NOOR ALBI 12

Kamar yanda Haj Anne ta sanar Masa da bayanin komai da Kawu saidu yayi Mata shiru yayi Yana sake juya zancen Dan kuwa Babu wani sauran abinda zai iya fada ayanzu tunda Anne tariga ta karba Auren Amma Kuma duk da hakan zai karba auren ne Dan taqaita maganar,
Zai karba auren Amma badan ya karbeta a matsayin Mataba,
Zai karba auren Dan inganta rayuwarta ta hanyar Bata ilimi Mai kyau da tsadarda zai iya bawa ‘yayan cikinsa da yanada,
Kar karbeta ne tamkar ‘yar riqo har zuwa lokacinda Allah zai bawa Amininsa nasa lafiya saiya sawwaqe Mata ayi Mata auren daya kamaceta,
Wannan shine abinda ya yankewa kansa da maganar auren
Dan kuwa bayajin har abada zai iya kallon ‘yar da Mahmoud da Zainab suka Haifa Amatsayin matarsa,
Macen da zai iya muamala ta daban da ita bayan ta uba da ‘ya.
Da wannan ya rufe maganar aka fara Shirin auren Wanda Babu Bata lokaci aka Sanya sati Mai zagayo ranar juma’a.
Wasu irin kudin gaske Aka aikowa Momy da Kawu saidu na hidimar Wanda yakusa haukata kawunan dangin momyn suka so cinye kudin
Dayake Kawu saidu shima idanuwansa a bude suke yace Babu wannan maganar shima Dole a fitarda na dangin uba abasa idan bahakaba zai fasa bada auren.
Wani irin murmushin bakada lafiya su Haj Karima sukai Masa
Alhaji Atiku kuwa Jin abinda Kawun Yafada yasashi kallonsa da kyau da hasaso irin dukan mutuwar dazasu saka Yan dabansu na shiyasa suyi Masa idan har ya kwatanta abinda Yafada din,
Umma Jamila kuwa cikin ranta fatar saukar masifar datafi ta Dan uwansa Mahmoud tai Masa.
Momy da har lokacin zuciyarta najin wani iri a al’amarin kallonsu tayi jiki a Dan mace ta rokesu akan subawa kawun haqqinsa na matsayin uba ko Dan asamu albarka a wannan auren.
Haka suka bawa Kawun saidu kudin dabai taba riqe irinsuba arayuwarsa hakama takamaimai baisan me zaiyi dasuba kawai dai yafison ya karba din Dan kuwa yagama ganin zallar kwadayin abun duniya da son zuciya a al’amarin dangin Zainab din.
(WAINDA SUKE RUDEWA DA SUNAN ZAINAB DANAKE FADA SHINE DA MOMY DA MAHAIFIYAR LAYLAH DA LAYLAH DUK SUNANSU ZAINAB,ITA LAYLAH SUNAN MAHAIFIYARTA AKA SANYA MATA BAYAN RASUWAR MAHAIFIYAR).
Sabuwar rayuwa Kawu ya bude a garin Dan kuwa tuni yasaka Abdullahi agaba akayo Masa manyan dinkunan bikin tareda huluna masu tsada da takarma harma dasu turaruka Kawun ya siya,
Dayake baida rowa har Abdullahi yabawa nasa kason kudi masu ‘yar tsoka wanda yasa Jikin abdullahi din yakuma sanyi da al’amarin yaji bazai iya boyewaba Dan Haka Ana saura kwana biyu daurin auren da daddare ya nufi gidan umma Jamila Dan ganin Sa’adah wadda ita kadai yasan zata fahimcesa sbd kaf kowa dukiyar tagama rufe idonsa
Shikuma yakasa danne al’amarin sbd sanin Auren Laylah da Turaki Kamar wani boyayyan burine Kuma Alqawarin Abba Wanda duk ranarda ya tashi yaga wannan sauyin bazaiji dadiba duk da itama Sa’adah din ‘yarsa ce Amma kamar sbd mahaifiyar Laylah yakeson Lallai laylance zata aura Turaki.
Babbar Sa’ar dayaci a zuwa gidan umma Jamila Bata Nan suna gurin hidimar bikin da aketayi duk da Turakin yasanar da cewan basason Ayada Dan kada Yan Media suji Amma zancen ya Dan firfita sbd sukam su Alhaji Qarami sunason asan Wanda suka bawa auren yarsu,sunason duniya tasan sun hada alaqa da ABUTURAB TURAKI Ko Dan matsayinsu da girmansu yaqaru a idon jama’a.
Lokacinda Anty Sa’adah taga Abdullahin ne Mai neman ta gabanta Saida yayi mummunan faduwa
Take jikinta yayi Sanyi sbd tasan tabbas kodai abbansu kokuma Laylah akwai Wanda wani Abu yasama.
Shigowa tayi dashi palon baqin gidan suka zauna takawo Masa ruwa tana kallonsa jiki mace muryarta na bayyanarda damuwarta tace”
Yaya Abdullahi Allah yasa lfy dai Dan nikam ganinka yasa jikina mutuwa.
Ruwan data kawo Masa ya Dan Sha Yana dauke idanuwansa daga kallonta ganin irin yanda ta sauya sbd zallar gyara da ake mata tayi haske sosai tayi fresh duk da ta rame Amma duk da hakan a idanuwansa ko ahakan batakai Laylah kyawu da haske ba.
Aje ruwan yayi tareda Dan kallonta kadan cikin nutsuwa yace”
Abba dai yananan yanda take hakama Laylah tananan da dama itama saidai Kam duk tayi wani iri sbd kadaici da rashinki ahakan ma dai aikin gidan yadawo kanta,
Saidai ba wannan ne yakawoniba.
Kallonsa Anty Sa’adah din tayi batareda ta iya cewa komaiba tana sauraron abunda zai fada.
Ya fuskanceta dakyau Yana tattaro nutsuwa yace”
Maganar auren Nan ne da za’a daura jibi nazo nafada Miki sbd naso daurewa nayi shiru nakasa hakan sbd Abba da Laylah dama ke din.
Ahankali ya zayyano Mata burin Abba da babban qudurin nasa na Bawa Turaki auren Laylah tareda sanar da ita asalin abindaya faru ranarda ciwon na Abban ya rikice sbd shima Kamar yanda Momy taji komai yaji komai ganin momyn zata juyo tabar gurin yasashi barin gurin tun kafin tagansa ya fice daga gidan
Dan Haka ya Dora da cewa”
Sa’adah ke kadaice gatan Laylah ayanzu tunda Babu Wanda take nuna yasanda ita bare damuwa da rayuwarta,
Kece gatanta ayanzu da Abban yake kwance,
Kece uwa Kuma uba gareta hakama ‘yar uwa,
Idan kikayi auren Nan Kika tafi Amatsayin Laylah da wace daraja Turakin da Mahaifiyarsa zasu kalleki?
Hakama Abban duk ranarda ya tashi da wace darajar zai kalleki da Momy,
Hakama babban abindayake faruwa shine Turaki yasa ahada takardu da komai na lafiyar Abban za’a daukesa daga Nan zuwa wata qasar Kuma ansanar da Momy ta aminta da atafi dashi din Dan Haka bayan aurenki bana tunanin Laylah tanada wani sauran abinda yarage anan bayan kunci.
Nidai abindayasa nazo nafada Miki gaskiyar lamarin sbd kome Zakiyi karki manta da ‘yar uwarki Dan Allah,
Kamar yanda Kika dauko tallafar rayuwar marainiyar Allah kici gaba da tallafa Mata Dan Allah karki Bari ta Shiga wani mummanan halin dayafi Wanda take ciki sbd nidai da antafi da Abba zuwana gidan nasan yaqare tunda dama dawainiyar Abban ke kainiā¦..
Dogon numfashin data saukene yasashi dakatawa Yana sauke nasa numfashin shima kafin ya kalleta ganin yanayinta ya sanyashi miqewa Yana kallon Agogo
Gwara ya tafi kafin umma Jamila tadawo ta taddasa gidan
Hardai idan tasan abin daya kawosa da Babu shakka saita Ari hauka ta Masa mummunan wulaqanci.
Bayan tafiyar Abdullahi Sa’adah na shiga gida tafara hada kayanta Dan kuwa ta yanke shawarar komawa gida ayau din,
Gwara Takoma gida kawai aqarasa komaima acan.
Koda umma Jamila tadawo agajiye take shiyasa Koda Sa’adah din Tai maganar komawa gida Bata kawo komai arantaba tasa driver yakaita Dan dama gobe za’a maida Sa’adahn gida sbd gobe su Haj Anne zasu iso
Dan Haka Kai tsaye tasa aka maida Sa’adahn gida da maraicen ta bugawa Mai hajiyar dasuka dauko ta musamman Dan gyaran Amarya waya cewa subi Sa’adah din can gida aqarasa acan na yau da goben.
Ko data iso gidan tsit kamar ba hidimar biki akeba Momy na Palo da baqi suna magana tashigo a natse fuskarta daukeda murmushi taqaraso gabansu cikin girmamawa ta gaidasu tana kallon Momy datake kallonta tana yaba kyawun datayi tace”
Momy kinata kallona
Na sauya Miki ne?
Murmushi momyn tayi tana cewa”
Dan sauyi kin sauya Kam kamar ba Sa’adah ba
Wannan hajiya Sa’adah shuwa Arab ce.
Dariya baqin momyn sukayi suna yaba gyaran na Sa’adah dake bayyane afili Dayar tace”
Momy ko Zaki bani numbern me gyaran Nan sbd auren sanah da zaizo qarshen watan Nan Dan Naga ta iya gyaran amare Kam gashi Sa’adah sai wani irin qamshi takeyi Mai Dadi.