NOOR AL HAYAT COMPLETEUncategorized

NOOR AL HAYART 1-10

A hankali Aliyu ya bude idanuwansa jin kwankwasa kofa da ake ta yi, ya tashi xaune yana kallon kofar yace “Who’s there?” Muryar small mum dinsa yaji tana cewa “Are you okay Aliyu? Baka fito sllh yau ba” a hankali yace “Nayi a nan Anty… Was having a slight headache ne” tace “Toh Allah ya sauwake, ka fito kayi break sae ka sha magani” daga haka tayi wucewar ta, mikewa yyi yana dafe kansa da yayi masa nauyi ya nufi window ya tsaya, lkci daya ya dawo ya xauna gefen gadon ya rike kan yace “Noo, nasan ba ita bace, ba Iman bace, it’s her look alike…. But….” mikewa yyi da sauri cike da damuwa da confusion yace “Why did she run then, me yasa ta gudu?? Does it mean ita ce? Ya Allah….” Jingina yyi da bango ya runtse ido, ya kusa minti ashirin a haka aka sake bubbuga kofa, ya bude ido a hankali cikin sanyin murya yace “Who’s there?” Muryar Maryam cousin sis dinsa yaji tace “Yaya ni ce” yace “Ya aka yi” bata ce komai ba, hakan yasa ya karasa ya bude kofar tace “How was ur nyt?” Ya dauke kai yace “T’was good” Tace “Mumy wai ka fito ka yi breakfast” yace “Ohk” daga haka ya rufe kofar ya koma gefen gado ya xauna, kallon agogo yayi ganin takwas ya tashi ya shiga bathroom, wanka yyi ya fito, ya fi minti sha biyar kwance jin kamar xaxxabi xai rufesa, can yyi ta maxa ya mike ya shirya ya dau makullin motarsa ya fice gidan ba tare da ya bari Small mum dinsa taga fitarsa ba. Mikewa xaune Khadijah tayi da sauri daga baccin da take ta dalilin bell da aka danna, ta tashi a hankali jin jiri na dibarta, ta shiga bathroom ta wanke fuskarta ta wanke baki sannan ta fito ta dau hijab ta sa ta fito parlor ta bude kofar, har lkcn yana tsaye gun, yana kallonta a hankali yace “Bacci kike na tashe ki?” Ta sunkuyar da kai cikin sanyin murya tace “Na tashi” yace “How are you feeling now?” Tace “Alhmdllh, ina kwana” yace “Lafiya lau” jin yyi shiru ta dago kai suka hada ido, saurin sauke idonta tayi, yace “You cried!” Ta girgixa masa kai kawai, yace “Noo you cried malama” lkci daya hawaye ya kawo idonta ta kasa ce masa komai, shiru yyi bai sake cewa komai ba, bayan wani lkci yace “Shiga ciki” ba musu ta juya ta koma ciki ya rufe kofar, daki ta koma ta kife kai da pillow wasu hawayen na xubo mata, duk taji ta tsani xaman UK din, ta tsani karatun, dago kanta tayi da sauri ta dalilin *SUDAIS* da ya fado mata, bata san lkcn da tayi murmushi ba kawai taji kamar an yaye mata bakin cikinta, tayi tagumi a sanyaye…. Ta fi minti sha biyar a haka, ji tayi duk duniya bbu wanda ta tsana… tsanar da bata da iyaka irin wanda tayi tozali da jiya a mall,  taji an bude kofa ta dago da sauri, jin shiru ta mike ta fito parlor tana goge idonta, xaune ta gansa kan kujera yana hada allura, ya dago ya kalleta, lkci daya ya hade rai , bata yrda sun sake hada ido ba, ya ajiye alluran hannunsa ya mike yace “Are you alright? under this condition stil xaki dinga xama daki kina kuka haka, dama kuka na magani? idan ma damuwa gare ki baxa ki sa Allah ran ki ba” bata iya tace komai ba bata kuma yrda ta dago ba, ya koma ya xauna, bayan kusan minti uku ya nuna mata cup din shayi da bread dake ajiye kan table yace “There” ta karaso ta dau shayin yace “With d bread” girgixa masa kai tayi ta fara shan shayin, murya can kasa yace “Look…” ta dago idanuwanta ta kallesa ya nuna mata kujera, a hankali ta karasa ta xauna, ajiye cup din tayi bayan ta sha shayin, yace “ur injection” tashi tayi ta wuce daki ta daura xani cikin Hijab din jikinta ta fito, nan parlorn yayi mata alluran ya bata maganinta, yace “You go get some rest now, ki yi bacci da yawa kin ji” yyi kasa da murya yace “And please kar sake kuka ur condition isn’t encouraging, always remember Allah xaki samu natsuwa sosai…” Bata ce komai ba ta mike ta wuce daki ya bi ta da ido, tashi yyi ya dau cup din ya fita. Sai bayan azahar ta farka daga baccin da tayi, sosai taji xuciyarta ya mata saukin xafin da yake mata don ta samu bacci da yawa, kuma taji ddin drugs din, yunwa taji na dawainiya da ita, ta tashi ta shiga bathroom ta wanke baki tayi wanka ta dauro alwala ta fito, shafe shafe tayi ta dau gown mara nauyi da tsayi ta sa ta shimfida darduma ta saka hijab har kasa ta tada sllh, tana idarwa ta cire Hijab din ta linke sannan ta fito parlor don dafa ko da indomie ne ta ci, still tayi ta juya baya da sauri a parlorn ganinsa da tayi dai dai center table ya ajiye ledan hannunsa da alamar shigowarsa kenan, Bata jira ta ji abinda xai ce ba ta nufi daki da sauri ta rufe kofa, xama tayi kan gado ta hade kai da gwiwa duk taji kunya ya kamata, ta fi minti goma a haka, can dai ta mike a hankali ta saka Hijab din da tayi slh ta fito parlorn, bbu kowa ciki ta karasa gun ledan ta bude taga abinci ne da drink, kadan ta ci ta fara gyaran gidan, dab da la’asar aka danna bell, ta kasa xuwa ta bude, can dai taa isa gun kofar tace “Who’s there?” Yace “Koh” bude kofar tayi ta juya ta dawo parlorn ya shigo ya tsaya daga bakin kofa yace “Sorry….” Da sauri ta katse sa tace “Ohh bakomai” yace “Bakomai me?? ai baki jira kin ji abinda xan ce ba malama” ta d’an kallesa, sai taji kunya, ya buda ido sosai yace “Dama cewa xan yi, sorry… me yasa kika gudu daxu?” Bata ko kallesa ba balle tace komai, yyi murmushi yace “Toh kin ci abincin” kai kawai ta gyada, yace “How you feeling now” tace “Naji sauki” duk wannan abun bata yrda ta juyo ba sai gyare gyare take, yace “Alluran ki…” Da sauri tace “No naji sauki, xan sha maganin” shiru yyi na kusan thirty seconds, yace “Malama” sai a sannan ta juyo suka hada ido, jallabiya ce Milk colour jikinsa da ya fiddo da ainahin kamanninsa na larabawa, shi ya fara dauke kansa sai kuma yace “ohk… Ki sha maganin” daga haka ya fita ta bi sa da ido har ya rufe kofar.

*Haske writers association*????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button