Noor Albi

NOOR ALBI 15

Lura da yanayinta yasa Anne kallonta da kulawa tace”

Laylah?
Lafiya ko?abincin baiyi bane a kawo wani?

Ahankali ta girgiza Kai tareda Kai hannu anatse tadauki spoon cikin cutlerys Dake gefen plate dinta tasaka cikin lafiyayyar fried basmati rice dataji veggies da nikakken Naman rago da spices na qamshi tafara ci ahankali.

Anne wayayyar tsohuwar Yar boko ce data Gama jiquwa acikin daula da hutu tareda rayuwar yanci Dan Haka batada wahalar zama saidai tsayayyar mace ce da Bata daukan shirme ko shiririta tareda zancen banza Dan Haka duk Wanda yasanta yasan Yar kaifi daya ce Dan Haka Dole Sa’adah ta tilastawa kanta sakewa tareda tilasta Laylah wadda tasan bazata Saba da mutane lokaci dayaba sbd yanda ta taso duk da hakan tanata nanata Mata sakewarta cikin mutane nada amfani.

Kwana daya sukai da wuni daya a gidan aka kawo wasu irin tarin kayan suturar sawarsu da abubuwan buqatarsu Wanda yasa Sa’adah kasa daina mamakin rayuwar gidan Dan kuwa hatta skin products set na kayan gyaran fatar jikinsu kusan kowa da kalar nasa fatar Haka aka siyo musu set set tunda ba kalar fatarsu dayaba Laylah tafita haske sosai.

Kaya kuwa bazasu iya gane iya adadinsuba Amma Kam sunada yawa Saida suka Kuma kwana daya sashen Anne kafin aka Ware musu babban shashe a gidan maqale da sashen Anne Wanda yake hade Dana Anne din Dan akwai palonda zai kaika Kai tsaye palon Sashen Annen daga nasu palon,
Palone Wanda yaji gyaran English royal set na komai blue and milk,
Kayan Dake palon ko Haj Karima da ake gani wadda tafi kowa a dangin Momy kaf gidanta Babu kayan dasukai kyawu da tsaruwar wainnan kayan,
Qatuwar TVn Dake palon tana aiki Laylah ta kalla tana sauke numfashi Dan said yanzune zata Dan sake da aka barsu suka dawo Sashen anty Sa’adah,
3 bedrooms ne apalon sai dining area da kitchen,
Babu abin Jin Dadi da Babu a Sashen Dan Haka Kai tsaye aka kaiwa kowacce kayanta makeken dakinta.

Kallo Sa’adah ta wuni Yi ranar bayan sungama cin abincin rana tareda Anne wadda yau ta fita,
Ita Kam Laylah aikin zama kallon Sa’adah tayi wadda take harta fara sauyawa da sakewarta.

Sai dare Anne tadawo Dan Haka can suka tafi sukaci abinci
Suna gamawa suka dawo sbd Anne a gajiye take shigewa tayi kawai Dan hutawa.

Ahaka ba sakawa ba fitarwa sukai sati biyu a gidan
Bayan cin Mai kyau da Shan Mai kyau su kwanta suyi bacci cikin AC da gado Mai taushi Babu abinda sukeyi
Har gwara Laylah da Bata Saba da zaman hutun ba Dole tasaka kanta fara Shiga cikinsu halima tana tayasu aikin Abinci
Anne dataga Kamar hakan na Bata nutsuwa sai Bata hanata ba Amma Kam su su halimar ba ruwansu tsananin girmanta suke Bata duk da gargadi da umarnin da Anne ta bayar na Kar Wanda yasan LAYLAH ce Matar gidan.

Ko ba’a fadaba sauyi yazo musu
Fatarsu ta bayyanarda hakan Dan kuwa tuni fatar kowannensu tafara wankewa dayake dama can tunda ba yawo sukeba anyhow sunada kyan fatarsu musamman Laylah da zaman gida da rashin fita yasa fatarta koyaushe a lafiye take Dan Haka sai taqara washewa sosai.

Sa’adah kuwa ba damuwa sabuwar rayuwa ta bude a gidan musamman kullum tana Kiran Momy suji yanda jikin Abban yake
Momyn dai har lokacin taqi cemata komai akan Abin daya farun Dan kuwa yanzu ita tagama shiga shock na mutane dakeson kasheta da qarfi da yaji.

Psychologist ta musamman ce take zuwa gida suna hadawa da therapy gurin kokarin dawo da Laylah daidai dan kuwa yanayin depression data Shiga yasa Sam sam tanada matsalar sabo da mutane ko kadan Dan Haka kafin maganar karatunsu hakan Anne taga yafi.

Babban cigaban da aka fara samu shine Dr Meenah wayayyar macen datasan me takeyi da Laylahn tafara dan sakewa da ita
Aikuwa hakan ba qaramin farin ciki yasaka Sa’adah ba da Anne.

Ms Na’imah wadda tabi Turaki Lagos Dan zai koma tun washe garin ranarda su Annen suka dawo batareda tasan abinda akayo Mata ba sai data cika wata biyu da sati daya a Lagos cif kafin tadawo Abujar.

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button