NOOR AL HAYAT COMPLETEUncategorized

NOOR AL HAYAT 51-60

Sai da sudais ya gama kallon d’an uwan nasa sosai kafin ya kai masa mari yana huci yace “How dare you call me that” Aliyu na ganin shureim yayi kan sudais ya daga sa sama ya rungume sa a hankali yace “Yi hakuri ka kyalesa sweetheart” kuka shureim ya fara yi hana sa dukan sudais da Aliyu yyi, Sudais na huci yace “I don’t like you both” dai dai fitowar Nanny daga shago, da sauri ta karaso tana tambayar me ya faru ganin shureim na kuka hannun Aliyu, sudais ya fashe da kuka shi ma yace “Nanny shureim started 1st, he insulted me” Nanny ta hade rai tace “Ohh har cikin market din ma sai kayi fada sudais, kai dai baka ji kuma nasan kai ka fara tsokanarsa ba ruwan shureim, silly boy kawai from henceforth bana sake xuwa ko ina da kai, ko kace xaka bi ni sai na ma duka” juyawa sudais yyi ya fashe da matsanancin kuka da gudu ya bar wajen xai je gun uwarsa, bin bayansa Nanny tayi tana kwala masa kira don ta can tsallake khadijah take kuma titin is very busy, amma sudais yaki tsayawa kuka kawai yake yana gudu yana kiran Anty, Aliyu na ganin haka shi ma ya bi su da sauri shureim na hannun sa, khadijah dake cikin mota tana xaune maxaunin driver don ita ta kawo su kasuwar haka nan kawai taji gabanta ya yanke ya fadi dai dai lkcn da taji ihun da mutane ke yi, tana juyawa kawai ganin Sudais dinta tayi a tsakiyar titi shi ma duk ya rikice ihun da mutane ke yi, ga mota har biyu sun taho da gudu ko wanne na son kauce masa, tunda take bata taba irin ihun da tayi ba a lkcn, lkci daya ko ina na kasuwan yyi tsit don duk yanda motar ta so avoiding sudais hakan bai yiwu ba, sai kuma a ka dau salati Khadijah ta fito a rikice jikinta na rawa ganin sudais kwance cikin jini ta fasa wani ihu kanta na juya mata, suman da ya kamata tayi nanny ce tayi sa a lkcn, ita kanta bata san me ya hanata sumewan ba, Aliyu da yyi still shi ma ya kasa motsi na few seconds ganin abinda ya faru lkci daya yaji strength ya dawo masa, ya ajiye shureim dake ihu yana kiran dan uwansa ya nufi gun sudais dake a kwance kan titi cikin jini mutane sun taru kansa mata na kuka maxa na salati, har da kyauta cikin mutanen, babu rabon Anty khadijah xata ga abinda ya faru don tsabar kunya bata jira Aliyu ya fito ba ta hau adaidaita da baby suka koma gida, cikin tashin hankali Aliyu ya karbi yaron hannun wani mutumi dake jijjigasa yana salati, a nan Aliyu yaji kamar bai taba xama likita ba duk rayuwarsa gaba daya basira ta dauke masa ya rasa ya xai yi da sumammen yaron dake hannunsa fuskarsa duk jini, cikin matsanancin kuka khadijah ta isa gun ta wani fasa ihu a gigice ta durkusa jikinta na rawa take cewa “Na shiga uku, don Allah ku taimakeni kar ya mutu ku rufa min asiri, kar ku bari ya mutu” daga kai Aliyu yyi a karo na farko yana kallonta jin muryarta, lkci daya signal dinsa ya sake daukewa yana mata wani irin kallo ita kuwa sai jijjiga sudais take ba tare da ta kula a hannun wa yake ba tana kuka tana cewa ya tashi kar ya tafi ya bar ta, kyauta ta saki salati baki bude tana kallon khadijah tace “Kamar khadijah nake gani ni kyautar Allah” khadijah ta kalleta ita ma da sauri, da gudu ta nufe ta rikota tana kuka cikin rauni tace “Anty ku taimake ni kar ya mutu don Allah, kar ya tafi ya bar ni” Kyauta ta kwalalo ido tace “Yaron ki ne Khadijah?” Khadijah ta dinga gyada mata kai tana kuka sosai, kyauta ta fashe da kuka tace “In sha Allahu baxai mutu ba xa mu tafi asibiti yanxu khadijah, baxai mutu ba…” wata mata ta fixge yaron a hannun Aliyu a mugun fusace ganin khadijah kawai yake kallo tace “Dubi mutum kamar an dasa sa a gun ya sa yaron da ba mu san ko ya mutu ba ko yana raye a gaba yana kallo, wannan wani irin uba ne kai, ni na xata taimkon gaggawa xai bada….” Khadijah ta tsayar da kukan da take ta sake kyauta ta nufi matar ta rikota cikin rudewa tace “yaro na bai mutu ba kar ki kara cewa ya mutu don Allah kar ki kara, wllh bai mutu ba, Allah baxai sa ya mutu ba” sosai ta ba mutanen gun tausayi wani mutumi ya sa sudais tare da matar a motarsa domin xuwa asibiti, mutumin ya kamo hannun Aliyu dake tsaye yana kallon khadijah da har sannan bata lura da shi ba yace “kar ka damu he will be alright in sha Allah shiga mu je asibitin tare” bayan motar Aliyu ya shiga suka dau hanyar asibiti, sai a sannan basirar sa ta likita ya dawo masa ya karbi sudais a rude ganin numfashinsa na sama ya dinga basa numfashi, banda kuka babu abinda matar dake kusa da shi take tana addu’ar Allah ya raya sa, jin mutumin dake ta sharara gudu a mota yyi parking Aliyu ya dago kai tare da bude motar ya ga asibitin da yake aiki ma mutumin ya kawo su, Aliyu ya fita rike da sudais yyi cikin asibitin da sauri nan aka shiga emergency da yaron, sai bayan kusan minti talatin Aliyu ya fito tare da wani likita daga emergency ward da aka shiga da sudais suka bar likita daya a kan sa da nurse, Dr Saif ya nufi gun su khadijah dake xaune reception da kyauta da wasu mutane har sun gaji da lallashinta don ko tayi kuka har ta gode Allah, tsabar tashin hankali ko gane asibitin bata yi ba, shureim dake jikinta ma kukan yake yana tambayarta me ya samu sudais, Nanny da ta suma an kwantar da ita asibitin ita ma, mikewa khadijah tayi da sauri ganin likitan, Aliyu ya tsaya daga inda yake har lkcn mask na bakinsa da hanci, Dr Saif yace “Ina mahaifiyar yaron?” Khadijah dake kallonsa gabanta na faduwa tace “Ni ce” Aliyu ya cire mask din dake fuskarsa yana kallon khadijah da wani irin mamaki, at the same time confusion, likitan ya tsaya kare mata kallo kamar bai yarda ba, can dai yace “Toh mahaifinsa fa?” Tana share hawayen dake xubo mata cikin rawar murya tace “Baya nan” likitan na kallon Shureim ya xaro ido yace “Subhanallah yan biyu ne?” Cikin kuka khadijah ta gyada masa kai, jikin likitan yyi sanyi sosai, ya shafa kan shureim dake kuka yana rike da mayafin Khadijah a hankali yace “Don’t worry my boy ur twin will be okay in sha Allah, madam xa ki iya shiga ki gansa amma plss kar ki wani damu ciwo ne kawai yaji a kai sai bruises, so don’t cry while inside, shi kuma wannan ki bar sa a nan ba sai kin shiga ba” daga haka ya juya yana kallon Aliyu dake nesa da su kafafuwarsa sun kasa daukarsa saboda shock yace “Dr plss see her inside, amma kar ta dade a ciki” daga haka ya kama hannun shureim yace “Big boy xo mu je office ka jira mumy” shureim xai masa taurin kai sai ya bi mamarsa ya daga sa sama kawai ya wuce office dinsa da shi don bai son ya ga dan uwansa a halin da yake ciki yanxu, Tuni Aliyu ya mayar da mask din fuskarsa yayi gaba kamar me counting step dinsa Khadijah na biye da shi a baya, tsabar tashin hankalin da ke tare da ita bata ko kalli wanda take bi ba balle ta san waye. Suna shiga ward din Aliyu ya tsaya bakin kofa ita ta shiga ciki gabanta na faduwa, ko gama ganin sudais bata yi ba ta fasa wani ihu, Nurse din ta karaso da sauri ta fitar da ita dakin tace “Haba madam, sai kace ba musulma ba wannan ihu haka” khadijah ta fashe da matsanancin kuka tana jijjiga nurse din tace “Don Allah Anty kar ku bari wani abu ya samu yarona, they all I have, plss ku taimake ni” rungumeta nurse din tayi tace “It’s ohk madam jikin ai da sauki, you just pray Allah ya tashi kafadarsa kuma kada Allah ya sa ya tashi da wata matsala” Khadijah ta xame kasa tana kuka tace “Na shiga uku wllh kilan mutuwa xai yi ya bar ni, don Allah ku taimaka min” juyawa nurse din tayi ta koma ciki ta rufe kofar, Aliyu ya kasa ci gaba da kallon khadijah lkci daya idonsa ya kada, yaranta? To waye ubansu? Abinda ya dinga masa yawo a rai kenan, kawai ya ga ta mike ta nufo sa, kana gani kasan ta gaji da kukan ta riko sa cikin rauni tace “Plss Dr kar ku bar min yarona ya mutu don Allah ina rokan ku, they are all I’ve got in this world bayan ummata, plss ka taimaka Dr ku cire masa abinda ku ka sa masa a hanci ina son yarona” Aliyu ya kasa ce mata komai lkci daya hawaye ya kawo idonsa, da ba don a rude Khadijah take ba bbu abinda xai hana ta gane Aliyu ne gabanta saboda kwayar idanuwansa amma saboda tashin hankali bata gane ba ganin, hawayen idonsa ta tsayar da kukan da take xuciyarta na bugawa tana kallonsa ko kiftawa babu, bayan few seconds cikin sanyin murya tace “Dr ya mutu koh?” Aliyu bai iya yace komai ba ya ji ya kasa controlling kansa hawaye suka shiga sakko masa, he don’t want to believe Khadijah conceived with him, he don’t want to believe she conceived that deadly moment, if so then he is not worth to be forgiven, bai cancanci ta yafe masa ba, don ya mata xaluncin da dole baxata iya yafe masa ba, sai a sannan maganganun da Anty khadijah take a waya daxu ya fara dawo masa, ya juya ya hade kansa da bango yana hawaye sosai duk ya ji ya tsani kansa, yanxu yaran nan nasa ne kenan?? He is there illegal father, the cute boys… Are his and Khadijah’s, they got them out of wedlock…. Lkci daya ya juya ta dalilin sound da ya ji bayansa, nan ya ga khadijah sume a kasa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button