Noor Albi

NOOR ALBI 14

Qarfe goma na safe su Momy jirginsu zai tashi Dan Haka tun qarfe Takwas na safe akazo da lafiyayyar mota motar Lexus aka dauki Amarya Laylah da ‘yar uwarta kokuma dai ace Amarya Sa’adah da qanwarta zuwa gidan Turakin Dake Nan,
Sosai Anne ta nuna yabawarta tareda karban Amanar yaran da zuciya Mai kyau
Nan akaiwa su umma Jamila yanda suke so wato kyautar girma data kusan sakata zubewa gaban Anne din Haka suka ringa zuba godiya suna qarawa da iyayi kala kala har suka tafi
Dan take daga umma Jamilan har Haj Karima da Matar Alhaji Qarami sukaji buqatar fita gidan Dan sanin yanda wannan kyautar tasu zata jujjuya a hannuwansu Dan kuwa dalolin Amurka ne Anne ta Basu wainda idan suka canjasu ba qananun kudade bane shiyasa ba kunya kowaccensu ta gifta uzurin rashin damar rakiyar Sa’adah din yanzu zadai suzo daga baya Idan sungama sallamar baqin nesa dasukazo biki
Illa kuwa canjin dalilinsu sukeson tsayawa suyi su kammala Kan dukiyar kowa yasan abinda yayi da tasa daga baya sunbi sahun su Sa’adah din Dan dama zuwa gidan Turaki yanzu Dole ne.

Bayan tafiyarsu motar daukar Momy zuwa airport tazo bakowane acikiba sai driver da Kawu a gaba.
Shigowa Kawun yayi Suka zauna Palo daga momyn sai shi sai Anne wadda kai tsaye tafara magana da cewa”

ZAINAB kamar dai yanda Kika sani Allah Yana jarabtan bawansa ne Dan gwada qarfin imaninsa Dan Haka ki dauka komai na rayuwa na samu da rashi dakuma wasu sauyin duk cikin jarabawa da qudirar ubangiji ne,
Kamar yanda kikafi kowa Sani da shaidawa idan rabo ya rantsa tunda ga Laylah Nan Kin gani ishara
Hakane yakuma faruwa auren da aka daura jiya da Laylah aka daurashi sbd itace da haqqin hakan kin sani
Dan Haka idan da ansaka son Rai an daura da Sa’adah to wlh matuqar akwai rabo tsakanin Turaki da Laylah wannan Rabon saiya kashe Sa’adah ta rasu Dan kawai ayi auren a haifosa yazo duniya Dan Haka mudai munyi adalci kamar yanda Sa’adah da kanta tazo tafada Kuma ta roqemu akan hakan sbd hakan dai shine daidai,

Zainab ki godewa Allah daya Baki ‘ya kamar Sa’adah wadda wlh samun ‘ya kamarta ayanzu Abu ne Mai wuya,
Tayi hankali sosai nakuma yaba Mata iya yabawa shiyasama Zan tafi da ita a hannuna na dauka riqonta da yardar Allah harsai Mahmoud yasamu lafiya Inshallah.

Wani irin kuka Mai sauti da shiga Rai Momy tasaki tana rufe fuskarta da tafukan hannayenta dake wata irin rawa.

Shiru sukai dukkaninsu sbd Bata damar kokawa Dan sunsan hakan akwai tsananin ciwo
Tana ganin ta aurar da ‘ya yanzu Ana fada mata ba wani aure.

Kuka takeyi sosai wanda yasakawa Anne tausayinta tafara Mata nasiha da rarrashi har zuciyar momyn ta Dan Yi sanyi Amma Kam wani nauyi da ‘daci sun Riga sun dasa Mata shi Dan Haka share hawayenta kawai tayi batareda ta dago ta kalli Annen ba murya a cikin yanayi na sanyi da ‘dacin zuciya tace”

Nagode nakuma bar Sa’adah a hannunku.

Jinjina Kai Anne Tayi tana sake Jin tausayin momyn sbd bayan qunci da baqin ciki Babu abinda yake zagaye da rayuwar momyn tsayin shekaru
Dan Haka tana Mata fatar samun budaddiyar zuciya Nan gaba.

Kasa ganin Sa’adah Momy tayi Dan bazata iya hada idanuwa da Sa’adahn ba Dan Haka Kai tsaye fice ta shige mota suka wuce airport
Suna Isa jirginsu ya daga.

Bayan tafiyar Momy da awa biyu Suma masu jirgin ya daga Wanda yasaka daga Sa’adah har Laylah cikin wani mugun yanayi Dan kuwa Babu Wanda yataba ko barin gari acikinsu bare Hawa jirgi har gwara Sa’adah tana Dan yawan tafiya wasu lokutan tareda umma Jamila kokuma Haj Karima Amma ba Wai tafiyar nesaba.

Tafiyar awanni sukai sai gasu a garin Abuja inda manyan Mercedes beymach ke jiran saukarsu Aka daukesu zuwa AB TURAKI RES.

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button