi suka dan fara hirarsu jefi jefi a wajen inoussa ma mikewa yayi yaficewarsa sbd shikam ko a kwalar rigarsa abinda yasani kawai ubansu yafison amninsa kaf cikin mata sannan kuma yafi sonsa shida dan uwansa dan haka shikam bashi da matsalar komai a rayuwa…!
kallonsu amni tayi inda tace su tashi su fice daga parlon… zainab ce ta fara kunkuni kan wani dalili za’ace su fita a wajen tunda na bbnsu ne?
husna ce taja hannunta kan su fita sbd sanin halib zainab na rashin kunya idan aka tabo ta gata dai yarinya karama … yaa husna allah ki kyaleni nikam babu inda zani zainab ta karasa maganar cike da rashin kunya…
sadeeya kam ko a kwalarta itama ba sa baki tayi ba acikin abin dan haka kawai ta dauki ilham suka fice dan dole zainab ma tabi bayan husna suka wuce amni tarakasu da harara…
itakam hakanan allah ya daura mata tsanar wannan husna da kuma tsantsar kishinta wanda tarasa dalilin hakan…
kowa a part nasa yakeyin girkinsa tare da yan aykinsu dan haka zainab ma tawuce part nasu inda su sadeeya suka wuce suma suka tarda momma da iya wata amintacciyar mai aykin momma suna kitchen suma jonata sukayi inda suka shirya kayan karinsu…
bakwa comment yadda yakamata pha nigeria ko niger…??
TEAM NIGER
TEAM NIGERIA
TEAM BUZAYEN AGADEZ
TEAM KANURIN BORNO
TEAM UMMIEN2018
*vote*
*comment*
*share*
*follow@ummie2018*
[9/8, 2:28 AM] ????oum muntaz????????????: *NIGERIA KO NIGER…?*
(wacece bora)
*©HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
*_( home of peaces, joint of entertainment to educate and enlight our readers)_*
*wattpad:UMMIE2018*
*whatsapp number:09076427357*
page 12
Haka rayuwar gidan ke tafiya cike da abubuwa na takaici da ban mmk…
saida su aliyu suka shafe tsawin wata daya a nigeria kana sukayiwa garin agadez tsinke inda aka masu tarba ta ban girma a matsayinsu na jikokin sarki…
A wannan lokacinne aliyu ya fara haduwa da fadimatou inda daya ganta sai yacika shima da mmakin ganin tsantsar kyawunta da take dauke dashi…
basa wani sakewa tsakaninsu da ita sbd kowa jinin sarauta na yawo a jikinsa dan haka dama idan kaganta tana dogon hira saida iyayenta dakuma yayanta inoussa…
wanda zuwa wannan lokacin kowa yasan akoi soyayya tsakanin fadimatou da inoussa jira ake tagama makarantarta a daura masu aure sbd manya ma sunsan da zaman zance kuma akayi zama…
saidai kuma itama fadimatou tana da burin taga tayi dogon karatu koda ace baxa a barta tayi ayki ba karatu na bata sha’a wa a halin yanxu itama tana da shekaru 15 sa’arsu husna ce saidai sun girmeta da kwana arba’in…
saida suka masu one month acan kana suka juyo zuwa nigeria inda sukayiwa garin bama tsinke sbd su gayda shehu abdul dakuma tsohuwa mai ran karfe maa asma’u…
aykuwa sunga gata a wajen kakarsu dakuma yayan mahaifinnasu… saida sukayi sati biyu a garin bama kana musa yayi ma garin dirar makiya inda hakan yasa suka karajin dadin zaman garin sosai kasancewar yana da sakin fuska bashi da matsalar komai saina kasaita da akasan duk wani jinin sarauta dashi kuma shima sai abin ya motsa masa bawai kullum ba…
maa duk tasashi a gaba kan lallai ya fidda matar aure amma ya buga kasa yace sam baisan zancen ba sbd shi har yanxu matarsa bata gama girma ba kuma shima da sauransa…kuma a lokacin fa yanada shekaru 30 a duniya…
shehu abdul dayasan akan wacce yake magana sai bai daga hankalinsa kan saiya takura masa yayi aure yanxu ba sbd sanin cewa aure lokaci me kuma shima yayi na’am da zabin dannasa abin alfaharinsa…
Kaf cikin yayansa yafi son musa kuma hadda soyayyar mahaifiyarsa ne yashafe sa dan haka yake matukar tausayinsa amma kuma hakan baisa yayi ragon azancin da baa ke kwabawa a cikin gidansa ba…
hakanne yasa kan yayansa duk a hade yake sbd kowa an ajiyesa a matsayinsa… saidai kuma matan suna dan kishin yaron kunsan gidan sarauta da jarabar son mulki…?