NOOR ALBI 12

AMARYAR KB GLOBAL ENTERPRISE 08067558902 itace Mai wannan aikin na gyaran Amare tareda kayan qamshinda ko a anguwa za’a San ankawo Amarya,
Turarukanta na musamman ne Dan kuwa daga Chad suke zuwa ga kayan Mata na gyara masu kyau da inganci
08067558902.
Kai tsaye daki Sa’adah ta wuce inda ta tararda Laylah a dakinta zaune tana ninke kayan wanki datai na tarin tsoffin kayan Sa’adah da aka Bata akace gashinan ta ringa sakawa can gidan idan Sa’adah din taje da ita Dan karta ringa saka tsoffin kayanta dasuka Gama kodewa.
Tana ganin Sa’adah taji wani irin sanyin farin ciki harsaida fuskarta ta bayyanarda hakan
Fararen idanuwanta akan Sa’adah din tabude baki tace”
Anty Sa’adah kindawo tun yau ne?
Qarasowa Sa’adah tayi gabanta fuskarta daukeda murmushi tana kallon kayan da Laylah din ke linkewa tace”
Meyasa zakiyi wankin kayana tunda banananma ba sakawa nayi ba.
Kallon kayan tayi tana qarasa Nade rigar Dake hannunta tace”
Jiya Umma Jamila datazo suka bani itada Momy sunce Dani zakije na ringa sakawa acan.
Shiru tayi tareda sauke Kai tana jiran abinda anty Sa’adah din zatace ko tana buqatarsa kayan nata.
Shiru anty Sa’adah tayi cikin Dan takaicin yanda idanuwansu umma Jamila ke rufewa Akan komai,
Koda zata tafi da ita amatsyinta na wadda zata aura Mai Hali yakamata ace andinka Mata ko kala biyu ne na tufafi Amma shine za’a Bata tsofin Kayan da ita takashe taje dasu.
Wani murmushin takaici da baqin cikine ya kufce Mata,
Ita yanzu sun kore Mai aurenta da qarfi da yaji sbd zasuyi auren yaudara da ita
Gashi yanzu zata tashi a Babu tunda biyu Babu takamata.
Kallon Laylah tayi tace”
Aje kayan bazaki dasuba za’a Baki wainda Zaki ringa sakawa idan munje.
Ba musu ta ajiye kayan tareda dagowa ta zubawa Anty Sa’adah din idanuwa tana kallon sauyawar datai tareda tayata farin cikin auren dazatai din Babu babban farin cikinta irin tafiya da ita dazatayi Dan kuwa ita kanta da kanta tasan kanta yakusa qarasa juyewa sbd wasu abubuwan datakeyi wani lokacin.
Akwai gyaran yamma da ake Mata Dan Haka Koda masu gyaran sukazo Laylah tasaka suyiwa tace”
Kuyiwa qanwata gatanan itama da Dan sauya tunda da ita zani.
Momy dai batace komaiba ta qyale akaiwa laylahn sbd lallaba Sa’adah dasukeyi asamu ayi auren tukuna.
Fes Akaiwa Laylah wata irin dilka da wankan lalle tareda wasu gyaran da fatarta ta amsa atake sbd tanada Hasken fata sosai hakama tafi Sa’adah fata Mai taushi sosai shiyasa gyaran atake yaringa shiga jikinta tayi Dan Shar da ita
Abdullahi daya shigo yayi Ido hudu da Laylan tsinkewa yawunsa yayi Yana dauke Kai zuciyarsa na basa qwarin gwiwa da tabbacin Ana Gama bikin Sa’adah zai bayyanarda kansa a manemin auren Laylah din yasan Kuma zasu basa tunda neman Kai su umma Jamila keyi da ita kokuma ya lallaba Kawu saidu kafin yakoma yabasa aurenta basaima Sa’adah ta tafi da ita dinba Dan zata iya fin qarfinsa idan taje daular gidan Turaki ta samu sauyin rayuwa.
Da daddare duk maganin da aketa faman dirkawa Sa’adah Haka ta tattarosu ta bawa Laylah tasata ta shanye a sunan maganin rashin lafiyartane ba musu laylan ta shanye.
Washe gari da safe bayan angama gyaransu masu gyaran sun tafi umma Jamila tareda Haj Karima suka iso gidan da wasu irin Kaya na Alfarma da aka dinkowa Sa’adah din wasu manyan lace ne dasuka Sha maqudan kudi tareda gyalensa da takarmi aka Bata ta shirya tafito fes a Amarya sai qamshi take zubawa.
Kallon Laylah dake zaune gefe tana kallonta tayi tasaki murmushi jikinta amace tanajin inama aurentane na gaskia da Amana za’ai
Datayi farin ciki sbd ita kanta tanason tayi auren Dan ta tallafa rayuwar Laylah din Amma wannan aurene da ake Shirin ginawa Kan yaudara.
Fitowa tayi riqeda hannun Laylah Dake sanyeda doguwar rigar jallabiya sabuwa Navy blue da Sa’adah din tabata tasaka
Kanta nade cikin gyalen Abayar
Idanuwanta ki kwalli babu
Babu komai akan fuskarta sai asalin zallan kyawunta da Allah yabata duk da Babu wata walwala ko sakewa a fuskar tata Wanda Kuma hakan dabiarta ne tunda ahaka ta taso ba walwalar.
Kallonsu Haj Karima tayi kafin ta tsayarda kallonta Kan Laylah Dake rabe bayan Sa’adah din
Ta bude Baki zatai magana
Umma Jamila ta tareta da cewa”
Karma kiyi wahalar magana barta taje da ita din dan taurin Kan Sa’adah Ni har tsoro yakeban yanda kikasan kafiran farko Haka take da taurin tsiya akan wannan Mai Kama da ‘yar tsanar.
Shiru Haj Karima tayi tareda dauke Kai daga kallon inda suke din ta kalli Momy dake zaune tana kallon su Sa’adah din itama tace”
Gatanan gurin gaida uwar mijinta dasuka iso yau za’a kaita.
Umma Jamila ce ta karba zancen da cewa”
Ga abinci dasu komai can a mota duk ansaka.
Miqewa Haj Karima tayi dayake ita zata kaita suka fito bayan umma Jamila tasake bin jikin Sa’adah din da turarukan (AMARYAR KB GLOBAL ENTERPRISE 08067558902) masu qamshi.
Suna fitowa suka shiga babbar CR-V din Haj Karima driver yajasu zuwa masaukin Anne wadda ta iso aranar tareda jamaarta su biyu.
Wani babban makeken guest house din Turaki dake garin suka dosa
Tun a gate Sa’adah ke kallon koina zuciyarta a sanyaye har aka abarsu suka qarasa harabar gidan sukai parking suka fito.
Kallon Laylah da kanta ke sunkeye cikin sanyi Haj Karima tayi Kai tsaye tana cewa”
Kwaso kayan abincin,
Ki dauko da kyau karki barar kosu hargitse.
To” tace anatse tareda daukan kayan abincin tanabinsu abaya.
Wani babban palon dayake a tsare da komai na irin Rayuwar turawa akai musu iso suka zauna Kan milk and golden Royal set dake palon
Banda Laylah data tsaya da kayan abincin tana jiran afada Mata inda zata aje
Kafin suyi wata magana qamshin turaren Haj Anne yafara iso musu kafin ta fito cikin doguwar jallabiyar kuwait baqa Mai Fadi sosai kanta yane da mayafi Mai Dan girma sosai Wanda yasaka Hasken fatar datake dashi fitowa sosai duk da tsufa da manyanci Amma komai nata a natse yake,
Fuska dauke da Dan murmushi take qarasowa tana kallonsu ta iso ta zauna Kan 2 seater tana amsa gaisuwarsu a mutunce musamman Sa’adah wadda ke zaune gefn Haj Karima din…. Sauka Idanuwanta sukai Kan Laylah Dake tsaye har lokacin daukeda kayan abincin…
Dukkanin hankalinta da idanuwanta zubawa Laylah su tayi sbd ba shakka fuskar Zainab take gani akan fuskar yarinyar,
Babu abinda tabaro na zainab face yanayin jikinsu daya banbanta ita sirirya zainab Kuma ba siririya bace Amma kamanninta da mahaifiyar sunyi nauyi sosai take taji qaunar datakewa Zainab din kafin rasuwarta tadawo Mata sabuwa fil akan Laylah
da mamaki Kan fuskarta Tace”
wannan ‘yar Zainab ce basai nayi tambayaba.
Haj Karima wani juyi tayi tareda Yi kamar batajiba tasake dasa sabuwar gaisuwa da barka da hanya kafin tacewa masu aiki dasuke kawo musu kayan tarba su karba abincin.
Suna karba ta kalli Laylah zatai mgn Anty Sa’adah tariga cikin nutsuwa da cewa”
Laylah kixo ki gaida Mutane.
Sabone data taso cikinsa na idan ba umartarta akai da Abu ba Bata Yi sbd kaucewa laifi da matsala shiyasa Bata qaraso ta gaida Anne ba Saida Sa’adah din tayi magana
Ta qaraso ahankali cikin natsuwa batareda ta kalli Annen ba ta gaidata da muryarta Dake yankewa.
Kasa rike mamakinta Anne Tayi takai tattausan hannuwanta ta kamo hannuwan Laylah cikin tsananin kulawa tace”