Uncategorized

TAKUN SAKA 43

 *_Chapter Forty Three_*………..Bayanine tiryan-tiryan daya shafi takardun da harƙallarsu, harda kuɗaɗen daya kwashe na Halilun da yanda akai ya amshesu, da masu mallakin dukiyar da alaƙar dake tsakaninsa da su A.G. A yanzu kam Hibbah ta sake tabbatar da Master baya tare da su A.G ɗin, duk da ya mata bayanin komai ta yanda ya shiga jikin nasu da tunanin shaiɗaninsu ne shi. Wasu irin irin hawaye suka gangaro mata saman fuska zuciyarta na tunano mata randa Isma’ill ya karyama Abba ƙafa akan abinda yay ma Ummi…..

       Zare takardar da akai ta bayanta da ɗisowar ruwan wankan jikinsa ne ya sata juyowa da sauri. Master daya tamke fuskarsa matuƙa kamar bashine ya gama tarairayarta yanzun ba, ya ɗan harareta yana ɗaukar sauran takardun ya maida cikin file ɗin. Ya ajiye ya juyo kawai yaji ta faɗa masa jiki a bazata ta rungumesa da sakin wani marayan kuka. Babu shiri ya dafe towel ɗin daya ɗauro a ƙugunsa dake neman faɗuwa. Dama ba wani rigan arziƙi bane a jikin nata, hakan sai ya bashi damar jinta bisa fatarsa dake ta faman raɓar ruwa yanda ya kamata. Ya lumshe idanunsa  yana riƙota da ƙyau shima da sakin nannauyar ajiyar zuciya. 

        Baice komai ba sai yatsun ɗayan hanunsa daya tura cikin gashinta, ɗaya kuma yana shafa bayanta a hankali, zuciyarsa sai wani irin zallo take da tsalle-tsalle kamar zata fito waje. Ganin kukan nata bana ƙare bane yajata suka zauna a bakin gadon tana jikinsa. Fuskarta ya ɗago dasa babban yatsansa yana share mata hawayen. 

       “Miya faru kuma?”.

  “Ka yafe min”.

Wani ƙasaitaccen murmushi ya saki yana ɗan ɗage gira sama, idanunsa na yawo akan fuskarta. “Ni baki min laifin komai ba”. Yay maganar yana ɗan sumbatar laɓɓanta.

       Kanta ta girgiza masa hawayen na sake rige-rigen sakkowa. “Nasan na maka laifi, na fahimceka a bai-bai, amma wlhy karkaga laifina nima inada hujjata. Nagode, ALLAH ya saka maka da alkairi, ya cigaba da baka kariya a dukkan motsinka da al’amuranka. Abinda naji wajen su Abba da shegen jami’in nan yasa nake maka kallon bai-bai. Kuma koba niba duk wanda yaji tunda baisan gaskiya ba zaiyi komai kamar nine”.

       “Na sani Muhibbat, shiyyasa naita miki uziri. Duk da kin hasalamin zuciya a ranar, dan kaɗan ya rage ki buɗemin dukanin aikina da zai iya sa harsu Ummi su rasa ransu ma. A hakanma kaɗan ya rage ki jefa rayuwarsu a haɗari, ALLAH ya taƙaita. Ina ƙaunar Ummi Muhhibat, hakama su yaya Muhammad. Bayan yaran nan da kike ganina da su a yanzu ahalinki sune ahali na biyu da nake kallo mafi kusanci dani a duniya. Tun bayan rasa mahaifiyata Ummi ce ta fara dafa kaina taimin addu’a cike da soyayya. Taya kike tunanin bazanyi yaƙi a kan zuri’arta ba. Taya bazanso haɗa jini da ita ba.” ya ɗaura hannunsa saman cikinta “Ina fata da addu’ar ALLAH yasa wannan cikin nayi ajiyar jinina da zai miki rakkiya zuwa wajen Ummina”. 

       “Nidai ba yanzu ba”.

Ta faɗa tana tura baki da kwantar da kanta a kafaɗarsa.

       “Haba baby luv kiji tausayina mana, Su uncle Habib mafa shi suke jiran gani”.

        “Waɗan nan na daina kulasu a gidan nan ai, dan suma haushina sukeji”.

      Ƴar dariya yayi mara sauti da kamo hannunta ya ɗaura bisa fuskarsa. “Kefa kikai musu laifi, kika sa aka harbar musu Yayansu. Ba dole suyi fushi da ke ba. Amma nasan da sunga kin ɗan fara amai sun samu ɗa zasu daina ai”.

          Baki ta tura tana ƙara cusa kanta a wuyansa. “Ni dai nace ba yanzu ba”.

         “To ai ya riga ya shiga insha ALLAH, dan ban buga ƙwallona da wasaba tun a farkon fari”.

        Tashi tai zata bar jikinsa da faɗin, “Nidai babu ruwana wlhy inada kunya”.

         “Nima ai inada ita. Bakiga tun shekaran jiya kunyarki nake ji ba”. Yay maganar yana binta da kallo.

        Juyowa tai ta kallesa da ɗan waro idanu tana riƙe haɓa “Kai ɗinne kake wani jin kunyata?”.

       A yanda tai maganar da waro idanun da bage bakin ya bashi dariya, amma sai ya gimtse baiyiba, yay ɗan murmushi kawai da ɗage gira ɗaya. “Baki yarda kin kalleni ba yazaki gani. Idan kina son tabbatarwa zoki gani”.

     Kafinma ya rufe baki ɓurum ta faɗa toilet da sauri. Murmushin fuskarsa ne ya sake faɗaɗa. Ya miƙe domin shiryawa yana godema ALLAH da wannan farin ciki daya bashi a lokacin da bai zata ba. Harya kammala shirinsa tsaf cikin ƙananun kayan nasa na fama Hibbah bata fito ba. Yasan inhar tanajin motsinsa a ɗakin kota gama bazata fito ba. Dan haka ya tattara wayoyinsa da lap-top yayo falo.

          Tun a ƙofar fitowa yaja ya tsaya saboda cin karo da baƙon dake zaune a falon ƙafa ɗaya kan ɗaya yana kallo. Abdull da ya ɗan ɗago ya kallesa ya ɗauke kansa yana wani shaƙiyin murmushi. Hararsa Master yayi da cigaba da takowa cikin falon. Ya zube kayan hannunsa saman centre table ɗin da fisge remote ɗin hanun Abdull ɗin ya rage ƙarar tvn. 

      “Banza ɗan nanaye ko ina ake sai an nuna hali”.

      Murmushi Abdull ɗin ya sake saki har da ƴar dariya. “Ni da kai a tantance ɗan nanaye ai ayanzun. Mutumina kafa samu lafiya da alama. Na wani tada hankalina a banza harda baro canada babu shiri”.

        “To ubanwa yace kazo mai kan gwanda kawai.”

      “Zakako cika baki yanzun tunda harbi yayi sauƙi, tsabar zalama ma ga ciwo sai da ka tafi kwaɗayi filin ball”.

            Murmushi master yayi dan Abdull ba ƙaramin tasa rayuwarsa yake gaba ba. Shima mutum ne mara son hayaniya da yawan magana, dan harma yafisa miskilanci. Amma inhar suna tare to bakin Abdull cau-cau akansa. 

        “Wai yaushe ka shigo haka dan ALLAH?”.

      “Tun randa aka harbeka. Daddy (I.G) ya sanarmin naji bazan iya kwana a canada banzo naga rabin jiki ba.”

        Dariya Master yay yana gyara zama. “Shine sai yau nake ganinka, kazo kuma kanamin iskanci anan. ”

            “Tun randa kasha harbi ina gidan nan, kai ne dai kai wahalar gani saboda kana daga lungu kana tsinkar fure.”

       “ALLAH ya shiryeka to”.

Master ya faɗa yana murmushi.

       “Amin ya rabbi tunda addu’a kaimin. Ina madam ɗin tazo na ganta, dan na huce zuwa yanzu tunda nasa an rama mana harbinmu”.

         “Mara kirki, ALLAH zai saka mata ai”. Master ya faɗa yana miƙewa. Dariya Abdull yayi yana binsa da kallo, “Eh lallai ka shiga hannu ɗan gimbiya. Da alama dai ƴar shilar nan taka tauraruwa ce cikin taurari”.

        Master da ke haɗo musu coffee yay murmushi kawai batare da ya bashi amsa ba. Sai da ya kammala ya dawo falon ya ajiye a centre table ya zuba musu sannan ya zauna bayan ya mikama Abdull ɗin nasa. 

      “Bestie ya yarana da madam?”.

   Abdull ya ɗan ɗage kafaɗa da faɗin, “Lafiya lau suke, sunata gaisheka.”

       “Ina amsawa, nayi kewarsu da yawa gaskiya”.

     “Karka damu suna gab da dawowa kusa da kai insha ALLAH. Ya gwagwarmaya? Daddy nata bani labarin ayyukanka da jajircewarka. ALLAH ya saka da alkairi ya ƙara girma”.

        Master dake murmushi ya kai kofin coffee ɗin bakinsa ya ɗan kurɓa. “Uncle baya gajiya da yabona, shi baya tsoron kar wataran naci amanarsa”.

    Harararsa Abdull ɗin yayi ya ɗauke kansa. Zaiyi magana Hibbah da batasan da zaman Abdull ɗin ba ta fito cikin shirin son zuwa gaida baba Saude yau. Ganin Abdull ɗin na kallon hanyar bedroom ɗinne yasa Master juyawa ya kalla wajen shima. Numfashi ya ɗan ja a hankali ganin yanda kayan sukai mata ƙyau, baiyi zatonma zasu mata ba a lokacin daya sayesu. Ganin ta ɗan daburce kamar zata juya yay mata alama da idanu tazo. Babu musu ta gyara ƙaramin gyalen data yafo saman wando da rigan parkistan ɗin ta nufosu cike da nutsuwa tamkar ba ita ba. Abdull da tuni ya ɗauke kansa da ga kallonta ya maida ga tv yace, “Amarya baƙya laifi ko kin kashe ɗan masu gida”.

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button