11.... Shiru Aliyu yayi bai ce komai ba yana sauraren fadan Kanwar Dad din tasa, A fusace tace "Wai ba da kai nake ba ka min shiru Aliyu" ya dago ya kalleta da kyar don har wani ciwon kai fadan ke sa masa, ya marairaice fuska yace "Wllh ina ji Anty, ina jin ki" tace "Nace ka gaya min me yasa ka bar min breakfast kayi ficewar ka daxu?" yace "kiyi hakuri mum, ban san xan jima haka bane" Tace "To xaka ga uwar da xata baka dinner yau a gidan nan kuwa" murmushin karfin hali yyi ta juya tayi ficewarta, komawa yyi ya kwanta kansa na ci gaba da sara masa, tun safe har xuwa lkcn bbu abinda ya ci ban da ruwa da yake sha, bbu inda bai shiga ba a wasu daga streets din UK ko xai ga Iman amma sam bbu alamarta, shi ya ma rasa gane ko ita ce ya gani ko ba ita ba, ya mike xaune da damuwa yace "Ya Allah..." Har agogo yyi stucking karfe shidda na yamma yana xaune dakin, aka bude kofa tare da sallama, Maryam ce ta shigo dakin tace "Yaya Aliyu are you sick?" Ya kalleta yace "No I am not Maryam" ta xauna gefen gadon tace "Toh naga tun jiya duk ka xama wani iri, gashi daxu ko breakfast baka yi ba ka fita, nasan baka yi lunch ba ma" yace "Kirana aka yi na fita" Shiru tayi bata ce komai ba, yace "Ya school ko baki je ba yau?" Tace "Naje daxu na dawo" yace "Ohk, ina su Baby da Fadil" tace "Suna assignment a daki" yace "Idan Anty ta gama lunch ki dibar min kadan ki kawo min" tace "Toh" sannan ta mike ta fita, ba a dau lkci ba kuma ta kawo masa abincin da ruwa ta ajiye masa.Kulawa sosai Khaleel ke bata a kwanaki ukun da tayi a gida bata je makaranta ba duk da shi ya hanata xuwa makarantar sae taji sauki sosai, kuma cikin ikon Allah ta warware bata jin ko wani ciwo sae dai Kawai ta kasa mance incident din ne, ba a minti goma Aliyu bai fado mata ba, ko kadan Khaleel bai son ganinta cikin damuwa, he's as kind as she never expected, duk da wani lkcn he is pretending not to be, kamar dai yasan tana da damuwa, bata kuma yi mamakin ya gano haka ba tunda likita ne shi din, duk Safiya kafin ya fita sae ya tabbatar ta karya ta sha magungunan ta, da yamma kuma idan xae dawo it's either ya taho mata da fruits ko abinci, har books masu dadi na turanci ya kawo mata ta dinga karantawa, ae kuwa books din also contributed don nishadi suke sa ta idan tana karantawa, idan kuma ta gaji da karatun ta dauko hotunan su Sudais da Shuraim tun daga lkcn da suke jarirai har xuwa girmansu, yawanci kuma hotunan duk tare da *Sudais* ne wannan dalilin yasa bata gajiya da hotunan, ko gida bata fadi ma su Umma bata da lafiya ba. Yau kamar ko da yaushe tana kwance parlor bayan ta raka su Vanessa da suka xo gaishe ta tun da rana, bell aka danna, ta mike don tasan shi ne, ta isa gun kofar ta bude, gaishesa tayi tana kallon sa, ya amsa yana mika mata ledan hannunsa, lkci daya kuma yana tambayarta ya jiki, ta karba tace "Da sauki" yace "Maa sha Allah" xae juya tayi saurin cewa "Are you sick?" Juyowa yyi yana kallonta yace "Just Stomachache, but na sha drugs da sauki sosai" da damuwa tace "Allah ya sauwake" yace "Ameen" daga haka ya rufe mata kofa ya shiga apartment dinsa. Ajiye ledan tay kan table ganin fruits ne, tana ta xaune parlor har kusan Magrib kafin ta tashi ta shiga toilet ta dauro alwala ta fito, nan parlorn tayi sllh, ta gama addu'o'inta sannan ta mike ta shiga kitchen, tunanin me xata dafa ta shiga yi don yunwa take ji, garnished cous cous tayi da yaji kayan hadi, duk da bashi da yawa kawai tayi deciding ta debar masa, ta zuba a karamar warmer snn ta sa hijab ta fita kai masa, a hankali ta kai hannu ta danna bell, sai da ta sake dannawa ya bude kofar, singlet ne jikinsa da dogon wando, kallon sa ta tsaya yi ya juya ya koma kan kujera ta bi sa da ido, can ta bi bayansa ta rufe kofar, ajiye abincin hannunta tayi ta durkusa gefensa tana kallonsa da damuwa tace "Cikin ne har ynxu?" Gyada mata kai yyi a hnkli yace "But... Sure I will be okay" cike da karfin hali yyi maganan, shiru tayi tana kallonsa taji tausayinsa sosai, a hnkli ya sauko kan kujeran ya duka kan gwiwowinsa, kamar xata yi kuka tace "Ko xaka je asibiti" girgixa mata kai kawai yyi, sai kuma ya kwanta nan gun, kana ganinsa kasan namijin kokari kawae yake, hawaye ya cika idonta, tashi xaune ya kara yi yana runtse ido a hankali yace "Get me water pls" tashi tayi da sauri ta nufi fridge ta bude taga duk masu sanyi ne, ta shiga kitchen ta dau glass cup ta dibo masa na tap, tana dawowa ta duka gun sa ta mika masa ya karba ya fara sha, sae kallon sa take sai ka rantse tare cikin ke masu ciwo ynda tayi da fuska, lkci daya ya ajiye glass din ya mike ya nufi bathroom dake parlorn, ita ma ta mike tsaye, amai sosai yake yi a bathroom din, ta kasa motsawa daga inda take, can ta durkusa ta fashe da kuka, yana fitowa parlorn ya hade kansa da kujera, tashi tayi ta isa kusa da shi cikin rawar murya tace "Don Allah mu tafi asibiti plss" ya dago idanuwan sa da suka sauya xuwa ja, komawa baya tayi da sauri don idanuwan suna kalau ma tsoronsu take barin kuma yanxu da suka kara wani kala kan na da, da alama ya kasa mata magana don girgixa mata kai kawai yayi, xai komar da kansa kan kujerar tayi karfin halin rikosa da sauri tace "Doctor plss let me drive us to the hospital, ina makullin motar yake" murya can kasa yace "I will be alright Khadija, go to my room xa ki ga 1st aid box..." Bata jira ya gama ba ta mike da sauri ta shiga dakin, da box din ta dawo, ta ajiye kusa da shi, ya xamo kasa idonsa lumshe ya bude box din, bayan yan sakwanni ya bude idon ya dau wani allura da syringe ya mika mata, ta bude ido da mamaki ta dai karba ya mayar da kansa kasa, rasa abin cewa tayi, can dai ta balle bakin alluran ta xuke a syringe tayi karfin halin cewa "Ga shi nan" ja baya tayi tana xare ido ganin ita yake nufin xata masa alluran, duk da ta iya kawai niyyar nuna masa bata iya ba ta yi, amma tausayinsa da yanda shi ma ya nuna damuwarsa lkcn da bata da lafiya yasa ta kasa, hannunta na rawa tayi masa alluran, kin bude ido yyi ta koma baya tana kallonsa, bayan wasu mintuna ya mike da kyar ya kwanta kan kujera, ko minti goma bai kara ba bacci ya dauke sa, dawowa tayi kusa da shi tana kallon sa da tausayi ganin alluran bacci yasa tayi masa, mikewa tayi ta dauke glass cup din da abincin da ta kawo ta kai kitchen, ta mayar da box din 1st aid din daki, tayi disposing alluran da tayi masa sannan ta xauna kusa da shi tana kallon sa, giransa kadai ma abun kallo ne a fuskarsa kafin a xo ga long lashes din idonsa, a hankali ta sauke idanuwanta kan dogon hancinsa da ko Kadan bai da miskila xuwa bakinsa, kai kana ganinsa kasan duk yanda aka yi yana da alaka da larabawa, dauke idonta tayi tana wasa da fingers dinta, da sauri ta tashi tunawa da tayi bata yi isha ba, alwala ta sake yi ta gabatar da sllhn nan parlor, tana xaune tana azkar wayarsa ya fara ring, har ya katse bata mike ba shi ma kuma bai ko yi motsi ba, ganin an sake kira ta tashi a hankali ta nufi kusa da shi ta durkusa tana laluban aljihunsa ta fiddo wayar tana kallon screen din, Jawahir ta gani jikin screen din wayar, har ya katse tana kallon wayar, can ta ajiye a hankali ta daura chin dinta bisa gwiwowinta tana kallonsa, bacci yake sosai, ta so tashi ta wuce apartment dinta amma ta samu kanta da kasa yin hakan, bayan minti kusan ashirin ta dago kanta ta jinginar kusa da shi, daga haka bacci yyi gaba da ita a yanda take, A hankali ya bude idanuwansa yana bin parlorn da kallo, lkci daya idonsa ya sauka kanta, ya mike xaune da sauri yana kallonta, kallon agogo yayi yaga biyu har yyi, fuskarsa ya kai dai dai nata, cikin bacci taji hannu a forehead dinta, ta bude ido da sauri, a hankali ya manna mata lips dinsa a kumatunta, a tsorace ta ja baya xata mike yyi saurin riketa, 6ata fuska tayi hade da buge hannunsa tace "Meye haka" sakkowa kasa yyi yace "Me kike yi a nan?" Sakin baki tayi tana kallonsa, can ta turasa xata mike ya ki saketa, hawaye ya cika idonta tayi da ta sanin kulasa ma da tayi, ya jawota jikinsa yana murmushi a hankali yace "Thanks for ur care Khadija, Neva knew you where this sweet...." Ta kara hade rai tace "Sake ni malam" ba musu ya saketa, ta mike ta nufi kofa, yace "Uhn.. it's pass 2 now fah" da sauri ta kalli agogo, dawowa tayi kamar ya fada mata mugun abu ta marairaice tace "Lahh ban sani ba... I don't know it's late...." yace "Wait... But... But it seems u came with food daxu, ina abincin" da kamar baxata ce masa komai ba sai kuma tace "yana Kitchen" yace "I am just hungry" kitchen ta wuce ta kawo masa abincin sai a sannan ta tuna ita ma bata ci abincin ba ai, tashi yyi ya shiga toilet din dakinsa sai da ya wanke bakinsa yyi wanka snn ya fito sanye da jallabiya yana goge gashin kansa da karamin towel, duk ta gaji da jiransa ya fito ya rakata, ya xauna ya bude abincin ya dau cokali ya fara ci, kallonsa take ta yi kafin ta mike ta tafi ta bude fridge ta dauko masa ruwa, sai da ya kusa cinye abincin ya sha ruwa sannan ya kalleta da sauri yace "But daxu kamar ruwan tap kika bani koh" tace "Uhn" xaro ido yyi yace "Subhanallah, but I don't take...." sai kuma yyi shiru, ita dai bata ce komai ba banda hararansa da take, jinginar da kai yyi da kujera ya lumshe ido, mikewa yayi ya shiga bathroom din parlor ya fito da alwala, a hankali tace "Ka raka ni pls dare yyi sosai" kallonta yyi kafin yace "Ohk as you wish tunda cinye ki xan yi a nan" daga haka ya nufi kofa tana biye da shi a baya, yana bude kofa ta matsa kusa da shi da sauri, ya fita tana biye da shi a baya suka shiga apartment dinta ya rufe kofar, ta sauke ajiyar xuciya tana bin parlon da kallo yace "Toh tafi ki kwanta" daki ta nufa yyi saurin cewa "Waittt... Xo ki kulle kofar tukun" dawowa tayi tana kallonsa ya buda ido yace "Sai da safe, I appreciate ur care" bata ce komai ba xai fita tace "You have.... A call" ya juya ya kalle ta, duk sai taji she sounds stupid, yace "Did you pick?" Tayi saurin cewa "Nooo, I just remembered now, I didn't even check, just heard the phone ringing" ita kanta tasan kame kame kawai take, yayi murmushi yana shafa lallausan gashin kansa. 12... Da asuba tana kitchen ta gama goge goge xata hada breakfast taji muryarsa ta waje yace "Morning" da sauri ta kalli direction din window taga bata hangosa ba, ta leka a hankali taga gym yake, ta bar gun da sauri ta ci gaba da hada ingredients din da xata soya eggs din da xata yi toasting da bread kasancewar bata yi da raw eggs, bayan wasu mintuna tace "How you feeling now?" bai amsa ba shi ma, hakan yasa ta juya ta kalli window direction, dai dai lkcn da ya iso kusa da window din kenan suka hada ido ya karyar da kai yana kallonta daga sama har kasa, juya baya tayi da sauri don rigar bacci ne jikinta, yace "Uhn... You look cute in that..." mamaki ne ya cikata ta kasa juyowa, ya ce "Ki shirya xaman gidan ya isa haka ki tafi makaranta yau koh" daga haka ya bar wajen, ko bai fada mata ba dama tayi niyyar tafiya makarantar yau. Karfe tara ta fito cikin shirin tafiya makaranta, fitowa yyi ya tsaya bakin door dinsa yana kallonta yace "Makarantar xa ki tafi yanxu?" Ba tare da ta kallesa ba tace "Yeah" yace "Alright you wait for me" daga haka ya koma ciki, k'asa wucewa tayi tana ta tsaye wajen har ya fito rike da makullin motarsa, as usual kananun kaya ne jikinsa, kallo daya tayi ma wandonsa ta dauke kai a ranta tace aiki, yace "to mu tafi" parking space ya nufa ta bi bayansa, sai da ta jira yyi warming motar sannan ta bude ta shiga. Haka kawai gabanta ke faduwa ta rasa dalili, idonsa na kan titi yana driving yace "Do you have problem with anybody here?" Ta kallesa da sauri, shi ma ya kalleta, mayar da dubansa yyi kan titi, tana girgixa kai tace "I don't think it's any of ur concern" shiru ya d'an yi kafin yace "Ohk then" bai sake ce mata komai ba har ya isa makaranta, bata yarda sun hada ido ba ta bude motar ta fita tace "Thanks" daga haka tayi wucewarta. Tafe suke da course mates dinta bayan sun fito lectures din karfe goma da suka shiga, cafeteria suka nufa ita kuma tace masu xata je library karatu, bayan sun rabu bata je library din ba, kawai she want to be alone ne dama, guri me shiru ta samu ta xauna ta tsura flower dake wajen ido, ta kusa minti talatin a wajen kamar ance ta dago suka yi ido hudu da khaleel dake xaune d'an nesa da ita da wata baturiya dake karatu ita ma, mikewa yyi bayan sun hada ido yana kallon baturiyar yace "Stephanie c yah later" mikewa khadijah tayi ta riga sa barin wajen. Da safe misalin karfe takwas ta fito apartment dinta, yau dai kam ta makara sosai, tsaye ta gansa parking space waya kare kunnensa, suna hada ido ya dauke kai, ita ma bata sake kallonsa ba har ta fita daga gidan a xuciyarta tace "Can ta matse maka" Ita kadai ce xaune Cafeteria bayan sun gama lectures din ranan, Vanessa tuni ta bi saurayinta suka tafi tun bayan da suka gama cin abinci, ita kanta ta rasa me yasa ta ki barin gun har lkcn gashi tana son wucewa, chatting take da kawarta Salima dake Nigeria a WhatsApp kanta a duke, kamar ance ta daga kai tayi still ganin wa enda suka shigo Cafeteria din, a hankali ta saki wayar hannunta ya xame ya fada kan cinyarta, da sauri ta kauda kai xuciyarta na mugun bugawa, table dake gefen nata ya xauna kan kujerar shi da Baturen da suka shigo wajen tare, cikin sanyin muryarsa yake cewa "I don't have intentions of coming here frank, let be fast" baturen yace "Yeah, they will be here soon..." baturiyar dake tsaye kansu ta mika masu takardar list din abinci dake hannunta, muryarsa ya kuma dakan codon kunnenta da accent din turawa yace "Number 6 content for my frnd, just table water for me....." Kamar ana tilasta sa yyi maganan, a hankali khadijah ta mike kamar an xare mata abu a ciki, tana boye gefen fuskarta da mayafin kanta ta nufi kofar fita sum sum tana hade hanya, satan kallonsa tayi suka yi ido hudu don bin ta da kallo yyi, lkci daya ya mike ya xaro ido yana kallonta, tana ganin haka ta kwasa a guje, bin ta yyi da sauri yana cewa "Imannn..... Imannn plss wait, Iman....." hankalinta bai gama tashi ba sai da taga bin ta yake tsakaninsa da Allah gashi ya kusa kamo ta, ta jefar da takalman kafarta da jaka ta fashe da kuka sosai, gudu take kamar her life depends on it, tana yi tana waiwayowa a tsorace, Gani tayi wasu wanda da alaman Africans ne sun rikesa suna tuhumarsa me yasa yake bin ta, hakan ya kara mata kwarin gwiwan gudun, taxi ta samu ta shiga tana waige waige muryarta na rawa tace "Bridge street" tuni mai cab din ya ja suka dau hanya, lumshe ido tayi hawaye masu xafi na sakko mata, tana son fashewa da kuka ko xata ji dadi amma tayi controlling kanta ganin inda take, number gidan ta gaya masa bayan sun kai yyi parking ta bude motar ta fita, tunawa tayi bbu kudin da xata basa, tana kallonsa a sanyaye tace bari ta shiga ta dauko masa kudi, a hankali take tafiya compound din tana goge hawayen dake sauko mata, dai dai fitowar Khaleel part dinsa rike da makullin mota da wasu takardu, tsayawa yyi yana kallonta daga sama har kasa mamaki dauke fuskarsa, hade rai tayi sosai ta turo baki ta dauke kai ta kuma ki motsi daga inda take, taku daya biyu ya iso gabanta tayi saurin barin gun, fixgota yyi ta fashe da matsanancin kukan dake cin ta tun daxu, da mamaki yace "What's wrong with you, me ya faru? where are you coming from?" Kin cewa komai tayi sai kukan da take yi sosai, damuwa ne sosai fuskarsa yace "Talk to me plss, me ya same ki?" Ta hadiye kukan da kyar tana share hawayen idonta cikin rawar murya tace "Ban ba mai Cab kudi ba...." Kallon gate yyi, can ya sake ta ya fita, Durkushewa gun tayi ta dinga rera kuka xuciyarta na mata xafi, a haka Khaleel ya dawo ya sameta, ya hade rai yace "malama tambayar ki nake where r u coming from" mikewa tayi tana share hawayen idonta har lkcn bata daina kukan da take ba xata bar wajen ya rikota yana mata wani kallo a d'an tsawace yace "Me aka maki nace, where r u coming from?" Ganin ba magana xata yi ba yana rike da hannunta ya wuce part dinsa da ita, xaunar da ita yyi kan kujera a parlor ya duka gabanta yana kallonta cikin sanyin murya yace "Now tell me what happen" cike da karfin hali tace "Nothing" ido ya xuba mata bai sake cewa komai ba, can ya mike ya koma bayan kujera ya rungume hannu ya tsaya yana kallonta, ta gama cin kukanta ta jinginar da kanta da kujera, tafi minti sha biyar a haka bbu kalan tunanin da bata yi ba har bacci ya dauketa. Shi kam yana tsaye har lkcn bayan kujera yana kallonta yana mamakin irin taurin kanta, sai da ya ga bacci ya dauketa sannan ya xagayo ya iso gabanta ya durkusa kusa da ita, shi dai ya san tausayinta kawai yake ji har ransa, though he don't know her that much but he knows she's pained, coz she looks so, lumshe ido yyi ya bude yana kallonta, Khadijah is just the definition of cool Beauty, tall.... fair.... Slim with a perfect shape, Best of all she have got d most sexiest lips and eyes, her nose..... Kauda tunanin yyi, a xuciyar sa yace not as beautiful as Jawahir, a hankali ya mike ya dafata da xumar yace mata ta kwanta, a firgice ta farka tace "Aliyuuu...." Ja baya yyi yana kallonta. Da kyar ta karashe bude idonta da yyi mata nauyi ta daga kai tana kallon sa, xamowa kasa tayi a hankali, ya mike ya rungume hannayensa yana kallonta a ransa yana nanata sunan da ta kira, tashi tayi ta runtse ido ta juya xata fita parlorn, murya can kasa yace "Malama" sake juyowa tayi, yace "Where are u coming from" bata iya ta kallesa ba cikin sanyin murya tace "School" yace "Me ya same ki a can?" Tace "Am not feeling fine" bai sake cewa komai ba ta nufi kofa ya bi ta da ido har ta fita. Magungunan ta ta dauka ta sha lkci daya kuma bacci ya dauketa, bata farka ba sai da asuba shi ma ta dalilin yunwa, ganin lkcn sllh bai karasa ba ta shiga kitchen don neman abinda xata ci, motsi ta dinga ji a waje ta leka a hankali, gym ta gansa yana yi jikinsa sanye da 3qtr kadai, suka yi ido hudu tayi saurin barin gun, parlor ta koma ta dauko Hijab ta sa sannan ta dawo kitchen din, har ta gama abinda xata yi bata sake leka waje ba, ta koma parlor da Indomien ta, tun da tayi wanka bayan tayi sllh gabanta ke ta faduwan xuwa schl gashi tana da test, hawaye ta dinga yi duk xuciyarta tayi rauni, gaba daya xaman kasar ya isheta taji gida take son komawa, to karatun fa, shekara bai kai biyu ya rage mata ba, danna bell aka yita mike a d'an tsorace, don ynxu kam gaba daya a tsoracen take, hijab ta saka ta fito, a hankali tace "Yes?" Yace "How you" bude kofar tayi ta gaishesa, yace "Baxa ki schl din bane yau?" Kamar xata yi kukatace "Ban sani ba" kallonta kawai yake bai ce komai ba, bayan yan sakwanni yace "Toh ki shirya, I am waiting for you" daga hka ya juya ta rufe kofar. Har dept ya ajiye ta, kowa ya ganta a lkcn yasan a tsorace take, yace "Yaushe xa ki gama lectures din?" Tace "Quiz ne" yace "Shi kadai?" Kai ta gyada masa, yace "ohk am around I will call ltr in ji ko kun gama" buda masa hannu tayi tace "Jakar ya fadi jiya ai" Kallonta ya tsaya yi, can ya ciro waya aljihunsa ya mika mata yace "I will call" ta karba tana gyada masa kai, daga hakata fita motar, shi ma ya fito yace "I think I will leave the car here" bin satayi da ido har ya wuce kafin ita ma ta bar wajen da sauri. *Haske Writers Association*???? ✨ *Noor-Al-Hayat*✨ _Khaleesat Haiydar_????✍???? (adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); 13.... Bata yarda ta fito dept ba tun bayan gama test dinsu, duk gaba daya a tsorace take, gani take kamar at anytime xata iya ganin Aliyu a gabanta, karfe sha daya da qtr wayar khaleel dake Jakarta ta fara vibrate, fiddowa tayi taga Emoji biyu na love gaban screen din, ta yi jim don bata san ko shi bane, har ya kusa katsewa sannan ta daga ta kai kunne tayi shiru, muryar mace taji tace "Hello Baby...." hakan yasa ta katse wayar, sake bugowa tayi bata daga ba har ya katse. Tana ta xaune da wani course mate dinta dake second degree dinsa d'an Nigeria but residing in Malaysia yana ta mata hira ita dai sai dai tayi murmushi tana saurarensa, dai dai nn wayar hannunta ya sake vibrate ta daga tana kallon number, sai kuma tayi picking ta kai kunne, daga daya bangaren taji yace "Are you done?" Tace "Umm" yace "Aiitt am waiting..... Near the car" daga haka ya katse wayar, ta mike tana kallon course mate dinta tace "Wanda xai daukeni yana jirana, xan tafi" ya mike shi ma yace "To bari in raka ki" da kamar baxa ta ce komai ba sai kuma tace "Ohk" tana gaba yana biye da ita har suka iso gun motar, Tun daga nesa Khaleel ke kallonsu, sai da ya ga sun iso ya dauke kai, Usman yace "Assalamu alaikum" sake juyowa khaleel yyi kamar baxai ce komai ba sai kuma ya bude motar ya basa hannu suka gaisa, Khadijah ta tabe baki ta xaga daya side din motar tana kallon Usman tace "Thanks.... sai gobe in sha Allah" Usman yace "Aiiit Allah kai mu lfya" Sallama yyi da khaleel sannan ya wuce, Khaleel ya tada motar suka bar wajen, har suka hau kan titi bai ce mata ba, ita ma bata ce masa ba, wayarsa dake hannunta ya fara vibrate kuma, kallon screen din tayi taga number daxu ce ta mika masa, sai da ya kalli screen shi ma kafin yyi parking gefen titin, ya jira wayar ya katse sannan ya kira yace "How you...." Satan kallonsa khadijah tayi ta dauke kai tana kallon waje, bayan yan sakwanni yace "Like serious, alryt sorry for that wayar baya gu na ne" d'an murmushi yyi yana shafa lallausan bak'in gashin kansa dake sheki yace "I left the phone with a frnd, and I guess....bata san ke bace da baxata dauka ba, yanxu dai I will cal back in 10 mins time, I am on the road" daga haka ya katse wayar yace "Why did..... You pick her call?" Kamar me counting words din yyi maganan ya juyo yana kallonta, bata kallesa ba bare ta basa amsa, hakan yasa ya ci gaba da driving dinsa, sai da suka kusa gida yace "Who was that guy?" Ta juya tana kallon sa da kyau tace "And why are you asking?" Tabe baki yyi bai ce komai ba, sai da yyi parking ta hade rai tace "Da Kasan da xata kiraka ka bani wayar" daga haka ta juya xata bude motar ta fita yasa lock, juyawa tayi tana kallon sa, yace "Ki dai bi a hankali da guys din makaranta da kike kulawa, and you even let him accompany you to where I am, toh ni meye hadina da shi?" Mamaki ne ya cika ta ta saki baki tana kallon sa, a mugun fusace tace "Ina ruwanka ma idan na bi samarin makaranta, I guess it shud be none of ur concern, let me outta here immediately.... Ka bude min mota in fita" Tun da ta fara ya kwantar da kujeran motar ya lumshe ido yana saurarenta, jin tayi shiru ya dago kujeran ya xauna yana kallonta yace "Kin gama?" Ta dago tana kallon sa ranta na suya, bude lock din motar yyi yace "Ok then, kindly move out and close d car door behind you" bude motar tayi kamar xata tashi sama ta nufi apartment dinta ba tare da ta kulle masa motar ba. Wayan da tayi ta yi da su Shuraim yasa ta mance duk damuwar dake tare da ita, ganin lkcn kwanciyarsu yyi tayi sallama da su ta kwanta don tayi shirin bacci tun bayan da tayi sllhn magrib, lkci daya baccin ya dauke ta. Tun da ta tashi take ta tunanin yanda xata tafi schl don kusan tests suke, tunanin hakan yasa ta rushe da kuka tace "Do I ever have to meet with him in my life again??" Ganin lkci na ta wucewa ta mike a sanyaye ta dau jakarta da mayafi ta fita parlor, kallo daya tayi ma motar khaleel dake parking space ta hade rai ta dauke kai ta rufe apartment dinta, a hankali take tafiya har ta isa titi, cab ta shiga suna isa makarantar ta biyasa kudinsa ta fito tana kalle kalle kamar munafuka, tafiya take da sauri ta shiga schl don a waje ta sauka daga cab din, kawai mota taga ya tsaya gefenta bata ankara ba sai ganinta tayi cikin motar ta fasa ihu a tsorace amma tuni aka ja motar. Khadijah ta bude idonta a hankali ta na bin parlorn da take ciki da kallo, ta mike da sauri xuciyarta na bugawa tana kiran Allah a xuciyarta, kamar ance ta juya bayanta ta ga mutum tsaye yana kallonta, xuciyarta tayi mugun bugawa tayi saurin dauke kanta, karasowa yyi parlorn cikin sanyin murya yace "Imannn" bata san lkcn da ta xube wajen ba ta fashe da wani matsanancin kukan takaici, durkusawa yyi gabanta a hankali yace "Imann... I...." Mikewa take son yi ya rikota fixge hannunta tayi da karfi, yyi still yana kallonta ko kiftawa bbu, tayi saurin dauke kai tana kuka sosai ta hade kai da gwiwa, mikewa yyi ya dago ta yyi hanyar wata kofa da ita, tashin hankalin da ba a sa masa rana, ihu ta sakar masa tana turasa amma da yake karfinsu ba daya ba sae da ya shigar da ita kofar ya rufe, cikin rawar murya take cewa "Me ka dawo yi rayuwata kuma Aliyu, I am no longer under you or ur family, let me plsss am begging you in the name of Allah, ka rabu da ni......" Jinginar da ita yyi da bango yana kallonta da idanuwansa da suka kada yace "Kinsan shekarun da na dauka ina neman ki xa ki ce in rabu da ke" a tsawace ya kare maganan, cakumosa tayi tace "Kana nemana?? in maka me Aliyu? Neman me kake min, ka rufa min asiri ka kyaleni in tafi don Allah" yyi wani murmushi yace "In kyale ki ki tafi? Haka kawai in kyale ki ki tafi?" Turasa tayi iya karfinta amma ko gezau ta kuma fashewa da matsanancin kuka xuciyarta na mata xafi da suka, cikin kuka sosai tace "Aliyu ba don ni ba kayi hakuri ka kyaleni" yana kallonta a hankali yace "Ki yafe min Iman...." Tsayar da kukan da take tayi tana murmushin takaici tace "In yafe maka? Aliyu dama kayi min wani laifi ne da xan yafe maka, gaskiya ban san shi ba, idan ma akwai to shari'armu sae a lahira" finciko ta yyi da idanuwansa da suka yi mugun kadawa yace "A lahira?" Kasa amsawa tayi ganin ynda ya sauya kamannin fuska, jefar da ita yyi kan gado ya karaso yana mata wani kallo yace "Wani Shari'ar ce sai mun je lahira xa ayi ta? Ki fadi me nayi maki?" Ta dinga ja baya tana ganin dishi dishi, a hankali ta kira sunansa tana girgixa kai daga nan kuma bata sake Sanin abinda ya faru ba ta dai bude ido a hankali ta dalilin axaban da xuciyarta ke mata, Kwance ta ga ta kan gado ita kadai dakin, da kyar ta mike xaune ta dafe xuciyarta, lkci daya ta sauka gadon ta nufi kofarta bude taji a rufe da key, sulalewa kasa tayi ta dafe kirjinta tana kiran Allah a xuciyarta, bude kofar taji kamar ana yi ta tashi tsaye da sauri ta koma bayan kofar ta tsaya aka bude ya shigo cikin dakin yana kalle kalle, da gudu ta fice dakin ya juya da sauri, bin bayanta yyi yana kiranta, ganin bbu inda xata tsira parlorn ta nufi dinning table ta dau wukar da ta gani kai ta juyo tana kallon sa hawaye na sakko mata, girgixa mata kai yyi yace "Wait Iman...." cikin sarkewar murya tace "I swear to Allah who made me kana isowa kusa da ni xan kashe kaina Aliyu" still yyi yana kallonta ya kasa motsi wajen, ta nufi kofa tana rike da wukar hawaye na xubo mata sosai, cikin sanyin murya yace "Noo khadija karki tafi don Allah" da baya da baya take tafiya har ta isa kofa ta fice, ikon Allah kadai ya kai ta gida duk da daren da yyi, ganin halin da take ciki mai cab din ma bai karbi kudi bata shiga gida, nan bakin kofa ta durkusa don bbu jakar makullin, ta kai minti biyar a haka kafin tayi karfin halin buga kofar khaleel, va a dau lkci ba ya bude, ja baya yyi yana kallonta da mamaki, can ya durkusa yace "Are.... are you okay?" Girgixa masa kai tayi numfashinta na sama, ya dago ta yana kallonta yace "Subhanallah" ta fashe da matsanancin kuka ta rikosa tana girgixa kai tana nuna masa kirjinta cikin rawar murya tace "It's hurting....." mikewa yyi da sauri ya shiga ciki ya dauko makullin mota ya dawo, cikin ikon Allah khaleel ya isa wani babban hospital don duk ta rikitasa driving kawai yake, tun da ta rufe ido bayan da suka shiga asibitin bata sake budewa ba sai washegari da safe, yana zaune gefenta ya jinginar da Kansa jikin kujerar da yake xaune, su kadai ne cikin ward din,ta mike xaune da kyar taa kallon ruwan hannunta, jin xuciyarta tayi fayau, sai dai har lkcn tana jin kamar numfashinta na seizing,ta kalli oxygen dake gefenta a dakin, ta mayar da kallonta ga agogo taga takwas ya kusa, cire drip din tayi cike da karfin hali ta sauka kan gadon, kofar da take tunanin na bayi ne ta shiga. Bata dade ba ta fito da alwala, sai kuma taga bbu hijab bare darduma, ta isa kusa da khaleel cikin rashin kuxari tana kallon sa, bacci yake a yanda yake, lkci daya taji tausayinsa sosai wanda hakan yasa hawaye ya cika idonta, durkusawa tayi a hankali ta dafa kujeran cikin sanyin murya tace "Doctor..." Lkci daya ya bude ido yana gyara xamansa, mikewa yyi da sauri ya durkusa gabanta yana kallonta damuwa yace "How you feeling now khadijah?" Murya can kasa tace "Naji sauki, you need rest, ka kwanta saman gado am nt sleepy" hannunta ya kamo yana kallonta xai yi magana daidai nn aka bude kofa wata nurse baturiya ta shigo ward din. Mikewa yyi nurse din ta karaso tana tambayar me yasa ta cire drip din, khadijah ta mike race "I used the restroom" mayar mata da drip din tayi bayanta koma kan gadon, khaleel ya bi ta tare suka fita ward din, tagumi khadijah tayi tana kokarin ganin hawaye bai xubo mata ba, ba a dau lkci ba khaleel ya dawo da mug a rufe ya xauna gefen gadon ya mika mata yace "Gashi ki sha xa a maki allura...." Ta sa hannu ta karba ya bude mata, a hnkli ta kai baki tana sha, ya kafa mata ido, bayan ta sha ta sauke cup din ta karbi murfin ta rufe, yace "Ina ke maki ciwo ynxu?" Ta girgixa masa kai tace "Bbu ko ina, just my chest" yace "Xai daina in sha Allah" nurse din ta dawo rike da tray me dauke da allura da magani, tana kallonta ta gama hadawa ta karaso, mikewa yyi ya fita dakin ya rufo kofar. Tana mta alluran ta bata maganin sannan ta fita bayan ta gwada mata yanda xa ta sha, bayan fitar nurse din khaleel ya shigo rike da table water, ta sha maganin, a hankali tace "I want to go home plss" yace "No sae kin kara samun sauki," ta girgixa masa kai tace "Am feeling better yanxu, bacci nake son inyi" yace "Toh ae sai sun yi discharging dinki koh" bata kuma cewa komai ba ya gyara mata pillow yana kallonta, ba musuta koma ta kwanta a hankali. Sai kusan karfe daya aka yi discharging dinsu ya biya bill din suka bar clinic din, sai da suka yi nisa cikin sanyin murya tace "How much is d bill" bai ce komi ba kuma bai kalleta ba, yayi parking wani eatry, da ido ta bi sa har ya shiga, rike da Leda biyu ya fito ya bude motar ya shiga suka bar wajen. Parking yyi ya juya yana kallonta, ta jinginar da kai da kujeran motar idonta lumshe, a hankali ya dauke kansa, can ya juyo murya can kasa yace "Khadijah" lkci daya ta bude ido, yace "We are home" kalle kalle ta fara yi, ya bude motar ya fita bayan ya dau takeaways din da yyi, ta fito ta rufe motar tana jin jiri na kwasarta, bata yarda ta bar jikin motar ba, kamar yasani kuwa ya xagayo yana kallonta, hannunsa ya mika mata, ta sauke idanuwanta ta mika masa nata hannun, yana rike da ita har suka iso apartment dinta ya kalleta yace "Key?" Shiru tayi kafin tace "A jakata yake" yace "Ina jakar?" Bata iya tace komai ba, ya bude apartment dinsa. *Haske writers association*???? ✨ *Noor-Al-Hayat*✨ _By khaleesat Haiydar_????✍???? (adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); 14..... Tsayawa yyi yana kallonta ta shiga parlorn sannan shima ya shiga, kan kujera ta nufa ta xauna, ya karaso bayan ya kulle kofar ya ajiye ledan hannunsa kan center table, sannan ya shiga daki, jinginar da kai tayi da kujera tayi xurfi cikin tunanin da take taji yana kiranta, dagowa tayi da sauri ta gansa tsaye gefenta ya rungume hannunsa, a hankali yace "Na hada maki bathing water a bathroom" sunkuyar da kai tayi, ta mike yana gaba ta bi bayansa xuwa dakin, towel ya dauko ya mika mata, ta karba murya can kasa tace "Thank you" ya juya ya fita dakin, da mouth wash na Listerine ta wanke bakinta, tayi wanka da shower gel, sai kusan bayan minti talatin ta fito daga bayin, bayan tayi ta tsayuwa bakin kofar bathroom din tana tunanin fitowa da towel, bbu kowa dakin sai Hijab dinta da ta gani kan gado, mamaki ya kama ta tayi ta kallon Hijab din, karasawa tayi ta dauka ta koma bathroom din, wanke kayan da ta cire tayi sannan ta sa hijab din ta fito da kayan da ta wanke a bucket, xaune ta gansa a parlor yana rike da remote, kallo daya yyi mata ya dauke kai har ta shigo parlorn, yace "Why did u wash, u still under medication" bata ce komi ba, yace "Na bude maki kofar...." Tace "Da gaske?" Yace "Ehh, ki tafi ki shirya" murya can kasa tace "Nagode" sannan ta wuce tana rike da Hijab din. Sai da tayi sllh snn ta wanke masa towel din a bayinta ta fito ta shirya ta tafi shanya kayan da ta wanke da towel din nasa, kwanciya tayi daki bayan ta gama lkci daya bacci ya dauketa. A hankali ta bude ido jin kamar ana tashinta, ta mike da sauri tana kallon sa, yace "I've been knocking and calling since, but.... Taso mu je ki ci abinci" ta girgixa kai tace "Am not hungry bacci nake ji" yace "Noo, baki ci komai ba yau, kuma kinga xa ki sha magani, you have to take something...." Daga haka ya mike yana kallonta, sauka tayi daga kan gadon ta bi sa suka fita parlor, xuba mata abincin yyi ya mika mata ta karba ta fara ci, wayarsa yake ta dannawa har ta ajiye abincin tana yamutsa fuska tace "Na koshi fa" ya kalli abincin sannan ya dau ledan maganin ya ballar mata drugs din ya taso ya mika mata da goran ruwa ta karba, ta sha maganin tana kallon sa yace "Allah ya sauwake" bata iya ta ce komai ba, yace "To ki je ki kwanta, sleep without thought plss" ta gyada masa kai sannan ta tashi ta shiga daki. Bata tashi ba sai kusan biyu da rabi na rana, ta shiga bayi tayi alwala ta fito tayi sllh, tana idarwa ta sake kwanciya. Knocking kofar dakin taji ana yi cikin bacci, ta mike xaune ta sa hijab sannan ta bude kofar, yana tsaye bakin kofar, yace "Have u prayed zuhur?" Ta gyada masa kai, yace "Abinci fa" tace "I am not hungry" ya girgixa kai yace "You are, fito ga abinci na kawo maki sai ki sha magani" daga haka ya juya ya bar wajen, bin sa tayi, yana daga tsaye ya nuna mata abincin kan table, ta karasa ta dauka, tuwon shinkafa ne da miyar vegetable ta gani da ta bude, ta daga kai tana kallon sa, ya daga kafada yace "Yea, a frnd of mine ce ta yi..." Tace "Kai baxa ka ci ba?" Ya girgixa kai da sauri yace "Noo I don't take heavy foods, I don't take swallow" murmushi tayi ta dauke kai, ya shafa kai yace "Sbda ke na karbo" tace "Toh ngd" yace "No thanks" plate taje ta dauko a kitchen ta debi abincin, shi dai har lkcn yana tsaye, ta kallesa a hankali tace "Baxa ka xauna ba" shiru ya d'an yi, sai kuma ya karaso ya xauna kan kujerar dake kallon nata yace "So u care" bata ce komai ba ita dai, a hankali ta dinga cin tuwon, duk lkcn da ta daga kai sai sun hada ido, daga karshe bata sake yrda ta dago ba har ta gama cin tuwon ta dau magani ta sha, sai a snn ta sake kallon sa taga kallonta yake still, hade rai tayi ta dauke kai, yyi murmushi yace "Who is Aliyu?" Kallon sa tayi da sauri, kamar yanda shi ma yake kallonta har lkcn, can ta tsuke fuska tace "Ban gane ba" bai sake cewa komai, bayan kusan minti biyar yace "don't pretend... Is he ur Husband?" xuciyarta na bugawa tace "Nooo" Yana mata wani kallo yace "Ur Ex Husband?" Hade rai tayi sosai cike da masifa tace "Noooo" sai kuma ta mike tana masa wani kallo tace "I know nothing about what u are saying" ya d'an yi murmushi yace "You passed out yesterday at the hospital with the name Aliyu in ur Mouth" shiru tayi tana kallon sa a sanyaye, lkci daya hawaye ya cika idonta, can ta juya ta bar masa parlorn da sauri, kiran ta ya dinga yi har ta shige daki ta xauna kasa ta hade kai da gwiwa ta fashe da kuka, bin ta yyi cikin dakin, ya karaso gabanta ya durkusa a hankali yace "Ohk, I am very sorry Khadijah, may be I shouldn't have say anything about that, but dole xan yi magana, Billah da xan ga Aliyun nan... Sai na sa ya d'an dani abin da kike ji, I guess he broke ur heart kuma yake kokarin dawowa rayuwar ki yanxu saboda may be selfish reason dinsa, he will regret that duk ranan da muka hadu face to face.... I vow!" ita dai bata ce masa komai ba sai kukan da take, duk jikinta yyi mugun sanyi, mikewa yyi ya fita dakin. Har dare khaleel bai shigo ba, tun da tayi magrib take hade abubuwan da tasan xa ta kai gida, don bata jin xata kara kwana a kasar, gaba daya xaman kasar da karatun ya fice mata a kai, hawaye kawai take duk jikinta a sanyaye, Sudais has always wanted her to be a doctor, ta xo ta samu kan ta a bangaren pharmacy, wanda a yanxu bata jin ma xata ci gaba, domin kuwa ta hakura da karatun, may be some other time she wil be d doctor Sudais wants her to be, to ko ta xama likitan ma what is that adding to her life, wanda take son yi dominsa ya tafi ya bar ta a lokacin ta fi bukatarsa a rayuwarta, baxa ta ce ya gujeta ba, but what's the difference? Kusan duk daya.... Ta share hawayen idonta ta fito parlor a sanyaye, tsaye tayi tana kallon Khaleel da shigowarsa knn a hankali ta sauke idonta kasa wasu sabbin hawayen na xubo mata, ya karaso kusa da ita yace "Ina xa ki?" Ta juya masa baya tana kkrin ganin bata fashe da kukan dake cin ta ba, a hankali yace "Khadijah" cikin rawar murya tace "Am going back to Nigeria" ya juyo da ita ya xaunar gefen kujera yana kallonta, ya bar ta tayi kukan me isarta, ta hade kai da gwiwa tana sauke ajiyar xuciya, cikin sanyin murya yace "Tell me about you Khadijah" Ta dago tan kallon sa hawaye na sakko mata, sai dai kuma tayi ma kanta alkawarin bayan Sudais bbu wanda xai ji ita wacece, muryarsa ya dawo da ita tunanin da take, yace "I still don't deserve to know you koh?" Ta sunkuyar da kanta tana goge hawayen dake sakko mata, a ranta kuwa tunani take anya xata iya fadi ma Khaleel ita wacece kuwa, a hankali ta xamo kasa daga xaunen da take kan kujera, ya sakko k'asan shima yana kallon kwayar idanuwanta da suka rine, kife kanta tayi da kujera cikin sanyin murya tace "Ka daina kallona da idon ka" ya d'an yi jim sai kuma yace "Why?" A hankli tace "Bana son irin su" murmushi yayi yace "Da gaske" taki cewa komai, a hankali yace "Toh na daina kallon ki" dagowa tayi suka kara hada ido tayi saurin mayar da kanta jikin kujera, dariya ta basa sai dai bai yi ba ya shafa kansa yana murmushi, murya can kasa yace "Am all ears Khadijah" ta dago kanta tana wasa da dogayen yatsun ta tace "Ohk....." Wayarsa ya da ya fara ring ya ciro aljihunsa, ta kalli screen din kamar yanda shi ma yake kallo, Jawaheer ne jikin screen din... Yyi silencing wayar ya ajiye a hankali, Tsura ma lallausan carpet din da suke xaune kai ido tayi ko kiftawa babu, cikin sanyayyan muryarta tace "I am an only child... I was raised from a very rich home, I was raised by only my Dad don kuwa ina da shekara uku kachal a duniya mahaifiyata ta rasu...." D'an murmushi tayi wasu sabbin hawaye na taruwa idonta tana kallon Khaleel da ya kafeta da nasa idon.... Who is Khadijah? #Shekaru 6 baya #6 years earlier #Flash back.... *Haske Writers Association*???? Uhm don't know how to announce this, Reason being that... the love, the prayer, the encouragement is ???????? but sai dai ina da na gaba da ni and i heed to their advice always, and babu wanda bai son progression, so?? ???? I think this all for the free pages of *Noor-Al-Hayat* sorry to those that I took unaware but don't forget I announced needing patronage in my previous book... you think you love the book, you think love Khaleesat Haiydar.... Then gladly patronize her.... If interested... ping Via Facebook inbox or Via WhatsApp 07087865788, they will be groups available, Thank you. ✨ *Noor-Al-Hayat*✨ (adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); _By khaleesat Haiydar_????✍???? _littafin Noor-Alhayat na siyarwa ne from this page, kindly patronize ur writer and read happily, duk wanda bai ji dadi ba hakan da nayi yyi hakuri pls_ Shekaru shiddah baya..... A hankali ta karashe shanye shayin dake hannunnta ba tare da ta bi ta kan soyayyen kwan dake gabanta ba ta ajiye cup ta mike tace "Umma to idan Kawu ya tafi da ni baxan sake dawowa ba?" warce ta kira da Umma dake duke tana goge mata takalmanta masu tsada tana xuba su a wani jaka ta juyo da rinannun idonta tana kallon 'yar yarinyar warce da kadan ta haura shekara sha uku tace "Xa ki dawo Khadijah in sha Allah" Khadijah bata sake cewa komai ba tana dai tsaye, tsadaddun ready made ne jikinta da cover shoe mai kyau sai kyalli yake, da farin hijab karami, kunnuwanta dauke da dankunnen zinari 'yan kanana, Khadijah tace "Toh Umma me yasa ke baxa mu je da ke ba" Umman bata kalleta ba tace "Nima gidanmu xan je Khadijah" Khadijah ta durkusa kusa da ita a hankali tace "Umma ni bana son gidansu Kawu ki tafi da ni gidanku don Allah" Umman bata ce komai ba har ta gama rufe jakar ta daura kan babban jakar dake dauke da kayan Khadijah, jin Umma bata ce komai ba Khadijah ta dau remote xata kunna TV, Umma ta jefa mata wani kallo tace "Xaki fara ko, ni dai na gaya maki kar kije gidan mutane kina masu irin wannan kallon da kike kamar wawuya, kashe TV din nan yanxun nan" Khadijah ta kashe tvn ta koma ta xauna kan kujera, dai dai shigowar kawunta, kuma wan mahaifinta, har ya karaso parlon idonsa na kan soyayyen kwan da Khadijah ta bari a plate, ya dau plate din ya xauna yace "Tsabar almunbazzaranci dubi abinda aka yi ma lafiyayyen kwai, karshen komai ya xo in sha Allah" ita dai Umma bata ce komai ba ta wuce daki don fiddo nata sauran kayan da ya rage a gidan, Kawu ya dinga cin kwan kamar his life depends on it, har dai ya gama daga karshe ya ajiye ya na kallon Khadijah dake ta kallonsa yace "Toh ki tashi ki fita ga adai daita can ki shiga ki jirani a kofar gida" ta xaro ido tace "Kawu ba da mota xa mu je ba" dakuwa ya mata yace "Tashi ki ban waje" mikewa tayi tayi hanyar kofa tana waigosa, shi kuma ya dau katon jakar ya bi bayanta, Umma ta fito da nata kayan waje ta dau plate da cup ta shiga kitchen ta wanke su ta ajiye, ta kuma sake tabbatar da komai a kashe yake sannan ta bi bayansu, Khadijah na tsaye jikin adai daitan Umma ta jawo ta, a hankali tana kallon eyeballs dinta tace "A duk inda kika tsinci kanki ki xamo mai hakuri kin ji Khadijah, nasan ki da shi, komai kuma aka sa ki kiyi, sannan most important of all banda kallon TV don Allah..." Khadijah tayi murmushi da ya bayyana beauty point dinta tace "Umma I can't do without watching tv fah" Umma ta hade rai tace "So u won't heed to what am saying koh?" A hankali ta sauke idonta tace "Am sorry mum" Umma ta ja kumatunta tana murmushin karfin hali tace "That's my girl" a hankali kuma a sanyaye ta kara da cewa "And always pray for daddy, kullum kika yi sallah ki masa addu'ar Allah ya masa rahama" Khadijah ta gyada kai tace "Toh Umma" Umma ta shigar da ita adai daitan tace "Safe trip dear, I will always pray for you" Khadijah ta gyada mata kai trying hard to control her tears, Tuni Umma ma ta juya ta nufi main road da jakarta ba tare da ta bi kan kawu Jibril dake kokarin maka ma gidan kwado ba, Khadijah ta bi stepmother din ta da kallo hawaye na sakko mata, a haka kawu ya shigo adai daitan, yana mata wani kallo yace "Kukan uwar me kike ma mutane" cikin rawar murya tace "Umma ta" Dungurinta yyi yace "Uwar ki ba Ummar ki ba" Khadijah ta sunkuyar da kai, mai adai daitan ya dau hanyar park, hannu Khadijah ta daga ma stepmum dinta ganin sun wuceta, ita ma ta daga mata tana goge hawayen idonta. Tasha mai adai daitan ya kai su, kawu ya sauke kayan Khadijah ya bai ma mai adai daitan kudi sannan ya biya masu kudin mota xuwa katsina, da kyar ya yarda ya biya seat biyu wai xai dauketa a kafa, sai da yan motar suka sa baki, bayan kusan minti goma motar ta cika suka dau hanyar katsina, tunda Khadijah take bata taba shiga motar haya ba, rabonta kuma da katsinan tun tana da shekara bakwai da suka je tare da Abbanta, kai kana ganinta kasan she is restless, matar da ke kusa da ita tace "Yarinya me ya faru?" Kamar xata yi kuka tace "Amai...." Kawu ya kwalalo ido yace "Me?" Tace "Amai" dungurinta yyi yace "Ke yarinya ce xaki ce ma mutane kina jin Amai cikin mota" matar tace "Haba bawan Allah, sai yara ke Amai idan suna tafiya" dakatar da ita yyi yace "Ke... Learn to mind ur business while in public, 'yar ki ko tawa" matar tace "Aa ba yar ka bace wllh, don da yar ka ce baxa ka yi mata abinda kayi mata ba yanxu" Bala'i kawu ya fara kamar mace a motar, ana haka Khadijah ta toshe bakinta jin aman xai taho mata, matar bata bi ta kan kawu ba ta sa driver ya tsaya, ta sauke Khadijah, nan kuwa ta dinga kwara Amai, matar na tsaye kanta, shi ko kawu yana cikin mota sai fada yake yana kumfar baki, kowa ya xuba masa na mujiya bbu wanda yace ci kanka, wani mutumi a motar ya ba matar ruwa ta mika ma Khadijah, ta wanke bakinta da fuska sannan suka dawo cikin motar ana mata sannu, wata mata ta bada leda ta rike a hannu idan ta ji wani aman, har suka isa katsina kawu bai yi shiru ba, Khadijah tayi Amai yyi sau biyar, dunguri kam ta sha sa gun kawu duk da ba a kusa da shi take ba, bbu wanda yace masa ci kanka cikin passenger din motar, a dai dai ta ya samu da xai kai su har gidansa.. Karfe biyu da kusan rabi suka shigo gidan, bungalow ce mai kyau, wanda Abban Khadijah Alhaji Muhd ya mallaka ma yayan nasa a lkcn yana da rai, sai dai ba lallai wanda ke nan lkcn da aka ba Kawu gidan ya yarda Cewar gidan ne a ynxu ba, don yyi mugun tsufa ga dattin bala'i, kuma dudu gidan bai yi shekara shidda ba, Duk matan Alhajin guda biyu suka fito jin shigowar mai gidan nasu suna masa sannu da xuwa, kawu dake kokarin bude jakar kayan Khadijah bayan ya xauna parlor yace "Toh ga ta nan, gida kuma ni da Isiyaka mun rufe an sa a kasuwa, ga ta nan ban san gun warce xata xauna ba cikin ku" Matarsa ta fari Hajiya Salaha tace "Toh ni dai yara sun yi yawa a gu na, ban san dai ko Maimuna ba" warce ta kira da Maimuna tace "Ni kuma sai nace maki yaran basu min yawa ba koh?" Kawu yace "A'a bbu xancen tada jijiyoyin wuya taje dakin ki Maimuna kayanta kuma a kai dakin salaha, shkkn" daga haka ya dinga fiddo da tsadaddun kayan Khadijah, daga shi har matansa bbu mai cewa komai sai kallon ikon Allah suke, Kusan set takwas ya cire ya ajiye gefe yace "Wannan siyar da su xa ayi in sha Allah, domin kuwa baxata xo nan ta dinga saye sayen kaya ba kamar wata er gote ta janyo ayi tunanin shi gareni..." Takalman ma duk ya ware kusan biyar, golds dinta na dankunni da awarwaro kuwa dama suna aljihunsa, Khadijah dake ta tsaye jikin kujera tana waiga ko ina na parlorn da idonta tana neman remote ta kunna TV amma bata gani ba, ganin kawu xai xuba duk kayan da ya ware a wani jaka ta karaso da sauri tace "Kawu ina son wannan takalmin, da shi nake xuwa makaranta" Dungurinta yyi da karfi ya kunduma mata ashar, ta koma baya a tsorace yace "Ki shiga hankalinki da ni fa xan xane ki wllh" xata mike ya fixgota ya cire dankunnin kunnenta, Hajiya Maimuna tace "Toh idan ba fitsara ba ita har xata gaya maka abinda xaka yi" mikewa yyi ya dau jakar yace "Ku shiga da sauran, ni na tafi kasuwa kan yamma yyi" daga haka ya nufi kofa" bayan fitarsa Hajiya salaha ta sake fiddo kayayyakin ta dau kusan kala biyu da panties da kayan bacci, Hajiya Maimuna ma ta jawo jakar ta dau huluna da kaya kala daya da dogon rigar kanti da safunayen hannu da kafa, Hajiya salaha xata sake jawo jakar Hajiya Maimuna ta rike tace "Tsiyace jakar xa ki yi" Hajiya salaha ta jefa mata wani tace "Ke ai arxiki kike karama jakar, abu baxa ayi sa da hankali ba, ita sai ta sa uwar me?" Hajiya Maimuna ta rufe jakar ta tura tana kallon Khadijah dake ta tsaye tana kallonsu tace "Dauka ki kai dakin can dake kusa da wancan kofar, kin wani tsaya ma mutane kememe" Khadijah ta karaso da sauri ta dau jakar ta bi hanyar da Hajiya Maimuna ta nuna mata, kafin ta fito sun dau takalma kala daddaya ta dau jakar takalmin ma ta kai dakin. Uban wanke wanken dake tule gun pampon da aka tanadar don yin wanke wanken Hajiya salaha ta nuna mata taje tayi, a hankali Khadijah tace "Ina jin yinwa" Hajiya salaha tace "Can baki ci abinci bane kafin ki taho, ki je bakin pampon akwai tukunyar taliyar da ta rage ki ci sannan kiyi wanke wanken" Fita khadijah tayi xuwa gun pampon, ta yi kusan minti daya tana kallon taliyar da kudaje ke bi, ta turo baki ta rungume hannayenta, Dawowa parlon tayi kamar xata yi kuka tace "They are flies perching all over the food, ni baxan iya ci ba" sakin baki suka yi gaba daya suna kallonta, can suka kwashe da dariya Hajiya Maimuna tace "Toh baturiyaa jikar mongo park...." Hajiya salaha tace "Kin wuce kin ba mutane waje ko sai na mike.. Ina ruwan ki da k'uda idan ba rainin wayo ba, ki bar abincin kar ki ci, kuma maxa ki tafi ki wanke kwanukan yanxun nan" juyawa khadijah tayi ta bar wajen, Hajiya Maimuna tace "Idan ba ma tsoron Allah ba har Alhaji xai yarda ya rike er Muhammad, uwar me ya tsinana sa yana raye" Khadijah dake ta turo baki ta dau omon da ta gani da sosan wanke, tsaye tayi ta rasa ta inda xata fara wanke wanken, can dai ta dauko babban bahon da ta gani ta tari ruwa ya kusa cika sannan ta xaxxage d'an omon, muryar wata mata da shigowarta gidan kenan taji tana cewa "Ke ya haka, da uban ruwan nan xaki kada kumfa?" Khadijah ta kalleta kamar xata yi kuka tace "Toh ban sani ba" matar ta karaso baki sake, nan ta rage ruwan ta kara mata omon sannan tace "Haka ya isa" parlor matar ta shiga wajen su Hajiya tana cewa "Ku kuma ina kuka samo wancan Ajebon" Karfe kusan hudu da rabi Hajiya Salaha ta fito bayan tafiyar bakuwarta, sakin baki tayi tana kallon Khadijah dake durkushe bakin pampo har lkcn, kwanuka ta ko ina, duk ta hade gumi ta jike kayanta jagab, kai kana ganinta kasan bata taba ba ne, Hajiya ta kwalo ma kishiyarta kira ta fito da sauri, ita ma ta xaro ido tace "Me xan gani ni Maimuna, wanke wanken awa biyu?' Khadijah dake kallonsu kamar xata yi kuka tace " plates din sun bushe, ya ki ya fita" Hajiya Maimuna ta rike ha6a tace "Ehh lallai muna da aiki, yanxu tsalelliyar budurwa kamar ki baki iya wanke wanke ba shekara sha uku sa'ar Murjata" Hajiya Salaha da ita ma ta bude baki ta kalli kishiyarta tace "kina da aiki dai, don ba ni aka kawo ma ita ba, mutum yaji da nasa 'ya yan mana, shima Alhaji wllh, da ba sai ya bar ta gun kishiyar marigayiyar uwarta ba" Juyawa Hajiya Maimuna tayi tace "Toh Allah ya kyauta" daga haka ta shiga ciki, Hajiya salaha ta mata tsawa tace "Tashi mana kan kwanuka yar banxa kawai, ke ga yar masu kudi ko, to xa ki ci kwakwa a gidan nan don bbu shegen da xai dau iskancin ki, kawai kin bi kin ma mutane asarar omo, maxa kuma ki dau tsintsiya ki tattare gaba daya gidan nan idan shima kuma baki iya ba sai in ga" khadijah da ta bata fuska xata yi kuka ta karasa ta dau tsintsiyar da take nuna mata ta fara sharan, takaici ya rufe Hajiya ganin gwara ma ta shekara a tsugunne bakin pampon da wannan sharan da take na yan iska, juyawa tayi ta bar gun daga karshe tana cewa "Xaki san inda kika xo yarinya" da daddare Khadijah na rakube jikin kujera gaba daya hankalinta da soul dinta na kan kallon cartoon da kananun yaran kawu Jibril suka sa a TV, an kirata ya fi sau uku amma inaa, hauri Sajida er Kawu ta biyu ta kai mata tace "Yau naga mayyar kallo ana magana bata ma san ana yi ba" a firgice ta mike sai dai har lkcn idonta na kan TV, Hajiya Maimuna dake lekosu daga kitchen don ita ke kiran khadijar ta xo ta karbi abinci, ta karaso a fusace ta kai mata dundu, firgita ta juyo Hajiya Maimuna ta murda kunnenta tace "Gafara shegen kallon nan xai maki ne hala, ka ji min yar kaza kaza" sunkuyar da kai khadijah tayi kamar xata yi kuka, Hajiya Maimuna ta turata kitchen tace "Ga tuwon ki can a kitchen ki dauka, gayyar tsiya kawai" tafiya kitchen din tayi tana yi tana waiwayo TVn ta dauko tuwon a wata yar roba an ya6a masa miyar kuka koriya shar, sai kallon miyar take kamar idanuwanta xa su fito, ta dawo parlon ta xauna cikin yara dake cin abinci su ma ta ci gaba da kallonta Hajiya Salaha ta shigo parlon tace "Wato kinsan idan mutum ba ayi masa tarbiya ba sai na kallo, kinga saura kadan ta xubar da tuwon tana kallo" da sauri khadijah ta kalli tuwonta taga ba daidai ta ajiye sa ba, Hajiya salaha ta fixgota a fusace ta juyar da ita tana kallon kofar kitchen tace "Duk kika sake juyowa sai na kashe ki" Khadijah dai bata ce komai ba ta kai hannu a hankali cikin tuwon ta mintsili kadan ta kai baki, yamutsa fuska tayi tana hadiyewa da kyar sai kuma ta kalli Er Kawu ta uku mai suna Rabi tace "Anty akwai indomie?" Yarinyar ta fashe da dariya sannan ta gaya ma Uwarta Hajiya Salaha, Hajiyar tace "Ehh akwai wanda ubanta ya kawo mana daga kabari" Khadijah dai bata ce komai ba, haka tayi ta kallon tuwon ta kasa ci, daga karshe haka ta mike ta kai kitchen ganin kowa na kai kwanonsa can, Hajiya Maimuna ta kwalo ma kishiyarta kira ta nuna mata tuwon da ta bari tace "kin dai ga koh? To wllh har in fita girki sai dai yunwa ya kashe yarinyar nan" *Haske Writers Association*???? 07087865788 Contact me here. ✨ *Noor-Al-hayat*✨ _By Khaleesat Haiydar_ (adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); _Littafin Noor-Alhayat na siyarwa ne, kindly patronize ur writer and read happily, duk wanda bai ji dadi ba hakan, yyi hakuri plss_ Washegari talata Khadijah na ta share tsakar gidan da aka sa ta tayi tun asuba har lkcn bata gama ba Kawu ya fito cikin shiga ta alfarma da daya daga kayan mahaifin Khadijah, matansa sun rakosa xuwa balcony ana yi masa Allah ya tsare hanya, ganin Khadijah da yayi ya juya yana kallon matan nasa yace "Gobe er can ta shirya da safe xa a kai ta makarantar boko" Hajiya Maimuna tace "Wanda su Sumayya ke xuwa?" Wani kallo yyi mata yace "Ke xa ki biya, ko ina naga kudin biyan wannan makarantar, makarantar da yaran Bala ke xuwa xa a kai ta, ina jin ko a Jss2 aka ce take ko one" Khadijah ta mike tace "Aa jss2 nake Abba" Wani shegen kallo yyi mata yace "Kun ga irin rashin tarbiyar ko, kun gani ko, to yanxu wa ya sako bakinta, dama na samu labarin an baki tuwo ki ci jiya da daddare kin ki ci tunda kin taho da abinci daga gidan marigayi Muhd, to wllh xa ku yi aiki hand in hand da yunwa in har baxa ki ci abinda ya sauwwaka ba, baxa ki taho gidana kina min sangarta ba" daga haka ya nufi daya daga motocin dake tsakar gidan, Khadijah ta ci gaba da sharanta na yan koyo da take yi. Throughout haka ta dinga aikin da ba ta iya ba bata taba yi ba a gidan, duk ta gaji amma ko kadan bata ce haka ba sai turo baki da take ta yi, Hajiya Salaha ta kai mata dundu yyi sau biyar daga karshe ta gaji da bin ta tana mata dundun ta kyaleta, Hajiya Maimuna kuwa ta surfa mata xagi ya fi a kirga, duk wnn abun sai dai ta turo baki ko ta bata fuska daga nan kuma shkkn, kunu da kosai a gantale aka bata a cup, ita ma ta ci a gantale ta bar masu abinsu don ba saba ci tayi ba, sai da suka yi baccin rana sannan ta samu tayi sallahn zuhr ta lallaba ta kunna TV ta rage volume ta xauna tana kallo happily, dauke wutan da aka yasa ta turo baki, a hankali ta kwanta nan kasan parlon nan da nan kuma bacci ya dauketa don tun tashin asuba. Ko abincin rana ba a bata ba wai sai yaran gidan sun dawo, basa kuma dawowa sai karfe biyar, suna dawowa kuwa da yamma aka xuba ma kowa shinkafa da wake da mai da yaji da Hajiya Maimuna ta girka, Hajiya Salaha ta sa Sumayya ta xuba ma Khadijah don ita Hajiya Maimuna rantsuwa tayi baxata bata ba, khadijah ta tsura ma shinkafa da waken ido da aka barbada ma yaji, a hankali ta kai hannu ta dinga tsince waken tana ajiyewa a kasa gefenta, Hajiya Maimuna dake ta kallonta ta mike ta karbe kwanon abincin ta kai kitchen ta rufe, abincin da ba ta ci ba kenan har aka yi magrib sannan isha, tana ganin aka ba kowa shinkafa da miyar da Hajiya maimunar tayi amma ban da ita, bayan ta idar da sllh ta samu Sajida dake waya ta duka gefenta a hankali tace "Anty ni ba a ban shinkafar ba" ta mata wani kallo tace "Toh ni na dafa ki samu su Hajiya mana" mikewa tayi ta wuce dakin Hajiya salaha, ta samesu xaune da yaranta ana assignment, kallonta tayi tace "Lafiya??" ta girgixa kai tace "Ni ba a bani abincin ba ina jin yunwa" tsawa tayi mata tace "Fita ki ban waje, ba dai shayi da soyayyen kwai kike jira ba yunwa xai kashe ki gidan nan" a hankali Khadijah ta juya ta fita, ta tafi gun kwanciyarta ta rakube hade da rufe ido tana tuno Ummarta. Washegari kamar jiya da asuba aka tasheta, har gari ya waye tana shara, sai da duk yaran suka wuce makaranta sannan Hajiya maimuna tace idan ta ga dama ta wuce tayi wanka ta shirya, tsaye khadijah tayi a bathroom dake tsakankanin dakunan su Hajiya, soson wankan ta da Abbanta ya siyo mata daga Kasar waje ya xama na kowa da kowa hadda sabulunta mai tsada, ta turo baki ta dau sabulun kadai ta yi wanka da shi ta fito cike da kyankyanin bayin, tun da ta fito parlor Hajiya Salaha ke kallon kayan jikinta, khadijah ta durkusa gefenta a hankali tace "Na gama" tabe baki Hajiya salaha tayi ta nuna mata cup din kunu tace "Gashi can ki dauka, kosan ya kare" Khadijah ta leka cup din da sauri a xaton ta shayi ne, a hankali ta mike ganin ba shi bane ta isa gun cup din kunun ta dauka, Hajiya salaha tace "Ko yau ma baxa ki sha ba" bata ce komai ba ta dinga shan kunun da yyi mata tsami a baki tana d'an yamutsa fuska, sai hararanta Hajiya salaha take tana kwafa, daga karshe kadan ta sha ta ajiye ta mike tace "Na koshi" duk da uban yunwan da take ji cikinta na kugi, Hajiya Salaha tace "Toh ki hutar da kanki tafi ki juye a flask ki hada duk kwanukan ki wanke, kuma ki min irin na ranan in fasa maki jiki da wayar wuta" ita dai khadijah bata ce komai ba ta mike taje yin yanda tace nata. Wani almajirin Kawu ne ya taho kai ta makarantar, shegen nisa ce da makarantar kuma almajirin me suna musa yace da kafa xata dinga xuwa kullum don haka gwara ta dinga kallon hanyar da kyau, tunda suka shiga makarantar Khadijah ke kalle kallen ko ina, don ita dai bai yi mata kama da schl ba, gashi ko plaster ba ayi ba, yaran ma basu da yawa, Musa ya shiga gun wani wanda da alama shugaban wajen ne, ita tana tsaye waje, tana jin mutumin na ce ma musa ai lesson ne wa yaran da basa gane karatu, kuma na shekara daya ne kafin yaro ya shiga boko, musa ya tambayesa nawa ne yace dubu uku da dari biyar, nan take musa ya basa kudin, ita kuma aka kira wata daliba ta kai ta ajin karshe musa ya wuce, su kusan goma ne a ajin, ita dai tunda ta shiga ajin take kallon malamin dake ta koya sentence making, "The boy was tall..." Shine abinda malamin ke ta nanatawa yaran na fadi su ma, khadijah dake ta kallon sa tace "Excuse me, but you said present tense sir?" Malamin yace "Yes" tagumi tayi tace "Sorry but that's past tense class master" kallon board din yyi da sauri sannan ya kalleta, bai kulata ba ya ci gaba, nan ma kuma sai da ta sake masa gyara, hade rai yyi yana kallonta, can ya basu classwork ya koma ya xauna, sai bayan kusan minti sha biyar ya karba sannan ya fara koyar da Multiplication a board, sai da ya gama tas, sannan ta kai masa gyaransa a littafi tana nuna masa, fita malamin yyi xuwa gun shugabansu, ba a dau lkci ba ya kirata, tana tsaye yace "Ke tunda baki da kunya kar ki sake xuwa makarantar nan daga yau, tunda kin iya abinda ake koyarwa ki xauna a gidan ku ko kuma a kai ki school ga kudin ku" karba tayi tace "Ohk, in tafi yanxu" yace "Tafi" juyawa tayi ta fice daga uncomplete building din, gano gida bai mata wahala ba saboda sharpness dinta, su Hajiya salaha dake xaune parlor suna hira suka saki baki suka ce me kika dawo yi, tace "Ba abinda suka iya fa a wajen, they are just teaching rubbish, ni bana son wajen school nake so, am in jss2" Hajiya maimuna tace "Shine kika dawo" gyada mata kai tayi ta mika mata kudin hannunta, ta tafi jikin kujera ta rakube ta xauna, duk suka bi ta da kallo baki sake. Yunwa sosai take ji amma bata ce komai ba, Kawu ne ya fito a shirye xae fita wajen karfe goma da rabi, ganinta yace "Wannan yarinyar musa bai kai ta makarantar bane" Hajiya salaha tace "Uhn gata nan ya kai ta ta dawo wai bbu abinda suka iya kilan mai tsada take so" ya juya da sauri yana kallonta yace "Me ya dawo da ke?" Tace "Abba they are teaching rubbish there, kuma ina ta correcting dinsa, ban san whether he reported me bane, sai aka kira ni wai in tafi kar in sake dawowa, har da kudin ma an bani na dawo da shi" Kawu ya gyara tsayuwa yana gyada kai yace "Ohhhw haka aka yi kenan, toh kin ma kanki, Alhmdllh Muhd baxae gan ni da ko wani laifi ba don na kai ki makarantar kika gudo, don haka sai kiyi ta xama gidan" daga haka yyi ficewarsa, ita dai bata ce komai ba, Hajiya Maimuna tace "Wato ke isassa kin raina makarantar shine kika je kina ma malaman fitsara ko, uban wa ke da kudin asaran da xai kai ki irin makarantar da ubanki ya sa ki tun farko?" Khadijah dai sai kallonta take, Hajiya Salaha tace "Ni da nace xan fara awaran siyarwa xan dauko mai aiki wllh da Alhaji xai yarda da sai ta dinga kai min can bakin kasuwa, kinga ai ba talla bane wnn, xama waje daya xata yi" Hajiya Maimuna tace "Ae ko da xai yarda nima sai in hada mata da Omon siyarwa na" Hajiya salaha tace "Toh bari ya dawo dai mu ji" suka gama dai hirarsu duk suka shiga dakunansu domin kwanciya suka bar ta ita kadai a parlorn ga yunwa dake dawainiya da ita, da rana yau kam taliya da wake suka girka, gashi ita bata cin wake tun tana karama, Hajiya salaha ta dan yarfa mata a kwano ta bata, kamar xata yi kuka tace "Ni ban iya cin wake ba" Hajiya salaha tayi er dariya ta mayar da abincinta cikin tukunya ta fito kitchen din, sai a sannan khadijah ta fara hawaye don tunda take bata taba jin yunwa irin wannan ba, ita shinkafa da miya take so, tsakar gida ta tafi ta xauna tana share idonta, har wani rawa jikinta yake don yunwa, tashi tayi ta fice gidan gaba daya, ta shiga gidan dake kusa da na kawunta, gidan shigen na kawunta ne, taga wani yaro xaune tsakar gida yana cin tuwo da koren miya, fita tayi da sauri har tana tuntube, gidan dake kusa da wannan ta tura ta ji a kulle, haka na kusa da shi ma, a gida na hudu ta tsaya tana kallon babban gidan don ya fi duk gidan anguwar, tura gate din tayi taji a bude ta shiga tana kallon mai gadin ta gaishesa yace "Wa kike nema?" Ta nuna masa cikin gidan sannan tayi wucewarta, har ta isa balcony kallon karen dake cikin cage a gidan take, ta murda kofa a hankali ta shiga parlorn, tsaye tayi bakin kofar ganin wani matashi da baxai wuce shekara ashirin da shidda ba yana xaune parlorn da plate din abinci a hannunsa idonsa a kan tv, yana kallonta da dan mamaki yace "Wa kike nema" ta kalli abincin hannunsa kamar xata yi kuka a hankali tace "Nobody, I am just hungry" ya buda ido kamar ya ji mugun abu, a hankali tace "Please" ajiye plate din hannunsa yyi yace "Take" ta karaso ciki da sauri ta xauna kan kafarta tana kallon shinkafa da miyar da naman kaza sai coslow dake gefe murya can kasa tace "Thank you" daukan spoon din tayi ta kai abincin baki ta fara ci, ya kafeta da ido irin kallon mamaki, muryar wata dattijuwa taji tace "Who's this?" Ya juya ya kalleta kafin yace komai Khadijah tace "Good afternoon ma.. I am khadijah" matar ta kasa cewa komai, ta kalli yaronta dake xaune kamar yanda shi ma yake kallonta, Khadijah ta dau kazar abincin tana ci tana kallon matar. *Haske writers association*???? ✨ *Noor-Al-Hayat*✨ _By Khaleesat Haiydar_????✍???? _Littafin Noor-Alhayat na siyarwa ne, kindly patronize ur writer and read happily, duk wanda bai ji dadi ba hakan, yyi hakuri plss_ Karasowa parlorn dattijuwar matar tayi har lkcn tana kallon khadijah tace "Where are you coming from?" Khadijah ta dago a hankali tace "Just 3 houses away...." Matar tace "Gidansu Hajiya Salaha kenan?" Khadijah ta gyada kai, matar tayi shiru tana kallonta, can tace "An aiko ki ne?" Ta girgixa kai tace "A'a kawai abinci nake son ci" kallon d'an ta da ke xaune matar tayi, khadijah ta ci gaba da cin abincin gabanta, shi dai bai ce komai ya mike xai bar parlorn, mahaifiyar sa ta bi sa da ido tace "Kaje to Sadiya ta xuba maka wani abincin koh" ya juyo yace "Noo dama it's not as if ina jin yunwa mum, anjima xan ci" daga haka ya wuce ciki, matar ta dinga kallon khadijah dake cin abincin sanyi sanyi, can ita ma ta juya ta bar parlorn, jawo remote khadijah tayi ta kunna TV ta gyara xama tana facing tvn, tana cin abincin amma gaba daya ta ba tv attention dinta, bayan kusan minti talatin taji ance "Wai ke baxa ki gida bane? Ba kin gama cin abincin ba" Ta juyo da sauri ta kallesa sai kuma ta marairaice tace "Plss ina son in gama kallon nan" sakin baki yyi yana kallonta ga plate din abincin ta gama, bai dai ce komai ba ya fita rike da makullin mota, ba a dau lkci da fitarsa ba sai ga yan mata uku sun shigo gidan sanye da kayan islamiyya, tun da suka shigo suke kallonta ita kam ko sanin sun shigo bata yi ba, Muryar matar daxu taji a parlorn tace "Ke baxa a nemeki gida ba" khadijah ta dago da sauri, sai kuma ta bata fuska tace "Anty bana son xuwa gidan" Matar ta buda ido tace "Baki son xuwa kuma?" Shiru ta d'an yi kafin tace "First... They are so dirty and unkept, and I don't like their dishes.... I don't just like the house" matar dake kallonta da mamaki tace "Toh ba gidan ku bane" khadijah ta girgixa kai a hankali tace "Noo uncle dina ne ya kawo ni" matar tace "Maza tashi ki tafi kar ayi ta nemanki kin ji" kallon agogo tayi taga karfe shiddah ta ce "plsss ma... am I always welcome here?" Matar ta d'an yi murmushi tace "Sure" khadijah ta kwashe plate da cups da ta ci abinci tace "Where can I find d kitchen" nuna mata matar tayi ta kai ta fito sannan ta dau ruwan goron da d'an ta ya ajiye tace "In tafi da shi?" Matar ta gyada mata kai, murmushi tayi ta risina tace "Thanks ma" daga haka ta nufi kofar fita matar ta bi ta da ido, tana fita gidan gaba daya ta hango mutane tsaye bakin gate din gidan kawunta, tafiyar minti kusan shidda tayi ta isa gidan, tsaye ta tadda su Hajiya Salaha da yaransu gaba daya ga makota ana ta surutu, Sajida ce ta fara ganinta tace "Lahhh mama kun ganta" sai aka juyo gaba daya ana kallonta, Hajiya Salaha ta isa inda take da sauri ta fixgota tace "Daga ina kike?" Khadijah dake bin kowa da kallo tace "Just few houses away....." Bata rufe baki ba Hajiya Salaha ta sauke mata mari, wani ihu ta fasa tana rike da fuskarta tana jin duniyar na juya mata, tunda take ba a taba kai hannu jikinta ba bare fuskarta sai ranan, iyaka a sa ta tayi kneel down ta daga hannu, har tsadadden bokon da take xuwa a kano ma ba a duka, Hajiya Salaha na huci ta shiga kunduma mata xagi tana cewa "Allah ya isa yawon da kika sa muka dinga yi muna nemanki kamar gantalallu, sai Allah ya saka mana... Kuma bari Alhaji ya dawo wllh xaman ki ya kare gidan nan ya je can ya kai ki gun talakawan dangin uwar ki..." Kuka kawai khadijah take tana rike da fuskarta, hakuri mutanen wajen suka dinga ba Hajiya Salaha suna cewa ai yarinya ce, Hajiya maimuna da ganin Khadijah ya sa ta shiga parlor ta fito da wayar wuta ta nufo ta, wata mata ce tayi saurin janyeta tace "A'a don Allah ki bari Maman Hafsa, ayi mata hakuri" wata mata ma ta rike wayar tana ba Hajiya Maimuna hakuri, Hajiya Salaha tace "Ku bar ta ta ci mata mutunci crook ce wannan yarinyar da ku ke gani haka, wa yasan gidan uban da taje" Matar da ta ja Khadijah ta duka dai dai fuskarta tana kallonta tace "Ina kika je ake ta neman ki yan mata" Khadijah na shessheka tace "I was hungry and I had to....." Kasa ci gaba tayi ta rushe da kuka, Matar ta d'an kwalalo ido tace "Tohhh bata jin Hausa ne?" Hajiya Maimuna tace "Iskancin fa?? Tsabar shakiyanci ne da iyayi da kinibibi ita er mai kudi, toh wai ma ina mai kudin yake yau? Ku ce min yana kabari, toh idan ma xata sauke kai ta yi rayuwa yanda ko wani talaka ke yi ya rage nata, uwar me suka tsinana ma mutane banda tsoron Allah har Alhaji xai daukota ya ajiyeta a gidansa, wai I am hungry... To kafafuwar uwarki xan dafa maki in baki banda abinda aka girka kika ki ci" Hajiya Salaha tace "Ae komai ya xo karshe, ya dawo yasan yanda xai yi da ita, wnn 'ya sai ta kashe aure, taje can inda xa a dinga dafa mata indomie da kwai a bata shayi mai kauri da custard ta sha, mu ba rainon tea da bread muka ma yaranmu ba" daga haka tayi shigewarta ciki, Matar dake rike da Khadijah tace "Ke me yasa kika fita baki sanar masu ba? Komai aka baki kuma bata sai ki ci ba khadijah" Khadijah ta kasa cewa komai sai kuka take, jin kiraye kirayen magrib duk aka fara watsewa ana ma su Hajiya Allah ya kyauta, wasu kuma na tausayin khadijah domin kuwa suna ganin iyayenta basu mata adalchi ba in har abinda su Hajiya ke fada gaskiya ne a kanta, ba a san yanda rayuwa xata kaya ba don haka iyaye ya kamata su dinga koya ma 'ya yansu both the right and left side of life, yau idan an ci na masu kudi gobe a ci na talaka bawan Allah, wannan xai sa yaro yyi adapting a duk situation da xai tsinci kansa. Khadijah ce kadai tsaye tsakar gidan duk sun shige ciki da yaransu, ta share idonta a hankali ta bude kofa xata shiga, a tsawace Hajiya Salaha tace "Ki shigo ki mana me? Maxa koma sai Alhaji ya dawo gidan nan, maxa fita kar in sumar dake annamimiya kawai" juyawa tayi da sauri ta bar wajen bayan ta rufe masu kofa ta nemi wani waje ta xauna ta daura kanta bisa kneels dinta, har aka kira Isha tana wajen ga sauro sai cixonta suke, Kawunta bai dawo gida ba sai wajen karfe goma, bayan ya gama parking xai shigo ciki ya ga kamar mutum a wajen ya haske waya, tana nan yanda take bacci ya dauketa a hakan, da mamaki yace "Ke!!" Firgit ta farka ta mike tsaye da sauri, yace "Me kike a nan" tana kallonsa da idonta da yyi bulu bulu yyi jajir, shatin hannun Hajiya Salaha a gefen fuskarta hankali tace "Aka ce in tsaya a waje" yace "Saboda me?" Tayi shiru bata ce komai ba, shiga gidan yyi ya tarar da su gaba daya da yaransu ana xaune parlor ana kallo ana shewa, duk suka fara cewa "Abba sannu da xuwa..." Bai bi ta kansu ba yace "Me wancan yarinyar take yi a waje?" Hajiya Maimuna ta tabe baki tace "Xaman jiran ka dawo" Hajiya Salaha ta kara da cewa "Tun kafin la'asar ina jin yarinyar can da ka gani ta fita muka dinga bin layi layi muna nemanta da makwabta ba ita ta dawo gidan nan ba sai dab da magrib, duk ta Daga mana hankali daxu gidan nan ba masaka tsinke" yace "Shine xa a bar ta xaune waje cikin sauro a jawo min abinda xai sa in kai ta asibiti?" Hajiya Salaha tace "Toh xan iya mata abinda raina ke raya min Alhaji shi yasa nace tayi ta xama a waje" yace "Toh kada warce ta sake turata waje war haka ko uban me tayi... Na gaya maku" juyawa yyi ya kalli Khadijah dake tsaye ta rakube a fusace yace "Xo nan" karasowa tayi da sauri ya wani hade rai yace "Ina kika je?" Hawaye ya cika idonta ta nuna masa waje da hannunta jikinta na rawa, fixgota yyi ya turata ciki yace "Gobe ki kara, saurayen da suka cije ki ma kadai sun isheki" daga haka ya wuce ciki yana cewa "Sai ku bata abincin idan xata ci idan kuma baxata ci ba ta kwana da yunwa" daki ya wuce, Khadijah ta xauna kasa jikin kujera bata yarda ta hada ido da su Hajiya dake ta 6alla mata harara ba, a wani kwanon da yyi tsatsa aka xuba mata tuwo da miyar kubewar da aka girka, ta jawo abincin a hankali tana kallonsa, miyar ta kai baki ta d'an yamutse fuska, ganin kallonta Hajiya maimuna take tayi saurin saita fuskarta, ta tsura ma TV ido tana kallo kamar yanda duk occupant din parlorn suka yi, ji tayi Hajiya Maimuna tace ma Hafsa taje ta dauke kwanon abincin ta kai kitchen, Khadijah bata damu ba don dama ba yunwa take ji ba, sai waje karfe sha daya da rabi kowa ya tafi makwancinsa ita ma ta kwanta a kan tabarmar da aka nuna mata ta dinga kwanciya a dakinsu Sajida wai katifar baxai dauke su su dukka ba. Bayan kwana biya Khadijah na xaune tsakar gida da yamma tana uban wanke wanken da su Hajiya suka tula mata, su kuma suna ciki da yaransu kasancewar ranar Friday ce bbu islamiyya, yi take kamar baxata yi ba tana turo baki an hanata kallo, wanda a kansa kusan kullum sai ta sha mazga amma ta ki hakura, ita dai tayi kallo, duk ta rame ta kanjale, kana ganinta kasan akwai yunwa sosai da wahala tare da ita, ga rashin sabon aiki, ba laifi yanxu tana d'an wanke plates din su fita sai dai ta kan fi awa biyu kan kwanukan wanke wanken, kayan jikinta kuwa yanda aka san ta shiga rafi tsabar jikewar da yake idan tana wanke wanken, yanxu an ma daina sa ta sharan gaba daya tsabar kawai bata iya ba sai dai wanke wanke da jan ruwa wani lkcn a waje idan bbu wuta, tun ranan da ta fita har yau bata sake fita ba sai dai idan an aiketa gun mai kanti ko kuma xata debi ruwa a er karamar bucket da take dauka, har yau bata sake cin abinci mai dadin gidan da taje ba, abincin gidan kawu daga taliya sai tuwo da shinkafa da wake da mai da yaji, gashi duk bata son su hakan yasa take tare da yunwa sosai, Hafsa ta fito ta jefa mata kudi tace "Khadijah wai Mama tace ki je gun mai kanti ki siyo sabulun wanki da Hypo leda biyu, sai ki siyo maggi mai tauraro na hamsin" Khadijah ta turo baki bata ce komai ba, tashi tayi bayan Hafsah ta wuce sanin Hajiya na iya lekowa taga ko ta wuce, ta shiga parlor Hajiya Salaha tace "Aiken fa" ta kalli kayan jikinta tace "Mama xan canxa kaya" dakuwa tayi mata tace fita Ki ban guri, shashasha sshe da gangan kike jike kayan wajen wanke wanke kenan kin san abinda ya kamata" juyawa tayi ta fita, ta sake kallon kayan dake a jike tun daga saman gwiwanta har kasa, gate ta nufa kanta sanye da hula don gaba daya Hijabs dinta yaran gidan sun gaje, tafiya ce me nisa xuwa gun mai kanti, tana tafe tana wasa da d'an karamin iccen hannunta, har ta wuce gidan da taje ta ci abinci idonta na kan gate din gidan amma ba daman shiga, tana isa gun mai kanti cikin aiken da aka mata maggi kawai ta tuna, gida ta koma da sauri ta shiga parlor tana kallon Hafsa kamr xata yi kuka tace "Me da me kika ce ma" Hajiya Salaha tayi wani murmushi ta na kallon kishiyarta tace "Me na fada maki" Hajiya Maimuna tace "Kin ji na maki musu? Ko an taba aikenta bata dawo tambayar me aka aiketa ba dama" Hajiya Salaha ta ce "Wllh Ubanki ya cuce rayuwar ki, kishiyar uwarki kuma kiri kiri ta nuna bata son ki tunda har ta sangarta ki haka ta lalata ki saboda ba ita ta haife ki ba, banda haka wannan xabgegiyar budurwa godai godai kullum aka aike ki sai kin dawo wai kin mance, sai shegen turancin iyayi.... ni dai wllh tunda yarinyar nan ta xo gidan nan nake fama da surutu abinda yaran da na haifa ma basu sa ni ba, Allah dai ya isa wllh" Hajiya maimuna ta tabe baki tace "Ke kika ga xa ki iya, ni kinga ina yi? Ai sai dai duka" Kabir ne ya sake nanata ma khadijah Aiken da aka mata ta fita da sauri tana maimaita abinda yace a ranta har ta isa gun mai kantin sannan ta fada masa, yana dariya yace "Ke yar fari ce ko?" Ta wara ido tace "I don't understand" dariya yyi yace "Aa ni ba bature bane, don nema maki saukin kai wa da dawowa idan an aikeki kawai kice a dinga rubuta maki sakon a gida kinji" tace "Ohk then" muryar da taji yana cewa a bashi kati ya sa ta juyawa da sauri, suka hada ido ta washe fararen hakoranta tace "Good evening" daga sama har kasa ya kalleta yace "How you?" Ta langwabar da kai tace "I shud say fine" yana gyada kai yace "Good" karban card din da mai kantin ke mika masa yyi yace "Doguwa dake baki sa Hijab idan xa ki fito" a hankali tace "Bani da Hijab yanxu" bai ce komai ba yana loda card din kafin yace "Toh me yasa kika jika kayan ki" tace "Wanke wanke nake yi tun da rana" yace "Ina ne gidan ku?" Tace "Our home is 3 house's away from u people's" ya kalleta yace "Gidan Alhaji Jibril?" Ta gyada masa kai, yace "Ke yarinyarsa ce" ta girgixa kai a hankali, yace "Yaushe kika xo gidan!" Ta kalli sama kamar me naxari sannan tace "10 days ago" ya gyada kai bai ce komai ba, ta amshi ledan sakonta da canji tana kallonsa kafin tace komai yace "Ya sunanki?" Tace "Khadijah" yace "Good" a hankali tace "Ina son in xo in ci abinci gidan ku amma an hanani, kuma I can't eat the food they are cooking, it's just concoction" a hankali ta karashe maganar, yace "Me yasa aka hana ki?" Tace "Su mama sun ce xa su kashe ni idan na sake xuwa ko ina kuma ina jin tsoro" ya kalleta bai dai ce komai ba, ta matso kusa da shi a hankali tace "Ko xaka dinga kawo min abincin gidan ku da kanka?" Ya buda ido yace "Ina?" Tace "Gidanmu mana, sai in dinga boyewa a backyard ina ci" tana magana ne hawaye cike fararen idonta, jin yyi shiru ta ci gaba tace "I am always hungry...." Ya sauke idonsa daga kanta bai dai ce komai ba. *Haske writers association*???? A hankali khadijah dake kallonsa tace "please" ya dago ya kalleta kafin yace "Sai in gan ki a ina in baki abincin?" Shiru ta yi kamar me naxari, can tace "Ohk, ae akwai flowers a kusa da gate din, to ka dinga ajiye min a wajen idan na fito sai in dauka" murmushi yyi yace "Koh?" Ta gyada masa kai, yace "Ohk" ta kara matsowa gaban sa tace "Promise u will do that plss" yace "I will" ta wara idonta ta hade hannayenta tace "Thank you very much, may Allah reward you, byeee" daga haka ta juya da sauri ta bar wajen ta nufi gida ya bi ta da ido, bbu wanda ya bi ta kanta ta ajiye sakon a kan kujera ta fito ta ci gaba da wanke wankenta Happily, sai kusan karfe biyar ta gama ta shigo ciki, Hajiya Maimuna ta hada ta da uban kayan yaranta ta linke su ta xuba a cupboard, sai kusan magrib ta fito ganin kowa na alwala ita ma taje bakin tap tayi alwala ta dawo tayi sllh, tana rakube jikin kujera aka fara kiran kowa ya je kitchen ya karba abinci, ita ma ta tashi sanin Hajiya Maimuna na iya kunduma mata xagi idan taga bata shigo ba, tuwo ne da miyar karkashi aka yi ranan, ta fito bayan an dungura mata nata tana kallon cikin tuwon, xaunawa tayi ta kai hannu cikin miyar dake turiri ta dangwala ta kai baki, ta kasa hadiyewa ta shiga satan kallon mutanen parlorn trying very hard to keep her face normal, kowa hankalinsa na gun kallon Hausa film da ake yi a TV, ita da yake can gida basa kallon Hausa film ko bin ta kan kallon bata yi ba, sulalewa tayi ta fita waje rike da kwanon tuwon ta ajiye nan verenda ta nufi gate da sauri, a hankali ta durkusa gun flowers din bakin gate tana addu'ar Allah yasa ya ajiye mata abincin, ta bude flower din a hankali tana dubawa ai kuwa ta ga leda fari, ta dauka da sauri ta bude taga takeaway ne da goran five alive, ajiye ledan tayi ta doka uban tsallen murna sannan ta dau ledan har tana tuntube ta shiga cikin gida, backyard ta nufa da sauri ta nemi wani lungu ta xauna ta bude abincin taga jollof rice ne da naman kaza da plantains sai sauce a gefe, Cike da murna ta fara cin abincin tana ci tana gyada kai har da lumshe ido, sauri sauri ta cinye abincin ta bude drink din ta sha kusan rabi sauran ta kasa shanyewa, ta mike ta boye goran drink din sannan ta dau takeaway din ta fita gate ta jefar cikin katon abinda ake xuba shara ta dawo ciki tana goge bakinta, sai da ta tsorata ganin tuwon da ta ajiye ta kauda kai da sauri kamar ta ga mugun abu ta daukesa kamar wani shara tana yamutse fuska ta fita waje, almajiri ta samu ta juye ma sannan ta dawo gidan ta tafi gun tap tana wanke kwanon sajidah ta leko da alamar sai lkcn aka lura bata parlorn, yarinyar ta juya ta koma Khadijah ta bi bayan ta da sauri rike da kwanon da ta wanke, Hajiya salaha tace "Daga ina kike?" Ta nuna mata kwanon tace "Naje wanke wa ne" salati ta saki tana tafe hannu tace "Yanxu abincin kika je kika xubar khadijah?" A tsorace tace "Wllh mama ban xubar ba" Hajiya Maimuna tace "Karya kike, kece xa ki ci tuwon nan har ki cinye?" Ta marairaice tace "Amma ban xubar ba wllh" Hajiya salaha tace "Toh ya kika yi da shi?" A hankali tace "Na ba almajiri" cup Hajiya Maimuna ta dauka ta jefeta da shi tace "Allah ya isa" Khadijah tayi kofa da gudu ta fita ganin Hajiya salaha ta mike, can bakin gate ta tafi ta tsaya a tsorace, yau ma dai kamar jiya kawu ne ya shiga da ita parlor, bayan ya duddungureta yyi gorin iya son ransa sannan ya juya kan iyalansa cike da fada yana nanata masu indai suka janyo ma khadijah malaria sisin sa baxai yi ciwon kai ba sai in su xa su kai ta asibiiti, bbu warce ta tanka sa cikinsu, ya gama bambamin sa ya shiga ciki. Washegari sai da kowa ya tafi makaranta khadijah ta fara wanke wanken kwanukan jiya, kamar xata yi kuka take yi don duk sun bubbushe, tayi kusan awa daya bakin tap din ta bar sauran kwanukan ta shiga ciki, Hajiya tace "Kin gama ne munafuka" ta girgixa kai tace "Na kai halve" koranta tayi taje maxa ta gama, khadijah ta fito tana kallon agogo ta ga karfe tara ya wuce har da rabi, cikin sanda ta nufi gate ta bi anguwar da kallo ta ga ba kowa da yake silent anguwa ce, bude flower tayi dai dai wajen jiya taga farin Leda, ta washe hakora ta dauka da sauri ta shiga ciki, backyard ta nufa tana waige waige kamar munafuka, ta samu inda ta xauna jiya ta xauna ta bude ledan ta fiddo takeaway din, fried potato ne na turawa da uban kwai a ciki, ta lumshe ido tana murmushi, ta fito da wani water bottle karami da ke ledan ta bude tana kallon ciki taga shayi ne yaji madara da Milo, ta wara ido tace "Wowwww" har wani rawa hannunta yake ta kai bakinta tana yi a hankali kar ya konata taji bbu xafi sosai, tun da ta kafa baki bata ajiye ba sai da ta ga bayan shayin, ta ajiye bottle din ta rufe tana lullumshe ido ta dau fork din cikin ledan ta soma cin dankali da kwan, da kyar ta gama cinyewa don ta koshi kuma bata son xubar da abincin, ta tashi a hankali tana leke leke ta fita da gudu ta jefar da takeaway din a bola, ta dawo bakin tap ta wanke bottle din ta sa a Leda ta koma jikin flower ta bude ta ajiye sannan ta shigo ciki ta ci gaba da wanke wanken, bayan ta gama ta shiga ciki Hajiya Maimuna ta nuna mata kunu a cup da aka rufe a walakanci da wani bushashen bread a leda tace "Idan kin ga dama gasu can, don bawa baxae biye ta halin ki ba tunda yana da baya" Khadijah ta girgixa kai ba tare da ta sake kallon direction din kunun ba tace "Ni na koshi mama" sakin baki Hajiya Maimuna tayi can tayi murmushin mugunta tana gyada kai tace "Toh maa sha Allah" xaunawa khadijah tayi a favourite position dinta, daga karshe Hajiya Maimuna ta mike ta wuce ciki, kwanciya khadijah tayi don ji tayi cikinta ya mata nauyi nan da nan kuwa bacci ya dauketa. Yau ma dai da rana shinkafa da mai da yaji aka girka, tana gani suka xubo ma baki da suka yi ita ko oho sai ma wankin socks da panties din yara da aka tula mata bakin tap abinda bata taba ba, sai shafa socks din take tana turo baki gashi ta fara jin yunwa da wajajen karfe uku ne, kalle kalle ta fara yi kafin ta mike kamar mara gaskiya ta fita wajen gate, bude gun flower tayi a hankali taga farin leda sabo, ta wara ido ta dauke ledan taga bbu na bottle din da tasha daxu, ta shiga ciki da sauri ta wuce backyard, snack ne a ledan da roban five alive. Nan da nan ta ci da sauri ta sha drink din sannan ta fita ta xubar da ledan a shara taje ta ci gaba da wankin ta. Sai kusan la'asar bakin suka tafi, Hajiya salaha ta fito ganin wankin da Khadijah tayi, kuka ne kawai bata yi ba, amma har kumfa bakinta yake don fada da xage xage ita dai Khadijah na tsaye jikin bango tana kallonta tana wasa da flower din gown din jikinta, sai da Hajiya salaha ta mayar da gaba daya kayan cikin bucket ta xuba omo xata sake wankewa, Allah ya isa kam Khadijah ta sha sa na barnar omon da tayi mata, daga karshe Hajiya Maimuna ta kirata kamar ta ji shawarar da mai kanti ya ba khadijahr ta dungura mata takarda dauke da abubuwan da xata siyo mata ta bata kudin ta je kanti, Khadijah na isa kantin bayan ta basa takarda ta sa ya bata fallen takarda da Biro, yana mika mata ta xauna shi kuma ya ci gaba da hada mata kayan Aiken da aka yi mata a Leda, rubutu tayi kamar haka "Assalam, I am soo happy you fulfilled ur promise, I am no longer hungry anymore, I love the foods, may Allah reward u abundantly, I like you." Ta tsura ma neat writing dinta mai kyau ido tana murmushi, can ta linke takardar ta mayar ma mai kanti biron sannan ta karbi kayan ta ta wuce da sauri, cikin flowers ta bar takardan yanda xa a gani sannan ta shiga gida, Hajiya Salaha dake ta wanke ta jefa mata kallon tsana tace "Shi yasa fa kayan ki can a kwandon kayan wanki har sun fara tsutsa maga uban da xai wanke maki, ba dai duk kin saye kayan ba" Ita dai bata ce komai ba ta shiga ciki ta kai ma Hajiya Maimuna sakonta. Karfe biyar da rabi yara suka dawo gaba daya, aka xuba ma kowa abinci amma banda ita, ko kallon inda abincin su yake bata yi ba banda kallon da take har kowa ya gama cin abincin ya kai kwanuka waje, Hajiya salaha ta shiga kitchen gun kishiyarta dake girki tace "Maman Hafsa kinsan yarinyar can daxu bata karya ba gashi yanxu ma ko damuwa bata yi tace ina abincin ta ba?" Hajiya Maimuna tace "Wallahi ina lura da ita, ke dai na mu ido, ranan yanke jikinta ta fadi ya kusa xuwa, ni dai baxan roketa ta xo ga abinci ba idan ma ba ta ci ba auki xai ma yaran mu" Hajiya Salaha ta fita tana cewa "Toh ni kinga ina bi ta kanta" Da daddare yau dai macaroni dafaduka aka yi ta manja, Khadijah ta ki xuwa kitchen ta karbi abincin sai kallo take, Tsawa Hajiya Salaha ta mata tace "Toh maxa tashi ki fita ki wanke kwanukan daxu da aka 6ata, ba dai kina xaune kina jiran a kawo maki abinci ba..." Khadijah ta mike ta fita da sauri daga parlorn Hajiya ta bi ta da kallon mamaki don a tunaninta xata shiga kitchen ne, wanke wanken taje ta d'an yi kafin ta fita gate da sauri ta bude flower sai ga wani ledan, tayi murmushi ta dauka ta dawo ciki ta wuce favourite position din da take xama ta bude take away din taga shinkafa ce da miya sai nama kusan yanka biyar ta wara ido cike da jin dadi ta fiddo goron five alive ta ajiye sannan ta fara ci, cikin few minutes ta gama saboda saurin da take ta koshi ba kadan ba don har ta kasa shan drink din gaba daya, ta boye a inda ta saba boyewa sannan taje ta jefar da ledan ta dawo ta ci gaba da wanke wanken tana gyangyadi tsabar koshin da tayi, da kyar ta karasa ta shiga ciki wajen karfe tara tana shiga kuwa isha tayi suna ta kallonta su ji ta ce ina abincinta amma sai ji suka yi tace xata je kwanta daga haka kuma ta tafi tayi kwanciyarta. Haka nan Khadijah ta ci gaba da rayuwa gidan har na kusan wata biyu bbu ranan da ya taba fashin ajiye mata abinci gashi tun haduwar da suka yi a kanti ta bukaci ya dinga ajiye mata abincin basu sake haduwa ba, duk kwana biyu sai ta ajiye masa note din godiya cikin flowers, Bbu abinda ke daure ma Hajiya Maimuna da Hajiya salaha kai irin yanda suka ga Khadijah ke ta kiba tana kyau gashi fa sai ta kai har washegari wani lkcn bata ko bi ta kan abinda suka girka ba, ga uban aikin xa take narka kullum a gidan, ranan dai abun ya ishi Hajiya Maimuna tace "Ni kam yarinyar nan ko dai akwai gun da take xuwa cin abinci ne ba mu sani ba, dubi fa ko bin ta kan abincin gidan nan bata yi ko da an xuba mata sai ta ki ci, gashi lafiya lau sai ma kiba da na ga ta yi kamar" Hajiya Salaha tace "Nima abun na daure min kai kuma kema kinsan bbu inda take xuwa sai gun mai kanti kuma bata dadewa take dawowa gida" Hajiya Maimuna tace "Yanxu dai kawai mu sa ma duk movement dinta ido sosai" Da rana Khadijah na ta xaune parlorn tana jiran su tafi su kwanta taje ta dau abincin ta a flowers, kallon wani Hausa film suke, taga basu da niyyar shiga ciki, ta mike ta dauke few plates dake parlorn duk da tayi wanke wanken safe tace "Mama in je in wanke" Hajiya Salaha tace "Toh sai kin tambaya, ko ba aikin ki bane" fita tayi da sauri don dama abinda take nema kenan, tana ajiye plates din ta fita gate, tuni su Hajiya suka fito suna lekan compound suka ga bbu ita, hakan yasa Hajiya Salaha xata nufi gate Hajiya Maimuna ta rike tace "Jira kamar ga kafafuwanta can a tsaye" ko rufe baki basu yi ba sai gata ta shigo da leda suka yi saurin makalewa da bango, ko lura da su bata yi ba ta wuce inda ta saba xama da sauri, ta bude soyayyen kwai da indomien dake turiri kenan ta ajiye five alive a gefe, sai ga su a kan ta, tsuru tsuru tayi tana kallonsa kamar yanda su ma suka saki baki suna kallon abincin, salati suka saki a tare, Hajiya Maimuna tace "Uban wa ta baki wannan abincin Khadijah" Khadijah da tayi mugun tsorata xata mike ta gudu Hajiya Maimuna ta cafketa tace "Gun ubanwa kika karbo?" Jikinta na rawa tace "Ku yi hakuri" Mari Hajiya Maimuna ta xabga mata tace "Dama shi yasa kika daina bi ta kan girkinmu a gidan nan, karuwanci kika fara ba mu sani ba? To yau sai kin fiddo wanda ke baki abincin nn" cikin kuka tace "Gidansu yana can mama" janta suka yi suka fita ko warce ta yafe dankwalinta a kai ana huci suka ce "Mu je gidan" Kuka kawai Khadijah take a tsorace tana biye da su Hajiya Maimuna na janta har suka isa kofar gidan, Cikin rawar murya tace "Nan ne gidan...." Hajiya Maimuna ta xaro ido tace "Nan kike xuwa?" Ta girgixa kai da sauri tace "Mama sau daya na xo, mutumin ne ke kawo min abincin ya ajiye cikin flower, ku yi hakuri don Allah" kwankwasa gate Hajiya salaha ta dinga yi da karfi mai gadi ya bude, tace "Ina masu gidan nan" Mai gadin yace "Daga ina?" Bin gefensa tayi a fusace ta shiga tace "Xaka ji da munafurcin ka, ni din ce xaka ce baka taba gani ba" Hajiya Maimuna ta bi bayan ta tana jaye da Khadijah suka isa parlorn gidan suka bude, Hajiya Maimuna ta rafka sallama kamar tashin duniya, Wata yar budurwar ce ta fara fitowa tana kallonsu ta gaishesu, a takaice suka amsa suka tambayi uwarta, ta juya kenan xata je kiranta sai ga ta ta shigo parlor, har ta karaso kallonsu take da mamaki, Hajiya Maimuna ta hade rai tace "Hajiya Amina mun wuni lafiya?" Hajiya Aminar tace "Alhmdllh, in ji lafiya" Hajiya Salaha tace "Ba lafiya ba, ina d'an ki yake?" Da mamaki tace "Da na kuma?" Cike da jaraba Hajiya Salaha tace "Kwarai, ya fito ya gaya mana menene tsakaninsa da yarinyar nan, ya fito yanxun nan" Hajiya Amina tace "Kar ku min hayaniya a gida don Allah, ku gaya min meye ya faru?" Hajiya Maimuna tace "Hayaniya kam dole, don wannan case din sai ya iya kai mu har kotu, tunda batanci yake yi da 'yar mu" bude baki Hajiya Amina tayi tana kallonsu, haka ma 'yar ta... Khadijah dai sai matsar kwalla take jiki na rawa, Dai dai nan kuwa sai ga shi ya fito parlor, tsaye shi ma yyi yana kallonsu da mamaki, Mahaifiyarsa da ranta ya gama baci tace "Sadeeq, what's between you two" ta fadi haka tana nuna masa khadijah, kafin yace komai Khadijah tayi saurin cewa "Nothing ma, kawai yana kawo min abinci yana ajiyewa cikin flowers ne in dauka in ci..." Buge mata baki Hajiya Maimuna tayi ta kunduma mata xagi tace "Kece sadeeq? Makira yar iska? Ke ta tambaya?" Sadeeq dai na tsaye yana kallon ikon Allah ya kasa cewa komai, mahaifiyarsa tace "Magana nake maka malam" ya juya ya kalleta yace "Mum I don't think I have time explaining my self to any of this women, ni dai nasan the girl told me about how hungry she was ba'a a bata abinci a gidan, and I volunteered...." Uwarsa ta xaro ido tace "Volunteered what Sadeeq?" Ya d'an hade rai yace "She requested in dinga ajiye mata abinci a flowers din kofar gidansu thats all, sannan tun ranan bamu sake haduwa da ita ba cox dama gun wancen mai kantin muka hadu, sai kuma yanxu da take tsaye a nan, ashe dama taimako na xama laifi, kuma da ba su barta da yunwa ba har xata ce in dinga ajiye mata abinci she's always hungry? Ba komai kuma yasa nake ajiye mata abincin ba sai don nasan bbu illar da ya kai barin 'ya mace da yunwa, bana son ta shiga wani hali shi yasa, if not what's my connection with her da har xan dinga bata 3 daily meals?" Tunda ya fara magana su Hajiya suka saki baki suna kallon Khadijah da ta sunkuyar da kai, Hajiya Maimuna tace "Toh kayi na farko kayi na karshe, dauki 3 daily meals din naka ka kai gidan almajirai ko marayu, kada ka sake xuwa mana kofar gida da abinci, ita kuma yanxu xa mu koma gida mu ji wanda yake barin ta da yunwa da tace she's always hungry" Hajiya Salaha tace "Sai ma kin fada, kuma wllh Allah ya isa tsakaninmu da ita tunda mu ta ke bi gida gida a anguwar nan tana cewa muna barin ta da yunwa, bbu abinda xai hanani yi mata jina jina yau" Daga haka ta ja ta xasu fita, khadijah ta hade hannunta tana kallon sadeeq cikin rawar murya tace "I am very sorry" Rankwashi Hajiya Salaha ta kai mata da karfi ta ja ta suka fice gidan, Hajiya Amina ta kalli d'anta tace "Daga this very moment na raba ka da abinda kake yi" Hajiya Maimuna tace "Da dai ya fi maku" daga haka ta bi bayan su. Duka da xagi kam khadijah ta sha shi ranan, duk ta fita hayyacinta sai kiran Ummarte take, don Kansu suka kyaleta daga karshe, indomie da kwan kuma suka dauke suka juye a plate suka cinye. Tun daga ranan sadeeq bai sake ajiye mata abinci ba, kafin kwana biyu ta rama duk ta xama wata iri har lkcn ta ki kwantar da hankali ta ci abinci da suke girkawa, sai taji yunwar xae sumar da ita take tura abincin ko yaya shi ma wani lkcn har da amai sai tayi, tafe take kamar iska xai kadeta tsabar weakness dake tartare da ita, ta isa gun mai kanti ta basa takardar da aka aiketa ya karba yana tsokanarta kamar yanda ya saba, ita dai bata ce komai ba unlike before da xata fara masa turanci, kiranta taji anyi ta juya da sauri jin muryar, ta ga Sadeeq tsaye bayan ta, ta yi murmushi tace "Good evening" a hankali yace "How you?" Tace "Fyn" kallonta ya dinga yi ganin yanda ta rame, ta juya ta karbi sakonta tace "Bye" yace "Khadijah" ta juya da sauri tana kallonsa, yace "You are always hungry koh?" Shiru ta yi hawaye ya cika mata ido, yace "I am sorry I cant help it" ta ce "Don't worry, I appreciate the one you did before....." Hannu ya sa a aljihu ya Ciro kudi ya kirga dubu biyar ya mika mata yace "Toh gashi ki boye wannan ko biscuits da doughnut sai ki dinga siya kina ci a nan kinji?" Shiru ta yi ya kamo hannunta ya sa mata yana murmushi ya gyada kai yace "Yeah" rike kudin tayi ya sake hannunta yace "See you some other time" ta daga masa hannu hawaye cike idonta tace "Thank you" hanya daban daban suka bi tana isa gida ta boye kudin, tana son fita ta siyo abinda yace da daddare ta kwanta amma tana tsoro, hakan yasa ta sha ruwa kawai ta kwanta cikinta na kugi don wake da taliya aka yi daren ranan. Bayan kwana biyu tana xaune ita kadai tsakar gida tana tankaden uban garin masaran da Hajiya salaha ta hada ta shi, duk kayan jikinta ya koma fari kamar warce ta yini a kusa da injin nikan, ga hawaye da ya bubbushe fuskarta, a kan tankaden nn tun safe Hajiya Salaha ke dukanta da tayi sai tace bai yi ba, hakan yasa take yi a hankli ynxu bayan ta ci kukanta ta koshi, bude gate aka yi ta daga kai ta ga Ummarta, still tayi rike da rariyar, kamar yanda ita ma Umma ta tsaya kallonta ko kiftawa bbu, hawaye ya cika idon khadijah ta mike da gudu ta nufeta ta rungumeta tace "Ummata" sosai Umma ma ta rungumeta duk jikinta yyi sanyi, can ta janyeta jikinta tana kallonta daga sama har kasa, hawaye ne ya cika idonta ta mata alamar ta dauko takalmarta, khadijah ta koma ta dauko takalman da duk sun tsinke ta sa su haka, Umma ta ja ta suka fice daga gidan, Khadijah dake ta bin ta tace "Ummata tafiya xa kiyi da ni?" Hawaye na sakkowa idonta tayi tambayar, Umma ta gyada mata kai kawai don ta kasa cewa komai, suna isa dai dai gidansu Sadeeq khadijah dake murmushin farin ciki tana rike da hannun Umma gam tace "Umma I have a frnd here, can I just go and bid him goodbye, he is more than kind" Umma ta kalleta for d 1st time ta bude baki cikin sanyin murya ganin hawayen dake ta sauka idon khadijar, tace Some other time dear, khadijah ta gyada mata kai har suka wuce kofar gidan, da sauri Umma ke janta har suka isa main road ta tsayar da adai daita, direct sai motor park, ta biya masu kudin mota bayan yan mintuna motarsu ya tashi xuwa garin kano, bacci Khadijah ta dinga yi jikin Umma don tun asuban fari aka tasheta a can gidan, har suka isa kano bacci take yi, Umma ta tasheta, ta bude ido a hankali, suka sauka cikin motar Umma na rike da ita suka fito bakin titi ta dau adai daitan da xae kai su har gidan da take aure. Ba laifi babban tsakar gida ne compound din mai dauke da small building har hudu, ko wani building na da parlor da daki a cikinsa, sai babban kitchen dake tsakar gidan, da kuma bayin wanka biyu da toilet ma biyu, a gefen kitchen kuwa ga rijiya a rufe, gidan da Umma ke aure kenan, tana kuma auren d'an kasuwa ne mai mata biyu, yara ne su kusan biyar ke ta wasa tsakar gidan da yake da yamma ne kuma ranan alhamis ba islamiyya, da wasu yan mata uku dake xaune kan tabarma suna danne dannen waya, umma ta amsa gaisuwar da yara kananan ke mata ba tare da ta sake kallon gun da yan matan suke va ta fiddo key ta bude part dinta, khadijah dai na tsaye sai kallon yaran take kamar yanda su ma ke kallonta, can ta kalli yan matan taga su ma kallonta suke, Umma ta kalli direction din kitchen jin kamshin girki suka yi ido hudu da Shafa kishiyarta dake lekosu ta cikin kitchen din, suna hada ido kuwa tayi saurin dauke kanta, Umma ma ta dauke nata kan, can ta hango uwar gidan mai gidan nata ita ma tana lekota ta windown parlornta ita ma suna hada ido tayi saurin dauke kai, Umma ta bude kofar ta ta ja hannun Khadijah suka shiga ciki ta dage labule ta daura kan kofar kasancewar parlorn ya dau xafi. (adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); *NOOR-AL-HAYAT* Khadijah ta xauna kan kujera tana kalle kallen parlorn tace "Umma nan ne gidan ku koh?" Umma ta bude fridge xata dauko mata ruwa tace "Ehh" Karban ruwan tayi tace "Umma yunwa nake ji ban ci komai ba" Umma tace "Toh me xa ki ci yanxu?" Murmushi tayi da ya bayyana fararen hakoranta ta langwabar da kai tace "Indomie Ummata" Umma ma ta yi murmushin ta juya ta fita, Khadijah ta dinga bin madaidaicin parlon da kallo kai kana ganinta kasan she is just happy, muryar Umma taji tana kiranta daga waje ta fita da sauri ta sa takalminta tace "Gani Umma" Umma ta mika mata ruwa a buta tace "Gashi ki fara yin alwala kiyi sallah" tace "Toh" sannan ta durkusa tana alwala tana yi tana kallon yaran dake ta kallonta har da matar dake girki a kitchen, Umma ta shiga kitchen din ta dauko indomie daya ta fito ta kai parlorn ta sannan ta dawo rike da naira dari tana mika ma wani yaro da baxai wuce shekara biyar ba tace "Mudassir je kanti ka amso min kwai biyu" yaron ya karba ya wuce waje da gudu, Karamin tukunya Umma ta daura kan electric madaidaici dake parlorn ta bayan ta shimfida ma Khadijah darduma, khadijah na idar da sallahn Umma tace "Kin fara xuwa school a can gidan" girgixa kai tayi tace "A'a, kin san me Umma ta" Umma tace "Bari ki ci abinci" soya mata kwan da yaron ya kawo Umma tayi sannan ta ajiye mata a gabanta da ruwa a cup ta mayar da wani tukunyar ta sa mata ruwan wanka, Umma tayi tagumi tana kallon yanda take cin abincin, kana ganinta kasan yunwa kawai take ji, kafin ta gama Umma ta juye mata ruwa ta kai bayi da sabulu, ita ta rakata bayin sannan ta koma parlorn, khadijah na gama wankan ta fito daure da xanin da Umma ta bata, Shafah dake girki daga cikin kitchen ta bi ta da wani kallo hakan yasa tace "Ina yini" dauke kai tayi kamar bata ji ba, khadijah ta wuce cikin parlorn Umma tace "Wannan matar dake girki na gaisheta bata amsa ba" Umma tace "Kar ki sake gaisheta" daga haka ta cire hular kanta bayan ta kawo mata man shafawa, sakin baki tayi tana kallon gashin don tun kalaba shidda da ta yi mata kafin kawu ya tafi da ita kasancewar gashinta na da tsayin bala'i kuma bata son ana taba shi, Umma bata dai ce komai ba, ta dau gyalenta tace "Ban ce ki fito ba ki jira ni har in dawo" khadijah tace "Toh" daga haka Umma ta fita, bayan kusan minti ashirin ta dawo rike da Leda ta sake labulen parlorn ta bude ledan ta fiddo wasu dinkakkun riga da skirt kana ganinsu dai kasan taje ta karbo su ne tace "Tashi ki sa, gobe xan je kasuwa in siyo maki kaya kinji" khadijah ta sa kayan tace "Umma in kunna TV?" Umma tace "Ban ce ba" kwanciya tayi kan kujera bbu bata lkci bacci ya dauketa, Umma ta xuba ma jikinta ido ganin shattin duka, tagumi tayi tana kallonta tana tausaya ma marainiyar. Khadijah na tsugunne tana alwala tsakar gida da magrib bayan Umma ta tasheta tayi sllh taji an fixge butar daga hannunta ta daga kai tana kallon yarinyar da baxata wuce ta ba, Yarinyar ta murguda baki ta tafi ta kara ruwan ta fara alwala, mikewa khadijah tayi tace "Are you okay?" Yarinyar ta balla mata harara tace "Ki fadi wanda xan ji mana" khadijah bata sake cewa komai ba har yarinyar ta gama sannan ta wuce da butar parlornsu, khadijah ta xaro ido sai kuma ta juya ra wuce gun Umma dake parlor ta tsaya bakin kofa a hankali tace "Umma wata yarinya ta karbe butan ta tafi da shi" Umma ta fito tace "Wace yarinya?" Nuna mata parlorn da yarinyar ta shiga tayi, Umma ta kama hannun ta suka je har kofar parlorn ta bude labule tace "Wacece a ciki" Khadijah ta dinga bin yara kusan biyar dake parlorn da kallo sannan ta nuna mata yarinyar, Umma tace "Rahmah dalilin me kika karbe buta tana alwala?" Yarinyar da ta tsuke baki tace "Toh Anty namu ne ai" Umma tace "Kar ki sake, idan ko ba haka ba sai na bata maki rai" daga haka ta ja hannun Khadijah suka bar wajen ba tare da ta bi ta kan Uwarsu Hasana dake xaune parlorn ba, Umma ta dauko buta parlorn ta ta bata, Wata yarinyar ce ta shigo parlorn da abinci a er warmer ta ajiye ta juya ta fita, Umma ta daga kan khadijah dake kafarta a kwance tana bata labarin abubuwan da aka dinga yi mata gidan Kawu sannan ta mike ta jawo warmer din, shinkafa ce da miya sai nama biyu da salad a gefe, iya cin ta ne abincin, ta daura dankwali ta fita xuwa kitchen din ta dau wani plate ta bude tukunkya xata debi abinci sai ga Shafah da sauri tace "Amma dai Amina kinsan ba ke ce da kitchen ba, don haka baki da hurumin shigar min kitchen" Umma ta kalleta tace "Ae kin gan ni da bakuwa kika yarfo min er shinkafa a cooler kamar mayunwaci, don haka ke ma baki da hurumin hana ni debar mata abinci" Shafah tace "Bakuwa? Kin gaya min xaki yi Bakuwa in sa girki da ita ne, to wllh kin yi kadan ki kara diban wani abincin don na almajirai ne" Umma ta Debi shinkafar kusan cikin plate ta xuba miya kai da nama biyu tana kallonta tace "In ji duka" daga haka ta fice daga kitchen din Shafah tace "Ai kuwa ni da ke shege ka fasa Amina, mu xuba" tsaye Umma ta ga Hasana bakin nata parlorn tana lekosu tana ganinta ta shige ciki da sauri Umma tayi tsaki ta shiga ciki ta ba Khadijah abincin hannunta. Da yake khadijah tayi baccin rana har karfe goma idonta biyu tana ta ba Umma da tayi tagumi tana saurarenta labarai iri iri, Yar Shafa ta farko fadila ta bude kofa tace "Abba yana kiran ki" daga haka ta juya ta bar gun, mikewa Umma tayi ta fita tare da Khadijah tana rike da hannunta suka tafi turakar mai gidan, ba wani babba bane mai gidan don baxai wuce 48 ba, Shafah na xaune kan kujera da Hasana a gefenta, Umma ta xauna ta nuna ma khadijah k'asa ta xauna ita na, Gaishe da shi tayi, khadijah na kallonsa tace "Good evening Sir" idonsa a kanta yace "How are you" tace "I am fine" Shafah da Hasana aka kyabe baki, mai gidan da suke kira da Abban Fadila yace "Wacece wannan Amina?" Umma tace "Kayi hakuri na so kiran ka tun kafin in iso kano daxu sai da bani da charge, duk da mun yi da kai gobe xan dawo kawai kuma na fasa, wannan 'er marigayin tsohon mijina ce Khadijah, na taho da ita ba tare da ixinin ka ba, kayi hakuri ban ji dadin yanayin da na same ta bane shi yasa na daukota bbu shawara da kai" shiru yyi bai ce komai ba, can ya jinjina kai yace "Toh Allah ya kyauta" Su shafa aka kwalalo ido ana kallon khadijah jin wai er kishiyarta ce da ta rasu, Abban fadila yace "Dalilin ki na shiga kitchen ba ke ce da girki ba daxu nake son ji? Shi yasa ma na aika a kira ki" Umma tace "Ehh toh, sun ganni da yarinya mun dawo Abban fadila, sai da aka tashi xubo min abinci da magrib sai aka xubo dai dai wanda ni xan ci a yar cooler" yace "Shine aka ce ko shiga ki diba? me yasa baxa ki nemi izini gun mai girki ba ko kuma kice ta k'ara maki kina da bakuwa, ke ce kadai me karya min doka a gidana fa Amina" Umma tace "Watana kusan uku gidan nan yaushe da yaushe na karya maka doka Alhaji?" Hasana sai wani blushing ake Shafa na taya ta, Abban fadila yace "Toh tashi ki je" mikewa tayi ta daga khadijah da su Hasana aka bi da harara ta fice parlorn ta koma nata, daki ta nuna ma khadijah ta tafi ta hau saman gado ta kwanta, khadijah tace "Toh Ummata" sannan ta shiga dakin ta kwanta hade da lumshe ido don har ta mance Rabon da ta hau gado har tayi bacci a kai. Washegari da asuba Umma ta tada Khadijah taje tayi sallah bayan ita ta idar, khadijah ta fita tsakar gidan rike da buta tana mitsika ido, yara ne kusan biyar ko wanne na alwala tana kokarin shiga bayi tayi fitsari taji an fixgota ta juyo da sauri a tsorace, yarinyar da ta kawo ma umma abinci jiya ce, tana kallo yarinyar ta shiga bayin, ta ja gefe a hankali ta tsaya tana jiranta, bata gaya ma Umma abinda ta sake yi mata ba, bayan ta idar da sallah ta koma daki ta kwanta ta ci gaba da baccinta. Gari na fara wayewa Umma ta kuma tashinta daga baccin ta kai mata ruwan xafi bayi da sabulu da soso, ba a dau lkci ba khadijah ta dawo tana wasa da yatsunta a hankali tace "Umma wata yarinya ta fitar min da ruwan ta sa nata ta rufe bathroom din" fita umma tayi ta tafi kofar bayin da sauri tana kallon xanin waye kafin tayi kwafa ta nuna ma Khadijah kujera tace "Xauna nan ki kyaleta kawai, idan ta fito ki shiga" khadijah ta xauna tace "Toh" umma ta koma ta ci gaba da sharanta, yarinyar na fitowa khadijah ta mike ta shiga da ruwan da kyar ta juyo xata dau sponge case wata ta sake fitar da ruwan nata ta hankadota waje ta shiga ta rufe kofa, tsaye khadijah tayi baki bude tana kallon bayin, dai dai fitowar Umma da abun kwashe shara da tsintsiya, karasawa tayi da sauri ta tura kofar ta janyo ruwan waje ta fiddo sabulun yarinyar sannan ta dau na Khadijah ta saka tana kallonta tace "Xo ki shiga" yarinyar ta fashe da ihu tana buga kafa, khadijah dake kallonta baki bude a hankali tace "Why are they behaving like this" Umma ta shigar da ita bayin tace "Maxa ki fara wanka" Hasana ce ta fito da sauri jin ihu da kukan yarta, tana kallonta a gigice tace "Walida ya aka yi, me ya faru" cikin kuka walidar tace "Xan shiga inyi wanka shine Anti ta fiddo min ruwana ta fito da ni ta saka yarinyar da ta kawo cikin bayin" Hasana da tayi mitsi mitsi da ido tace "Toh Allah ya isan ki, kuma mu xuba da su a gidan nan xan ga ko agolarta xata samu gun xama, ita ma da take a dosane ta ji da kanta mana, tsabar munafurci da neman kugun xama taje ta jajibo yar kishiyar da kilan ma ita ta kasheta ta kashe ubanta, shege ya fasa mu da ita a gidan nan" Umma bata ko kalleta ba ta shiga share kofar parlorn ta, Shafa ta fito tace "Ya aka yi ke kuma da sassafe, ke da wa?" A fusace Hasana tace "Ki rabu da yar kaxa kaza, wai Walida ce xata shiga wanka shine ta fiddo mata da ruwan ta ta saka na shegiyar da ta kawo mana mai kama da aljanu" Shafah ta rike ha6a tace "Ikon Allah Walida da xata makaranta? Ita kuma agolar da take gida, Mutum dai bashi da aiki sai neman fitina, banda jakanci ma ina aka taba dauko agola ace xa a takura ma masu gida dominta" Hasana tace "Ke fa kika san jakanta, amma ni nasan maganinsu wllh, kuma xa mu sa kafar wando guda da su" daga haka ta kalli yar ta tace "In ta fito ki kwara ruwa bayin ka fin ki shiga, Allah dai ya tsine duk mai son takura ku gidan ubanku ehe" daki ta shiga tana ci gaba da kumfar baki, Shafa ta bi bayan ta tana cewa "Amin dai, Allah kuma ya kawo mana karshen bala'in nan, muna xaman xamanmu dai" Khadijah bata fito ba duk da ta gama wankan, sai leken tsakar gidan ta kofar bayin take taga ko sun tafi, ganin Walida ce kadai xaune tsakar gida ta fito tana gyara daurin da tayi ma Xanin jikinta ta ta nufi dakin Umma da sauri, taji Walida tace "Shegiya kawai" kallonta khadijah tayi tace "Back to sender" sannan tayi saurin shigewa dakin ummanta. Kafin karfe bakwai da rabi duk yaran gidan an shirya wucewa makaranta, jin muryar Abban fadila a waje, Umma ta kalli khadijah tace "Go outside and greet him. Come back immediately after that" khadijah ta fita waje ta gansa tsaye ya shirya alamar xai fita kasuwa yana sauraren yaransa mata biyu da suke requesting kudin wani littafi da xa su siya a boko ga iyayensu tsaye bakin kofa, Khadijah ta karasa kusa da shi ta durkusa a hankali tace "Good morning sir" ya kalleta yace "Morning yar turawa, how was ur nyt?" Ta washe hakora tace "It was splendid" yace "Good, ina mamar taki?" Ta kalli kofa tace "Tana ciki" yace "Kira min ita" Shafa da Hasana da lkci daya mood dinsu ya canxa suka kalli juna, juyawa khadijah tayi taje kiran Umma suka fito a tare, Yace "Naga baki shigo gaisheni ba" Umma tace "Bayan nayi sallah I just slept off" yace "Ohk, anjima sai ki je ki mata registern islamiyya ko xuwa next week sai a samu boko a sata" Umma tace "Toh nagode, Allah ya kai mu" Naira Dari ya Ciro ya mika ma khadijah yace "Gashi ki siya biscuit" xaro ido tayi ta kalli Umma, Umma tace "Amsa" ta karba da hannu biyu tana murmushi tace "Nagode uncle" daga haka Umma ta ja ta suka shiga ciki ba tare da ta yarda ta kalli inda kishiyoyinta dake cika suna batsewa suke ba, Shafa tace "Toh Abban Fadila kudin kitso da na tambaye ka tun jiya fa?" Hasana tace "Ni tun shekaranjiya nake ta bi ya sa min kati amma kinga wani gwaninta a nan" Tuni ya isa kofa bayan ya sallami yaransa mata dake turo baki kudin bai ishesu ba, sai da ya fita gidan, Hasana tace "Toh wllh abinda baxai yiwu ba kenan, ya gama ji da nasa yaran mana, har xa a kara daura masa nauyi bayan wanda ke kansa, ko ita yarinyar bata da dangin uba ko uwa ne sai karere??" Shafah tace "Ke fa kika San karere, ita nan gwaninta take a idon duniya ko, toh kuwa xata sha kunya in har bata mayar da yarinyar nan gun dangin ubanta ba, sai yarinyar nan ta ja mata masifa da bala'i sai kuma ta dauko mata abun kunya muna nan dake, sai dai idan ba ni ce nan Shafa'atu yar gidan Sanusi jikar Yakubu na bude baki na yi magana ba" Hasana tayi shewa tace "In sha Allahu kuwa" Umma dake ta jin su ta girgixa kai tana murmushi a ranta tana masu addu'ar samun sauki, sai bayan da duk suka gaji suka shiga ciki ta dauko kibiya da comb xata tsefe ma khadijah gashinta, Tuni khadijah ta fara matsar kwalla tun kan ta kama kan din right from Beginning idan ana son tashin hankali toh a taba gashinta, sosai ta ba Umma wahala ta dinga rusa kuka tana ihu, har dai aka gama tsefewa ta bata Hijab ta sa suka fito don xuwa saloon a wanke mata gashin, da ido su Hasana suka bi su har suka fita. Sai kusan azahar suka dawo gida, Idon khadijah ya kumbura don kuka, Hasana na xaune tsakar gida tana jajjagen tafasasshen nama da alama dai dambunsa xata yi, Shafah kuma na daga xaune bakin kofa suna ganin shigowarsu suka yi shiru daga xancen da suke ko wacce ta hade rai, Umma ta bude kofar ta ta ja khadijah suka shiga ciki, xaunawa khadijah tayi kan kujera Umma na harararta tace "Duk kika tsefe kan nan ke kadai xaki saloon din baxan iya wahala ba, dubi idanuwanki kamar warce aka yi ma duka, ke ba yarinya ba ki dinga ma mutane ihun kitso" Khadijah ta kwanta kan kujera bata ce komai ba, Umma ta fita ta shiga kitchen ta dau indomie biyu ta fito, Hasana ce tace "Gaskiya Abban fadila ya dawo ya kasa ma kowa indomie ya ajiye a dakinsa tun jiya ake ta shiga ana daukar indomie abinda yaran gidan ma sai su yi sati basu ci ba, wnn ai mugunta ce" Umma tayi yar dariya bata ce komai ba ta shiga ciki, dama da kwai hudu ta dawo gidan, don haka ta girka indomien a daki ta dafa kwan ta tada khadijah da ta fara bacci ta bata nata sannan ta fita yin alwala, Da daddare yau ma kamar jiya a karamar cooler shafah ta aiko ma Umma abinci, Tea ta hada da yake tana da kayan shayin a daki ta fita da kanta ta siyo bread ta ba khadijah ta ci ba tare da ta bi kan yan gidan ba. A can katsina kuwa neman duniya kawu da matansa sun ma khadijah amma bbu ita babu labarinta, gidan da suka fara xuwa kuwa gidansu sadeeq ne, nan mahaifiyarsa ta nuna masu the other side of her don har sai da suka tsorata kuma tace kada warce ta sake shigo mata gida, har station kawu yaje da gidan radio, bai taba kawo wa cewa Umma ta san gidansa ba balle ta xo ta dauke khadijah, Duk da ba wai abun ya wani dame su Hajiya salaha da Hajiya maimuna ba amma ganin yanda mai gidan nasu ya dage yana nemanta yasa su ma suka xage, har shawara Hajiya salaha ta bada su kai karar Hajiya Amina da d'anta, kawu ya gwaleta cike da masifa yace "Kinsan waye uban yaron?" Hajiya Maimuna tace "Alkali" Kawu yace "Shine xata dinga magana kamar mahaukaciya?" Ita dai Hajiya Salaha bata ce komai ba. Washegari da safe Umma ta fita tare da Khadijah don sama mata islamiyyan da xata fara xuwa, bata yrda ta kai ta wanda yan gidan ke xuwa ba ta kai ta wani dake gaba da shi sosai, bayan ta biya komai ta wuce kasuwa tare da ita don yankar mata uniform daga can tayi mata siyayya kananun kaya. Da yammacin ranan Umma ta amshi girki, tuwon shinkafa da miyar vegetable take girkawa, Khadijah na xaune kan tabarma bakin kofar Umma tana cin gyadar da Umma ta siya mata a hanyarsu ta dawowa, da ta bare sai ta jefa ma wani kadangare dake tsakar gidan yana yawo bawon gyadar, tsawa taji an mata ta waiga da sauri Hasana da fitowarta kenan tace "maxa tashi ki tsince su don baki da bawa mai shara a gidan nan" Umma kallo waje tayi daga kitchen din bata dai ce komai ba ta ci gaba da girkinta, mikewa khadijah tayi ta isa gun da ta ke ta jefa bawon ta shiga tsince su tana xubasu a shara har ta gama, Hasana ta nuna mata wasu bola dake kusa da kofar Shafah wai taje ta tsince, Umma ta fito tace "Wannan kuma ne baki isa ba" kujerar da ke kusa da kofar kitchen ta nuna ma khadijah tace "Sit here" khadijah ta karasa da sauri ta xauna, Hasana ta rike ha6a tana kallon Umma bata dai ce komai ba. Umma bata bar khadijah ba sai da ta tabbatar ta yi bacci sannan ta tafi bangaren Abban Fadila, bata yi mamakin ganin kishiyoyinta ba a xaune parlorn, da kuma alamar yana shigowa suka bi sa don bai jima da dawowa ba, har Umma ta ajiye tray din abincin hannunta kallonta yake, ta xauna ta gaishesa, bai amsa ba yace "Dama kin taho da yarinyar nan ne don ki ci xarafin mutane Amina?" Umma ta kallonsa tace "Ban gane ba" yace "Toh daga yau kar ki sake nuna iko a kan ta Idan ba haka ba ki mayar da ita dangin ubanta, banda janyo yaro ya raina babba don me Hasana zata sa ta aiki ki hanata, akan me? Meye amfanin xamanta gidan idan baxa a ci moriyarta ba!" Umma dake saurarensa tayi murmushi tace "Tun da na shigo gidan nan cikin yaransu akwai warce na taba sa aiki ta min? Babu.... domin kuwa duk sun hanasu amma na taba kai maka kara? Ni wllh matan ka basu isheni kishi ba Alhaji, banda kaddara ba lallai su gan ni cikinsu ba balle su sa ni gaba, ina ce ni ka fara sani ma kafin su? Wllh basa gabana balle inyi kishi da su, marainiya ce dai na daukota sae dai bakin ciki ya kashe su tunda ba a kansu xata xauna ba" Tana kai wa nan ta fice daga parlon idan sun fita sai ta dawo. Ka'ida ce duk safiya a gidan su Fadila ne ke yin wanke wanken safe da sharan tsakar gida ko ma wacece ke girki kafin su tafi makaranta, yau kam suna tashi da safe wanka suka yi ko wanne ta tafi ta saka uniform, Umma bata ce masu komai ba tana ta soya dankalin irish da xa ayi breakfast da shi a gidan, Khadijah na durkushe kitchen din sai dai ta bude babban cooler a Umma ta xuba wanda ta soya, Umma ta gama soya Irish din da ta fere gaba daya ta soya kwai, kananun yaran gidan ne suka dinga tahowa karban nasu duk ta basu ko wanne sa cup din shayi da ta hada, Khadijah dake ta kallonsu tace "Umma why are they so plenty?" murmushi umma tayi tace "Just as the one ur uncles home" Khadijah ta langwabar da kai tace "Noo, they are nt as much as this" Fadila ce ta taho kitchen din tace "Anty ina kwana, ina dankalina" Umma ba tare da ta kalleta ba tace "Idan kin gama wanke wanken can xan xuba maki" juyawa tayi ta wuce sai ga Shafah ta fito, "Amina ban gane baxa ki ba Fadila kalachi ba, meye dalili" Ko tanka ta Umma bata yi ba, ta hau masifa tayi mai isarta daga karshe tace "Bar ta ita ce mayunwaciya Fadila, ta hada da Wanda ta ajiye ma kanta da agolar da ta kawo su cinye, mu je in baki kudi ki siya kosai da bredi a hanya, wanke wanken su shekara nan, in dai baxa ta ba ma agolarta tayi ba" daga haka ta wuce ciki Fadila na biye da ita a baya, daga Hasana har Shafah bbu warce tayi kalaci da girkin da Umma tayi, duk wainar shinkafa suka aiki almajiri ya siyo masu a makwabta, Umma kam ko a gyalenta, wanda ya rage ra kira almajirai ta basu ta hada kayan wanke wanke xata yi, Khadijah tace "Umma na iya wanke wanke fa yanxu xan yi" da kyar ta amince ta bar ta, Ganin yanda ta fara jika kayan jikinta Umma ta karbi kayanta ta shiga yi tace mata ta tafi daki ta kwanta. Da rana cous cous umma ta girka gidan d'an dai dai, daga ita sai khadijah a gidan don tun misalin goma su Shafah da Hasana suka fita basu dawo ba, ta dibar ma kananun yaran gidan a warmer ta kai can dakinta da miyar ta ajiye bayan ta xuba ma Khadijah, ta dawo ta tsaftace kitchen din ta wanke tukwanen da tayi amfani da su da utensils sannan ta koma ciki. Sai kusan karfe Uku su Shafa suka shigo gidan Hasana na cewa "Wash wajen nan ba dai nisa ba Maman fadila, na xata bai fi tafiyar minti talatin ba fa" Shafa tace "Nima farkon xuwa na na sha wahala sosai, ga hanyar bbu kyau mutum na mota kamar ya hau jaki duk jikina ciwo yake..." Shiru Umma taji sun yi suna kallon kofar ta, ita ke ganin su ta labule amma su basa ganinta, suka kalli juna basu dai ce komai ba, kitchen Shafah ta wuce, can sai ga ta ta fito tana kallon Maman walida tace "Ke kamar fa bata yi girki ba" Maman Fadila tace "Bata yi girki ba kuma? Kin ga uban yunwar da nake ji ga shi bani da kosisi kudin sun kare a kudin motar" Daga labulen Umma Maman walida tayi suka yi ido hudu, d'an kame kame ta fara da farko, sai kuma tace "Ba a da niyyar yin girkin rana ne yau a gidan nan ga yara su kusa dawowa" Umma tace "Ehh" sake labulen tayi ta bar wajen Maman fadila ta bi bayan ta, tana jin Shafah na jajjage a kitchen xa su dafa indomie, ita dai tana xaune inda take. Uku da rabi yaran suka dawo kuwa, nan Umma ta xuba ma kowa abincinsa ta ajiye masu tsakar gida, Shafah dake kan tabarma ta kalli kishiyarta dake bakin kofar ta ita ma a xaune, yaran suna gama ci suka fara shirin tafiya islamiyya, Umma ta sa Khadijah ta shirya cikin dinkekken uniform din da tela ta kawo mata daxu, sai murna take har ta gama shiryawa, har bakin makarantar umma ta rakata na ranan kadai sannan ta dawo gida. Umma na kitchen tana girkin dinner ta dinga jin kamar kukan khadijah, ta mike da sauri ta nufi kofar fita, su Shafah da Hasana dake xaune kusa da juna suka bi Umma da ido, a bakin kofa ta kusa cin karo da Khadijah ta riko hannunta tana kkrin cire Hijab din da ta rufe fuskarta tace "Me ya faru?" Cikin kuka tace "Umma wannan yarinyar dake gidan nan ne ban mata komai ba na gansu a hanya, she just slapped my eyes and pushed me na fadi a kan wani dutse" Umma da ranta ya gama baci tace "Wace yarinya kenan?" Dai dai nan walida ta shigo fuskarta tsuke, Khadijah ta nuna mata ita tana shessheka, fixota Umma tayi ta wanka mata mari ta ja kunnenta tace "Don uwarki kika sake taba min 'ya sai na cire maki hakori wallahi, muguwa kawai mai halin banxa" daga haka Umma ta hankadata, walida ta fasa wani ihu kamar xata tsaga gida tana kiran uwarta. Mikewa Hasana tayi baki bude tace "Amina??? Ita walidar kika mara??" Umma ta juya tana facing dinta tace "An mareta, ki taho ki rama mata, d'a ya fi d'a ne, ai wllh duk shegiyar da tace 'ya ta baxa ta xauna lafiya ba gidan nan sai dai ita ta rasa xaman lafiya, me marainiyar ta maku? Ko ba a cin arxiki dama a duniya, kishin naku ya tsaya iya kai na mana, toh wllh duk ku ja ma 'ya yan ku kunne, duk wanda ya sake ko da yi ma khadijah kallon banxa ne, sai nayi masa abinda bai yi xato ba" tana kai wa nan ta tafi daki da Khadijah ta tura ta ciki tace "Maxa ki canxa kaya" daga nan kuma ta dawo kitchen ta ci gaba da abinda take rai bace, daga Hasana har Shafah haka suka bude baki suna kallonta bbu wanda ya iya cewa komai cikinsu. Da daddare Abban Fadila ya dinga kwalo ma Umma dake xaune kan darduma kira, ta mike ta fita don bata ma ji shigowarsa ba amma tuni har ya shiga parlon sa, bin bayansa tayi ta shiga parlon tana masa sannu da xuwa, bai amsa ba ta xauna ba tare da ta yarda ta kalli kishiyoyinta dake xaune parlorn ga Walida a durkushe a kasa, Abban Fadila yace "Amina, so nake xuwa gobe ki mayar da yarinyar nan dangin ubanta da kika daukota, I agree zan yi sponsoring dinta ko tana can din, idan ya so duk bayan watanni uku ko hudu sai ki je ki dinga dubata, I think that will better, I didn't buy d idea of her staying here anymore...." Tun da ya fara Umma ke kallonsa a sanyaye, Hasana da Shafah da aka wani hakikance kan kujera kamar wasu Hajiyoyi xa a iya ganin murnar dake shimfide fuskarsu, trying hard to control her tears Umma tace "Saboda me kace haka Alhaji? Kada ka mance yarinyar nan marainiya ce ba ta da kowa, tun tana yar shekara biyu mahaifiyarta ta rasu, mahaifinta kuma bai mata gatan nuna mata dangin mahaifiyarta ta ba, da na sansu da can xan kai masu ita baxan kawo ta ba gidan ka Alhaji" Abban fadila yace "Kiyi hakuri iyakar taimakon da xan ma yarinyar kenan, ko nawa ne kudin karatunta xan biya idan ya kama ma da feeding expenses duk xan ba da, kawai dai gidana ne baxata xauna ba, kuma baki min kara ba da har xaki daga hannu ki mari diyata a ido don abun su can ya hada su, so tafiyarta xai fi, I think that's all... Gobe ki hada kayanta ki maida ta inda kika dauko ta" Umma da hawaye ke xuba idonta a hankali tace "Ina jin da ka sauwake min kawai in tafi da ita xai fi don ni baxan mayar da ita dangin mahaifinta ba" yana gyada kai yace "Kema xa ki iya sauwake ma kanki ai Amina ba sai na sauwake maki ba" mikewa Umma tayi ta fita ta koma bangarenta, ta shiga daki tayi kukanta mai isarta, duk tausayin khadijah ya cika xuciyarta, to yanxu ina xata kai marainiyar nan, ita ba ta da kowa mahaifiyarta ta rasu da sai ta kai ta gun ta tasan xata rike mata ita, bata da wani abun hannu don duk cutar ta yayyin mahaifin khadijah suka yi a rabon gado bayan ya rasu, domin kuwa kafin a ankare sun boye abubuwa da dama cikin dukiyarsa, banda haka da ko boarding sai ta kai khadijah, har gari ya waye Umma bata ritsa ba tana ta tunanin inda xata kai khadijah domin ta ma kanta alkawari first thing da safe xata fitar da ita da gidan, yayarta warce suke uba daya dake Kaduna ta fado mata ta yi shiru tana naxari. Daukar waya Umma tayi ta shiga kiran layin step sister dinta Yakumbo amma baya shiga alamar dai wayar a kashe yake, da safe bbu abinda ta girka ma mutan gidan a madadin breakfast, ta dai hada ma Khadijah tea ta siyo mata bread ta bata, Karfe takwas ta shiga bangaren mai gidan nasu ta sanar da shi xata mayar da Khadijah gida, ya kirgo dubu biyar ya mika mata yace "Gashi ku yi kudin mota, idan kin dawo sai a san yanda xa ayi batun makarantar nata in ji ko nawa ake biya" Umma ta girgixa kai tace "A'a ka bar shi mun gode Alhaji, muna da kudin mota" Yace "Shi kenan, Allah ya tsare" mikewa tayi ta fita dakin, a cikin wata karamar jaka Umma ta hada ma Khadijah d'an kayan da ta fara siyo mata, suka fito parlor ta sa ma kofar kwado bayan ta rufe, khadijah dake sanye cikin doguwar riga da karamin Hijab tace "Umma ina xa mu?" Umma ta kasa kallonta tace "Xa mu d'an yi tafiya ne khadijah" daga haka ta kama hannunta suka nufi kofa, tana jin su Shafah da Hasana na dariya suna cewa "Toh a sauka lafiya, sai a kara gaba can da ita" ita dai bata tanka su ba har ta fita. Tasha suka tafi cikin a dai dai ta, can suka samu motar Kaduna, bayan wani lokaci motar ta cika suka yi set off xuwa Kaduna garin gwamna... Ko barin kano basu yi ba khadijah tayi bacci jikin Ummanta, har suka isa Kaduna bata tashi ba, suna isa kawo bayan driver yyi parking kowa ya fara alighting daga cikin motar, Umma ta tada khadijah suka sauka su ma, sai kalle kalle khadijah take tace "Umma where is this?" umma tace "Kaduna" Khadijah tace "Wow I've heard of Kaduna in school" Umma ta samar masu napep suka yi ciniki sannan suka shiga xuwa hayin rigasa Unguwar da yakumbo take, tafiya ce mai nisa kafin su iso rigasa, da yake Umma sunan layin kadai ta sani ba wai ta wani san gidan yakumbo bane a bakin layin tasa mai napep din ya sauke su ta basa kudinsa tana rike da hannun khadijah suka shiga layin umma na bin ko wani gida suka xo wucewa da kallo don ta haka kadai xata gane gidan yayarta kasancewar ta jima bata xo wajenta ba, sun fi minti talatin suna bulayi a layin, Khadijah sai tambayarta take "Umma where is this, everyway is dirty, they are smelly gutters everywhere" Umma tace "look I don't want to here ur mouth again" shiru khadijah tayi, daga karshe dai wata mata da ta gansu suna ta yawo ce ta tambayesu gidan da suke nema, Umma tayi shiru tana tuna sunan da aka fi sanin yakumbo da shi, can tace "Kulu mai waina" Matar tace "Ikon Allah, yo ai ga gidan can kun wuce" Umma ta juya tana kallon gidan da matar ke nuna mata, matar tace "Wancan gidan mai keke a gaban sa" Umma tayi murmushi tace "Kin ga kuwa sai yanxu na gane, gaskiya na nagode sosai" daga haka suka juya khadijah na biye da ita a baya, tsallake gutter din dake kofar shiga gidan Umma tayi Khadijah ma ta yi haka sannan suka shiga xauren gidan, gida ne ginin kasa duk ya kwarabe, Khadijah ta xaro ido tana bin gidan da kallo, Yakumbo ce xaune tsakar gida tana hura icce duk hayaki ya cika ko ina, Umma tace "Yaya" dagowa yakumbo tayi ta xaro ido tace "Aminatu" karasawa Umma tayi ta rungumeta tace "Rai kan ga rai yaya" cike da farin ciki Yakumbo tace "Sannu da xuwa Amina, daga ina haka? ya mai gidan naki?" Umma tace "Wllh daga kano Yaya, yana nan lafiya yace duk a gaida ku" Yakumbo tace "Maa sha Allah sai dai kin rame kan lokacin bikin, wacece wancan" Yakumbo ta fada tana nuna Khadijah, A hankali Umma tace "Yar marigayin mijina ce Alhaji Muhammad" Yakumbo ta rike haba tace "Ikon Allah gashi ta kusa xama budurwa, sun hakura sun baki ita kenan?" Umma tace "uhn, labari ne me yawa yaya bari dai mu yi sallah" Yakumbo tace "Gaskiya ne bari in kawo maku ruwa" tabarma ta fara shimfida masu kafin ta tafi debo ruwan alwala, Umma ta xauna ta nuna ma khadijah dake tsaye gefenta, khadijah ta karaso tana tsattsallake bololin dake watse tsakar gidan, Umma tace "yaya ina mutan gidan?" Yakumbo tace "Toh jikokin nawa sun fita wasa, tun safe rabona da su, yaran makwabtana kuma duk sun tafi talla, iyayensu kuma aikatau suke na yini, Ladi ce kadai ta shiga makwabta daxu, nima anjima xan fita suyan wara da dankali a bakin titi" shiru Umma tayi jikinta yayi mugun sanyi, yakumbo ta kara da cewa "Ai Allah ma yyi ban tashi a gidan nan ba kika xo, don duk mai gidan ya ba mu notice xai rushe gidan wai, to gida ne duk ya rube" Umma ta kalleta da sauri tace "Ina xa ku koma yaya?" Yakumbo tace "Oho dai har yanxu ina lalube ne, kudin kama wani gidan ma ai xaune yake da kugunsa, talauci yyi yawa ta ko ina, ko daxu na fita duba gida don sati daya ya ba mu xai watsar mana da kaya waje" Umma tace "Ikon Allah" Yakumbo tace "Ai ke dai kawai sai du'a'i duniyar ta xama abinda ta xama" Yakumbo ta kalli khadijah da ta takure gu daya tace "ke yar nan tashi ki fita waje gun mai kanti ki siyo min farin maggi" Umma tace "Yaya ai bata san ko ina ba" Yakumbo tace "Ka ji ki, nan nan ga masu kanti kamar jampa a jos ta ko ina a anguwar nan, tana fita duk inda ta bi akwai mai kanti" daga haka Yakumbo ta kunce kullin xaninta ta fiddo wani naira ashirin dake a dunkule ta jefa ma khadijah, mikewa khadijah tayi ta karasa ta duka ta dau kudin tana kallon Yakumbo tace "How much own" yakumbo ta d'an bude ido tace "Eh??' Umma tace " twenty naira" khadijah ta juya ta fita, yakumbo tace "Sai na ji kamar yare tayi" Umma tayi murmushi tace "Turanci tayi" Yakumbo tace "Au tohhh abun na manya ne Ashe" ita dai Umma bata ce komai ba ta mike taje tayi alwala ta dawo tayi hau kan tabarman ta tada sallah, jin shiru shiru Umma na idarwa ta bi bayan khadijah, a bakin xaure suka kusa cin karo Umma tace "Ina magin kuma me ya sa kika dade?" Khadijah tace "Umma I've forgotten the one she mentioned" Umma ta hade rai tace "Bani kudin" mika mata khadijah tayi ta umma ta koma ta dau dari a Jakarta ta fita, farin magin hamsin ta siyo mata da maggi star saba'in sannan ta dawo gida, garau garau na dafaduka Yakumbo ta girka masu, ta xubo a faranti. Umma kadai ce ke cin abincin a sanyaye tana tausayin khadijah dake tsintar shinkafar, yakumbo kuwa na ta yankan warar da xata fita soyawa kamar yanda tace suna yi suna hirar xumunci da yar uwarta, la'asar nayi Yakumbo ta kira almajiri ya kai mata kayan bakin titi gun da take suyar, Tana kokarin saka Hijab dinta da yyi dukun dukun tace "Toh Amina xan fita kasuwa, idan kun ji yunwa ku kara deban abincin, sai ki d'an taimaka ki share min daki ki fiddo kayan wanke wanken ki ajiye su bakin kwararon can ko yarinyar nan ki sa tayi" Umma tace "Toh yaya, amma fa har yanxu yaran basu dawo ba" Yakumbo tace "Rabu da gantalallu suna makwabta na sani, idan yunwa ta kwakulesu xa ki ga sun dawo da daddaya da daddaya" daga haka yakumbo ta fita rike da roban dake dauke da dankali a ruwa, Umma ta bi ta da kallo, Khadijah ta yatsine fuska tace "Umma the food is somehow" Umma ta hade rai tace "Haka nan xa ki ci, ko ni ma baki ga hakan na ci ba" Khadijah bata ce komai ba, Umma ta mike ta shiga d'an karamin dakin yakumbo, har wani wari dakin yake gashi bbu ventilation don windown dan karami ne, ga kaya ta ko ina, plastern dakin duk ya faffashe gashi ko leda babu, jikin umma yyi sanyi ta daga dan karamin katifar da tayi bakikirin ta shiga gyaran dakin ta fidda duk kwanukan da har da funfuna jikinsu sannan ta fara sharan dakin. Ko da ta fito bayan ta gama bacci ta tarda khadijah na yi, ga shinkafar ta bar sa, Umma ta tada ta ta bata Dari biyu tace "Kije kantin da kika je daxu ki karbo Nutri milk da biscuit din hamsin ki xo ki ci" Karba khadijah tayi ta fita. Sai kusan karfe biyar jikokin yakumbo uku suka dawo gidan sun yi dukun dukun da dirty, duk kanana ne yaran, Umma ta masu wanka da sabulun wankin da ta gani, ta xuba masu abinci, Khadijah dai na xaune sai kallonsu take da wani expression, nama Umma ta fita ta nemo a anguwar ta xuba masu kan abincin ko khadijah xata ci, nan ta tsince naman ta bar mata shinkafar wai ta koshi, sai dab da Isha yakumbo ta shigo gidan tare da Almajiri da ya dauko kayan suyanta, Sannu ta dinga ma su Umma, Umma ta mike ta taya ta karban kayan.... sha dayan dare bayan su khadijah sun yi bacci Umma ta shiga yi ma Yakumbo bayanin abinda ya kawo ta da Khadijah, bayan yakumbo ta gama saurarenta tace "Ikon Allah, mugunta fa yyi yawa a duniyar nn yanxu ki kuluwa" Umma tayi shiru bata ce komai ba, Yakumbo ta kyabe baki tace "Toh ni wannan ai ba matsala bace, don dai in rike marainiya, bakomai wllh" Dubu 30 Umma ta kirgo ta ba yakumbo tace "Wannan sai ki siya kayan abinci da indomie ki ajiye yaya" makaranta kuma ayi mata Register da ta gwamnati idan Allah ya hore min sai in canxa mata, dubu ashirin ta kuma bata tayi ma khadijah siyayyar makaranta, yakumbo ta dinga godiya kamar ita ta ba kudin, sai kusan karfe daya suka kwanta bayan yakumbo ta gama tsine ma matan mijin Umma, da su kawu. Washegari da safe Umma ta dau hanyar kano bayan ta rubuta ma Yakumbo lambarta kan cewa duk inda suka koma ta sanar da ita in case xata dawo duba khadijah, dubara aka ma khadijah aka aiketa daga nan Umma ta samu ta bar gidan duk jikinta a sanyaye, da Khadijah ta dawo ta kyallara ido taga ba umma ta dinga ihu tana kuka a gidan tana cewa a kai ta gun ta, Bakin yakumbo a leko ta dauko muciya tace "Kin ga wannan abun hannu na? To wllh da shi xan fasa maki kai idan kika ci gaba da tona min asiri a anguwa, kaji min katuwar banxa, maxa ki tafi tare da Fauxiyya ku siyo min ice da xan yi tuyan awara anjima" Jikin khadijah na bari suka fita, matan gidan dake ta kallon ikon Allah suka ce "Yo ke kulu da kike jiran fauxiyya ta kara wayo ki kai ta aikatu kina samun kudi don me baxa ki kai wnn budurwar da aka kawo maki ba? Ai wannan da ganinta bbu aikin da baxata iya ba har wanki" Yakumbo tayi shiru tana kallonsu. Ko da suka dawo gidan firewood kwara biyu kadai khadijah ta riko a hannu, fauziyya kuma ta rike ya kusa shidda, daga matan gidan har Yakumbo sakin baki suka yi suna kallon Khadijah da ta ajiye tana haki, yakumbo tace "Meye wannan din kika dauko?" Da kyar khadijah tace "Firewood, it's too heavy, and it's pricking me all over" a fusace Yakumbo tace "Kin ma uwar ki Amina turanci ba ni ba, kuma ke kadai xaki koma ki kwaso duk wanda ga rage fauziyya baxa ta je ba tunda ba ki da mutunci" korata Yakumbo tayi ta fita ta na share hawayen dake sakko mata, mai firewood din ganin yanda take hawaye kuma kana ganinta kasan baxata iya dauka ba ta dauko wani rabanta ta xuba mata su a ciki ta daura mata a kai tace "Kina kai wa ki dawo min da roba na kin ji" a hankali khadijah tace "Toh nagode" A haka ta isa gida tayi ta tsayuwa da roba a kai wai bbu ke sauke mata inji Yakumbo, daga karshe ladi ta kike ta sauke mata tana cewa "Idan ka xa ki kama jiki ki kama jiki ki daina ma mutane kamar mara laka a jiki" Khadijah dai bata ce komai ba, bayan ta juye iccen tace ma yakumbo xata mayar da roban, ko kallonta yakumbo bata yi ba ta juya ta fita kai ma mai iccen robar ta. Yakumbo ce tsaye tsakar gida bayan kwana uku da xuwan su Umma, tafi minti talatin banda kumfar baki da masifa bbu abinda take, ga matan gidan da yaransu a xaune babu mai bata hakuri sai ma xugata da suke, khadijah kuma na tsaye bakin xaure duk tayi wani duhu ta rame sosai, idonta duk ya kumbura don kuka ga shatin bulala a jikinta, Ladi tace "Yo da kinsan haka ne tun farko kema ai baxa ki fara daukarta ba, meye amfanin yaron da baxa ka amfana da shi ba sai shegen son jiki da iyayi, ai kadan ma kika mata da kin hada kin fasa shegen bakin turancin da take xagin mutane da shi a gidan nan" Yakumbo na huci tace "Ai Amina ta cuce ni, ta yaudare ni... Tasan haka shegiyar yar take xata kawo min ita tun farko, gode gode da yarinya bata iya komai ba wanke wanke duk ta jika kayan jikinta tayi awa da awanni a bakin kwararo, shara duk a gantale, gyaran daki gwara ka da fauziyya mai shekara biyar, aike sai kayi yyi sau uku, har yau ta kasa iya hura icce, girki dama ba a maganar sa, wa ennan yan mitsimitsi yaran idan na sa ta tayi masu wanka ta shaka masu sabulu a hanci ko a ido, ni dama tun farko abinda ya sa na karbeta na yi xatan xan amfana da ita ne, banda haka me xai kai ni kowa na ta kansa a rayuwar nan gashi gobe ko jibi xa a xo a fitar mana da kaya har ynxu ban kama wani gidan ba, ni wllh wllh da nasan gidan Amina sai in yi kudin mota in mayar da ita ta bani kudi na don baxan iya kayan tsiya ba, dama can Aminar ma ba wani kyautata min take ba uba ne kadai ya hada mu" Salamatu tace "Ai irin yaran nan kyansu aikatu wllh, a can xa a horasu su ladabtu...." Katse ta yakumbo tayi tace "Yar da har yanxu bata iya shara ba xan kai aikatau, ai koramu xa ayi daga ni har ita" Ladi tace "Yo ke nuna masu xa ki yi bbu abinda bata iya ba ai, a can xa su gyara mata xama ta iya komai, mutanen da basu san darajar d'an Adam ba, ai tuni wahalar da xa su dinga mata xai sa ta xage a nan kuma xata koyi komai, wannan d'an abincin da kike bata ma take kin ci take yawo da yunwa can nema xata yi ta rasa, hakan xai ladabtar da ita wllh" Yakumbo ta ja kujerar tsugunno ta xauna tace "Kai amma fa kun kawo shawara, amma...." Sai kuma tayi shiru ta kalli khadijah dake kallonsu, tsawa tayi mata ta ce "Fita ki ban waje kije gun mai kanti da hamsin di ta dake gunsa ki amso min barkonu" juyawa khadijah tayi da sauri ta fita gidan, Yakumbo ta mayar da dubanta gun su Ladi tace "Toh Amina fa? Kunsan baxa ta yarda ba" dariya Ladi tayi tace "Ka ji ki, sai ki gaya mata, barin ma yanxu tashi xa ku yi Ku bar anguwar, shawara a nan shine kada ki kuskura ki gaya ma ko inda kika koma a anguwar nan, kawai cewa xa ki yi ba ki ma samu gidan ba gidan wata yar uwarki xa ki kafin ki samu, ke kuwa kije shanono abun ki ki kama ko daki daya ne bbu wanda yasan inda kike, dama ba waya gare ki ba, har ki tara kudin da xa ki tara da yarinyar daga nan idan ma mayar da ita gun Aminan xa ki yi sai ki ja mata kunne ki mayar da ita" Yakumbo tayi murmushi tace "Dadina da ku akwai shawara mai ma'ana, amma fa har da kudin da xan sa yarinyar a makarantar gwamnati ta bani, yanxu haka ma da kudin xan je kama haya a shanonon, dubu hamsin kuma jari xan ja na su omo da sabulu ina siyarwa, ita can na kai ta gun aiki ana biyanta dubu uku misali, kun ga ni ban ma kai da nisa ba...." Ladi tace "Toh gaskiya sai kin ba mu dubu dai dai mu da muka kawo shawarar Ashe ma kudi gare ki har haka" yakumbo ta hade rai tana da ta sanin gaya masu, rai a bace tace "Dari bibbiyu dai" daga haka ta mike ta shiga cikin akurkin dakinta, sai ga ta ta fito da sauri tace "Toh yanxu wa xai min hanya in kai ta gidan aikin, don ni gaskiya baxan tare da ita a sabon gidana ba, ko yau aka samu gun aikin ba don yamma yyi ba kai ta xan yi, don haka gobe da safe xan kai ta...." Ladi tace "Akwai wata kawata Habiba dillaliyarsu ce, xan baki lambarta... Ko kuma ki sa katin dari a wayata mu kirata, in sha Allah nasan baxata rasa inda xata kai maki ita ba" hakan ko aka yi Yakumbo ta sa kati ladi ta kira Habiba, suka ci sa'a number ya shiga, bayan ladi ta gaisa da kawartata tace "Bibalo dama wata yarinya ce da ake son kai ta gidan aiki to shine muke son ki yi taimako" Bibalo tace "Kai yanxu haka Ina hanyar dawowa daga kauye na mayar da wasu yara, amma gobe da safe xa ki gan ni duk da bani da wa enda ke son masu aiki yanxu, amma nasan kawata Abu baxata rasa ba don ta ma fi ni sanin gidajen manya" daga haka suka yi sallama ladi ta katse wayar tana kallon Yakumbo don ba sai ta mata bayani ba tunda a handsfree tasa ita ma ta ji komai, Yakumbo tace "Toh Allah ya sa a dace, ni wllh ko dubu biyu ma xa a dinga biyanta na yarda" tagumi tayi tace "Allah gani gare ka, kasa a karbi yarinyar nan ni kuluwa" Washegari da safe kuwa sai ga Bibalo tare da kawarta da ta fada Abu, Yakumbo dake ta washe hakora ta gaishesu suka amsa aka xaxxauna kan tabarma ladi ma ta fito akurkin ta tana masu sannu da xuwa, bayan sun gaisa Bibalo tace "Toh kinga ni bni da inda xan kai ta amma Abu tace kawarta ta taba hadata da wata Hajiya mai neman mai aiki, da xata dinga share share da goge goge sannan wanke wanke, akwai ma wata babbar mai aiki dake girki a gidan, to Abu taje gidan ya fi sau uku ba a bude mata gate, yanxu ma gwada sa'a xa ayi kuje har da ke kika wajen, idan sun dauketa to, idan kuma sun ce A'a sai ki jira har a bukaci mai aiki a wani gidan sai in kai ta" Yakumbo tace "A'a mu je kawai mu gwada sa'ar mu" Bibalo tace "Toh ki sallame ni ni xan wuce" Yakumbo ta hade rai tace "In sallame ki? Me kika min da xan sallame ki" Bibalo ta bude baki tace "Au haka ma xa ki ce, shi kudin motar da nayi da kuma bata lokacina da na yi na xo nan tare da kawata har xa ki ce min me na maki" mikewa Yakumbo tayi rai a bace ta shiga ciki ta fito da dari biyu tana cewa "Ko daukar yarinya ba ayi ba xaki wani ce in sallame ki idan ba hadama ba" dungura mata dari biyun tayi a gabanta rai a bace, Bibalo ta dauka ta mike tace "Ya fi babu ai" daga haka ta yi ma Ladi sallama da Abu tayi ficewarta, Abu tace "Toh inji kinsan mu dubu daya ce sallamar mu?" Yakumbo ta hade rai tace "Idan an dauki yarinya ba" Abu tace "Toh gwara da kika san haka don ni baxan tsaya cacar baki ba, yanxu Ina yarinyar take?" Yakumbo ta nuna mata khadijah dake ta fama da wanke wanke, kwalalo ido tayi tace "Warcen da ta fi minti ashirin tana d'an wanke wanken can, tun shigowar mu fa take wanke wanken kamar ayi kamar baxa ayi ba" yakumbo ta marairaice tace "Haka take Abu, akwai iya aiki amma ba sauri ne kawai, amma tana xuwa can nasan xa su gyara mata xama ta xama mai hanxari" Abu ta tabe baki tace "Toh unguwar da nisa, don can Gra ne, kuma wllh gidan babban mutane ne, ni dai Allah ya sa su dauketa, yanxu sai ki tashi ku shirya ta hada kayanta ina jiran ku mu kama hanya" Yakumbo ta mike da sauri ta shiga ciki tana cewa "Toh bamu minti biyar kacal" tana shiga dakin ta kwalo ma khadijah kira, khadijah ta mike ta shiga da sauri. Yakumbo ta jawota tayi kasa da murya tace "Dijangala ta mai gari, ba auren talaka ba" tana washe hakora ta fadi haka, ita dai khadijah kallon ta kawai take, Yakumbo tace "Kinsan inda xa mu yanxu kuwa?" Girgixa kai khadijah tayi, Yakumbo tace "Gidan da xa a dinga biyanki kudi mai yawa in tara maki in sa ki a boko, kai har in maki aure ma" khadijah tayi shiru bata ce komai ba, yakumbo ta marairaice tace "Don haka muna xuwa kice kin iya aikin komai, sai ki bada himma idan an saki aiki ki yi da sauri da sauri, sannan don Allah Idan mun je gidan khadijah kar ki masu wannan yaran naki na turanci kin ji koh? Kawai Hausa xa ki masu, idan kuma baki san Kalmar da xa ki fada da hausa ba sai kiyi shiru abun ki ba sai kin yi turancin ba" yanxu maxa canxa kayan Ki bari in tusa maki wa encan a jaka tunda basu samu wanki ba idan kin je can ko ba ki iya wankin ba ki tsoma su a ruwa ki xuba omo ki shanya" daga haka Yakumbo ta shiga tusa kayanta a wani karamin Ghana must go, don har ta siyar da jakar da Umma ta kawo mata kayanta ciki, karfe tara da kusan rabi su yakumbo suka bar gidan tare da Abu bayan ta yi ma yan gidan sallama suka dinga yi mata Allah ya bada sa'a, tana rike da hannun khadijah suka isa bakin titi, Abu tace "Amma kinsan ke xa ki biya kudin abun hawa dai koh?" Yakumbo ta tsuke fuska tace "A kan me?" Abu tace "A'a mayar da wukar ae dai naga ba xuwan kai na xan yi ba gidan don hka idan kinsan gidan ke sai ki kai ta, yakumbo ta rikota da sauri tace "Naji, mu je ya na iya, daga yau ai babu wanda xai xo yace in biya masa kudin napep dai koh?" Ko tanka ta Abu bata yi ba ta shiga napep din da ta tsayar, Yakumbo ta shiga ta daura khadijah a cinya. Tafiya ce mai nisa kamar yanda Abu tace masu, tun da suka bar hayi dama Yakumbo ke addu'ar Allah ya sa a dau khadijah gidan aikin idan ba haka ba asirinta ya tonu don ta sa rai da kudin da xa a dinga biyan khadijah, tun da suka shigo anguwan Yakumbo ta saki baki kamar yawu xai dalalo tana kallon gidaje na alfarma, Abu ta dinga nuna ma Mai napep din inda xai bai, har suka iso wani cool silent anguwa mai cike da shuke shuke a ko wani gate, ga bakin kwalta a shimfide daga farkon layin har inda yakumbo ke tunani karshe ne, bakin wani gate Abu ta sa mai napep din ya tsaya, yakumbo ta wage baki tana kallon jibgegen gidan da aka yi ma ginin xamani kamar ta sure ta gudu, gidan ya hadu ne kawai don ita a ganinta duk ya fi sauran gidajen dake layin haduwa, suka sauka sai kuma Yakumbo aka tsuke fuska da ta tuna kudi xata bada yanxu, ta dungura ma mai napep din kudin da yace lkci daya kuma tana hararan Abu, Abu da ko lura da ita bata yi ba tace "Toh Allah ka bamu sa'a don kwanaki da na xo haka na sha xamana bakin gate rana yayi maganina ban samu shiga gidan ba... Yakumbo tace "Yana da kyau mutum ya dinga fadin alkhairi ko yayi shiru, yanxu me ya kawo wannan xancen, in sha Allahu ma sai mun shiga don haka ki mana shiru" daga haka Yakumbo bta kwankwasa gate din a hankali kamar me tsoron kada ya fashe don ita fa gani take kamar glass ne a kauyancinta, ta kwankwasa ya kai sau hudu kafin wani da alamar mai gadi ne ya bude yana kallonsu, Yakumbo ta durkusa har kasa ta gaishesa, yace "Wa ku ke nema?" Yakumbo ta mike tace "Matar gidan muke nema ce mana tayi mu samo mata mai aiki yarinya karama, to cikin ikon Allah gashi mun samo mai haxaka, shine muke hadaka da Allah yaro ka bar mu mu shiga, mu gabatar mata da aiken da ta mana" ya girgixa kai yace "Ai akwai mai aiki yanxu haka a gidan don haka ban ji xa a bukaci warce xa ku kawo" Bakin yakumbo ya fara rawa tace "Wllh xa su bukata dubeta fa kaga bbu abinda bata iya ba, sannan Hajiyar da kanta ta sa mu ko daxu mun yi waya da ita tace sai mun xo, haba yarona ka duba tsufana mana gashi daga hayin rigasa muke wllh" Mai gadin yace "Toh yanxu ma ku kirata idan tace ku shiga toh shkkn" daga yakumbo har Abu aka hadiye yawu da kyar don babu mai waya cikinsu, Yakumbo tayi karfin halin cewa "Wallahi wallahi na mance wayar a gida kaji rantsuwar musulmi" Abu ta saki baki jin rantsuwar da Yakumbo tayi alhalin taji Bibalo tace bata da waya.