NOOR AL HAYAT 51-60

Jannah….” Jin Khadijah tayi shiru ya dago kanta a hankali yana kallonta, a hankali yaji tana neman sulalewa hannunsa yaki saketa, a haka ta suma yana rike da ita. A hankali khadijah ta bude idanuwanta bayan lokaci me tsawo, kwance take kan gado ta dinga bin mutanen dake xaune dakin da kallo, Wata kawar Umma ta taso ta dawo kusa da ita ganin tashi take son yi ta taimaka mata ta xauna, da kyar tace “Anty me ya ke faruwa?” Umma tayi karfin halin xuwa kusa da ita ta xauna tace “Ya jikin khadijah” shiru khadijah tayi tana ta kallon umma, lkci daya ta fasa ihu ta mike ta fice daga dakin da gudu suka bi ta, Aliyu ne ya fara mikewa a compound din ganin ta fito, ga maxa ko ina, Khaleel dake rungume da Shureim dake bacci jikinsa ya dinga kallonta amma ya kasa tashi, haka barrister sudais, tana ganin Aliyu ta taho gun sa ta rike hannunsa cikin matsanancin kuka sosai tace “Aliyu don Allah kar ka ce min sudais ya mutu, you assured me he will be fyn, kar ka ce min ya mutu don girman Allah” kasa cewa komai Aliyu yyi yana kallonta, ta rungume sa tana kuka kamar ranta xai fita tace “Ka ce min bai mutu ba Aliyu, wllh ina son sa, kar ya tafi ya bar ni” Aliyu ya ja ta suka bar wajen xuwa inda babu mutane ya xaunar xa ita ya durkusa yana kallonta, a hankali yace “Iman kin san Allah xai baki shi?” Ta girgixa masa kai hawaye na xuba idonta tace “A’a”
*Sorry if I disappoint anybody*