Noor Albi

NOOR ALBI 13

Sanin daga Laylah din har Sa’adah suna buqatar rayuwar da Anne ke fatar Basu yasa ya amince da tafiya dasu duka biyun tunda koba komai Abba ma wata qasar za’a kaisa dan Haka zamansu cikin zuriar Zainab da basuda Imanin na sanin komai bayan kudi akwai matsala gwara su tafi gurin Annen har Allah yabawa Abban nasu lfy.

Bayan ya amince rokon Anne yayi akan abar zancen auren ayanda yake abar dangin Zainab da sanin da Sa’adah za’a daura sbd karsu cutatar da Laylah.
Momy kuwa dayake da ita za’a tafi qasar daza’akai Abban itama yace abari sai bayan daurin auren zai sanar Mata a sirrance ko zatai hankali tabar rakiyar danginta taje tayi jinyar mijinta tasamu lada ko zunubanta na shekaru sa kakkabe.

Da wannan Ya tafi yabar Sa’adah din wadda Anne keyiwa nasiha cikin hikima da tambayayi akan Laylah datake iya amsa wasu
Wasu Kam bazata iya amsawa sbd basuda dadin saurare Kuma hakan tamkar zubarda mutuncin mahaifiyarta ne zatai.

Anne da kanta da Yan bayanin data samu daga Sa’adah din tasake fahimtar rayuwarda Laylah ta taso aciki Dan Haka ta yanke shawarar hadawa har Laylah din ta riqesu da Sa’adah bazatai saurin sakata a rayuwar aureba sai Laylan tadawo kamar kowane ‘da mai walwala da rayuwar yanci,
Bama za’a nuna Mata tanada aurenba a yanzu tana buqatar Abubuwan sauyin rayuwa harma da ilimi duk bayan tadawo cikakkiyar lafiyayyarta kenan idan depression yabarta Dan Haka zata barta Akan riqo ta daukosu kokuma akan biyo Sa’adah datai gidan Aurenta.

Tafiyar Kawu ba jimawa Haj Karima tadawo tareda Laylah dake bayanta kamar Mara lafiya tana tafiya a sulale
Kallon qauna Mai girma Anne ke Mata tana Jero adduar samun tsaftatacciyar zuria daga gareta.

Kasa boye kulawarta tayi tasa aka dauko kyauta ta musamman na kayan Alfarma da aka dinko masu tsadar gske da sunan Amaryar Turakin tabawa Laylah tace”

Gashinan kema gobe ranar daurin auren kiyi ado.

Saida takalli anty Sa’adah kafin tasaka hannu biyu ta karba tana godiya kanta aqasa.

A hanya ba kalar fada da masifar zuwa da ita da Sa’adah tasa sukai Wanda Haj Karima din bataiba kamar ta rufe laylan da duka duk da yau Sa’adah dinma tafi qular da ita Haka suka koma gida masu gyaranta na jiranta ayi za’ai Mata qunshi.

umma Jamila taso karbar kayan ta sauyawa Laylah da wasu Momy ta Hana da cewan Kar ayi abunda zai zubarda mutuncin ko wani kallon daban daga Anne.
Hakan yasa ta hakura ta barwa laylan Amma Kam mugun kallo Babu kalar Wanda ba’a bita dashiba ta sulale tashige daki ta zaunawarta anata hidima da hayaniya sbd gidan acike yake tap da dankin Momy anata bidiri cikinma an hanasu bikin komai da Allah kadai yasan irin shagalin dazasuyi.

Qunshi akaiwa Sa’adah sai bayan magriba aka kammala tasamu ta wanke tayi wanka tayi sallah har lokacin Laylah na daki Bata fitoba dan yau fitowa daki tafi qarfinta a gidan sbd dangin Momy duk Babu Wanda yake qaunar ganin ko giftawarta.

Duk yanda taso janta da zance akan ta sake kasa sakewa Laylah tayi dan itadai matuqar dangin momyn na gidan batada sauran nutsuwa ko sukuni.

Haka Sa’adah ta qyaleta har lokacin kwanciya yayi Laylan tayi bacci tabar Sa’adah na binta da kallon gobe Kamar wannan lokacin ra igiyoyin Turaki uku cif na Aure akan Laylahn,
Wannan shine babbar nasara sbd batada masaniya,
Lokacinda zatasan da aurensa akanta kilama lokaci yaja lokacin zatafi Jin zancen auren Al’amari Mai girma.

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button