NOOR AL HAYAT COMPLETEUncategorized

NOOR AL HAYAT 51-60

Kallonsa Khadijah take ko kiftawa babu, bakin ciki da takaici ne fal idanuwanta, xuciyarta ya dinga mugun bugawa, ta hadiye abu da kyar, lkci daya idanuwanta suka yi jajir cikin muryar da ba ta ta ba tace “Come again Aliyu… I didn’t get you” Cire mask din bakinsa yyi gaba daya yana kallonta da kyau cikin husky voice dinsa yace “You are not daft Iman, you heard me right, or you ask ur bodyguard xai maki bayani da kyau” bai rufe baki ba ta sauke masa mari tana huci, wani murmushi khaleel yyi yana shafa sajensa yace “Seems you both need privacy” daga haka ya juya ya bar wajen har sannan yana murmushi, Aliyu ya kauda kansa na few seconds kafin ya juyo a hankali yana kallonta da wani irin mamaki, hawaye na sauka idonta tana girgixa kai tace “Allah ya isa tsakanina da kai Aliyu, shari’ar mu da kai dama na fada maka sai a lahira, kuma yarana ba naka bane, ba kai ka haifar min su ba, you don’t have any right over them, idan duk duniyar nan xa su hade nan wlh wllh baxan baka su ba, ni na sha wahalan kayana ni na haife su, baka isa ka raba ni da su” ta fashe da matsanancin kuka xuciyarta na mata xafi, hakan yasa su shureim ma suka fara kuka suna rike da ita, kallonta kawai Aliyu yake da idanuwansa da suka yi jajir, ganin khaleel ya bar wajen khadijah ta kama hannun yan biyun ta da sauri ta juya xata bi bayansa Aliyu ya fixgota yayi jamming kofar yana mata wani mugun kallo, lkci daya ta cakumosa tana kuka mai taba xuciya tace “Ka bude mana mu fita Aliyu, ka bude kofar in fita da yarana kar in tara maka jama’a” yanda ta rikice haka yaranta ma suka rikice suna kuka, daukar ta Aliyu yyi ya nufi bathroom dake ward din ya tura ta ciki yace “I will teach you sense Khadijah….” daga haka ya rufe kofar da makulli ta dinga bubbuga kofar a rude tana kuka tana kiran sunansa, Sudais ya kara fashewa da matsanancin kuka yace “Why are you doing this to our Anty, plss let her out” Shureim ya dinga bubbuga kofar shi ma yana kuka yana kiran ta, Aliyu ya hade kansa da bango ya runtse ido xuciyarsa na bugawa, lkci daya ya juyo ya kama hannun yaran gaba daya suna turturjewa ya watsa masu wani mugun kallo da idanuwansa da suka yi ja, ba shiru suka yi tsit ko wanne a tsorace, ya bude kofar ward din ya fita da su, ward na intensive care ya shigar da yaran tunawa da yayi bai taho da motar clinic din ba, banda kuka babu abinda suke yi suna kallonsa a tsorace, fuskarsa daure yace “I don’t want to hear any of you cry again” shiru suka yi sudais ya riko hannunsa yace “plss bring out our Anty from the toilet” sauke idonsa kasa yyi a hankali yace “Ohk i will do that now” daga haka ya fita ya rufe kofar yanda baxa su bude ba, sama ya wuce da sauri ya shiga office din Muktar ya dau makullin motarsa sannan ya sauko, yana bude kofa su sudais suka yi tsit daga kukan da suke, Shureim yace “Uncle where is she plss” hannunsu ya kama ya fita da su, ya bi ta bayan asibitin xuwa parking space, back seat ya saka yaran gaba daya sannan ya shiga driver seat ya tada motar ya bar asibitin. K’asa kuka twins din suka yi a motar saboda Aliyu da ya hade rai, kana ganinsu kasan a tsorace suke barin Shureim, driving kawai yake har ya iso gida bayan yyi parking ya fito ya bude masa motar yace “Come down” da farko kin sakko suka yi, ganin kallon da yake masu duk suka fito, Shureim na goge idonsa cikin rawar murya yace “I thought you where a good friend, plss don’t kidnap us away from our Anty, she will be sad” Duk da hawayen da ya taru idon Aliyu hakan bai hanasa durkusawa gabansu ba ya rungume su gaba daya yace “I didn’t kidnap my kids, I brought you two to ur Granny” Sudais ya xaro ido yace “We left her at d hospital and this is not our home” Aliyu na kallonsu cikin sanyin murya yace “This is your father’s home” A tare suka hada baki gun ce masa “Where is he?” Shiru Aliyu yyi yana kallon handsome boys din, sudais yace yace “Anty told us our father… Is a Barrister, she said he travelled immediately we where born and that… he will come to us one day” Jikin Aliyu yyi mugun sanyi yana kallonsu, Shureim yace “We will love to see our dad” mikewa Aliyu yyi ya kama hannunsu ya wuce cikin gida da su. Sudais ya bata fuska kamar xai yi kuka yace “I thought you are taking us back to our Anty” gaba daya yan gidan na parlor xaune ana jajanta abinda Kyauta ta ma Anty khadijah, saleem sai cewa yake da ma da shi aka je ya lallasata ya cire mata hakora ya ga wanda ya tsaya mata,  mumy dai bata ce komai ba sai kallon Anty khadijah dake kwance kasa take duk jiki yyi tsami don ma ta gasa jikin da ruwan xafi, baki a kumbure har da ido, iklima ma an sallamota tana sama a kwance, gaba daya occupant din parlorn suka dinga kallon Aliyu da twins din hannunsa, Anty khadijah ta mike xaune da sauri ita ma tana kallonsu, Baby ta mike da mugun mamaki tana kallon yaran tace “Laah yaran da muka gani a kasuwa daxu, yaya where did u knw dem from, mai ya samu kan wannan” Aliyu ya isa har gaban Mumy dake kallon yaran ya sake hannunsa, a sanyaye yake kallonta, yyi gathering courage da kyar yace “Yaran da Iman ta haifa kenan, she got pregnant after the incident” Ba Anty khadijah kadai ba har Mumy sai da ta girgixa ta mike tana kallon yaran dake ta kallonta sannan ta mayar da dubanta kan Aliyu cikin wani yanayi tace “How did you knw Abuturrab, where did you get dem from???” hawaye suka shiga sakko masa yana kallon mahaifiyar tasa a sanyaye yace “I met them today mum, I don’t knw if Khadijah will ever forgive me… I ruin her at a very tender age, this boys are my blood, Mumy na kawo su gida ne don nima in yi facing ko da kadan ne daga cikin abinda tayi facing a rayuwarta duk da ni na fita ga ta….” Kasa ci gaba yyi ya bar parlorn ya wuce sama hawaye na sakko masa, Anty khadijah dake ta xufa ga cikinta da ya tsure tace “Mun shiga uku, Anty fati kin ga wani sharri koh, kin ga wani hauka irin na Aliyu ko? yaushe Aliyu ya isa haifan wa ennan yaran? ta je an mata ciki a wani waje ta makala masa kuma ya yarda saboda wawa ne shi… a ina ma ya ganta???” Kai kana gani kasan kame kame kawai take duk ta rude, Su Shureim sai bin kowa na parlorn suke da kallo a tsorace, baby ta fashe da kuka cike da tausayin yayanta, Salim ma sai kallon yaran yake a duk jikinsa yyi sanyi ganin kamannin Aliyu sak tare da su, Mumy ta fashe da kuka sosai ita ma tana kallon yaran, hakan yasa su ma suka fashe da kuka, babu abinda take gani tare da yan biyun sai Aliyunta lkcn da yake kamar su, Anty khadijah ta haura sama kusan a guje tana cewa “Yau na ga abinda ya isheni bai ishi Allah ba, ina yake ya xo ya fitar mana da shegun nan da ake shirin kakaba masa, ya xo ya mayar da su inda aka basa su, amma Allah ya isa tsakaninmu da yarinyar nan, ta rasa wanda xata ma sharri sai Aliyu saboda tsautsayi ya gifta tsakaninsu? Ni dai nasan da hankalin Aliyu baxai mata fyade ba, sharrin shaidan kawai da kuma sharrin ta don ita ke shisshige masa, wlh baxa mu amshi shegu gidan nan ba, kaf xuri’ar mu ba a taba haka ba baxa a fara a kan d’an yayata ba” tana wucewa sama mumy na share hawayenta ta kama hannun yan biyun ta wuce sama xuwa dakinta da su. Wata nurse ce ta shigo dakin ba ma sudais allura ta ga babu kowa dakin sai kofar bayi da ake ta bubbugawa ta isa da sauri ta bude kofar da mamaki ganin key aka sa ta waje, khadijah ta fito tana bin dakin da kallo ganin ba kowa ta riko nurse din a rikice tace “Na shiga uku nurse ina yarana? Where are they plss” nurse na kallonta da confusion tace “Yanxun nan na shigo madam” da gudu khadijah ta fita xuwa ward din da aka kwantar da ita, ta ga Umma ce xaune sai Nanny da khaleel dake tsaye ya jingina da bango idonsa a kan wayar hannunsa, ta fashe da matsanancin kuka ta xube wajen tace “Wayyo Umma na shiga uku ya tafi min da yarana” khaleel ya iso gabanta da sauri da mamaki yace “Ya tafi da su ina? Kina kallonsa ya tafi da su” ficewa yyi ward din da sauri, Umma da ta gigice tace “Wa ye ya tafi da su Khadijah, waye shi” Khadijah ta riko Umma tana kuka sosai tace “Umma Aliyu, ya tafi da yaran, ya wuce min da yarana” a sanyaye Umma ke kallonta, Nanny ta bi bayan khaleel da sauri tana cewa “Me ya kawo sa asibitin, mun shiga uku” umma ta dago Khadbijah ta rungumeta, cikin rawar murya take cewa “Umma kar ku bari ya raba ni da su, baxan iya rabuwa da su ba, don Allah a taimake ni a karbo min yarana ni na yafe masa duniya da lahira ya bar min yaran, wllh na yafe masa har cikin xuciyata amma yayi hakuri ya ba ni yarana” tana kai wa nan ta kara fashewa da matsanancin kuka tana kiran Umma, hawaye ya shiga sakko ma umma ta rasa abinda xata ce ma ‘yar tata.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button