Uncategorized

MUSAYAR RUHI 13-14

 

*⚜️MUSAYAR RUHI⚜️*

 *Page 13 & 14*

*_Assalama alaikum inayima kowa barka da Sallah Allah ya’amshi ibadummu amin Allah kuma yamai maita mana fatan alkairi gakowa_*

*R* ai ‘bace Hammat yafito cikin ‘bacin rai yace ” tobasenadawoba sannan har za’a matsamin akan nayi aure alokacin daban shiryaba ina nikam inama tunanin anya anma haifi yarinyar dazan aura ? “

garasawa yayi part d’in Ammi dan sanar da ita Hajiya hajara  cikin sauri tashiga part d’in Hajiya mariya tana shiga tadubeta ganin Haisam a zaune yasa tace ” Hajiya mariya inaso muyi magana ” jin haka yasa Hajiya mariya saurin tashi suka nufi cikin bedroom binsu da kollo Haisam yayi cikin zuciyar shi yace ” Allah yasa kugane abinda kukeyi badede bane  ” daga haka yamiqe yabar part d’in suna shiga Hajiya hajara tace 

” Hmmmm Hajiya mariya yau naji abinda kunnuwana suketasonji wato Maimartaba yau yayima Hammat maganar aure zaiyi tafiya ayanzu yana dawowa yace dole yayi aure kinga kenan lokaci yayi da Kumsat itama zatayi aure dan kam senayi duk yadda zanyi wajan ganin Hammat ya auri Kumsar yazama dole nayi shirin komi kafin dawowar shi ”  murmushi Hajiya mariya tayi had’i tafa hannu tace ” yazama dole kiyi shiri ko yazama dole nayi shiri ay atunanina Hammat da Amina yadace sbaida idan kika lura ay ……” 

” Dakata Hajiya mariya bangane abinda kikeson kiyiba tayaya kinsan tuni nikeda wannan burin shine kema zakizomin dawata banzar magana idan kema so kikeyi Amina ta auri jinin saurauta to ay ga Ansar nan gakuma Fadil baseki za’bi d’aya daga cikinsu ba ? Murmushi Hajiya mariya tasakeyi tace 

” Ina idan kinaganin sunfi Hammat riba toke maiye zai hana kiyi hakan kumama idan banda abinki ay Amina duk tagirmesu tayaya kike ganin hakan zai yiwu karki manta kowafa yanadanashi burin ni aganina baikamata wani yaji kanmuba kowa ya’iya allonshi ay seyawanke karki manta koda nice nasamu bazan manta da abokiyar makircinaba hakama kema ina zaton haka to kar wannan yasa wasu suji kanmu ”

Wani shi’umin murmushi Hajiya hajara tayi tace ” hakane iya ruwa fidda Kai amma nasan tabbas nikeda nasara dukda cewa babbar matsala ta shine Mama sabida tananan akan wannan al’adartasu wadda basa auran wani bare se jinin saurauta muma dayaya tabari aka auromu ” murmushi Hajiya mariya tasaki irin namugunta tace ” hmmm ay kinga wannan tsohuwar yakamata museta mata hanyafa idan mukabarta tofa Allah babu abinda zamusamu cikin masarautar nan ” wata ‘yar qaramar shewa Hajiya hajara tayi tace” barta ankusa zuwa dede lokacin dazamu qaramata gudu zuwa lahira ” haka sukacigaba da tattauna mugun nufinsu 

misalin 9:pm Hajiya Fulani tashiga part d’in Sarki Jabir cikin tsananin damuwa a kishin gid’e tasameshi gaidashi tayi cikin girmamawa kamar kullum ko kallonta baiyiba balle ya amsa cikin damuwa sosai tace ” ranka shidad’e dama maganar makarantar su Fadil ne naji cewa su Ansar zasutafi nanda sati 1 amma naji bakayimin maganar su Fadil ba kaga shi yad’an jima yanajira to senayi zaton had’asu kakesonyi dasu Ansar shiyasa banyi magana ba ” wani irin mugun tsaki yaja yace ” tashi kibani guri jin muryarki ta’isheni haka idan kuma kikacigaba dazama zakisha mamaki  …….. ” kamar Yaya fa Maimartaba ? ” Cewar Hajiya Kilishi dake tsaye bakin qofar part d’in tun bayan shigowar Hajiya Fulani qarasawa ciki tayi tazauna tadubeshi sosai tace

” Gaskiya Maimartaba hakan baikamataba nikam abinda kakeyima Fulani yafarabani tsoroma kenan har yaran nakama abin yake neman shafa ina gaskiya ni bazan iya jurar hakanba idan har baza’ahad’a su Fadil dasu Ansar tafiya Skul ba tofa suma su Ansar d’in sede suhaqura sutazama har zuwa lokacin daka canza tsari dan kam bazan iya jurar zargin jama’a ba sabida wallahi nasan nice abin zagi tunda nice mai yara barima nace nasanar dasu sudakatar da duk wani shiri bayanzuba ” tana gama fad’ar haka tamiqe zatabar parlour dakatar da’ita yayi dafad’in 

” Dakata Hajiya Kilishi to meye kuma nayin fushi bayan bakiji nace hakaba  nifa tare nanemar musu Skul amma senaga kamar mahaifiyar tasu batabuqatar hakan shine dalilin dayasa nike ganin kamar batashiryabane ” girgiza Kai Ammi tayi tace ” haba Maimartaba itakam maiye nata idan kace ayi akwai wanda zaice a a ? dan Allah kayi adalci atsakaninmu dakuma tsakanin yara dan gujema fad’awa cikin fushin Allah da azabar shi dan Allah kar kasa nima nadinga zargin kaina wajan hanaka yin adalci sabida nice babba duk cikinsu kuma munada kyakkyawar fahimta ni da Kai dan Allah Maimartaba kaji tsoran Allah ” 

Ajiyar zuciya yasauke yadubi Fulani wanda raban daya d’aga ido yakalleta har tamanta yace ” kiyimusu duk wasu shiryeshiye tare zasutafi Ansar da Fadil Hanan da Fadila idan akwai wani abu kituromin Fadil ko Fadila susanar dani ke basekinzoba ” murmushi Hajiya Fulani tayi tace ” in sha Allah zanyi yadda kace nagode Allah yaqara girma ina godiya agareki Aunty Kilishi Allah yaqaramiki tsoran Allah ” daga haka tamiqe tafita jiki a sanyaye binta dakallo hajiya Kilishi tayi cikin tausayawa shiko Sarki Jabir fuskar Hajiya Kilishi yake kallo dawoda dubanta tayi gareshi kafin tayi magana yace 

” Basekince komiba Kilishi banada amsar baki banace ga lefin Fulani agareniba zuciyatace kawai ta tsaneta lokaci d’aya babu dalili nasha bambayar kaina meye dalili amma har yanzu nakasa ganoshi badan babu saki a gidan sarautaba idan babu wani dalili mai qarfiba datuni nasaki Fulani kodan itama tahuta to amma babu dalilin yin haka ” nannauyar ajiyar zuciya Ammi tasauke tace ” gaskiya yakamata kadage da addu’a dukda nasan kanayi to amma kaqara Allah yashiga tsakanin nagari da mugu ” shima ajiyar zuciyar yasauke yace amin dubanta yayi sosai yace ” wato Hajiya Kilishi akullum jinki nikeyi sabuwa fil cikin wannan zuciyar tawa ” yata’ba setin zuciyar shi kuma har qarshen numfashi  ahaka zaki dauwama ” murmushi tayi tace nagode sosai amma inaso acikin kasona na soyayyata dake cikin wannan kyakkyawar zuciyar taka karabashi 2 kabama Hajiya Fulani rabi zanyi matuqar farinciki idan kayi hakan ” rumtse idonshi yayi yace ” bazan iya hakanba kiyi haquri amma daga yau zuciyata zata dinga tunasar dani cewa Hajiya Fulani tanada alfarma awajan abar qaunata har abada yanzu tashi muje ciki wannan kamshin turaran naki yajawo miki magana ina matuqar son wannan turaran naki ” 

Murmushi Ammi tayi tace ” ayya shiyasa yamantar dakai cewa yau ba Hajiya Kilishi keda haqqin sauke maka buqatar takaba ? Hajiya Fulani ce kabata duk kulawar da wannan zuciyar taka tayi shirin bani dan Allah ” tana kaiwa nan tayi saurin miqewa tafita tana shiga part d’in ta babu jimawa tafito tanufi part d’in Hajiya Fulani tana shiga tasamesu zauna saman Cushion d’aya itada yaranta suna kallon Sunna TV sallamarta yasa suka maido hankalin su wajanta  cikin sauri Fadil da Fadila suka miqe suka isa gareta rungumeta sukayi suna gaidata cikin farinciki shafa kansu tayi suduka had’ida saka musu albarka sannan taqarasa ciki nufar bedroom kowa yayi sukabar iyayen nasu cikin farinciki Hajiya Fulani tashiga yimata barka dashigowa bayan sun gaisa Ammi tadubeta sosai tace 

” Hajiya Fulani ayau zanyimiki magana akan abinda yake faruwa tsakanin ke da Maimartaba gaskiya lamarin yanacin zuciyata batun yanzuba amma kasancewar lamarine na tsakanin miji da mata kuma ni ina matsayin kishiya baikamata nashigaba sabida nima dole ina cikin abun zargi sabida zaman kishi lamarin yanada wuya idan ke baki zargeniba to babu shakka wasu senun zargeni sede ni nasan har ga Allah kowannen ku zuciya 1 nike zaune dashi tsayin 18 yrs kuna zaman rashin jituwa a tsakaninku amma nayi tunanin ko wani lefi kikayi mishi to amma yau nayimishi magana akan haka abin mamaki shima bashida wani dalili hakanne yasa nazo nabaki shawara koda yau 1 ki’aje matsayin kishiya agareni kid’auka Aunty kice zatabaki shawara yakamata kisake dagewa da addu’a aduk lokacin dakikayi sujjata kidinga karanta wannan addu’ar barinayimiki misali da kaina dan nima karki cireni cikin zargi halin kishi ne 

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button