Noor Albi

NOOR ALBI 10

Gobe Zan wuce Abuja da yamma.

Marairaice fuska tayi tana sake shigewa jikinsa tace”

Please Turaki ka qara ko kwana biyu ne kafin zuwa abujan,
Idan muka koma gobe kana zuwa can bazakai lokacin hutawarmu ba.

Ki zauna anan idan nagamo daga Can kafin nakoma zanyi kwana biyu anan bayan tafiyata din saiki koma Abujan.

Ba Dan tasoba tace”

Ok Amma dai zanbika Abujan Kuma idan zaka dawo nasake biyoka.

Kallonta ya Dan Kuma waiwayowa yayi sbd yasan tsoronta akan zuwansa bada itaba baifi akan maganar qarin aure da Anne keson yayiba ko zai samu haihuwa.

Juyar da idanuwa tayi tana kokarin boye yanayin data shiga din Dan kuwa har cikin ranta Bata qaunar kebewar Anne da Turaki tunda tasan zancen dai daya ne na qarin auren.

Wani irin lafiyayyan murmushi ne dayafi komai kasheta yasaki Yana dauke kansa daga kallonta yabarta tana qarasa zubewa ajikinsa Dan kuwa murmushin abune dabai cikayiba Amma yanayi din sosai.

Har qarfe goman dare Yana tareda Ita yabata lokacinsa sosai kafin buqatunta suka biyo baya inda ta wawashi kudi masu matuqar yawa agurinsa Wanda dama ita sune suka riqeta a auren.

Sai daya rabu da Mss Na’ima kafin ya nufi office room dinsa na cikin gidan inda A Abdoul ke jiransa da tarin bayanansa
Yana shigowa kuwa A Abdoul din ya miqe Yana Masa barka da fitowa kafin ya zauna Kan kujerar 1 seater dake facing din A Abdoul ya miqa hannu ya karba iPad din Dake hannun Abdoul din Yana duba bayanan.

Sai dare sosai ya fito ya ta kofar Dake palon qasan ya nufi sama ya Haye
Kai tsaye ya nufi bedroom dinsa.

Washe gari qarfe Tara an kammala komai na breakfast din gidan an jere sai qarfe goma yasauko sanye cikin Ash Kaftan na babban yadin Ambassador sai hular qube
Hannunsa sanye da agogon Chanel
Take qamshinsa ya gauraya palon kallo daya A Abdoul da M Sarat sukai Masa Suka sauke Kai ganin Mrs dinsa a gefensa sai wani Jan girma takeyi cikin nata adon.

Breakfast yayi tareda Ms Na’imah da A Abdoul kafin ya fito zuwa Inda zai gana da baqinsa.

Qarfe biyu yagama da baqinsa yadawo gida yayi lunch tareda Ms Na’imah kafin ya haye Bai fitoba sai qarfe hudu da rabi Ya sauko Kai tsaye suka shige mota zuwa airport dukkaninsu.

A jirgi ma hankalin Na’imah gabaki daya yakasa kwanciya Dan ita harga Allah ma rashin zuwan Turakin yafi Mata kwanciyar hankali akan zuwansa
Dan zuwansa kullum cikin sakata fargaba yake,
Kishinsa take sosai sbd bazaso akaro wadda zata tayata cin wannan dukiyarba.

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button